Showing 51001 words to 54000 words out of 197960 words

Chapter 18 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15028

shirme a kitchen nabarsu su kadai, bari naje saika dawo"
katse wayan tayi da sauri ta jefar da wayan man gado ta kife kanta zuciyata na wani
irin kuna kaman an watsa garwashi, tadade ranta bai baci hakaba, mikewa tayi tsaye
tace "aiko I promise you yau zaku iso gidan nan ku tatrar da bakin cikin da baku
taba tunani ba, wlh sainasa murnan ka takoma ciki" tai maganan tana bude kofa
tafita, sake bude kofar dakin Rahima tayi ganin har lokacin bacci take yasa ta
kalli agogon bangon dakin biyar saura ahankali tace "by 6" tawuce tai falo tsabagen
bakin ciki kasa shiga kitchen din tayi tawani kwanta akan dogon kujera tana kallon
agogon bango tana jiran 6 yayi.

Wuraren 5:50 Rahima tabude idanunta ahankali dasuka sanyi ja sabida baccin datashi,
tashi ahankali tayi ta zauna tana yatsine fuska kaman zatai kuka tace "uhmm" daidai
Mummy tazo wajen zata bude kofan ta shiga jin muryan ta yasa tai wani irin murmushi
tareda taune lips tajuya ahankali sadaf sadaf takoma falo ta zauna.

Hannu tasa ahankali ta zare hijabin jikinta tanaji ko ina na jikinta namata ciwo,
tashi tayi ahankali daka kan dadduman tadauke dadduman da hijabin nata ta wurgasu
kan madubi tawuce ta shiga bayi fitsari tayi tai tsarki ta wanke hannunta sanan
tasa toothpaste a toothbrush dinta ta shiga wanke bakinta dan ta tsani ta tashi
daga bacci taji bakinta namata wani iri, wanke bakin tayi tsaf sanan ta debi ruwa
ta wanke fuskanta taja towel ta share ruwan fuskan nata sanan tabude kofa ahankali
tafito feeling headache kanta yawani saramata, hannu ta daura kan goshin nata
tareda lumshe ido tana tsaye daga bakin bayin saida kan yadan lafa sanan tabude
idanunta ahankali ta daga kafafun ta zata fara tafiya idanunta suka sauka akan
kwalaban codeine guda uku dake kan side drawer gadonta an ajiyesu gasunan acike tap
bawai empty bottles ba, ga karan weed guda uku gakuma light, wani irin racing heart
dinta yayi she can't believe wat she is seeing, tsabagen mamaki da rudewa kulle
idanunta tayi sanan tabude da sauri tasake kallon saman side drawer taga still dai
suna wurin dawani irin sauri takarasa wajen wani irin zama tayi dirzhan akasa tana
kallonsu kaman mai daukan karatu agaban Malam tana bude baki har wani yawu take
hadiyewa kaman wacce aka gabatar mata da farfesun kan sa, hannunta har rawa yake
tamika tadau kwalba daya na codeine din tarike a hannu jikinta har bari yaje bar
bar kaman irin yaron daya ga abinci for the first time after like a whole year of
starvation, kanta gabaki daya ya kwance kaman wacce akama baki ko kadan bata tunani
all abinda zuciyanta idanuwanta gangan jikinta da ruhinta ke gani dakuma tunani
shine wayannan kayan mayen, dawani irin sauri ta shiga bude codeine din wani irin
cillar da marfin tayi ta daga sai bakinta tana sha tana nishi tana lumshe ido kaman
yaron karami da akabama bobon dayagama kuka abashi, saida ta shanye shi tass sanan
tawani irin cillar da bottle din tadau na biyun da gudu tana sauke ajiyan zuciya
tabude ta yarda marfin takafa abaki saida ta kwalkwale tass sanan ta wurgar da
bottle din vamatare da tasan inda take wurgawaba tadau 3rd bottle takafa abaki,
harwani lumshe ido take tana sauke ajiyan zuciya gwanin ban tausayi tsabagen yanda
tai kewansu fess ta shanye na ukun sanan ta cillar tawani irin yin doguwar gyatsa
tana murmushi tai maza ta kwaso duka karan wiwikan tana kallonsu, kallon dakin nata
tayi ganin babu komi na sha yasa tasake kallon side drawer, ganin lighter akai yasa
tai shiru to kodai ta gwada smoking nashi ne ai taga Chris yay smoking nashi ranan
yana shan codeine yana zukanshi wai mugun dadi kakeji, da sauri tamika hannu tadau
lighter ya kyasta na wiwi wuta yakama ta yarda lighter takai wiwi baki ta zuko
ahankali sanan ta fuzar tana lumshe ido tawani mike kafafu akasa tanajin dadin da
bata tabajin irinshi ba.



Fitowa su Siddiqa sukayi daga kitchen rike da kulolin abincin dasuka dafa suka
shiga jerawa kan dining, wani irin strange wari Siddiqa taji daya gauraye da
kamshin abincin daya cika falon hakan yasa Siddiqa ta kalli Zeenatu dake kara rufe
kulan abincin da kyau tace "Zeena bakiji wari ba?" da sauri Zeena ta dago daga
abinda take tace "wari Ya Siddiqa? A'a ni banji wani wariba" da sauri Luba tawani
yatsine hanci tana huroshi tace "huuuu nima naji warin wlh, kaman warin taba" Mummy
dake kan kujera tana kallo tai kaman bataji suba tace "me haka? Astagafurullah
lafiyan ki kuwa Luba kike kira mana sunan taba agida? Baku kukagama girki ba yanzu?
Halama kun kona tukunya ne, ko wani abun barinma ke Luban nan mai shegen cinne
cinne awuta, Common kuzo nan kusa mana zee World mu kalla Mahek" da sauri suka taho
falon suka zazzauna dudda warin sai cigaba yake da damunsu amma Mummy tahansu
magana sai labarin Mahek din take basu.


Yarda kara dayan wiwi data gamasha tayi, dukta bata carpet din dakin nata da tokan
wiwi, lighter tadauka ta kunna na biyu ta shiga sha idanunta na mugun juyawa,
jikinta nawani irin saki, tanajin ta a sama, sama kaman tana tafiya akan ruwa
kifaye na lasan diddigen ta, silin din dakin take kallo tana zukan wiwi sai taga
Maman ta sojoji sun sata kneel down, jikinta sai rawa yake wai tana tsoron bindiga
tafashe da kuka, kyalkyacewa da dariya tayi tana zukan wiwi cikin wani slow murya
tace "sooooja ci ubanta muuuguuuwaaa ceeeeee, batada imani kusada tsinto duwatsun
kwata" takara kyalkyacewa da dariya ta mugun buguwa to the extend da bamata duniyan
nan she is high....


Horn da Mummy taji na motar Abba yasa tawani irin tashi zaune da sauri tana yatsine
hanci takalli su Siddiqa tace "Siddiqa are you sure kun kashe su gas da komi nima
inatajin warin nan wlh yasoma hawa kaina" da sauri Luba da sauran suka tashi
Zeenatu tace "Mummy wlh mun kashe komi nima warin ya isheni kaman taba" da sauri
Siddiqa tace "kaman warin anan kona itacen magani" da sauri tai Mummy tace "kumuje
kitchen nakara dai dubawa nagani" kitchen Mummy tayi yaran biyeda ita.
Shigowa gidan Abba yayi dawata sabuwar mota dall fara kujerun ko leda ba'a bareba,
saiga motar Sameer shima ya shigo gidan dan tareda Abba suke, parking yayi yabude
yafito yana sanye dawani farin bugaggiyar shadda data mugun yimai kyau kanshi babu
hula, he looks very matured well compose a kayan kaman ka saceshi, karasowa inda
yake Abba yayi yana murmushi yace "mu shiga ciki Son kagama an kusa kiran sallan
magrib, kwanan nan dare na saurin yi, kaman ana period of shorter day longer night"
gyadamai kai Sameer yayi yace "hakane Abba" daidai sun karaso hannu Abba yasa
yabude kofar dakin taredayin babban sallaman nan nashi ya shiga ciki Sameer biyeda
shi daidai su Mummy dasu Siddiqa sun fito daga kitchen, chak Abba ya tsaya tsaye a
tsakiyan dakin sabida warin dayama hancinshi sallama Sameer ma haka, kafin Abba yay
magana Mummy cikeda damuwa tace "sannu da zuwa Alhaji" , ta kalli Sameer daya tsaya
chak tace "welcome Lieutenant" kafin da sauri ta kalli Abba cikin damuwa tace
"Alhaji kataba ganin abu haka wai bakuji wariba kaman na taba taba kaman na kona
saiwan magani, su Siddiqa sun gama girki yanzun nan nadauka sun kona abune but na
shiga kitchen naduba ko'ina komi is fine narasa daga ina warin nan yake zuwa kuma
sai tadamin da zuciya yake wlh" kafinma Abba yay magana Sameer ya kalli Siddiqa
strictly babu alamun ko wasa daya akan fuskan shi yace "where is your sister?
Rahima" ahankali Siddiqa tace "tana dakinta bacci take, har yanzu bata tashiba tun
bayan mun gama basketball" da husky voice dinshi yace "take me to the room" da
sauri Siddiqa tai hanyar corridor ko kadan bai damuba kai tsaye yabita Corridor sai
a lokacin Abba ya iya daga kafa yabi bayanshi, Mummy ta kalli su Luba tace "menene
duk aka tafi dakin autana? Kumuje" bin bayan Abba tayi su Luba biyeda ita, har
gaban dakin Rahima Siddiqa taje sanan ta kalli Sameer tace "nanne dakinta" yanda
mugun warin wiwi yacika corridor yasa Sameer yakarasa gaban dakin Abba da jikinshi
yay wani irin sanyi tareda shi hannu yasa yabude kofan ahankali, baya Abba yayi
zai fadi da sauri kowa yay ihu. "Abba!" rikeshi gam Sameer yayi yace "Abba calm
down, don't panic" yay maganan yana shigo dashi cikin dakin ya jinginar dashi jikin
kofa sanan ya kalli Rahima, har lokacin sillin din dakin take kallon ga karan wiwi
na uku a hannunta ga kwalaben codeine data wawwatsar dasu kasan dakin tana wani
irin buso hayaki ta hanci da bakinta sunayin saman dakin.


_this is the last free page, nabaku 30 pages free, BIN ABINDA ZUCIYA KESO novel ne
one of it kind, gabaki daya daban yake da sauran littafai nai, is a blockbuster, I
pour knowledge in this novel say I brag naji na yarda🤣_

_in kinaso kicigaba da karantawa zaki turo 300 ta account number na 3107021073
aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to my watsapp number
07012181461, sainai adding naki a group din danake posting BIN ABINDA ZUCIYA KESO
zakuma ku iya turo kati MTN na dari uku marasa banki_

_ko Allah yasan irin effort and research dana saka a book dinan, some of my fans
kun sani dan nayi tambayoyi kan shaye shaye kuka Bani amsoshin abubuwan da kuka
sani, dan haka ba danniba bakuma dan halina ba, dan Allah ubangijina ni da ku
kubiya just 300 kuyi subscribe ku karanta hankali kwance, ku ilmantu ku nishadan
tu, dan duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafemata ba Allah zai sakamin_

_CHASING THE HEART CRAVINGS novel ne daya kunshi Soyayya, tuzuranci, Tausayi,
drugs, addiction, rehabilitation, sugar Mummy, and many more, just pay and enjoy
this book, I love you all_

_Awoof Bonus! Bonus! Bonus!_
_inhar kinzo zaki biyama mutane biyar zan barmiki akan dari bibbiyu instead of dari
uku uku_
_in zaki biyama mutane goma, mutum takwas zaki biyamawa 2 nasamiki su free_
_mesa zakiyi satan novel? Just come pay for your friends and family akwai huge
massive discount dazan miki inhar zaki biya wa mutum dayawa, this Awoof last for a
whole week, daga next week Wednesday yay expire yay💃🏼💃🏼_31.

Arude Mummy da isowarta dakin kenan tadafe kirji ganin Rahima tace "innalillahi wa
innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, Abban su! Sameer! menene
wanan a hannun Auta na? Kwalaben meya wayan nan akasa? Wiwi, taba, Rahima, Auta na"
tai cikin dakin da gudu tai kan Rahima fizge karan wiwin tayi tayar akasa cikin ihu
kaman wacce tasoma zarewa tace "Auta kina haukane tarbiyan da muka baki kenan?
Wanan wani irin abin kunya ne kikeyi agidan mahaifinki eh? Agidan mahaifinki kike
shaye shaye?" ko kadan Rahima batasan me Mummy ke cewaba idanunta kan wiwi ta da
Mummy tayar akasa yanaci harya soma kona carpet din wurin, da sauri tai rarrafe tai
wajen wiwi kaman wata tsohuwar mayya zatasa hannu tadau karan wiwi jikinta har rawa
yake wani irin zuciya ta kwashi Abba yaji karfi yazomai ya tashi daga jikin kofan
dayake, cikin wani irin kunan rai daidai tadau karan wiwi zatakai baki yasa kafa
yay wani irin kwallo da ita saida bayanta ya bugu da wardrobe din dakin wiwin
yafadi akasa ta buga bayanta awurin, kaman wacce bataji zafiba, bude idanunta tayi
ahankali dasukai jajir, kaman wata wawiya tasa hannunta akasa tadafa ta tashi tsaye
da kyar tana kalle kallen kasan dakin tana neman wiwin ta tana layi, so kawai take
ta cigaba da sha tana ganin sojoji nabama maman ta wahala, ganin bamata san ya
daketa ba haukanta take tana neman wiwi yasa Abba yawani fizgota ya jijjigata
tareda dauketa da Mari ya kwala ihun kaman zai fasa gidan yakirata da kakkausan
murya. "Rahimaaa!" dafe kuncinta tayi dan wanan karan marin ya shigeta kafin tasa
hannayenta ta shiga dirza idanunta kaman wacce idanunta kemata kaikayi sanan ta
cire hannun tabude idanunta da kyar tana zaro idanun dan bata ganida kyau kafin
idanun su washe ta kalli Abba ido cikin ido, turo baki tayi cikin maye tace "wlh ka
kara dukana saina rama mugu kawai azzalumi, angayama yanzu dane, bana tsoron ta
mutu balle tai tsami, nice owlet, and I am a pj mask, bari kaga Halloween wind"
tawani daga hannu tana huroma Abba iskan bakinta adole zata dagashi sama ta yar
kaman yanda owlet keyi a cartoon din, ganin bai matsaba yana tsaye agabanta yasa
tafashe da dariya tanunamai muscles dinta duka biyun tana zaro mai idanu, cikin
fushi Abba yasake jijjigata yace "Rahima bazaki dawo hayyacin kiba, Rahima, Rahima
Allaahumma ajirni fi musibati w......." kabar da hannun Abba tayi daga kan
kafadarta tace "leave me alone this man, I hate you wlh, dama kowa baya sona dukkun
tsaneni nima na tsaneku, kullum kaita dauremin fuska ka kira su Ya Siddiqa, Ya
Lubabatu, da Ya Zeenatu kan kujera kusada kai amma bakako kallona, nima I don't
need you kaji old man, Mummy na kadai nakeso, ita kadai, only Mummy, only Mummy"
tai maganan tana washe baki duka fararen hakoranta awaje tana layi tace "I love my
Mummy, Mummy I love, zankai ki all the 7 continent damuke dashi in the world,
Europe, Asia, North America, South America, Antarctica, Australia yayyyy oya give
them Mummy zannnnku legg work" yashiga rawa tana zanku agaban Abba sanan ta tsaya
tareda rike kwankwaso takawo fuskarta kusadana Abba tana kallon kwayan idanunshi
har harshinta na gogan nashi tana busamai warin wiwi datake yi, cikin mugun
fitsarin da shaye shaye kesawa tace "kaiko mugun, bakasona bansonka, I hate you! I
hate you! I hate you" tai maganan tana turashi baya ta hanyar sa hannayenta akan
kirjinshi ta tureshi da karfi, da sauri Siddiqa tace "Rahima!" dakuwa Rahima tamata
tace "babu ruwanki dani jaririyar kunkuru tom" komawa baya Abba yayi yana kallonta
kirjinshi nawani irin bugawa dabai tabayiba yana kallonta, biyoshi tayi tazo har
inda yake tsaye kusada Sameer da yatsa tanuna shi tace "ka kara zuwa nan wlh saina
zaneka ciki dabai, mugu kwai, wicked man, wlh bansonka" wani irin fadawa jikin
bango Abba yayi kaman wanda aka tura any kalman I hate you na Rahima nasa
zuciyarshi bugawa, wani irin nishi ya shigayi da baki trying to control yanda
numfashi ke fita daga kirjinshi yana kallonta yana bude baki dan kaman nostrils
dinshi sunmai kadan wajen fitar da numfashi, ganin haka yasa Sameer da sauri yarike
shi yace "Abba Abba, listen Abba calm down kaji, batasan metake cewaba, bata
hayyacin ta, don't allow her words gets to you, muje kafita daga dakin he falo ka
huta" hannu Abba yasa kan kirjinshi yana bubbugawa yana wani irin lumshe ido kaman
wanda ke shirin mutuwa, da sauri Mummy tazo wajenshi tace "innalillahi wa
innailaihi raji'un, Alhaji" da sauri Sameer yadago kai ya kalli Zeenatu dahar
tafara kuka duk suna kallon yanda Abban nasu yakeyi yace "kawomin ruwa" wani irin
tari Abba yashiga yi yay kasa kafafunshi na lankwashewa zai fadi da sauri Sameer
yatare shi tareda zaunawa yadaura kanshi kan cinyarshi yadan dago kafan nashi sama
sabida mugun tarin dayakeyi, ruwa Zeenatu takawo da gudu tabama Sameer, karban
ruwan Sameer yayi yabude yakafa abakin Abba yazuba ruwan, tari sosai Abba ya shiga
yi ruwan na fitowa kafin ruf yarufe idanunshi kaman wanda ya mutu ko suma, ihu
Zeenatu tayi tace "Abba, Abba, Mummy Abba na menene" da sauri su Siddiqa da Luba
suka karaso suka duk tsugunna suka zagaye su suna kuka "Abba, Abba" tsawa Sameer
yadaka musu cikin fushi yace "ku fita! Out! he need air ba mutuwa yayiba, he's
under shock, just a mild heart attack, ku fita kutafi dakinku" da sauri Mummy dake
tsaye kansu jikinta na rawa tace "kufita kufita kunji me yayanku yace baban ku
needs air, Siddiqa ki dauko wayana kan gado ki kira likitan baban ku kice yazo
yanzu he is sick" da sauri suka fita suka rufo kofar Mummy ta fashe da kuka sosai
tadau pillow gadon Rahima tana kallon Rahima dake tsaye tana kirga silin din dakin
da yatsun tana layi bamatasan me akeyiba, kaima Sameer filon tayi tana kuka sosai
ta ijiye akasa tace "sakanshi anan Sameer ya kwanta" ahankali Sameer ya kwantar
dashi yana kwancemai neck tie din wuyanshi, fashewa da kuka sosai Mummy tayi ta
tashi tai kan Rahima kifa mata Mari tayi ta jijjigata tana kuka tace "sokike ki
kashe babanki? So kike ki kaishi lahira tun kafin lokacin shi yayi, Rahima waya
lalata ki haka eh?" ta kalli Sameer cikin kuka daya dago kai yana kallonsu tace
"wlh Sameer dazu ina kitchen naga tafice tsakar gida I tot maybe tafita kwaso
shanyan kayanta ne fita kikayi ko?" ta jijjiga Rahima cikin fushi tace "kananun
samari nan dakike dashi da basu gama balaga ba su suka kawo miki kwayoyin nan ko
Rahima wani kudi kika basu dan nasan bakida ko anini" Mummy tafashe da kuka kaman
mai shirin shidewa tace "to kodai ciki suka miki?" da sauri Sameer ya kalleta, ta
gefen ido Mummy taga yana kallonta hakan yasa tasan yes! She just hit the right
spot, hakan yasa ta cigaba cikin kunan rai tace "I've noticed kwanan nan bakida
aiki sai bacci, bacci, bacci, Rahima look at you, you are just 20yrs but kinmafi
babban yarku Siddiqa komi na y'a mace, kinfi yayyunki cikan nono, hips da sauransu,
zuwa kike maza na kama miki suna matse kiko, dama ranan da wata yar ajinku ta
tareni danaje dropping naki a department dinku tacemin taganki agidan wani dan
ajinku dake zama offkay kuna wasa yana kama jikinki taga ku shiga daki sai yamma
kika fito sanye dawata riga daban dana wanda kika shiga dashi, nama yarinyar fada
na karyatata na zageta dan nasan baki taba dawowa gida dawani kaya dabamu muka
saimiki ba yasa ban yardaba, Rahima NDLEA suka kamaki still shima ban yardaba
dannasan birthday party kikace min zaki na classmate dinku ashe kinyi irin bacin
nan, kin lalace, bin maza, shaye shaye dukke kadai wani irin JARABTA (M Shakur
book) dahar zaki iya kunna sigari ne ma ko wiwi agidan ubanki, gidan iyayen ki
kinashaye shaye, innalillahi wa innailaihi raji'un, me kikeso mufadi ma Allah akan
tarbiyan da muka baki, mahaifinki ya killaceki yahanaki zuwa school, yahanaki fita
ashe jira kawai kike yabar gida na sakan daya kiyi abinda ranki keso, dama baccin
karyane eh Rahima? Ban taba dukanki ba amma yau kinyi kuskure wlh saina zaneki
Auta, saina zaneki auta" Mummy tai maganan tana rufeta da duka tako ina Rahima na
tureta tana turo baki kaman ma batajin dukan, Sameer na kallonsu baice ko uppan ba
ko kyafta ido bayayi Rahiman yake kallo, daddaggewa Rahiman tayi ta tura Mummy
cikin maye Mummy tai baya da gangan tawani irin fada kan jikin Sameer dake shafama
Abba ruwa a goshi, unexpectedly yajita kanshi before you know it Mummy tafashe
dawani mahaukacin kuka sosai tana kara shiga jikin Sameer din, tunda take aduniya
tsawon shekaru hamsin da hudu zuwa hamsin da biyar kenan bata tabajin kamshin
turare mai dadi kaman irin kamshin da Sameer keyiba, chusa kanta tayi awuyanshi
kaman sabuwar vampire tana kuka tana goga fuskarta a thick neck dinshi tace "zan
mutu Sameer Rahima zata kashe iyayenta da bakin ciki, innalillahi wa innailaihi
raji'un" tureta Sameer yayi daga jikinshi da sauri cikin wani irin yanayi yatashi
tsaye da sauri yana kakkabe jikinshi hakan yasa Mummy kaman wacce hankalinta ya
gushe ta kwanta warwas akasa tana kuka harda

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login