Showing 30001 words to 33000 words out of 197960 words
until your
daughter's father is back and come here dakanshi I'm not releasing Rahima nor
giving her to you" yana maganan yay hanyar office dinshi binshi Mummy tazo zatayi
security suka tareta hakan yasa ta tsaya daga wurin, ganin bala'inta bazai yi
komiba burinta shine tasamu su saki Rahima su koma gida asirinsu arufe batare da
Abban su yasani ba amma taga ina wayan nan basuda mutunci hakan yasa ta shiga rokon
security su barta taje taga Chairman sukaki.
Shiga office din sukayi daidai wayar chairman yahau ruri karasawa table din yayi
yadau wayan ganin Mahaifin Rahima ne yasa yay picking yasa a kunne ya nemi waje ya
zauna yace "good evening to you Sir, this is Alhaji Muhammad Mustapha Abdullahi
Chairman din NDLEA, I've been calling you na sanar dakai wani muhimmin abu, mun
kama yarka awani gida nan hanyar Kaduna kano express road ita da wasu yara maza da
mata su talatin da daya da sunan birthday party tana shaye shayen miyagun kwayoyi
da gwamnati tabada umarni duk randa muka gani yanayi mu kamashi sanan mu aika dashi
rehabilitation centre, ganowa damukayi Rahima yarka ce mukuma dan matsayin ka
akasar nan munkuma san yanayin matsaloli da fitintinu dazaka fuskanta in duniya
tasan me ake ciki yasa mukace bari mu maka alfarman kiranka mu sanar dakai shima
badan komi ba saidan labari dakuma yanda ake yabata akan aiki bisa gaskiya dakake
yi ne" shiru Abba yayi na kusan minti takwas tunani yake Rahima shaye shaye, party
da maza ahanyar wajen gari, shaye shaye, innalillahi wa innailaihi raji'un,
Chairman ne jin shiru yasa yace "kana jina" ahankali cikin murya datai rauni sosai
Abba yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un,
innalillahi wa innailaihi raji'un" saida yafada sau uku yasake yin shiru yama rasa
maizaice, Murya chan kasa data nuna karara alamun bacin rai da tsantsan damuwa yace
"Chairman banda abinda zan cemaka sai Allah nasaka da alkhairi, wlh bazan maka
karyaba wutan kaina ta dauke dib I don't know wat to think, alfarma daya zakamin
kawai yanzu zan kira mahaifiyar ta tazo ta dauke ta sutafi gida, first flight zan
biyo nadawo garin nan gobe dasafe zanzo har office dinka nasameka zamuyi magana da
kyau, nakumayi alkawari binciken case dinan da kyau nagode" ahankali Chairman yace
"mahaifiyar yarinyar is already here badai mubata yarinyar bane daman munce dole
sai munyi magana dakaine, yanzu kuma tunda munyi zamu sa abata ita sutafi gida"
ajiyan zuciya Abba yasauke yama kasa magana hakan yasa Chairman ya katse kiran yana
girgiza kai yace "rayuwa kenan saikaga a good man ya haifi boka, jarabawan Allah
kanzo tako ina, please Lieutenant help me tell them sukaima matar yarinyar nan
sutafi gida" tashi Sameer yayi yafita daga dakin ganin babu kowa a upstairs din
yasa yay dining din dayake anan sama dama dining din yake yasaba zuwa NDLEA din so
ba bakonshi bane babu inda baya shiga saidai in baisoba, bude kofan dining dinyayi
tana zaune kan kujera ta kifa kanta kan table tana kuka ga takeaway din rice da
stew dinta agefe ko kallonshi batayi ba, hannayenshi yazuba a aljihun wandonshi yay
wani irin tsayuwa irin na sojojin nan yace "Ke!" da kakkausar muryan shi da sauri
ta dago kanta gabanta na faduwa sabida yanda ya kirata, dauke kai tayi daga
kallonshi ganin wanan mugun bakin sojan nanne daya mata wankan ruwa dazu. "zoki
fita ur Mum is waiting at the reception" dawani irin mugun sauri ta juyo tareda
ware jajayen kumburarrun idanunta tace "Mummy na kace?" shiru yayi bai amsata ba
sai zubamata manyan idanunshi masusa mutane shakkan shi dayayi yana kallonta,
dawani irin sauri ta tashi gabanta nafaduwa ta taho tana dingishi tabi ta gefenshi
tafita da sauri tai hanyar stairs, ahankali yajuya yafito shima ya tsaya a daidai
bakin benen har lokacin hannayenshi na cikin aljihun wandonshi yana kallon yanda
take tafiya tana dingishi da sauri tana sauka, saida tagama sauka daga benen sanan
tafashe da kuka sosai tana yarfe hannu kafin ta kwalama Mummy data juyama stairs
din baya tana waya kira. "Mummy!!!" da sauri Mummy dake waya tajuyo ganin Rahima
ga bandeji a goshi tabi tai daka daka kaman ba yarinyar data bar gida fess fess ba
yasa ta zare wayan daga kunnenta tana kallonta, dawani irin gudu Rahima ta taho
tana dingishi takarasa tawani fada jikin Mummy tareda fashewa da kuka sosai mai
tsuma zuciya, bayanta Mummy ta shiga shafawa tace "ya isa, ya isa, am here now stop
crying" dagota tayi tasa hannu tana sharemata hawaye tareda shashafa goshinta inda
taga bandeji tace "maiya sameki anan maisa kike dingishi" cikin kuka tanuna Chris
ashagwabe tace "wanchan matsiyacin ne Mummy mai kama da jaririn kunkuru shine ya
fesamin goshi" wani mugun kallo Mummy tamai batason tai magana dan tasan yariga
yasan few things gameda Rahima batason ya tona musu asiri hakan Yasa tace "barshi
yama kanshi, let's go" security ne suka tare musu kofa bazasu barsu su wuce ba,
Sameer dake gaban stairs a sama yana kallon komine cikin husky voice dinshi yace
"let them pass" da sauri Mummy ta dagokai tareda juyowa hada ido sukayi da Sameer
wani wawan faduwa gabanta yayi, chak ta tsaya tana kallonshi harsaida Rahima ta
kalleta cikin muryan kuka tace "Mummy mutafi" ajiyan zuciya ta sauke takalleta tace
"okay Auta muje" fita sukayi daga wurin security zasu maida kofan su rufe takara
juyowa ta kalli Sameer daya fara tafiyan shi nan dai dai yay office din Chairman.
[6/3, 9:42 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
1️⃣9️⃣
9️⃣
1️⃣ 1️⃣9️⃣
Mota suka shiga Mummy taja motar suka tafi, saida suka shiga titi Mummy tace "what
kind of matsala kika sani Rahima yanzu? Yanzu wani irin karya zan shiryama baban ki
dazai yarda eh? Mezan cemai, kai! Innalillahi wa innailaihi raji'un, wanan Chris
anyi dibabben yaro mai bakin jini da badluck mtsww" taja tsaki tana gudu ahanya,
Rahima ba tace mata komiba gabanta faduwa kawai yake babu abinda take tsoro aduniya
yanzu haka kaman haduwanta da Abban ta ahaka suka kai gida, su Siddiqa duk suna
daki, dakin Mummy suka tafi direct wanka Mummy tasa tayi tabata abinci, kasaci tayi
tace "Mummy bazan iya ciba, in Abba yadawo gobe kasheni zaiyi ko Mummy?" zama Mummy
gefenta kanta takama ta daura akan kirjinta ta rungume ta tace "Hey am ur Mum ko,
so kibar komi a hannuna, now eat ko kadan ne saiki sha paracetamol dinan karkiyi
zazzabi kije ki kwanta kinji" gyadama Mummy kai tayi tasa chokali cikin abincin
zata kai baki ta yatsine fuska tadago kanta ta kalli mummy, murmushi Mummy tayi
tace "ina zuwa" tashi tayi tai wurin safe ta bude kara daya na wiwi ta dauko tazo
ta juyemata a abincin juyawa tayi ta shiga ci da sauri dan yunwa takeji rabon ta da
abinci tun rana, tana gamaci Mummy tabata paracetamol tasha ta kwanta ba'a wani dau
lokacin ba bacci yay awon gaba da ita, tsayawa Mummy tayi tana kallonta barinma
goshinta dake sanye da bandeji har lokacin da kafadarta dayadan kumbura sabida
kulkin da matarnan tabuga mata sai wrist din kafarta, wani irin murmushi tayi ta
tashi daga inda take tadau kulan tajuya tafita daga dakin.
Sai wuraren 10 yakoma gida sabida tsareshi Chairman yayi sai hira yakemai, shidai
chairman arayuwanshi starting from rana na farko daya fara ganin Sameer yake
bala'in sonshi, gabaki daya yama maida Sameer din wani abokinshi dudda ya girmeshi
amma yana son yaron, jan Sameer din yayi har zuwa gidan shi sukai dinner mai rai da
lafiya sanan wuraren 10 Sameer yamai sallama yarakoshi waje saida ya shiga motarshi
yafita daga gidan sanan yakoma cikin gida yana murmushi.
Wuraren 10:30 ya isa gidansu Gate aka budemai yay Parking yafito, flat dinshi
yawuce direct dan yasan Ummi tariga ta kwanta, sabida hawan jini dakuma matsalan
kafanta yasa Dr yace tadinga kwanciya da wuri, yasan ta kwanta saisa bayason yaje
yatadata, part dinshi yawuce ya shiga ya maida kofan ya rufe bathroom ya shiga yayi
wanka yafito daure da dan towel a waist sanan yadawo falo agogo ya kalla so yake
yakira Mu'az he has been busy da tubda yadawo daga zaria baisamu ya kirashi ba,
sanin yay bacci yanzu yaja ya kunna laptop dinshi ya shiga yin some work da
yakamata ace yayi, almost 1hr yabata sanan ya kashe ya ijiye agefe yay addu'an
bacci ya kwanta.
Aka'ida dama ana kiran sallan asuba yake tashi, tashi yayi yashiga bayi brush yayi
yay wanka tareda dauro alwala yafito jallabiya yasaka ya feshe kanshi da turare
yafito, mai gadinsu yatada sanan yawuce masallaci.
Wuraren 6 na safe ya shigo gidan flat dinshi yawuce ya shirya cikin wasu sport
wears, bubu short ne daya tsayamai iya gwuiwa sai wani riga mai kama da singlet da
wani karamin towel a wuya na goge zufa ya saka sport sneakers dinshi na Nike yafita
gudu haka daily routine dinshi yake kullum ka'idane saiya motsa jiki da safe na
1hr, da yamma inya dawo daga aiki dawuri saiya shiga gym dinshi yay work out har
zuwa gab da magrib sanan yay wanka yatafi masallaci.
Around 8 na safe ya shigo gidan, shashin shi yawuce yay wanka ya shirya cikin
uniform tsaf sai uban kamshi yake yafito yay flat din Ummi, tana zaune kan dogon
kujera sanye da dogon riga tana lazimi, tana ganinshi ta zuba mai harara hakan yasa
yay dan murmushi yakarasa inda take, kusada ita yazauna yace "good morning Ummi"
addu'a ta shafa sanan ta kalleshi tace "Sameer dama ido kanga ido" kaman zaiyi kuka
yace "Ummi am sorry nowww please kidena magana haka" dan tabe baki Ummi tayi tace
"toya kakeso Sameer kanunamin kafi karfina" da sauri yace "Ummi dan Allah kiyakuri
please forgive me, I've been busy jiyan nan koda nadawo was late saisa ba shigo ba
banso natade ke, am sorry kinji Mamana" yanda yay magana cikin kwantar da murya
danko kadan baiso yaga Ummi na fushi dashi yasa tace "to shikenan yawuce, tashi
muje kaci abinci".
Tashi yayi sukai dining, kunun gyada Ummi ta zubamai da kosai da aka soya sanan
tawuce dakinta, faracin abincin yayi dan he loves all this natural local food, he
is not a fan of all this abincin yan gayun, bai wani jima da faraci ba Ummi tafito
dawani 5liter jarka dayake cike da ruwan rubutu akan dinning table ta ijiye tadau
cup ta bude ta tittila ruwan ta cika ta ijiye a gefe sanan ta rufe jarkan tace
"maganin da Baffan ka yakawoma ne, ruwan rubutu ne akama na ayoyin Allah koma
menene ajikinka dake hanaka aure zai kone ne da izinin Allah, ungo karba ka shanye"
tamikamai cup din, dan murmushi yayi dan baiso yasami matsala this early morning
hakan yasan ahankali yamika hannunshi ya karba yay bismillah yakai bakinshi ya
shanye yabata cikeda murna tace "yauwa ko kaifa, Allah yamaka albarka soja na,
Allah kuma yahadaka da matarka kwanan nan" baice mata komiba yacigaba dacin abinci
dan bai wasa da cikinshi yanada ci sosai dama ance dogo nada dogon ciki, sanan duk
soja nada ci , saida yagama ci tass sanan yatashi tareda goge bakinshi da tissue
yace "thank you Ummi na koshi, natafi" kanshi ta shafa tace "adawo lpy, Allah
yabada sa'a Allah ya tsaremun ku duka" ahankali yace "Ameen" sanan yawuce yafita
saida ya tsaya yabiya mai gadinsu salary shi dan on 25th of every month yake
biyansu sai murna Gate man yake yanamai godiya sanan yawuce ya shiga mota yatada
yatafi office.
Karfe sha biyu da minti ashirin jirgin su Abba ya sauka a Airport din Abuja, yariga
yafada driver yakawo mai mota, key motar kawai ya karba yabama direba kudi yahau
taxi yakoma gida shikuma ya shiga mota yatafi kallo daya zakamai kagane yanada
damuwa sosai, a parking space din headquarter NDLEA yay parking yafito, ya shiga
ciki Chairman yariga ya sanar dasu zuwanshi hakan yasa cikin girmamawa sukamai iso
har office din Chairman shiga ciki yayi cikeda girmamawa Chairman yatashi kan
kujeran shi tareda bashi hannu yace "barka da zuwa Alhaji" karban hannunshi Abba
yayi cikeda murmushi yace "barkan mu dai ya aiki yakuma fama da jama'a"
"Alhamdulillah please sit" Chairman yanunamai kujera hakan yasa ya zauna ahankali
tareda sauke ajiyan zuciya yace "bakomi yakawo ni nanba nazo namaka godiyan
karamcin dakamin ne nagode Allah ya rufa naka kaima haka" girgixa kai Chairman yace
"wlh is all thanks to Lieutenant Sameer, konima jiya kaina ya kwance he was the one
that advised me akan yanke wanan decision din, Nigeria is just lucky to have that
guy" "are you talking about Lieutenant Sameer Simran Sameer dana karanta a news an
karamai girma?" da sauri chairman yace "shine, shine ma yagano yaran anan Abuja
express road yana dawowa daga zaria shine ya gansu suna shaye shaye awani gida
cikin daji suna raye raye yasanar damu, all the children are student babu wani
tsayayye mai aikin yi Allah dai yakawo mana karshen shaye shayen nan na yara
matasa" shiru Abba yayi kafin ahankali yace "Alhaji Rahima, Rahima na that is just
20 itace aka kama tana shaye shaye?" dan murmushi Chairman yayi ya gyara zama yace
"I know yanda kakeji yanzu haka I understand you, Rahima da aka ganta ita tama gama
buguwa saida aka kwara mata ruwa sanan ta farka, yaron ma da ya gayyace ta wurin
sunanshi Chris birthday dinshi ne anyway is a long story basai kasan komi ba kawai
ka kula da yarka Alhaji karabata da abokanen banza dansu ke batama yaranmu tarbiya
ayau kadage kanama yaro tarbiya agida wani nachan awaje yana batasu, kawai ka tsaya
tsayin daka akanta, karabata da yaron dan yace waishi saurayinta ne soyayya suke
dan makarantan sune ajinsu daya, karabata dashi dan Allah dan he will only cause
more harm to her life, Allah ya shirya mana iyalinmu gabaki daya" ahankali Abba da
jikinshi yay wani irin mugun sanyi yace "Ameen" duk shiru sukayi Chairman na kallon
Abba ba karamin tausayi yabashi ba sai zufa yake kana ganinshi kasan yadamu toyama
za'ayi bazai damuba yarshi na shaye shaye ga yawo da abokan banza, ahankali Dady
yasauke ajiyan zuciya yamikama Chairman hannu yace "I will not forget this, nagode
nagode, yau dinan zanje har Barrack na nemo Lieutenant namai godiya duk wanda keson
cigaban ka sanan duk wanda yarufa naka asiri a lokacin da u can't do anything mutum
ne daba zaka taba manta wa dashi arayuwaba, dan Allah karkace a'a am inviting you
for a dinner a gidana gobe dakai da Sameer shima yanzu innaje mai godiya zan
gayamai hakan" washe baki Chairman yayi a whole Chief justice na Abuja High Court
is inviting over to his house for dinner this call for celebrating, cikeda murna
yace "that will be an honour sir, nagode zaka ganmu da izinin Allah, Allah kuma
yanuna mana goben, this mark the beginning of amazing friendship anzama daya da
izinin Allah, and karka damu komi will be fine kadage da mata addu'a kaida
mahaifiyar ta she will change" ahankali Abba yace "Allah ubangiji yasa" atare suka
fito har wajen motarshi chairman yarakashi sanan sukai sallama yatada mota yawuce
Barrack.
ID card dinshi kawai yanuna cikeda girmamawa sojoji suka barshi ya shiga Barrack
din tareda hadashi da wanda zai kaishi har office din Sameer, parking yayi bayan
sun iso suka fito suka shiga, lift sukahau, sanan suka sauka a 4th floor sukai
office din Sameer, knocking sojan yayi daga taciki akace come in, bude kofan soja
yayi ya shiga Abba biyedashi Sameer ne zaune kan kujeran shi yanama wasu sojoji
guda shida dake tsaye a office dinshi magana, sojan dake tareda Abba ne ya saramai
tareda kamewa. "Sir, someone is here to see you" tashi Sameer yayi daga kan kujera
dan kallo daya yamai yagane shi yasan chief judge sosai kawai ne wani abu baitaba
hadasu bane, karasowa yayi har gaban Abba inda yake tsaye tareda bashi hannu yace
"you are welcome sir" sanan yajuya ya kalli sojojin dakin yace "you guys can go"
saramai sukai suka fita sanan ya nunama Abba kujera yace "please sit" zama Abba
yayi tareda yin murmushi ganin yanda yakemai magana cikeda girmamawa yasa ya zauna,
komawa Sameer yayi ya zauna akan kujeran shi, ahankali yace "ina yini Sir" murmushi
Abba yamai cikin natsuwa yace "barka da ware haka Lieutenant, daga wajen Chairman
nake, I went there to thank him, I came here to thank you as well, thank you so
much Lieutenant Sameer" cikin dan kunya dajin nauyin mutumin Sameer yace "but why
sir? You don't have to thank me am only doing my job, dan Allah kadena min godiya"
wani irin burgeshi Abba yaji yayi ganin yanda yake da hankali ga natsuwa, murmushi
yayi yace "I have to, chairman told me everything, duk wanda yamin abin alkhairi
koda kankani ne saina mai godiya that is the policy dana dauka tun ina yaro Sameer
hakan yasa Allah ya albarkaci rayuwana, kuma darajan hakan nakeci haryau, thank you
so much Sameer Allah yamaka albarka" dagokai da sauri Sameer yayi ya kallai yanda
yace Allah maka albarka saiya tunamai da baban su kafin yarasu, ahankali yace
"Ameen nagode" ahankali Abba yace "am inviting you over to my house for dinner gobe
kaida Chairman don't say no please son, ina jiranku gobe," wani kati yaciro ya
ijiye mai akan table yace "this is my address, ina jiranku, sai anjima" yajuya
yafita binshi da kallo Sameer yayi sunan son da yakira shi dashi namai yawo akai
ahankali yadau katin ya kalla kafin ya ijiye agefe yacigaba da aikin dayake yi.
[6/3, 9:42 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
2️⃣0️⃣
0️⃣
2️⃣ 2️⃣
0️⃣
Bayan yabar Barrack office dinshi yaje yay failing 1week leave daga aiki he want to
stay at home yasama Rahima ido dakanshi.
Tunda garin Allah ya waye Rahima tarasa natsuwa tayi zuru zuru duk idan anbude Gate
sai gabanta yafadi dan tasan Abba zai shigo in any moment, Mummy tayi tayi tai
calming dinta down amma abin yaci tura tsoron mahaifinta da Rahima takeji dabanne
dan ba yamata wasa ko kadan, kosu Siddiqa sun gani akwai wani abu akasa tunda suka
tashi sukaga bandeji a goshinta gashi tana dingishi kuma tai zuru zuru ko kallon
banza bata musu ba ma ranan dan ta gaishe dasu duka, tai salla kuma sanan ta shigo
kitchen dudda babu wani abun kirki data iya amma saida ta taya Zeena aiki Zeena na
wanke wanke ita tana dauraya, bayan sun gama kuma ta kwashe bawon doyan da Siddiqa
ta fere ta zuba a bola, duk tanayi ne sabida batason akai