Showing 144001 words to 147000 words out of 197960 words

Chapter 49 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15045

tsarki da kanshi ya nadota a towel
yafito da ita duk agurguje yake komi, bra dinta da pant dinta ya dauko yasaka
matasu yadauko riganta zai samata yaji ana knocking wani irin faduwa gabanshi yayi
yana addu'a, rigan yasa mata a hannu yakai hannunshi kan fuskarshi ta share mata
hawayen daya zubomata yace "stop crying" gyadamai kai tayi ahankali yay gaban
wardrobe dinshi ya ciro wata milk jallabiya ya shirya cikinta ta mugun mishi kyau
sanan yafita yay falo, har zuwa kofa bude kofan yayi yaga matar dake ma Ummi
aikine, cikeda girmamawa tace "sannu Soja, mahaifiyar ku tace nazo nataho da
Rahima" gyadamata kai yayi yace "gatanan zuwa" sanan yajuya yakoma ciki tareda rufo
kofa ayanda yabarta haka ya taddata, rigan ya karba yasaka mata tareda jamata zip
yadau hulanta yasamata tareda tula duka gashinta ciki sabida kar Ummi taga yanda
gashinta ya jike sanan yariko hannunta ya rungume ta bayanta ya shafa yace "sorry
baby girl, I love you so much kinji" gyadamai kai tayi yadagota tareda manna mata
kiss tareda kama hannunta yana tafiya da ita ahankali sosai take dingishi kana
ganinta kasan anmata wani abu yabude kofar falon har lokacin yar aikin na tsaye a
wurin batare daya bari sun hada idoba yace "muje Baaba" murmushi tayi tace "to soja
muje, Soja matarnan naka akwai kyawu wlh tubarkallah, kasan mine na kalleta sainaga
tanamin yanayi da Ummin ku sama ma daku yaran Ummin, dayake ku dukanku da
mahaifinku kuke kama bada mahaifiyar kuba" dan murmushi Sameer yayi yajuya ya kalli
Rahima shi baiga yanayin datake yi da Ummi ba, saida yakaisu har gaban flat din
Ummi sanan yasaki hannun Rahima tareda mata waving hand yabisu da kallo har suka
shiga cikin dakin yana kallon yanda take dingishi sosai Baaba ta mayarda kofan
dakin tarufe sanan yajuya yakoma flat dinshi, fridge yabude yaciro farm fresh
yogurt da wata goran yadau cup ya zuba sanan yazuba zuman yahada yasha yadau remote
yana kokarin kunna TV yaji wayarshi na ringing daga bedroom, ajiye remote din yayi
yay bedroom dinshi yadau wayar ganin Ummi ke kiranshi saida gabanshi yafadi sosai
yakasa daukan wayan, akaro na uku yadauka yakara wayan a kunnenshi yama kasa magana
cikin fushi Ummi tace "wats wrong with you Sameer eh? Dama jira kake a sallamo
yarinyar nan Sameer kasake afka mata? For God sake Sameer bakada tausayine ko
bakasan bata warke ba eh? Gashi yanzu zazzabi yarufe ta, wlh wlh duk randa kasake
afkama yarinyar nan saina mugun saba maka Sameer, saina mugun saba maka last
warning, iyayen yarinya zasuzo gobe so kake suzo su ganta duk wata kala?" da sauri
Sameer yace "iyayen Rahima Ummi?" dan azatonshi Mummy da Abba ne zasuzo gobe
haryaji ranshi yabaci, dan shiru Ummi tayi batare da tabashi amsa ba saikuma chan
tace "nakira real mahaifiyar Rahima, they're coming tommorow dasafe zasu iso bakaga
anata gyaran dakin bakiba" sosai Sameer yaji he is confuse hakan yasa yace "Ummi,
how did you know Rahima biological mother?" dan jim tayi saikuma tace "Allah kaimu
gobe duk zaku sani kaima rashin zumunci da shiga yan uwa yasa ka kasa gane Rahima
da at a glance zaka gane yar uwarka ce, anyway at aside wlh duk randa ka kara
afkama yarinyar nan daganan har one month saina sassaba maka, Sameer bari ake
stitches ya warke inba hakaba zakaja ya warware akara wani dinkin" ta katse
wayanta, kasa ko motsin kirki Sameer yayi yana tunanin kalaman Ummi har aka kira
magrib yaje masallaci baidawo ba saida akai isha'i, koda ya shigo gidan ya tarar da
kannenshi da matansu duksun cika falo anaci ana dariya baida lokacin surutunsu yasa
yawuce dakinshi yakasa manta maganan Ummi.




_BABBAN RANA!_
kamshin girke girke da soye soye yatada Rahima daga baccin data koma bayan sunyi
sallan asuba tareda Ummi, ahankali ta tashi ta zauna tanajin jikinta yay mata dadi
sosai dan yan ciwuwukan datakeji duk sun ragu sai gabanta da kwata kwata takeji
kaman banata ba saikuma faduwan gaba datake ji, ahankali tadau wayan Ummi dake
gefen ta wanda yadawo kaman nata ta shiga daddannawa kaman takira Mummy danta
haddace number ta saikuma tafasa tareda hararan wayan ta ijiye ta tashi, faduwa
gabanta yayi hakan yasa tadafa kirjinta tace "subhallahi" sanan tasauke hannun
tawuce ta shiga bathroom wanka tayi bayan tai sith bath sanan tafito daureda towel
daidai lokacin Ummi ta shigo dakin ganin Ummi yasa akunyace tace "ina kwana Ummi"
murmushi Ummi tamata ta maida kofar tarufe tazo har gabanta tama forehead dinta
kiss sanan tace "ya jikin?" murya chan kasa tace "Alhamdulillah naji sauki"
hannunta Ummi takama tanuna mata kayan dake kan gadon sababbi tace "zokisa kayan
nan yau zamuyi baki, saikizo kitchen muyi aiki ko?" gyadama Ummi kai tayi ahankali,
sanan Ummu tace "inkin shirya kifito kizo kitchen, duksu Fadila na nan suma, Mu'az
da Noor kuma sun tafi dauko bakin daga kano" ahankali tace "Ummi su waye bakin?"
fuskarta Ummi ta shafa tace "kanwata ce uwa daya uba daya, da mijinta saikuma
yarsu, daga Dakar sukazo sunma iso am sure suna hanyan dawowa gida yanzu" dan
murmushi Rahima tayi tace "to Allah yakawo su lpy" "Ameen my babygirl, oya yimaxa
saka kayanki kisame mu a kitchen, Baffan su mijinki ma na nan" gyadama Ummi kai
kawai tayi, Ummi tajuya tafita itakuma tadau kayan, wani hadadden material ne mint
green mai bala'in kyau.
[14/07, 05:04] Aishat Muhammad: 89




Free style ne kawai sai crystals aka bishi dashi shiryawa ciki tayi tsaf sanan ta
dan light makeup dayay mata kyau sosai, tadau dankwali ta daura tai bala'in kyau
kaman ka saceta sanan ta zura slippers tabude kofa tafito tana tafiya ahankali
tafiyar tadanyi kyau babu wani sign na alamun ancita, Sameer dake magana da Baffa a
falon yafara dago kanshi yadaura akanta, jiyayi kaman yasaceta yagudu da ita flat
dinshi, kayan sun mugun amsanta, kanta akasa tana wasada yatsunta ta gaida Baffa.
"ina kwana" cikeda fara'a Baffa yace "ina kwana yar albarka, ya karfin jikin?"
"Alhamdulillah" tafadi ahankali, cikeda so Baffa yace "to Allah kara sauki Allah sa
kaffara ne" gyadamai kai kawai tayi tama kasa magana sanan tadago kanta ta kalli
Sameer adan tsorace hada ido sukayi yay bala'in kyau yana sanye da manyan kaya
faran shadda magic ne ajikinshi dake wata irin kyalli dinkin fitted ya bala'in
yimai kyau kasa jure kallon dayake mata tayi ta saukar da kanta kasa da sauri murya
chan kasa tace "ina kwana" ta gefen ido yaga Baffa ya kallai hakan yasa ya saukar
da kanshi kasa yace "morning ya jiki?" da sauri tai kitchen batare data bashi
amsaba, su Fadila da Ummi tagani kowa yaci gayu sai wani irin murna suke suna
ganinta suka shiga mata ya jiki ta jonasu suka shiga yin aikin da sun riga sun gama
juice kawai suke hadawa, daga kitchen duk sukaji horn din mota, sake faduwa gabanta
yayi ta tsaya chak da filtering nikakken cittan datakeyi tadaura hannunta kan
kirjinta, wanke hannu Ummi tayi tai murmushi ta kallesu tace "sun iso ku karasa
ayyukan bari nazo" fita tayi daga kitchen din ta sami su Sameer a falo, Baffa yace
"sune ko sun iso?" gyadamai kai Ummi tayi cikeda farin ciki tace "eh sun iso"
kallon Sameer yayi yace "zomuje mutaho dasu" tashi Sameer yayi duk sukabi bayan
Ummi sukai compound din daidai babban jeep din Sameer da Noor ya dauka yay parking
a parking space bude kofa yayi yafito Mu'az ma yafito dake gaba sanan Noor yasa
hannu yabude bayan motan wani magidanci ne dan yafi Baffa tsufa yafito yana sanye
da manyan kaya farare ga farin gilashi a idanunshi, sai ga wata mata da batakai
Ummi tsufa ba amman tafi Ummi kiba dan tanada jiki sosai inka ganta zaka zaci yan
biyune itada Ummi tafito tana sanye da lafaya tana ganin Ummi na tahowa tace "oyoyo
Adda" daidai Ummi ta karaso rungume juna sukayi tsam tsam sanan saiga, ahankali
wata farar leg dake sanye dawani hill yafito daga motar, kafar kadai abin kallone
sabida yanda yake da haske gashi cikin fine shoe, aka kara sauko da dayan kafar
sanan wata kyakywar mace ajin farko tafito daga motar da kana ganinta kaga Rahima,
wani irin faduwa gaban Sameer yayi dum! Tana sanye dawata baki da farin abaya kana
ganinta kasan ba yarinya bace a kalla zatai 39 zuwa 40 haka, karamin jikinta yasa
baka ganewa tana rike da wata yar jaka da waya iPhone 11 a hannunta tana murmushi
sosai dake kara bayyanar da kamanninta da Rahima tana kallon Ummi da mahaifiyarta
kafin ta matso kusada su ashagwabe tace "Ummi na nifa nikisaki Momma and hug me
koyar uwarki kadai kikai missing?" ahankali Ummi tasaki yayarta tana kallon fuskan
wacce tai maganan, cupping face dinta tayi tana kallonta murya chan kasa kaman
zatai kuka tace "Safa" cikedaso matar tafada jikin Ummi tace "Ummi am sorry dan
Allah kada kiyi fushi dani" rungumeta tight tayi sosai gabaki daya su Noor da
Sameer duk sun tsaya suna kallonsu, Baffa kuma na gaisawa da magidanci, Baffa yace
"kaga matan nan babu alamun zasu gama wanan gaishe gaishen yanzu anbarmu a tsaye
muje ciki kahuta Alhaji" dariya akayi Safa ta dago kanta daga jikin Ummi ta kalli
Sameer dahar lokacin ita yake kallo cikeda mamaki takama bakinta tace "Ummi haka Ya
Sameer yadawo wani lutete kana ganinshi no body needs to tell you soja ne, rabon
danaga Ya Sameer ina ganin yafi shekara goma sha biyar wlh duk bamu da zumunci jibi
Noor da Muhammad duksun zankale an ijiye iyali, jibidai Mu'az da aka haifa agabana
Ummi yaron dayasha fesomin zawon hakori duk innazo gaidaki" dariya duk akayi banda
Mu'az daya zumburo baki, Momma tace "kibarni autana yasha iska, kumuje ciki" da
sauri Safa tai wajen Sameer dan hararanshi tayi tace "kana wani feeling kanka danna
cemaka Ya Sameer ganin su Ummi ne fa yasa nadaura Yaya akan sunan dududu da wata
uku kacal fa ka girmen mara zumunci kawai" dan murmushi yamata yama kasa magana dan
many things are running in his mind right now gawani anger dayaji yanaji yadai
daure yacigaba da tafiya, har sukakai falo, zubewa akayi afalon aka shiga hira Safa
ta janye gyalen lafayan daga kanta hakan yabama uban tulin gashinta daman fitowa
dayasha gyara sai murmushi take she is so happy rabon ta dataga su Ummi ta manta
saidai awaya, daman yaran duka ta manta rabon data gansu, lokacin datake Abuja tana
yawan zuwa Sameer bayama kasan dan lokacin yatafi wani course a China, 3 and half
years course ne saisa basu cika haduwa ba, su Noor kam lokacin duk suna University
chan zaria.



Ganin filter da Rahima ta rike tana tache citta ya fadi daga hannunta hannunta
narawa sosai yasa da sauri Fadila takama hannunta cikeda damuwa tace "sannu bar
aikin bakida lpy, zauna" tajawo kujera ta daurata akai sanan tasakin mata murmushi
tadau filter ta cigaba da aikin, Ummi ne tabude kofar kitchen din ta shigo tana
kallonsu tace "sannunku da aiki" Fadila ce ta amsa tace "Ummi yanzu zamu kawo musu
abincin naji sun iso, Ummi Rahima taje ta kwanta batada lpy jikinta rawa yake" dan
murmushi Ummi tayi tashafa kan Rahima ahankali tace "akwai dalilin rawan, jini jini
ne, sannu Rahima kihuta in kingama hutawa saiki fito ku gaisa, kufara gabatar musu
da abinci da abubuwan sha Fadila" cikeda girmamawa sukace to Ummi sanan Ummi tajuya
tafita sukuma suka fara jera abinci a tray suna fita da shi Rahima na zaune tana
kallonsu harsuka fita da komi, Nabila tadawo kitchen din ta kalli Rahima dake zaune
duktai wata kala tace "tashi muje falon mun gama fitar da abincin" gyadamata kai
tayi tamike tsaye ahankali, sake faduwa gabanta yayi hakan yasa tadaura hannunta
kan kirji da sauri Nabila tace "menene?" kaman zata fasheda kuka tace "gabana keta
faduwa" wani irin mugun tausayinta Nabila taji gaskiya this small girl has been
through so many things, kanta ta shafa tace "karki damu kidinga addu'a kinji"
gyadamata kai tayi ahankali, Nabila tace "yauwa kokefa kinga yanda kayan nan suka
miki kyau kuwa, gaskiya Ummi ta iya zabe, sun miki kyau sosai duk wanda ya ganki
saiyaji kaman ya saceki Ya Sameer ya iya zabo mata" dan murmushi Rahima tayi Nabila
tace "yauwa kokefa kinyi murmushi mutafi yanzu mune kawai bama falon anata cin
abinci" gyadamata kai Rahima tayi Nabila ta bude kofa suka fita Rahima biyeda ita
suka shigo dinning dan kana fitowa daga kitchen zaka shiga dining saika sauko daga
stairs din dining ka shigo katoton falonsu.

Wani irin faduwa da gaban Safa yadingayi tanajin step din tafiya azuciyarta yasa ta
tsaya dacin abincin datakeyi chak, tana kallon spoon din da fried rice dinda ta
debo keciki. "yauwa Ummi ga Rahiman nan" Nabila data fara fitowa daga dinning din
tafadima Ummi datace mata takira Rahima, da sauri Safa tajuyo ta kalli dining din
da babu wanda yabullo trying to see wanan matar Sameer din da acewanta takeda this
special name.
Ahankali Rahima da yanda gabanta ke faduwa sosai yasa tama kasa sauri tana tafiya
kafafunta na hardewa babu ko kuzari daya tattare da ita tasa fararen hannunta
dasuka sha lalle ta yaye labulen dinning din tafito tareda saukar da kafarta daya
kan stairs din dining, dun! Dum!! Dudum!!! Gaban Rahima yawani irin fadi da tunda
take aduniya bai taba fadi hakaba hada ido datayi da Safa da tunkafin ta bullo daga
dinning din take kallon dining din longing to see who is coming out from this
dinning, hada ido da sukayi da Rahima yasa numfashinta ya dauke gabaki daya na
about 20sec sanan yadawo gabanta yamafi na Rahima faduwa, har abada, har abadan
abidina bazata taba manta kamannin abinda ta tsugunna ta haifa ba, sanan ta raina
for good 12yrs! Dakin kaman kowa naciki yamutu ko motsi bakaji sai sautin
numfarfashi, yanda Safa ke kallon Rahima haka Momma da da Abu magidancin kusada ita
ke kallonta, spoon din da Safa ta debo rice dashine ya subuce yafadi karan spoon
din yadawo da koya hayyacin shi, cikin wani irin yanayi Momma ta taba Ummi dake
kusada ita, cikin wata murya dazai nuna abubuwa daban daban na kunshe acikinta tace
"Adda, Adda wani.....ke....g....ani haka?" tai maganan ararrabe, cikin zafin harshe
Ummi tace "kin fini sani ai" dafa kujera Momma tayi tana kallon Rahima dahar
lokacin kallonsu take one by one dudda she was small then but tsaf tagane
mahaifiyar ta, sanan kakanta dan tana yawan zuwa gidan kakanninta da mahaifiyarta.
Ahankali Momma ke tafiya tana dumfaro Rahima data janye idanunta dagakan Safa ta
zubasu kan Momma Rahima tayi, idanun Momma sun kawo kwalla sosai tana tahowa da
sauri zata rungume Rahima da sauri Rahima ta matsa gefe tareda saukowa daga kan
stairs din tafara tafiya ahankali Momma kuma ta tsaya chak a inda Rahima tabarta
awulakance, duk taku daya na Rahima sai Safa tajishi a zuciyarta har gaban Ummi
Rahima tazo ta dage ta danne zuciyarta tahana kanta kuka ita karan kanta batasan
she is this strong ba sai yau, murmushi ta kakalo ta sakinma Ummi tace "Ummi gani
Anty Nabila tace kina kirana" murmushi itama Ummi tamata yauce rana ta farko
datakeji kaman ta hadiye Rahima danso and she is ready to support Rahima akan
kowani hukunci zata musu, cikeda so tace "eh jewel cewa nayi kufito kizo ki debi
abincin ki kici" murmushi tasakeyi cikin yar siriruwan muryanta mai shegen dadi,
tace "banjin yunwa yanzu Ummi, anjima zanci, kwanciya zanyi yanzu" gyadamata kai
Ummi tayi tace "to shikenan yar albarka, jeki kwanta abinki" gyadama Ummi kai tayi
kaman wata yar yarinya looking so adorable kaman ka kamota kacinye tai hanyar daki
without giving anybody in the room another look, ahankali tabude kofa ta shige
tareda maido kofan tarufe har cikin zuciyarta Safa taji karan buga kofan ta runtse
ido da sauri wasu hawaye masu zafi sharrr suka zubomata.
[15/07, 19:08] Aishat Muhammad: 90
Da sauri Momma tazo wajen Ummi cikin wani irin yanayi tanuna kofar dakin da Rahima
ta shiga tace "Adda Ra...Rahim.....a, jikana ne ta girma haka? Please kifadamin
itace?" lumshe ido magidancin yayi yabudesu kafin ahankali ya ijiye kopin hannunshi
kasa, Ummi dataji wani irin bala'in haushin su takeji tace "wanan tambayar kuma
kezan mawa Saratu, keda jinin ki" hannu Momma tadaura kan fuskarta tafashe da kuka
ahankali tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Allah natuba, Allah natuba,
astagafurullah", ahankali Safa tasaka hannu ta share hawayen daya zubomata tass
tadauki chokalin abincin ta daya fadi akasa tsabagen rashin sani meme zatayi
tasashi cikin abincin ta debo abincin zatakai baki, cikin wani irin fushi da zafin
rai Sameer yace "I swear if you dare take that food to your mouth I will choke you
to death Safa!" tsabagen yanda ranshi ke tafarfasa yana kallonta dagakan kujeran
dayake ance babba duk inda yake babba ne, Sameer feel at his age he can talk to
kowa in his family koda agaban iyayensu ne, dago rinannun idanunta Safa tayi ta
kalli Sameer ahankali, cikin fushi yace "bantaba sanin ajininmu akwai people dazan
kalla naji dama ace ban hada komi dasuba sai akanku" yafada yana kallon Abu, Momma
da itama Safan, yace "like how dare you Safa kikai abondoning abinda kika haifa da
cikinki batare dakin kara waiwayanta daidai dasau daya ba bayan kin barta at the
verge of death eh!?" yadaka mata tsawa daba ita kadaiba har saida sauran yan dakin
suka girgiza, yace "wlh you are very very lucky, rabon dana hadu dake tun muna
yara, harkikai aure in fact nibanma san kin haihuba, I knew nothing about haihuwan
ki dako ina kike aduniyan nan dasaina nemoki and beat the stupidity out of your
head nonsense!" yay shiru kirjinshi na tafarfasa yana kallonta Ummi bata hanashi
magana ba ta tsaya tana kallonshi kawai with so much love and admiration tana kara
godema Allah yanda ta tarbiyantar da mazajenta duk inta kalli Sameer tasan cewa she
gave birth to a fearless leader anan wurin family coordinator, tasan kodayau zata
fadi ta mutu, sanan Baffa yafadi ya mutu Sameer will coordinator this family yahada
kan kowa and keep moving, Sameer is strong, bold, and fearless wanan ajininshi
yake.

Karkada kafa yayi yana kara tunano abubuwan da Rahima went through yace "kinsan
wani abu?" yace "inhar baki roki yarinyar nan gafara tayafe miki ba kidena ganin ke
mahaifiyar ta ce kenada hakkoki akanta, kidena ganin haka, wlh inhar this girl
Rahima dakike gani dinan bata yafemiki ba Allah will punish you cus this girl went
through hell, this are witness" yanuna su Noor da Ummi yace "Rahima has been
through alot, alot kawai tanada rabone and Allah na kareta saisa but I truly feel
disgusted over your act, what's the relationship between abinda mahaifinta yamuku
da yarda kika haifa tasha nonon ki eh?!" yasake dakamata tsawan dayasa at this
point tafashe da kuka sosai jikinta na kakkarwa dan gyaran murya Abu yayi zaiyi
magana yace "ahhh Same......" hannu Sameer yadagamai babu ko atom of tsoro ko
shakka yace "Abu with all due respect, am talking to my sister, zandawo kanka"
sanan yamaida hankalin shi kan Safa dake goge fuskarta da yatsunta amma takasa dena
kuka yace "I know nasan Abu ne yacemiki baki ba yarinyar kibarma mutumin daya
aikashi prison yarshi kirabu dashi, lemme tell you this Safa, kinsan cewa ba'ama
iyaye biyayya awurin sabama mahalicci? Ko bokane iyayen ka kanada hakki, dolene
kamusu biyayya, inyace bani abinci, bani ruwa, bani kaza bani kaza, dukkimusu
biyayya dudda sudin bokaye ne amman inhar bakimusu ba sai Allah ya tambayeki, but
aduk lokacin dasuka saka aikin da sabone yinshi sabama Allah ne karkayi wanan bakai
laifi ba, tayaya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login