Showing 27001 words to 30000 words out of 197960 words
Asiya ai
kaman ya yankin ma kanshi ticket din raini ne, ni nasan dama bazai taba koda da
wasa he will not accept maganan nan, kawai kiyitamai addu'a Ummi what goes around
comes around, Yaya Sameer zaiyi aure one day one day" cikeda damuwa sosai Ummi tace
"Ya Allah, Ya Allah kadubi lamarin nan nawa, Ya Allah ka karkata zuciyan Sameer
zuwaga wata mace, Ya Allah kahadashi da wacce zaiso sosai, Allah ka aurarmin da
yaron nan badanni ba badan halina ba" tasake share hawaye daya zubo mata rungumeta
Nuru yayi yace "is okay Ummi ya isa hakanan" haka yacigaba da lallashinta har
Muhammad shima yadawo duk suka taru suna bama maman nasu baki harsuka samu ta dawo
normal tadan wartsake tabiye musu sunata hira.
Tunda aka shigo dasu headquarter anan reception aka zubesu duk wanda zai wuce saiya
kallesu, gabaki dayansu akasa suka zauna bama abasu kujera ba, Rahima tai kuka har
idanunta sun kumbura kaman zaka taba jini yafito, daukan sunayen su akayi gabaki
dayan su saiga wata mata ta taho da kayan first aid box a hannunta tareda daya daga
cikin officers din dasuka kawo su suka taho gaban Rahima. Rahima yanuna mata yace
"ga wacce batason ta mutun nan amma take shaye shaye, duba kafan Dr, tai targade
Lieutenant ya gyara mata dazu" murmushi Dr tayi ta tsugunna a gabanta tana tattaba
kafan ahankali kafin ta bude first aid kit din tadauko wani man zafi ta shafa mata
sama sama tace "ya gyaru kamai muscles pain take having, wanan balm din kuma will
kill it nan bada jimawa ba" sakin kafan tayi auduga ta dauka ta daura kan goshin
nata tana share mata jinin wajen tace "what is your name yanmata?" shiru Rahima
tayi batare databata amsaba tai banza da ita hakan yasa Dr din ta kalli fuskarta
tacigaba da aikinta tace "young girls kaman ke always think shaye shaye is a
gateway to having fun, inspiration, zero worries da sauran, aganinku shaye shaye
wayewa ne irin kema kin isan na, but my dear is a lie bahaka abin yakeba, yes nasan
shaye shaye nasa ka manta da matsalolinka, ka manta da bakin ciki da duk wata
damuwa data addabi zuciyarka, kaji kaman kai kadai Allah ya hallita a duniyan nan,
kaji yes a yanzu u can stand up to anybody kodakam babanka ne, inkayi you can stand
up against anyone and anything in fact u can even stand against the world, shaye
shaye nabaka wanan karfin da boldness din da jarumtar aganin ku but my dear is not
true, duk ba hakabane, shaye shaye is mess with the heart and mess with your brain
the IQ dinki, baya komi illa destroying dan Adam, tundaga na lafiyan shi harda
sauran su and kill u wulakantaccen killing ma, but you know you still have time, u
are young, you are too beautiful karki bata rayuwanki akan wanan shaye shayen da
kikejin dadinshi nayan mintoci, see duk abinda dadinshi ba dawwamamme bane den babu
amfani yi, dadin da last for few hours ko for a day dadi ne? Ki natsu kituba Allah
zai yafemiki kisan me kikeyi kokya samu rabauta" tana maganan tana shafa gyaramata
injury din goshin nata sanan ta shiga hada kayanta, ahankali Rahima tasa hannu ta
share hawayen dasuka cika idanunta suka sake zubowa sharr, ganin Dr looks friendly
yasa murya chan kasa tace "I want to use the restroom" dagokai Dr tayi ta kalleta
jin tamata magana for the first time, murmushi ta sakin mata tace "stand up muje na
kaiki" ahankali ta tashi tana dafa bangon wurin tanadan dingishi suka wuce itada Dr
din, officer yace "kuma two minutes nabaki" da Dr suka tafi daidai sunkai wajen
bayin wani yafito daga wani office ya kwalama kira yace "Dr you are needed here" da
sauri ta kalli Rahima tace "shiga this is the rest room, zakiga ladies side inkin
shiga" tai magana tana tafiya, bude kofan Rahima tayi ta shiga rest room din, dan
passage ne awajen dakeda two pathways dama da haggu da akwai kofofi, ko kadan bata
lura da sign din ladies da gentlemen ba take nuna Wannene bayin maza dana mata ba
tabude kofar dama ahankali tanadan dingishi ta shiga, maida kofar tayi tarufe tai
ciki, saida tai dan tafiya sanan ta iso main falon bayin wasu jerin bayi guda shida
ne sai wash hand basin da manya manyan mirror a bangon, da sauri takarasa tabude
bayin farko ta shiga ta mayar ta rufe, bayin so clean babu datti kodaya kodan bayin
maza ne saisa oho, but bayin mata dai always yacika datti, mayar da kofan tayi
tarufe tasa sakata sanan ta daga riganta sama tasa hannu a aljihun bayan wandon ta
taciro wayarta da tuntuni take wurin Allah yaso ta babu wanda ya kirata da asiri ta
yatonu sun kwace dan duk an karbe wayan sauran, maida wayan silent tayi da sauri
sanan taciro number Mummy tana goge kwallan datake yi tai dialing number har wayan
ya katse ba'a daukaba, haka tasake kira shima ba'a daukaba fashewa tayi da kuka
tayi mara kara tana taushe bakinta, ba karamin tashi hankalinta yayiba takira mummy
sau 17 times bata dauka ba bakaramin tashi hankalinta yayi ba yanzu kwana zatayi a
wurin nan, gashi an fara kiraye kirayen sallan magrib, share hawaye tasakeyi,
ahankali tasa hannu ta sauke cover bayin, zama tai kan sitter ta rufe fuskarta da
duka hannayenta tana kuka tajima ahaka sanan tai shiru ta share idanunta tana
kallon wayan sanan ta shiga saka wasu nambobi tadanyi jimm tana kallon number kaman
mai tunanin wani abu kafin ahankali tai dialing number tasa hannu ta share hawayen
daya zubomata takara wayan a kunenta, har wayan tagama ringing ba'a dagaba hakan
yasa tasake dialing number akaro nabiyu, wayan na gab da tsinkewa aka dauka batare
da ance komiba, ajiyan zuciya ta sauke mai kara kafin cikin muryan ta dake rawa
sosai tace "h......he.....hello" hannu tasa tasake share hawayen daya zubomata
tareda jan majina irin na wanda yaci mugun kukan nan, ahankali cikin kuka tone
tace "In..i.....ina police station ankamani dazu, please come and get me Mama, am
so scared, please come and get me kinji" tafashe dawani irin kuka mai tsuma zuciya,
katse wayar akayi batare da ance komiba hakan yasa ta kifa kanta abangon bayin
tafashe da kuka sosai, tai kuka na kusan minti biyar sanan tadago kanta tasake
dialing number, ringing daya wayar tayi akai picking call din kafin ma tai magana
muryan wata mata tarigata tace "I told you time without numbers karki kara kirana
in your life, I don't have anything to do with you, an kamaki a police station what
is my business with that? Mahaifinki judge ne so call him up not me, banda alaka
dake or anything yarinya, stop calling me Mama mamaki kin barota achan gidan
ubanki, in danta ninema rot a police station din ko agefen yatsana stupid girl,
mtsww" ta katse wayan tareda jamata dogon tsaki, wani irin kuka tafashe dashi she
is feeling kaman ta shake kanta ta mutu why did she even call this woman? takai
almost 10min tana kuka kafin tadago kanta ranta yay mugun baci, cikin fushi tasake
dailing number matar ringing daya aka dauka kafin matar tai magana tarigata tace
"you know what calling you was the biggest mistake danayi sama da mistake din
dayasa aka kamani aka kawoni nanma, how can I think a wicked woman like you can
help me? Your heart is so black and dark da baisan menene help ba in this life, I
hate you nima, I hate you with every single heart beat dina, My Mummy is better
than you sau miliyan she can't never ever stand and watch me in pain, she is the
best Mummy in the world, best Mummy, the absolute best, and I love her, I love her
with all my heart, I can ever rot here saidai in Mummy na bata duniya, inhar nakara
sa wanan hannun nawa nakiraki ba sunana Rahima ba, trust me inda ace Allah na laifi
dazan iya cewa laifin dayayi shine yabama a wicked woman like you ciki harta haihu
you deserve to be a barren cus you don't have soul saidai Allah baya laifi, I hate
u, I hate......." katse wayan da akayi dip yasa tazare wayan daga kunnenta ta
wurgar da wayan a kasan bayin ta shiga rera kuka tana kiran Mummy, she is so sad,
she is so so sad, how can she even think if calling this woman mema yakaita eh?
Mema yakaita, buga kofan bayin datake ciki taji anyi. "open the door"[6/3, 9:42 AM]
Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
1️⃣8️⃣
8️⃣
1️⃣ 1️⃣8️⃣
Muryan mace taji, azabure ta tashi tsaye ta shiga kalle kalle bayin tana neman inda
zatabi ta gudu, dan karamin window dake wurin babub abinda zai mata dudda rashin
kibanta bazata iya wucewa tawajen ba hakan yasa ta tsaya tana kallon kofan tana
share hawaye batare data bude kofan ba, cikin tsawan matar tace "I said open the
door Lady, da uban wa kike waya abayi haa, and maiya kawoki bangaren maza, open the
door!" aka mugun daka mata tsawa da yasa ta matso kusada kofan tasa hannunta kan
sakatan tabude, turo kofan officer tayi batai wata wataba ta dauke ta da mari tass!
Rike kuncinta tayi tana dafa bango, tsugunnawa officer tayi tadau wayar data yar
akasa tasa hannunta agaban riganta tawani irin finciketa tajata tareda bude bayi
suka fita, suka fito main waje daidai lokacin Sameer ya shigo wajen shida wani dake
rike da byro da wani paper dayake nunamai.
Ganin yanda ake kallonta yasa ta hadiye kukan datake yi ta dage ta ture hannun
officer data kama mata gaban riga tace "dalla malama kidena jana tunda ni ba akuya
bace muguwa kawai" da hannu officer ta nuna kanta tace "ni kike cema muguwa?"
hararanta tayi da idanunta dasukai jajir suka kumbura tsabagen kuka tace "eh ance
muguwa azzaluma m....." tass! Officer ta dauke ta da mari saida Sameer dake duba
list yadago kanshi ya kallesu, fashewa da kuka sosai Rahima tayi tana shafa inda ta
mareta tace "ance muguwa azzaluma, uban mena miki zakiyi ta marina kina jana, what
have I done, banza kawai wacce tai kwantai ba miji" wani dan gajeren murmushi
Sameer yasaki da gefen baki, ya maida kanshi kan list din da aka bashi yana dubawa
zagin ya mugun bashi dariya ne tayaya akai tagane tai kwantai batai aureba, ohhh
this Indomie generation children are damn hilarious.
Cikin fushi matar ta waiga ta kalli all the staff dake aikinsu abinsu dan irin
wanan fadanne tsakanin yan shaye shaye dasu sun saba gani is not a new thing, hannu
tasa tadau kulkin dake kan desk din Kusada su tace "zanci ubanki ne yau" cikin
tsiwa tana kuka tace "ubana yafi karfin kicishi wlh, a inda ubana zai ubanki bai
isa ya tsayaba saidai yazo bara" bugamata kulkin officer tayi a kafada hakan yasa
tafasa wani wawan ihu da saida kunen kowa ya amsa, sake dago kai Sameer yayi ya
kallesu ganin haka yasa officer dake nunamishi list din yajuyo yace "officer!"
batare data kalleshi ba tace "officer I caught this gurl tana waya abayi shine on
top of that takemin rashin kunya tana zagina, tana....." juyowa officer tayi zatai
magana chairman yabude kofar office dinshi yafito yana kokarin sanya glasses dinshi
a ido yace "Laraba enough! Lieutenant come with me please, officer give him the
list" bama Sameer list din officer yayi yakarba yataho yawuce ta gabansu batare
dayama kallesu ba yay upstairs, bude office din chairman yayi ya shiga, zama yayi
akan kujeran da chairman ke nunamai yabashi hannu gaisawa sukayi, cikin harshen
hausa Chairman yace "welldone Sameer am proud of you wlh, kasan mesa nakira ka,
acikin yaran nan akwai mutum daya da I really don't know what to do about, am a
leader you know Sameer and I don't want to be bias during the course of my work,
bansan mezanyi ba I had to call you, kanada hankali sosai duk girman mutum
sometimes idan zakadau hukunci dolene ka nemi shawara koda wajen dan cikin kane"
yadanyi shiru kafin yamikama Sameer din hannu yace "kawo list dinan kaga" mikamai
list din Sameer yayi ya karba yace "sunan yaran nan ne dakuka kamo, wanan yarinyar
da officer ke bugunta yanzun nan she is the daughter of Chief judge of the federal
High Court na nan Abuja, Rahima Sambo Rikadawa, da farko danaga sunan I was like
maybe is just a random person dat happens tanada surname na judge din garin nan,
saida na kira wani friend dina lawyer danasan yasan Chief Judge sosai and asked him
about yaran Chief judge nawa yacemin four and call the names for me which wanan
yarinyar dakake gani happens to be his last born, kana hango abinda nake hangowa
Lieutenant?" ya tambayi Sameer daya natsu yana kallonshi gyadamai kai Sameer yace
"a Chief Judge is someone that is very vulnerable, mutum ne da kusan idanun kowa na
kanshi, aikinshi aikine dakesa kai makiya dayawa sanan kai masoya dayawa abin
kanzama kaman 50-50, ko 60-80, cikin makiyan harda nakusa dashi wanda kawai neman
abinda za'ai amfani dashine atunkudeshi wani ya gaje kujeran shi na Chief judge din
babban birnin tarayya, inhar press zasu samu koda gutsuren information ne kan
yarshi na shaye shayen illicit drugs abin can cost him alot to the extend da zai
iya tarnishing image nashi and his reputation a society mu, bayan haka, yanadaga
cikin mutane masu yankewa drug dealers hukunci yau ga yarinyar shi na drugs" dan
ajiyan zuciya Sameer ya sauke ya gyara zama tareda ijiye hannayenshi akan table
yace "me kakeso daga gareni Chairman?" ajiyan zuciya Chairman ya sauke yace "bakaga
nasa akai yarinyar dinning ba, all the staff anan babu wanda yasan abinda nasani, I
want to isolate the girl from the rest of the gang sainai contacting mahaifinta
yazo dakanshi ya dauke ta kaita rehab yarage nashi, mun bashi itane yanzu dan kare
shi dakuma aikinshi daga bakin Al umma amma in muka kara kama yarshi akaro nabiyu
ni I will release d information nabar press suzo su gudanar musu da interview kafin
atattarasu akaisu government rehabilitation centre koya kagani?" gyadamai kai
Sameer yayi yace "sauran yaran fa?" cikin dan damuwa kadan Chairman yace "what do
you think Lieutenant?" dan shiru yayi kaman mai tunani yace "they have to go for
rehabilitation, rayuwan su zai taimaka, Nigeria muna so muyi eradicating shaye
shaye idan aka samu yara kusan talatin suka dena shaye shaye cigaba da Nigeria ne
sosai, yayinda idan ka barsu baka kaisu ba ka kaddara mutane talatin dinan zasuje
su koyama wasu mutane talatin din shaye shayen ne, kaga rate of shaye shaye yasake
increasing kenan" gyadamai kai Chairman yayi yana yaba fikran Sameer yace "hakane,
za'a kaisu, bari na nemi mahaifin nata abokina yabani contact dinshi dazan iya
samun shi" gyadamai kai Sameer yayi, dialing number Abba chairman yayi harta gama
ringing ba'a dauka ba, hakan yasa yacigaba da kirashi har sau biyar ba'a dagaba,
knocking kofar akayi hakan yasa ya ijiye wayan yabada izinin shigowa, wanan officer
data daddaki Rahima ne ta shigo rike da wayan Rahima dake ringing tace "Sir wayan
yarinyar chan ne her Mother has been calling, I want to ask for your permission
idan na amsa na sanar da ita mun kama yarta kokuma na kashe wayan" hannu chairman
ya mikamata alamun tabashi wayan hakan yasa ta mikamai ta juya tafita, sake daukan
ruri wayan ta shiga yi ganin Best Mum akan screen yasa Chairman yay pikin tareda
sawa a speaker kafin yay magana Mummy tariga shi. "Autana where are you, sorry
dakika kira ina kitchen dasu Siddiqa, wai har yanzu baku gama birthday party bane
da Chris I think I asked you to come back kafin 6 gashi yanzu ana kiran
magrib......." dan gyaran murya Chairman yayi yace "this is Alhaji Muhammad
Mustapha Abdullahi the Chairman of National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) in
Nigeria, please madam is your husband there I will like to speak to him" sosai
gaban Mummy yafadi hakan yasa tace "innalillahi Malam please ina y'ata take? Ina
Rahima na? Ina Autana? Yarinyar dataje birthday maiya badaku da ita kuma?" yanda
duk take maganan a hargitse yasa yace "calm down madam, I asked is your husband
there I want to speak to him" arude tace "no, no, bayanan yay tafiya yace port
Harcourt this morning, please ina y'ata? Me takeyi awurin ku?" shiru Chairman yayi
yana sauraron yanda Mummy tarude ahankali yace "I am sorry to announce this sad
incident like this Madam, but your daughter Miss Rahima Sambo Rikadawa has been
caught taking Illicit drugs, Codeine, Crack, Tramadol, Weed, and shisha, she has
been detained here according to the constitutional law, after some inevitable steps
da we must carried out akanta, we are going to hand her over to rehabilitation
centre inda zatai spending period of 6 months, thank you Madam for your time and do
have a wonderful night rest" ya katse wayan tareda kashe wayan gabaki dai ya ajiye
kan table Tareda danjan tsaki yace "mahaifinta yay tafiya Yaya kenan? Kaga tashi
muje muyi salla" tashi sukayi suka fito daga office din suka sauka kasa inda suka
tarar su Chris duk nacin abinci anbasu abinci a takeaway faran shinkafa da stew da
dafaffen kwai, duk sunyi zuru zuru sunaci kaman ance in basuci ba za'a kashe sune.
Magrib sukayi suka fito daga masallaci suka shigo cikin premises dinsuna dan
tattaunawa, reception suka shiga wata mata suka hango sanye dawani bakin dogon riga
dayaji stones tayafa wani mayafi milk color na manyan mata akai tarike wani handbag
na LV tana magana da receptionist din wurin tana fada tace "ina kuka kaimin y'ata
where is Rahima? Kubani y'ata natafi da ita shairi ake mata Rahima batashan komi
saidai in wanchan yaron Chris shine ya koyamata taga yanasha ta dandana dan dama
shiyay inviting nata to birthday party shi" cikin masifa Chris yace "No dey lie
Madam, your daughter sabi everything so tey she dey carry for bag go school, no dey
lie for my head ha'a see me see gbese o" cikin fushi Mummy ta juya zatai magana
taga wani magidancin mutum tareda wani cikakken dogon bakin yaro dake sanye da
jacket baki dabai ja zip dinba, rigan dayasaka mai ruwan toka ya bayana da
kirjinshi hartana hango kwantaccen gashin kirjinshi baki sidik, dan girgiza kanta
tayi ta saita idanunta kan Chairman kafin ta kalli wasu manyan hotunan frame dake
jikin bangon reception din na president, da vice president saikuma hoton shi da aka
rubuta chairman NDLEA, cikeda masifa tace "good ka iso Chairman, I guess you are
the one I spoke to a while ago, ina y'ata take? Kubani y'ata natafi gida, shairi
kuke mata Rahima babu abinda tasani, she is my last born, yaushe na haifeta duka
duka da zaku kamomini yarinya daga taje birthday coursemate dinta kucemin shaye
shaye take? How on earth is this possible?" anatse Chairman yace "Madam