Showing 81001 words to 84000 words out of 197960 words

Chapter 28 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15046

maganan babu wasa
yana kallon idanunta datake zarowa tsabagen tsoro kaman zasu fadi akasa hawaye
nabin idanunta, yace "one more thing, ko tari kikamin anan not just ihu I will
shock you Rahima, zan baki mamaki" yay maganan tareda tashi ya cisge seletep din
bakinta ta runtse ido sabida azaba batare datai koda tari ba tana sauke ajiyan
zuciya, sanan ya zauna yace "clean those tears" da sauri tasa hannu ta sharesu
kirjinta dukan a shirin a shirin kawai suke tsabagen tsoro ita dama harga Allah
batawani yadda da abokin Abban nan wanan sojan ba tasan mugune, gyara zama yayi
yace "are you ready?" gyadamai kai tayi tana hadiye hawayen dake shirin zuba, yana
kallonta right into the eyes irin kallon I dare you to say lies dinan yace "ranan
da mukazo gidanku da magrib nida Abban ki, baki fitaba, after basketball Mummyku
tace min duk bacci kukayi kece kadai suka bari adaki baki riga kin tashi ba, ya
akayi a ina kika samo 3 bottles of codeine da weed dat u were smoking ranan?" wani
irin racing heart dinta ya shiga yi zata fashe da kuka yace "this is the last time
dazan fada miki karkimin kuka, cry kika idan ban fasa miki tear bags dake cikin
idanunki ba" hadiye kukan tayi tai gum tana kallonshi kaman zata cinyeshi da ido
yace "answer me!" gyadamai kai tayi da sauri tace "a....kagako..." takasa magana
tsabagen yanda kirjinta ke bugawa bakinta kerawa sosai ya tsareta da wasu irin
mayun idanu yace "am listening" tace "wlh ina tashi daga bacci na shiga bathroom
nai brush na wanko fuska na nafito shi....ne" tai shiru yanda yamata wani kallo
yasa tace "shine na gansu akan bedside drawer dina su uku da weed guda uku, wlh
baruwana bani na ijiye ba na rantse da Allah" tai maganan bakinta na rawa tana
shirin kuka amma yanda ya tsareta da ido da wukake yasa ta hadiye kukan, sosai yake
kallonta yasha interrogating criminals so yanada knowledge inhar yama tambaya ka
saki karya zai sani kana fadin gaskiya zai sani kuma yasan tambayan nan iyakan
gaskiyan datasani tafadi mai hakan yasa yay shiru, puzzle questions zai mata dashi
ne zai bama kanshi da kanshi final amsa din, yace "how did you escape from rehab?"
rawa bakinta yafara da kyar ta danne kukan tace "ranan I was bathing in the morning
all of us muna bayi shine one woman tafado bayin nakusan ihu shine tarufe min
baki......" nan tabashi labarin har inda suka kwana da abinda suka bata duka tai
maza ta share hawayen daya zubomata gyadakai yayi cikeda gamsuwa yace "who was that
Chris your boyfriend me hadinki dashi?" fashewa tayi da kuka kallon daya mata yasa
ta hadiye kukan da sauri tace "wlh wlh ba boyfriend dina bane, ajimu daya a vet,
kagako ni banda ko kawa daya a school dinmu, I don't talk to anybody a class dinmu
shine kullum kullum yayta kallona yanamin magana wlh bantaba cemai komiba, ranan
damuka zo school zamu fara sauke ya Siddiqa a accounting department su Yaya Siddiqa
da Luba da Zeena sunata xagina, shine direba wai sudena biyemin ni yarinya ce,
shine fa naji haushi nace yakara cemin yarinya saina marai shine Yaya Siddiqa ta
daddakeni ta fizgoni ta yardani akasan wajen" tafashe da kuka, mugun kallon daya
mata yasa tahadiye kuka tace "Ya Siddiqa tacema direba yatafi yakaisu Ya Luba tunda
rashin kunya nakemai nai trekking to department dina kumafa duk yafi nasu nisa chan
karshen school dibfa muke, shine tai tafiyanta tabarni natashi ina kakkabe jikina
saiga Chris ya tayani daukan jakana yace nazo muje da kyar na shiga damuka je har
an shiga lecture shine saiyaga Codeine ajakana saiyace......." tabashi labarin tsaf
harda yanda Mummy saida tamaga Chriss din tace su tafi, Sameer baice komiba harta
gama yana sauraronta yace "Rehab Dr ki ya sanar dani you have been taking drugs
8yrs ago, jikin ki yabasu dat record" ya kalleta kaman yanda take kallonshi yace
"your Dad told me baki dade da shiga 20yrs ba, bari namiki simple mass, subtract 8
daga 20" da sauri tace "12" gyadakai yayi yace "you've been into drugs tun at the
age of 12, yaran 12yrs bama susan me drugs ba, basusan akwai wani abu shaye shaye
aduniya ba, children of 12yrs ko balaga basuyi ba basu mallaki hankalin suba, bama
Susan menene duniyan nan ta kunsa ba, listen Girl" ya gyara zama yace "idan kika
kawomin any gargada akan wanan tambayan zan baki mamaki, I need answer tell me ya
akayi kika fara shaye shaye at the age of 12, ranan farko and everything" faduwa
gabanta yakeyi bana wasaba Mummy tasha fadamata kar wanda yaji tsakanin su, koma
menene karta sake ta kira sunanta mutane da society sun dauka shaye shaye is bad
but is actually fun, da dadi su basu sani bane. "Rahima!" Sameer yadaka mata tsawa
tareda kai wukan kasan wuyanta yasa tafara wani nishi kaman mai shirin mutuwa duka
jikinta moving yake yawani zaro red eyes dinshi yace "tell me how did you start
doing drugs, who the hell introduced you to drugs at 12yrs old, who! Yasaka mata
wani mahaukacin tsawan da batasan lokacin datace "Mummy! Mummy na! Mummy nane!!"
kallon kwayan idanunta Sameer yayi kafin yadan koma baya saikuma ya zauna yana
kallonta bai bari yanuna mata anything ba, hawaye ta share da sauri saikuma tafashe
da kuka tace "Ya Sameer dan Allah karka fadama Mummy, wlh tace duk randa nafadama
wani daga ranan zata dena sona tunda ni ban rike sirrin ta amana ba please kaji,
dan Allah wlh zan fadamaka amma karka fada kaji" wani mugun kallo yamata shiru tayi
tace "kaga ko Ya Sameer duk duniyan nan wlh babu mai sona kaman Mummy tana sona
dama dasu Ya Siddiqa data haifa, kaga su Ya Siddiqa kullum suyi ta dukana da ina
kwana a dakinsu Mummy tacireni daga dakin tasa home decor tazo aka tsantsaramin
dakina yafi nasu kyau, kuma kullum da daddare a dakinta nake kwana dan bana iya
kwana ni kadai, kaga bayan Mama na ta karyani tabar gida nadinga ciwo zafi ko ina
yakemin anata karyani ana mayarwa mummy in anamin dauri harsai Abba yakoreta dan
kukanta harya kanfi nawa sabida yanda take tausayina mu dawo gida inta kuka bana
iya bacci wata rana tazo da Abba yafita sallan magrib su Siddiqa basa daki ta zauna
tareda rugumeni tana tofama hannun karyan addu'a tacemin zata bani wani abu dazaisa
nadaina jin zafin hannun amma karan fadama kowa inaso na gyadamata kai tace kuma
abin zai dinga sani farin ciki na manta da mamana muguwa my mum is wicked but she
is here now, she is my Mum she loves me more than her banga bata taba dukana ba
kuma bata tababa so ma manta da ita zatamin komi, tasa na kulle idona nabude baki
ta naji dai wasu kwayoyi guda uku tasamin sanan ta zubamin wani ruwa mai daci
nasha, ta kwantar dani ajikinta tanamin tatsubiya nai lamo ina jinta ahaka nai
bacci sai washe gari natashi aiko hannuna babuma inda kemin ciwo I was so happy
nadinga murna ina tsalle ina rawa itama ta tayani, dazaran naji zai fara zafi zanje
dakinta nace tabani abun tacemin nabari da magrib kullum da magrib take Bani
lokacin kuma saina rufe ido nadena rigima harnazo na girma, tacemin nai browsing
uses of weed nayi, kagako Ya Sameer Mummy duk wani abu dazai amfaneni takemin
bamatama yayanta, naga weed na bude brain hakama shisha dan akwai nikotin aciki
tundaga ranan tace kullum zata dinga samin a abinci saisa in babu shi a abinci ban
iyaci danna saba kuma ko nafi duka su Ya Siddiqa brain because of weed 9As nafito
dashi a Waec jamb kuma naci 362, Mummy ko tsinke bata bari na daga anything
dazaiban wahala bata bari nayi bana aiki nan shara ban wanki ban girki kuma insu Ya
Siddiqa sunkai karana ta dakesu, su kadai keyin aikin suyi abinci su kawomin har
kan gado, ran Saturday da Sunday kawai take sani nabisu islamiyya
shima sai in Abba na nan sabida karya mata fada amma inhar bayana van zuwa sabida
duka akeyi, su Ya Siddiqa kadai ke zuwa, in kanwar Mummy taje dubai ni kadai zatasa
ama tsarba kaya dan nine autan ta, kaga yawan kayana yacika wardrobe dina some
kayana ma a wardrobe dinta suke, takaini saloon kullum dani take fita, in Abba
yadaken taita fushi, insu Ya Siddiqa suka daken takamatsu tace inzo in rama kaga
bata bari aci zaluna, batason ta ganni cikin bakin ciki duk wani abu dazai cireni a
damuwa zata bani, Mummy na bala'in sona tacemin that my wicked Mother ta taba sata
tai bari bayan ta haifi Luba wai mamana tasata tai barin cikinta na boy amma bata
riketa da hakaba yasa taci zaluna ba kota lalatamun rayuwa ba saidai ma tasoni sama
da yanda taso nata yaran, kuma bata taba bari Abba kosu Siddiqa sun gane ba da
daddare take bani nasha nai bacci, kuma Abba shi yawanci a studyroom yake kwana
yana aiki sai tsakar dare yake dawowa kuma wani zubin a sati baufi yay 3daya a gida
ba sauran yay tafiya saisa duk basu saniba sai ranan shima nasan Mummy ta ijiyemin
ne kawai dantaga bana cikin farin ciki to tazaci da daddare zansha shine nikuma na
dauka nasha alokacin nai mistake" tai shiru tana kallonshi kaman yanda yake
kallonta, jikinshi yay mugun sanyi jikinshi yay sanyi, all he sees a idanun Rahima
is yarinta da mugun rashin wayau, akwai yaran 20 da hankalin su is intact but
Rahima kam Mummy tai brainwashing yarinya da bama tasan different between right and
wrong ba, tadawo da brain din Rahima a fool, ajiyan zuciya ya sauke ahankali yan
abubuwan dayagani couple of times dayaje gidansu nadawo mai, maida wukan yayi cikin
box din yarufe box din yana kallon Rahima dake kallonshi har lokacin gabanta na
faduwa tace "ai ba zaka fadaba ko" gyadamata kai yayi yadau box din yatashi yafita
daga dakin binshi tai da kallo saikuma tafashe da kuka takoma kan gado ta kwanta
duk zuciyanta yaki natsuwa.


Tunda Sameer yahadu da Rahima yauce rana ta farko dayaji rayuwanta da ita kanta
Rahiman ta mugun bashi tausayi, a mota ya zauna yana tunanin me zaiyi dudda dai bai
basani ba for now abu daya dayasani shine zaman bazai kara bari tazauna da Mummy
ba, and duk inda maman Rahima take aduniyan nan he will find her kiran magrib da
aka fara yasa yafito yatafi masallaci, wuraren sha biyu ya shigo dakin yaga tadade
daya in bacci bayan tasha fruits salad ta koshi.

Ranan bacci sosai tai da daddare bata tashi ba har sauda yatada ta da safe yace tai
salla tai wanka zasu koma yau faduwa gabanta yayi shikuma yawuce ya sauka kasa dan
zaiyi checking out and clear his bills, wuraren nine yadawo yaga tao wanka tana
sanye da dayan doguwan rigan tai kyau dudda har yanzu da muguwa raman nan datayi
hijabi yanuna mata yace "saka mutafi" dauka tayi tasaka tadau kayanta data hada a
ledan suke suka fito sai kallon hotel din take tunda sukazo sai yau tasake fitowa
sukai mota, gaba ta shiga shima haka hakanan saita tuna abinda tayi ranan wani
kunya yakamata tada motan yayi sukadau hanya sai faduwa gabanta yake kaman akwai
abinda zai faru da ita ahaka har bacci ya kwashe ta.



Saida sukai parking a hanya lokacin azahar yatada ta suka shiga wani masallaci kan
hanya dudda na maza ne yasa ta koma chan baya tai salla shima yay nashi agaba sanan
yasaya mata snacks suka koma mota bamata iyaci ba bacci yakara awon gaba da ita.
Horn dataji yasa tabude ido ganin suna kofar gidansu yasa ta gyara zama tana zaro
ido gabanta nafaduwa Gate gateman yabude musu Sameer yaja motar ya shiga da ita
ciki sai kallon motar Abba dayake a pake take sanan yay Parking yafito tareda
kallonta, bude wa tayi tafito ahankali gabanta nafaduwa sosai sanan yafara tafiya
tana biyeda shi, labewa tayi abayanshi yay knocking kofar sitting room dinsu, Zeena
ne tafito tana sanye da atampa da dan kwali bamata lura da Rahima dake labe bayan
Sameer ba dayake yanada tsayi, cikeda girmamawa tace "ina yini ya Sameer, Abba na
nan amma Mummy taje sunan wata kawarta a Suleja gobe zata dawo...." "wa kika cikada
surutu haka Zeenah" cewan Abba dake zaune a falo, da sauri Zeenah ta matsa tace
"Abba Ya Sameer ne yazo abokin ka" da sauri Abba ya kalli kofan ganin Sameer yasa
wani sahihin murmushi ya bayyana a fuskanshi yace "Lieutenant, bismillah, son
shigo" ahankali Sameer yadaga kafa ya shiga dajin da murmushi kan fuskan shi hakan
yabama Abba dasu Siddiqa daman ganin Rahima dake tsaye bakin kofan takasa shigowa
kanta akasa sai rawa kafafuwanta suke sabida muryan Abba dataji, wani irin mikewa
Abba yayi tsaye idanunshi kan Rahima saikuma ya kalli Sameer yace "are you together
with this girl?" gyadamai kai Sameer yayi yace "Abba ka zauna is a long story"
cikin fushi Abba na danne zuciyarshi yace "wani irin long story Sameer?" ganin
yanda Abba ya harzuka he is not even ready yazauna and listen to him yasa yace
"Abba sarkin garin dakakai yarinyar nan tried to molest her, he tried rape her, and
she called naje and rescued her" cikin wani irin fushi Abba yace "try to rape her?"
gyadamai kai Sameer yayi, dan shiru Abba yayi saiyadan yi murmushi kaman wanda
yazare, kafin cikin wani irin masifa yace "finally tasami mashinshini" saikuma yay
shiru kafin ahankali yafara walking hdown zuwa bakin kofan dakin inda Rahima take
tsaye, sauka yayi duk su Sameer na kallonshi sun zaci magana zai mata kawai gani
sukayi ya dauketa da mahaukacin mari yace "dan uwaki yau dinan ba gobeba komi dare
aurar dake zanyi badai shaye shaye kika saka agaba ba zakiga hukuncin shaye shaye
ya fizgi hannunta da sauri Sameer yafito kafin yafito Abba harya kaita motan shi
yabude baya yajefata ciki ya rufe Sameer yagani, hannu Abba yadagama Sameer da
zaiyi magana yace "quit son" Siddiqa data iso wajen da sauri tace "Abba dan Allah
kaya...." shiga motan yayi ko kallonta baiyi ba ya danna uban horn, gateman yabude
mai yafita.[6/30, 10:16 AM] Marsy😘: 53.....




Dafe goshi cikin masifan fushi Sameer yayi ya shiga motarshi kafin gateman yarufe
yafice yabi Abban dayaga motarshi yamai nisa danhar yahau kan titi, sosai Rahima ke
kuka tace "Abba dan darajan iyayen ka karka maidani kauyen nan, Abba dan Allah,
wayyo Mummy na" ko sauraronta Abba baiyiba ranshi tafarfasa kawai yake duk in
yatuna shaye shaye Rahima keyi sai yaji he can go to any limit to discipline her,
dawani mahaukacin gudu Sameer ke binshi saida sukai nisa sosai saida Sameer yaga
babu motoci sosai a express road din dudda yasan wat he is about to do is risky
sanan yay wani irin over taking Abba kafin yay kwana yasha gabanshi motar Abba dat
was on high speed yataka wani mummunan birki da saida Rahima ta kwala ihu dan
tazaci mutuwan tazo kiris yarage baufi tsayin finger ba da motar Abba tadaki ta
Sameer, Sameer bai damuba yabude motar yafito shima Abba ya kashe motar yafito yayo
kan Sameer cikin fushi yace "so kake na kashe ka Son?" Sameer baimabi takan
tambayan da Abba kemai ba cikin fushi yace "where are you taking Rahima to?" sosai
zuciyar Abba ke tafarfasa yay pointing motarshi yace "Sameer that girl Rahima shaye
shaye take, babu namijin kwarai dazai yarda ya aureta tariga tama rayuwanta illa,
Sameer inhar Rahima tasami wani dake kokarin mata fiyade alamun sonta yake kenan,
tunda dai sarkin musulmi ne kuma magidanci zan maidata kauyen, nace mai ni mahaifin
tane he don't have to rape her gani nan nakawo ta nabashi aurenta ko karfe nawan
dare nakai gombe saina daurama that stubborn girl aure da sarkin nan" Abba yay
maganan yana kumfan baki kaman baisan meyakeyi ba, dawasu red eyes Sameer ya kalli
Abba yace "Abba kariga kace am your son, kabani amanan not just Rahima your last
daughter but your whole entire family, and you call Siddiqa, Lubabat, Zeenat and
Rahima my sisters, as a Son, kasan Son can stand up to mahaifan su su nuna musu
sunyi kuskure, Abba you are blind today, ka makance da fushi da anger, children
smoke children take illicit drugs but this you are doing will push them suyi drugs
din more" yy shiru sanan ya kalli Abban dake kallonshi babu ko tsoro yace "there's
no way am going to allow you marry this gurl off to a rapist, kasan hukuncin
mutumin nan kuwa, metayi? Wani laifi tayi dazaisa kamata wanan hukuncin dat will
affect her life forever, just because of shaye shaye? Eh? Eh" yay ma Abba ihu cikin
fushi kafin yakama hannun Abba yadaura kan saman kanshi yana kallon Abba a ido yace
"Listen Abba! I Lieutenant Sameer Simran swear to you I will marry her, tunda dai
aurar da ita kakeso kayi zan auri Rahima Abba, just give me from now zuwa anjima, I
will meet my parents da zancen meanwhile I take her back to rehab centre, anjima
around isha'i nida da yan uwana zamuzo muje masallaci ka daura min aure da ita, you
will see how I will change the Rahima dakake kokarin wulakanta rayuwanta ayau
sabida tana shaye shaye to Rahima da tadena shan komi tadawo that dream daughter da
u always picture Rahima to be, and I swear to you, swear to you, wlh, wlh baxaka
taba aurar da kanwata to that man ba, you are a judge kafin kowa sanin hukuncin shi
amatsayin na mutumin dake raping underage, that pervert of a man, a pedophile but u
are too blind da fushi yahanaka gani kana kokarin bama yarka auren shi, as am
talking to you now that man is under hot hot interrogation while the whole village
government have evacuated them, babu kowa on that village, yaran dayama ciki sama
da 15 are under serious check ups, you can check the news channels television news
sun dau rahoton komi and see the work of the man u are trying to get your daughter
married to, dats all am going to tell u" yawuce shi cikin fushi yaje wajen motan
Abban yabude back sit Rahima yagani takife kanta kan cinya kuka take kaman zata
shide, hannu yasa yadagata yakamaa hannunta yarike yafito da ita daga motar sukazo
suka wuce tagaban Abba taba kuka sosai yabude motarshi yasata ciki ya shiga
mazaunin direba yaja motar yay kwana yabar wajen a zuciya batare daya kalli Abba
ba.
[6/30, 10:16 AM] Marsy😘: 54 & 55



Abba yadade tsaye kan titin nan ko motsin kirki yakasa kalaman Sameer kaman sunyi
resetting brain dinshi, he can't believe what he just heard, uban horn da ake
dannamai ana Malam lafiya sabida yanda ya kashe mota yafito shikadai ya tsaya kan
titi tareda rungume ciki kaman wanda yasoma zarewa, horn din suka dawo dashi daidai
hakan yasa yajuya da sauri yay cikin mota ya kunna yabi u turn yakoma gida haryaje
gida yaran namai magana kasa amsasu yayi sai dakinshi kawai yawuce yarufe tareda
zama, ko Allah yasan yana cikin wani farin ciki da mugun mamaki ne abu biyu atare,
Sameer, Sameer this well mannered yaro, baligi dakeda cikakken hankali, da yasan
yakamata, yakeda aikinyi, wanan babban mutum dinne zai auri Rahima yasake tambayan
kanshi heart dinshi na racing, saikuma yace "ahhh haladai kawai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login