Showing 1 words to 3000 words out of 197960 words
[6/3, 9:39 AM] Marsy๐: ๐ซ *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*๐ซ
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always๐
_โ๐ฟ
M Shakur_
_Bismillahil Rahmanir Raheem, da Sunan Allah Mai Rahama, Mai Jinkai_
_This Novel is solely work of fiction, banyi dacin zarafin wani ko wataba, dafatan
zan nishadantar daku_
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
_What is drugs?_
_What are illicit drugs?_
_mesa people do drugs?_
_What do they feel when they do it?_
_why why why shaye shaye?_
_Oh Hey VIPs dina๐๐ผ ever been curious about this questions? Well this novel will
walk you through everything dangane da shaye shaye, overcoming it and many many
more ku gyara zama a kakkabe zani_
1๏ธโฃ
Horn da akayi yasa mai gadi yafito da saurinshi daga dakinshi that is just beside
the gate ya zare sakatan gate din ya wangale gate din sabida motar ta shigo,
wangale gate din da akayi yasa wata yar budurwa da bazata wuce 25-26yrs ba da wani
matashi ke zaune gefenta kan plastic chair yana sanye da bugaggiyar shadda milk duk
suka dago kansu suna kallon Gate din ganin wanda zai shigo ciki da alamun tadi
sukeyi abunsu dan kowannen su na dauke da murmushi kan fuskarshi, motar gidansune
ta shigo har zuwa inda ake parking motar yay parking, bude bayan motar akayi wata
yarinya fara dake sanye da jean da t-shirt ne tafito ta tsaya tana turo baki tai
kini kini da rai, white flat shoe ne na vine a yar karaman kafarta da dududu size
dinta bazai wuce 37 ba yar kafar, sai pencil jean din jikinta daya tsaya mata a
daidai idon sahu, kafarta na haggu sanye dawani hadadden leg chain daya kama yar
faran wrist din kafan nata, yama kafan nata kyau sosai bana wasaba dan silver color
ne, ba karamin kamata sky blue Jean din chinos din yayiba batada wani girman ass
but is a lil bit bumpy saidai tanada wani mahaukacin hips curve, irin matan da ake
cema cylinder shape kenan, wani white non logo t-shirt ne ajikinta yadin so soft
fari kal babu ko single stain ajikin rigan, tasaka wani simple necklace mai hawa
uku masu dauke da pendent din moon shape wanda the last one ya sauko har kasan
wajen gab da cikinta suna walkiya, babu komi kan fuskarta batasa makeup ba, dan
ficicin pink lips dinta sun bushe sosai sai manyan idanunta da kwayan idanun kenan
mai ruwan toka ko kadan ba bakake bane, tanada cikan gira baki, sai dan karamin sky
blue dan gyalen data yane kanta dashi da ana ganin almost rabin kitson ta yan fici
fici kalaba masu kyau sosa, wrist dinta na haggu sanye da digital watch sai dayan
wrist din tadaura wani fine simple bracelet daya karama little tiny hand din nata
kyau, ko kadan bata da girman jiki, batada wani tsayin kirki badai gajera bace,
sanan batada kiba kawai she is super portable, bata da girma kuma baxaka kirata
karama ba. Kallon direban daya bude kofa yafito tayi bayan ya kashe motar, turo
baki tayi tareda hararanshi cikeda tsiwa tace "kai Isa bazaka bani jakana ba
ninagaji da tsayuwa" da sauri Isa direba yazo wurin cikeda girmamawa yace "sorry
Autan Mummy, dan gyara na dauko miki to" matsawa gefe tayi tana kwafa tareda kama
waist dinta da hannu daya tana jiranshi yadauko mata jakan ya bata, wani bagpack
yadauko mata irin na yan matan nan da yan makaranta ke amfani dashi da ake goyawa
abaya fari ya mikamata yana murmushi yace "yauwa to ungo gashinan nadauko miki
Auta" hannu tasa ta fizge jakan kaman ana fada sanan tajuya ta tafara tafiya tana
fita daga parking tent din tai cikin yard dinsu, das das take tafiya kaman bataso
tayi hips dinta na juyawa gashi jean ne ajikinta abin looks so alluring to the
eyes, tundaga nesa take ballama Ya Siddiqa dake kallonta cikeda takaicin ta harara,
saida takaraso wajen taja wani mugun tsaki tace "bashi ko tara eh? Anwani kafe
mutun da idanu kaman za'a tsotsemai jinin jiki, sa'ido dai sana'ar banza ne" tai
wani fari da ido tai gaba abinta batare data gaida koda mutumin dake gefen Siddiqa
ba, azuciye Siddiqa ta tashi daga kan kujeran zata bita da sauri Sadiq yarike mata
hannu yace "me haka ina zaki? Ki barta yarinya ce bakigani ba" cikin fushi Siddiqa
ta fizge hannunta tace "Baby wlh duk rashin kunyan ta tai dani ni kadai bazan ma
tanka taba, amma tsabagen rashin kunya ta kallemu taja tsaki sanan tacemana
sa'idawa, that's an insult wlh saina fasa mata baki yau agidan nan" kafin yamayi
magana ta fizge hannunta tai ciki tsabagen yanda kirjinta ke zafi yana tafarfasa
sabida yanda Auta tamasu itada Sadiq rashin kunya haba mana, agaban wanda zata aura
zata disgata.
Bude kofar falon nasu tayi ta shiga daidai Auta dake shirin shiga corridor ta waigo
jin anbude kofan, harara ta balla mata cikin murya kasa kasa tace "mayyar tabiyoni"
dawani irin gudu Siddiqa tanufota dan taji metace wato itace mayya, ganin Siddiqa
tabiyota da gudu yasa ta yunkura zata gudu amma ina Siddiqa tariga ta chapke bayan
riganta ta fizgota azuciye ta bugata da bangon corridor cikin fushi tace "uban waye
sa'idawa? Su waye zasu shanye miki jini sanan wakike cema mayya?" zaro idanu tayi
cikeda rashin kunya tana kokarin ture hannun Siddiqa data chakumo gaban white t-
shirt dinta tace "me haka? Kika batamin white rigana wlh saikin wanke shi, ki
sakeni nace ko" bude kofar wani daki dake corridor akayi wasu yan mata guda biyu
suka fito duk sunfi Autan girma alamun yayyunta ne suma dake kama da Siddiqa sosai,
black beauty dasu, daya daga cikinsu wacce daga gani ita kebin Siddiqa tace "yauwa
Ya Siddiqa cimana uban mara kunyan shegiya mai idanun mazuru" cikeda tsiwa tana
kokarin ture hannun Siddiqa ta kwace kanta tace "eh kekuma mai idanun gapiya,
gapiyan ma maicin kashi" dariya tayi sosai tace "eh gwaradai gapiya maicin kashi da
mazuru mai satan kaji, kinji Ya Siddiqa lallasata dama atike nake da ita" bude wani
kofa akayi dake facing corridor alamun dakin shine kodai master bedroom kokuma
dakin wani babba agidan ne, wata matace baka itama Siddiqa na kama da ita sosai ta
fito da akalla zatai shekara hamsin da hudu 54, dattijuwa ce amman jikinta nada
kyau sosai tana sanye da doguwan rigan atampa da aka mata stone work hayaniyan
dataji yasa tafito agurguje daga bayi dan tun dazu tana bayi ganin yanda Siddiqa ta
chakume Auta yasa da sauri tajawo kofar dakin tanama Siddiqa wani irin mugun kallo
tace "me haka kika chakume auta kasheta zakiyi?" cikeda fada dajin haushi Siddiqa
tace "Mummy wai yarinyar nan nida Ya Sadiq zata kalla tacema sa'idawa, sanan wai
zamu shanye mata jini, kuma wai ni take cema mayy......" da sauri Auta ta chabe
maganar cikin muryanta mai zaki da dadi kaman zatai kuka tace "Mummy karya take
mini, aini bance hakaba, sune keta kallona kuma sai hararana Ya Siddiqa takeyi fa,
ni banmata komiba daga dawowa na" kafin Mummy tai magana Siddiqa ta bugata da bango
tana jijjigata tace "dan ubanki nike miki karya, bakida kunya ko sabida kinga kinyi
girma kema kin fara nono" cikeda jin dadi Lubabatu Mai bin Siddiqa tace "yauwa Ya
Siddiqa ki gurje shegen bakin datake mana rashin kunya dashi abango, shegen bakin
kaman tsuliyan kaza" harara Auta data fara kuka ta watsama Lubabatun tafashe da
kuka tace "muguwa kawai, agulmawiya, ai nadai fiki nonon kumadai, da fuska ki kaman
burnt abinci" yowa wajen Lubabatu tayi cikin son ta jibgeta tace "dani kike?"
Lubabatu tai wajen ta daga hannu zata sharara mata mari Mummy ta daka musu tsawa.
"Siddiqa! Luba!" duk dagokai sukayi suka kalleta, harara Mummy ta zuba musu tama
Siddiqa dahar lokacin ke chakume da Auta tace "cikamini yarinya kafin na mugun
sabamiki" sakinta ahankali Siddiqa tayi da sauri Auta tai wajen Mummy tafada
jikinta tasaki kuka, cikin kuka tace "Mummy kinga Ya Siddiqa ta shakemin wuya
kasheni takeso tayi, Mummy kice mata karta karacemin nafara nono banso" tafashe da
kuka sosai, ta tsani insuna fada suce mata sabida tafara nono ne kaman su take musu
ranshin kunya ta tsani maganan, shafa bayanta Mummy tayi cikeda lallashi tace "zan
musu magana, ta Allah batasu ba kinji, je wuce dakinki kiyi wanka zan kawomiki
abincin ki yanzun nan" gyadama Mummy kai tayi tasa hannu tana share hawaye tawuce
sumi sumi sanan ta juyo ta kalli yanda suka tsaya charko charko suna kallonta wani
matsiyacin murmushi tayi irin na neman tsokanan nan sanan tama Siddiqa da Luba
gwalo, da sauri Luba tace "Mummy kinga tana mana gwalo ko" da sauri Auta tabude
kofar dakinta ta shiga, kwafa Luba tayi cikin konkoni tace "wlh gamuwata dake
bazatai kyauba, nakama yarinya wlh sainai mata jina jina saidai duk abinda za'amin
amin" cikeda fushi Mummy tace "mafashi, inbaki daketa ba kin raina Allahan daya
hallice ki, shegiyar yarinya yar bala'i kawai, da katon kanta kaman na giginya"
bude kofa Luba tayi ta shiga tana magana ciki ciki tana kunkuni tace "badai kaina
ba kan autanki dai" daga murya Mummy tayi tace "me kikace dan ubanki?" turo baki
tayi da kyar tace "aini badake nike ba" "kimayi kiga in ban zubar miki da hakora ba
da ranan nan" Mummy tafada tana huci, tabe baki Zeenatu da tuntuni tana tsaye tana
kallon draman batare datace musu komi ba tayi tajuya zata shiga dakin da sauri
Mummy tace "zonan Zeenah" juyowa tayi tama Maman tasu kallon haushi tace "gani
Mummy" binta Mummy tayi da kallo daga sama har kasa tace "nasan duk yayana kece
slow poison, wanan dabakice uppan ba Allah kadai yasan me kike hadawa aranki, wlh
ko kurjewa naga Auta tayi, kurjewa nace to wlh sainaci ubanki, wuce kije kitchen
kihado mata abincinta kikaimata taci" hararan kofar dakin da Autan ke ciki tayi
tajuya tai hanyar fita daga Corridor, kallon Siddiqa dahar lokacin ke tsaye
idanunta sun cika da kwalla tap tsabagen yanda abinda Mummy tayi ya bakanta mata
rai tayi, yarinya tazo tamata rashin kunya sanan tama wanda zata aura Ya Sadiq
rashin kunya dudda haka Mummy batace komiba, murmushi Mummy tayi ta taho wajen kama
hannun Siddiqa tayi suka fita daga corridor sukai falo cikeda lallashi tace "ya isa
to kekuma, bakomi Auta zatayi kudingajin haushinta ba, yarinya ce, dududu guda nawa
take aduniya eh? Daga ke har Sadiq din ai duk yayyinta ne? Yakuri kinji zan mata
magana zata dena, wuce ki koma wajen Sadiq kinbarshi shi kadai, kuma ki saki ranki
karya ganki duk wani iri yagane akwai matsala, nunama saurayi ake kana tsananin son
dan uwanka, tashi kitafi" tashi Siddiqa tayi tawuce tafita daga dakin deep down
bata hakura ba tai alkawarin saitaci uban Auta wlh.
Fitowa da Zeenatu tai daga kitchen rikeda plate da jellof rice kekai dayaji fried
plantain akai yasa Mummy tace "ahaka zaki kaimata abincin kaman zaki kaima awaki?
My friend go back to that kitchen ki daura abincin nan kan tray, ki dauko mango
juice din dana hadamata kidaura akai da glass cup, ki kuma samata salad ki sako
mata nama guda biyar kinsan tanason nama" juyawa Zeenatu tayi tana kunkuni tace
"saikace president zan kaima abinci" kasan cewan Mummy bataji taba yasa ta gyara
zama tacigaba da kallon datake yi, jin Zeenatu tasake fitowa yasa tadago kai ganin
tayi yanda tace yasa tace "kuma wlh ko kallon banza kika mata sainaci ubanki, kina
bata abincin kifito kinajina ko banso adameta bacci zatayi" gyadamata kai tayi tai
corridor.
Bude kofar dakin Zeenatu tayi babu kowa adakin saidai karan saukan ruwa dataji
alamun tana wanka, dakin fess fess sai kamshi yake, fentin dakin off white ne sai
dan gadonta dakeda girma normal normal an shimfida bargo mustard, curtains dinta
kuma combination of white and Mustard kana shiga dakin zaka gane mai dakin nason
this two colors white da mustard, karasawa ciki Zeenatu tayi tana kallon cookie
jar dake kan bedside drawer ta dako rabi basuyiba, suma sunada cookie din dan Mummy
ke ijiye musu adaki yara sudan sami kayan kwalama but su harsun cinye nasu dayake
su ukune da ita sai Ya Luba, da Ya Siddiqa, itako Auta dakinta ita kadai dudda ma
tsabagen rigima da fadan dasuke yi ne yasa Mummy taraba musu daki but dudda haka
shegiyar bata iya kwana ita kadai dakin kawai zamanta ciki da ranane kawai dare
nayi takeyin dakin Mummy, Mummy ma saitai bacci take iya sneaking out ta tafi dakin
babansu in yana garin in kuma bayanan to tare suke kwana, ajiye mata abincin tayi
akan gado daidai lokacin tabudo kofan bayin tafito daure da mustard towel dinta
akirji daya saukan mata iya cinya tana kallon Zeenah data ijiye mata abinci tana
turo baki takaraso ciki tana hararan ta tace "me kikemin adakina dakin kine eh,
kifita kona hadaki da Mummy wlh" hararanta Zeenah tayi saikuma tai murmushi cikin
lallabawa ta kalli jar din cookies din tace "auta indan dibi cookies dinki?" wani
kallo auta tamata saikuma ta balla mata harara ta zauna kan gado abinta tareda
daukan tray din tadaura kan cinya zata faraci, ahankali Zeenatu ta zauna kusada ita
murya chan kasa irin muryan begi begi dinan tace "haba yar kanwata Rahima naaa,
indan dauka, 2 kadai zan dauka namufa yakare ne please" turo baki tayi ta make mata
kafada ashgawbe tace "ba bakusona ba Mummy kadaine ke sona agidan nan, kuyita sa
Dady namin fada, jiya saida kikaja Dady yasani nai wanke wanke bansan wani gulma
kikamai ba, bazan bayarba" da sauri Zeenatu tadaura hannunta kan kafadarta aranta
cewa take "shegiya mai shegen kafiya wacce bata mantuwa kawai, zaki gane kurinki ne
yau" cikin sigan lallashi tawani jawota jikinta tace "kai, Allahu Rahima, to
kiyakuri bazan karafadamai ba kinji Autan mu, yakuri, in dauka eh Autan Mummy da
Daddy mu" wani irin murmushi tayi cikedajin dadi ta gyadamata kai tana gyara zama
tace "dauki 10 nabaki duka" tashi Zeenatu tayi da sauri cikeda jin dadi tai wurin
jar din tace "thank you Rims Auta" tadebi cookies din tai hanyar fita daga dakin
sanan ta juyo ta kalleta ganin bata faracin abincin ba tana kallon abincin tace
"kici abincin mana" yatsine fuska tayi ta dago kanta ta kalli Zeenatu tace "Ya
Zeenah the food smell peprish wlh" aran Zeenah tace "mayya, ba Ya Zeenah ba ko Anty
Zeenah zakice min bazanji tausayin ki ba, kinsaba kirana ai gasai, hancinta kaman
na aljanna hartaji kamshin yajin" murmushi tayi tace "common ai Mummy bata bari asa
yaji tasan bakison yaji, ci babu yaji ko kadan, natafi" gyadamata kai tayi tadebo
rice din takai baki, maida kofar Zeenah tayi tarufe bayan tafito takafa kunnenta
jikin kofar tana murmushi kaman an mata kyautan makka ba'a banza Mummy ke cemata
kunama slow poison ba saitayi baxaka taba cewa ita bace ko zata iyaba, su Siddiqa
da Luba biyemata suke suyita hauka tana haukata su, itako cin ubanta take ta
karkashi.
Ahankali take tauna shinkafan dan bata iyacin abinci da sauri sauri ba, wani irin
masifan yaji dataji waaaa abakinta kaman an nika attarugu buhu daya a abinci yasa
tafeso abincin waje furururr da gudu, da sauri tadau mango juice din dake kan tray
din ta kwankwade tana nishi da sauri da sauri, ajiye cup din tayi ganin batadena
jin yajin ba yasa ta shiga hurama bakinta iska tawani irin zabura ta mike tray da
abincin duka suka kifo kasa tana nishi fast fast, idan akwai one thing da her whole
body baya iya tolerating in this life is pepper, wani irin ihu takurma tareda
fashewa da kuka tana kiran Mummy hakan yasa Zeenah ta kwasa da gudu tana dariya tai
dakinsu ranta fess, tai maganin mara kunyan.
[6/3, 9:40 AM] Marsy๐: ๐ซ *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*๐ซ
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always ๐
โ๐ฟ_ M Shakur_
2๏ธโฃ
Bude kofan dakinsu da gudu tayi ta shiga tasaka sakata da sauri Lubabatu dake
kwance tana danne dannen awaya tace "kekuma dawa zaki shigowa mutane daki da gudu
haka?" hannu Zeenah tasa abaki alamun tai shiru kar Mummy tajisu hakan yasa
Lubabatu tai shiru tana kallonta, ihun auta dukansu sukaji ta kwalama Mummy su kira
tana kuka sosai atare dukansu suka fashe da dariya Lubabatu ta taso daga kan gadon
da sauri tazo wajen da Zeenah ke tsaye tana dariya tace "me kika mata makira eh?"
wani irin murmushi Zeenah tayi kafin tace "wanan Black Cameroon pepper dinan na
container na juyemata duka a abincin aiko taci shine take kukan nan gobema takara
zama bayan tasan hanyan kitchen asa nakai mata abinci saina samata wanda yafi
wanan" takara kwashewa dawani dariyan, shiru Lubabatu tayi tana kallonta cikin jin
haushi tace "haba Zeenah ai duka kuma yay yawa kema kinsan koni bana iyacin Black
pepper nan fadanshi yay yawa balle ita dabama tason yaji ko kadan inda tata ta
za'abi da karma ai girki da attarugu just tomato and onion, inama laifin 1 spoon
koshi ya isa yakoya mata lesson kika juye duka kinsan awa nawa zatayi tanajin yajin
kuwa?" maganan Luba yasa Zeenah itama duk taji wani irin badadi zatayi magana
sukaji muryan Mummy tana ihu tace "wlh, wlh kashekine kawai bazanyi ba yau Zeenatu
inna kama ki, muje Auta" takama hannun Autan dake kuka sosai tabude dakinta suka
shiga ciki dakine hadadden gaske komi tsaf yana kamshin turaren wuta, zaunar da ita
tayi akan gado tace "zauna ina zuwa bari na kawo miki gishiri da ruwa yajin zai
tafi stop crying" gyadama Mummy kai tayi tana hura baki tana kuka Mummy tajuya
tafita da sauri daga dakin tai kitchen dinsu taje ta dauko salt da ruwa a fridge
tahado mata da yogurt tadawo, gishiri da ruwa tabata da sauri ta karba tasha sosai
tana kuka idanunta sunyi ja kaman wacce akama shegen duka, karban goran ruwan Mummy
tayi ganin tana neman shanye duka ta ijiye tace "ya isa kekuma zaki fasa cikinki da
ruwane? Karbi yogurt dinan kisha yajin zai tafi duka I promise" karban yogurt din
tayi tana sauke ajiyan zuciyan kuka ta shiga sha itakuma Mummy ta juya ta ijiye
ruwan kan side drawer gadon sanan tadawo ta zauna gefenta akan gadon, ahankali
Rahima ta janye Yogurt din daga bakinta ta ijiye tawani matso jikin Mummy tadaura
fuskarta kan kafadan Mummy tai lamo jikinta nadan bari, cikin wani irin murya na
mugun shagwaba tace "Mummy kibani abun please, yau baki baniba at all, am feeling
hungry" daga kanta Mummy tayi da sauri daga kan kafadarta tana kallon yanda tayi
kaman mara lapiya tace "kindai san babanku na garin nan ko, kuma kinsan baya bacci
batare daya ganku dukaba, ki rufamin asiri kibari yay tafiya yacemin kwana uku
zaiyi, gobe ko jibi zai tafi kibari inya tafi saina baki kinji" fashewa da kuka
tayi sosai tana makema Mummy kafada tana goge hawaye da bayan hannunta, dan tsaki
Mummy tayi cikeda gajiya da shegen rigiman banzan Rahima tace "ohh My God, Ke wlh
kincika matsala Auta, nace kibari babanki yatafi ko kin wagemin baki kina kuka"
kara kara karfin kukan nata tayi tana kallon Mummy tana ihu da sauri Mummy tace "to
naji yishiru, yishiru lemme think, ki bari nai tunani to" shiru tayi tana sauke
ajiyan zuciya tana kallon Mummy nata, hannu Mummy ta daura kan goshi tana tunani,
kafin chan tabude ido ta kalleta murmushi ta sakinmata tace "shikenan to naji zan
baki but saida daddare, kinga anama kiran sallan la'asar yanzu any moment from now
babanku zai shigo,