Showing 63001 words to 66000 words out of 197960 words
yanda yama Siddiqa maganan saida gabanta yafadi da
sauri suka matsamai yay wurin motarshi yabude boot ya wurga jakan ciki sanan yarufe
yakoma gaba yabude motar ya kunna dantai warming sanan yadawo inda Rahima take
tsugunne tai fitsari tana wasa dashi yazo wajen hannunta yakama ya finciketa ta
mike tsaye tace "leave me Abba, bacci nakeji" ko takanta baibiba yajata ya wurgata
a bayan mota saida kanta yabuge yamaida kofan yarufe, yakoma gaba ya shiga yatada
motar gateman yabude mai yafita batare daya lura da motan su Shagali dake gaban
gidansu kadan ba, wani irin fanfala uban gudu yake akan titi, ikon Allah ne kawai
ke tafiya dashi saida yawuce zuba tawajejen hanyar Suleja ya tsaya awani babban
farm house dinshi ya kashe motar ya fito ya shiga Rahima na cikin motar tana yaren
da baiji, shiga cikin gidan yayi babban gidan gona ne dake daukeda bishiyoyi kala
kala, ana kewan kifi da kaji masu kyau ciki, daga Gate ya tsaya ya shiga kwalama
wani mutumi dake cikin dakin kaji kira cikin fushi. "Habu, Habu, Habu" da sauri
wani dan mutumin dake cikin dakin kaji yana dubasu yajuyo jin ana kirashi ganin
Abba yasa yafito da sauri yakaraso gaban Abba ya tsugunna cikeda girmamawa cikin
hausan shi da bata fita da kyau tafi kaman da fulatanci yace "barka da zuwa Alhaji"
cikin kunan rai Abba yace "Habu kataba bani labarin garinku dakace mini kauyen
kayayau ne ko gwamnati batasan da itaba hakane?" gyadama Abba kai Habu yayi yace
"kauyenmu asalin kauye ne aradu, ba wuta ba ruwa, ba waya, arafi muke wanka muyi
wanki, adaji muke zuwa muyi bahaya, yawancin yan garinmu bama susan da akwai wani
abu wai binni ba, wayanda kuma sukasan da binnin tsoron zuwa sukeyi wai cinye
mutane kukeyi anan binni, konima wanan kaddaran nanne yafito dani daga garin dahar
yau bansan akwai binni ba, sanan mutanen binnin nada kirki" ahankali Abba yace
"gud, matarka nachan ko da yaranka guda tara daka fadamin?" da sauri ya gyadamai
kai yace "I, duk suna chan taki yarda tadawo binni wai tanaso ku mutuwa ya kamata
ta mutu a inda aka yanke mata cibiya, kudi albashina nakan raba biyu nakai mata
rabi, tana saida su gyada dafaffiya, mascara, sanan baban d'ana jauro mun sayamai
shanu ahirin da biyar yana kiwansu muna sayar da hura da nono a kauyen mu" gyadakai
Abba yayi cikeda gamsuwa da bayanin shi yace "Habu kasan mesa nakemaka tambaya kan
garinku yau?" da sauri Habu ya girgiza kai, Abba yace "kasan shaye shaye?" da sauri
Habu ya gyadakai yace "nasani ba giya ba ahai ai tatil aita hauka ana layi akan
hanya" gyadakai Abba yayi cikin wani irin bakin ciki yace "to Habu y'ata na shaye
shaye, an kaita wurin magani tagudu, sonake kazo kashiga motar nan ka kaini garinku
inaso nabama matarka rikon y'ata, inaso nakaita kauye, inda bazata tataba samun
access to shaye shaye bane, bazata ga inda zata sayo abubuwan shaye shaye ba, danko
namaidata Rehabilitation centre sake gudowa zatayi dan tariga tasan hanyan guduwa,
kauyenku kauyen kayayau ne kuma irin wajen nake son mata harsai tayi wata ni
shiddan nan tabar shaye shayen, tahakura dan kanta sanan zan koma na dauko ta,
Rahima needs iron hand tana bukatan abu haka, by the time tai rayuwa irin wacce
bata saba da itaba hankali zai shigeta dan kanta, zata gane gata ake mata a rehab
datake samun gado ta kwana, tasamu shawa tai wanka, lokacin dataga batada wani
option dayarage ta shiga rapi tai wanka, kokuma tasha ruwan rapi, kokuma ta kwanta
tai bacci akan gadon kara ko kasa, tasha nono tai hamdala ta goge baki, tai
kwadayin shaye shaye ta nemi inda zata samu tarasa, tai kewanmu takasa ganinmu wlh
zata natsu, I believe tahakane kadai Rahima zata natsu tabar wanan mugun dabi'an na
tir" da sauri Habu ya kalli Abba gabanshi nafaduwa dim dim yace "tooofah, saidai
wani hanzari ba gudu ba garinmu akwai wani......." da sauri Abba yatare shi yace
"zaka rikemin y'a ko ba zakayi ba na nemi wani wajen Habu?" Abba yay maganan cikin
bacin rai, da sauri cikin kuma damuwa sosai Habu yace "zanyi wlh Alhaji, kaida
kamin komi karufamini asiri, kabani ci, sha, tufafi da abin kwashewa na gagara maka
wanan, wlh zanyi wlh" "gud rufo gidan mutafi banson jin wata magana" komawa yayi
ciki da sauri yadauko key yafito yarufe gidan sanan yazo gaban mota Abba yabudemai
ya shiga yarufo kofa Abba yakoma ya shiga motan yana kallon Rahima dake hauka sosai
har lokacin tana wakoki, girgiza kai yayi hawaye yataru a idanunshi da sauri ya
hadiye su yatada motan yaja, koshi kanshi Habu saida yaji tsoron irin gudun da Abba
keyi, tun Rahima na haukanta hartai bacci.
Awa takwas yadauke su suka shigo garin Gombe, Habu nata nunamai hanyar kauyensu,
suka dau wani hanya wacce itace hanyar kauyen, kauye da yadauke su kusan awa biyar
sanan sukakai wani daji, ahankali Habu yace "dole zamu ajiye motan anan Alhaji mu
karasa da kafa dan babu hanyar motar kuma, kauyen mu chan bayan dajin nanne saisa
bama asan damu ba a Nigeria nan" saukowa Abba yayi batare daya damuba Habu ma
yafito boot Abba yabude yaciro akwatinta yabama Habu yace "rike wanan" akai Habu
yadaura sanan Abba yabude baya yajawo kafafun Rahima dake narka uban bacci, kuka
tahauyi cikin Bacci tace "sakeni" kota kanta Abba baiyiba ya kulle motar yarike
hannunta gam yahau janta bacci take dan taki bude ido bin Abba kawai take luuu
kaman zata fadi tsabagen karfin mix din data sha tafiya kawai suke, har dare tamusu
ahanyan nan amma ko darr Abba baiji aranshi ba, sunyi tafiya kusan na awa daya
akafa sanan Abba yafara hango haske hasken fitilu Habu yace "mun iso, ga kararkaran
mu chan" karasawa sukayi dudda darene amma all abubuwan da Abba ke gani shine
bukkoki kusan hamsin ko dari azagaye, baiga ginin gini ba saidai ginin kara dasu
bukkoki, sai gaishe gaishe Habu yake dayan kwararrun mutanen dake waje kafin
yakarasa chan gaba wurin wasu bukka guda biyu da bishiya ke tsakanin su, sallama ya
kwada. "Assalamu Alaykum mutan gidan nanan" daga ciki aka amsa. "muryan wa nikaji
kaman mai gidana" dan dariya Habu yayi saiga wata mata tafito da daurin zanu a kugu
babu riga ajikinta sai wani yaro agwai data rike akan cikinta yanshan dogon nonon
ta dayakai cikin ta tsabagen tsawo dayan kuma yaron na wasadshi da hannu yana
surutu irin na dadin nonon nan da yara keyi, bata da kiba sosai sai tsayi da gashin
kanta data tufke kaman na yar bararoji, an kitse na gefe da gefen gaban kanta guda
biyu jelar gashin har wajen kirjinta, saiga wata yarinya dazata fi Rahima tsayi
itama rikeda fitila tana dagawa tana haska fuskokin su ganin Habu yasa matar da
saka uban tsalle nonon na lilo da sauri dan karamin yaron ya saki nono ya juyo jin
maman shi ta daka uban tsalle yana kalle kalle, matar tace "wayyo Allah na mai gida
kadawo, Mairo kufito ga babban ku yadawo" wasu yarane suka dinga fitowa daga bukkan
Abba ya saukar da kanshi kasa ganin babu riga a jikin matar, dudda baya ganin
fuskokin su da kyau sabida darene bai hanashi ganin yaron dake shan mama ba, tsalle
sukahau yi har wasu mutane suna fitowa daga bukkoki su suna lekowa, ganin haka Habu
yace "bamu asabari muzauna magana zamuyi ba dawowa nayiba" da sauri ta kalli yarta
tace "Mairo dauko as abari babbanku yazauna" da sauri yarinyar ta shiga ciki ba'a
jimaba tafito da asabari ta shimfida Abba na kokarin zaunar da Rahima ta kwanta
tana bude idanunta tana kallon kowa, zama matar tayi takalli yaran dasuke tsaitsaya
suna kallon baban nasu duk maza gabaki daya kansu daya kaman yan shidda ta haifa,
sai wani babba da yake sanye da kayan fulani da tsayinshi daya da Mairo wacce take
itakadai ne mace ayaran, sai wanda ake bama nono shima namiji yakama yara Tara cib
cib, yaran kaman bakwaini, anatse Habu yace "kinga wanan shine Alhajin danake
fadamiki daya bani aiki a binni" da sauri takama baki tace "laaaaa shine baka
gayamin ba ke Mairo kawoma Alhaji fura dan Allah yasha" da sauri Abba batare daya
dago kai ya kalleta ba yace "a'a kibarshi nagode, magana nazo nayi dake dan yanzun
nan zamu koma" da sauri ta gyara zama tace "to to ina jinka" Ahankali Abba yanuna
Rahima dake kwance kusadashi databude idanu tarr tana kallon kowa awurin yace
"nakawo miki y'ata ki rikemin ita na tsawo wata shida ne, kisamata tsaro bana
wasaba, banda haka zan biya ki kinji, sanan zan aiko muku da kayan abinci gobe, dan
Allah zaki rikemin ita?" da sauri tace "Alhaji harda su biya? Nawa zaka biyani to
dan kaga yar bukkan mu tamana kadan nida yara Tara gakuma ta goma ta kawomana, dole
sai....." da sauri Habu yace "Ladi" hannu Abba yadaga mai yace "barta, nawa ake
Gina bukka anan?" ahankali tace "sun karamai kudi da muttala hudu ne yanzu muttala
goma ne wlh wasuma har muttala shadaya suke karba" bandir din yan dubu guda biyu
Abba yaciro yamika mata yace "ga dubu dari biyu agida bukkan na block amuku ginin
sanan sauran kudin ki rike, ki kulamin da ita, gatanan gakuma kayanta intai ba
daidai ba ki gyara mata, amana nabaki ita dan Allah kar wanda yanuna mata hanyar
barin garin nan nasan ko zata shekara bazata taba ganewa ba" rudewa kam Ladi tarude
karshen rudewa ma ganin uban kudaden da Abba yabata kaman a mafarki, dama sune yan
gayun kauyen nan sabida Baban su Safara dake aiki a binni yanzu kuma ga wayan nan
kudin ga yarinyar binni ai bakanta, da sauri tace "wlh, wlh, wlh na dauka zan kula
da yarka na rantse da Allah, amana na dauka halak" ta kalli Habu tace "kagayamai
komi kan kauyen ko?" kafin Habu yay magana Abba yace "ya sanar dani kuma dama irin
kauyen nan nakeso ta zauna aciki, kome yataso ayi badamuwa wlh nan da wata shidda
zanzo na dauketa" murmushi tayi tace "masha Allah, Allah yakusan bamu jika kenan"
murmushi Abba yayi dan baigane hausan nata sosai ba yace "to mun tafi, Habu tashi
mutai" wani irin zabura Rahima tayi ta tashi tsaye tana kallon Abban daya tsaya
yana kallonta tace "Abba ina zaka ka barni anan? Su waye wayan nan?" ko kallonta
Abba baiyiba dan baimaso yay magana da ita tsabagen haushin ta dayakeji yace "Ladi
ariketa karta biyomu muntafi" mikama Safara yaron hannunta matan tayi takama Rahima
gam tarike hakan yasa Rahima ta shiga kokawa da ita amma takasa koda fizge hannunta
dan kashin Ladi yafi na rodi karfi, ganin takasa kwatan kanta yasa ta fashe da kuka
tana kwalama Abba kira. "Abba meyakawo ni nan? Su waye wayan nan? Abba ina zaka ka
barni eh? Ina mummy na Abba? Abba kaima ka tsaneni kaman mamana ko? Ka kaini chan
wani wuri da bansan su ba yauma kasake kawoni wani wuri daban San kowa ba? Abba
waime namuku da babu wanda kesona? Abba katafi ka barni kuma? " Abba yanajin duka
kalamanta dudda sun mugun tabashi amma yadaure ko juyowa baiyiba har suka bace mata
daga gani yanaji tana kuka tana kwalamai kira har suka shiga daji yadena jin kukan
ta.40.
Saida sukaga sun bace bat sanan Ladi tasaketa ta kama hannunta gudun karta gudu
tace "kinga muje daki dare yayi kiyi bacci yarnan" fashewa da kuka Rahima tayi tace
"dalla chan kisaken ni" janta Ladi tayi tai cikin yar bukkan da ita yaran suka
biyosu duk suka shigo ciki, dakin babu komi sai kwanuka da aka jera irin kwanukan
da dinan masu kama da langa tuwo da miya, sai asabari da aka shimfida akasa, sai
buhun simenti da taga lodi lodin kaya aciki kaman kayan sawan sune, dakin zarnin
fitsari, washe baki Ladi tayi ta zaunar da ita kan as abari mai kyau tace "sannu da
zuwa yar binni" ta kalli Mairo data zauna kusada ita tana kallon Rahima kaman zata
hadiyeta tace "kawo ma yar binni fura da nono tasha" make musu kafada Rahima tayi
tace "baza'a sha kazamin fura da nonon ba" da sauri Mairo ta kalleta tace "kika
karama Maman mu rashin kunya saina fasa miki baki aradu" babban namijin ne daya
shigo da akwatin Rahima yana wasa da tayoyin kafan trolley yadago kai ya kalli
Mairo yace "dalla to dake tayi ki wuce kakawo mata furan akace" kwafa Mairo tayi
tai wajen randa shikuma saurayin yataho kusada mamansu ya zauna yana washe mata
hakora yace "mama dan ban wani abu man cikin kudin" hararan shi maman tayi tace "to
sannu tunda ina tsoron kane Maccido, kaga gobe da safiyan Allah Mairo zataje saro
mini gyada da masara, su Tasallah zataga nariga nafita ne wlh, na kece raini, sari
zanyi na kece raini na azo agani, saina siye amfanin gonan tass saidai suzo suna
siya awurina" furan Mairo takawo ta ijiye mata a gabanta Rahima tasa kafa ta shure
furan yazube da sauri Ladi tace "ke yar binni zanci miki kaniya fa, huran kika
zubar, yasin zan batamiki raifa, Ke kauyen nan ba'a haka mai wulakanta abinci
kyalli madam na zuwan mai da daddare wlh barina kiga yanzun nan zaki gansu sunzo,
munada dodanni kala kala, akwai abubuwa agarin nan da inhar zaki kwantar da kanki
muyi zaman lpy zan kareki inkuwa kince a'a barinki zanyi, dama kin ishi ubankine
daga gani yakawo minke riko" hararanta Rahima tayi tana share kwalla kafin tawani
irin kife kanta akan guwiwa tajuya musu baya tana kuka sosai dan bamatason ganinsu,
tagaji dakomi da kowa, tun tanajin su sama sama suna lissafi abubuwan da za'ayi da
kudin gobe har tajisu shiru sunyi bacci, kasa bacci tayi ta tashi ta zauna tana
kallonsu, dukansu chakure akasa adan tsukukun dakin nan sai uban minshari suke
barin ma wanda taji an kira da Maccido dake minshari kaman wata katuwar tirela
nazuwa, Mairo ce abayanta sanye da kayan jikinta tana bacci tana surutai da dafarko
bataji danji tayi kaman tana wani yare. "Wadugaga u'uhm, wayyo, zafi Wadugaga,
kamin rai kaji, Mama!" ta kwala karan dayasa ta tashi zaune a firgice tana waige
waige tana kallon dakin kafin ta juyo ta kalli Rahima dake zaune tana kallonta tana
zaro idanu dan tsoro taji, ajiyan zuciya Mairo tasauke tasa bakin dankwalinta ta
share zufan daya fito a goshinta sanan takara dagakai ta kalli Rahima ganin har
lokacin kallonta Rahima take yasa ta balla mata harara tareda murguda mata baki
tace "naci miki bashine?" watsa mata harara itama Rahima tayi tace "kindai cinma
aljanin daya biyoki amafarki kina ihu kin hana mutane bacci bashi" tsaki Mairo taja
tamika hannu tadauko fitilan zata kashe da sauri Rahima tace "karki kashe tsoro
nakeji" hararanta Mairo tayi tace "fitilan ki ko namu rasai" ta kashe fitilan
takoma ta kwanta tareda kankame jikinta, ahankali Rahima ta kwanta tajuya mata baya
tana kallon bango ta runtse ido sosai hawaye na fitowa daga gefen idanunta, jikinta
ciwo yake, gawani irin tsoron mutanen nan datake ji, banda ma haka kawai wani tsoro
taji tanaji tarasa dalili, haka ta dinga kuka takai kusan rabon dare sai bacci yay
awon gaba da ita.
Wani kara kaman na busa algaita ana bubbuga ganga dataji a kunnenta gakuma karan
kuka dataji tanaji yasa tabude idanunta ahankali cikin bacci batare data juyowa
tana kokarin wassakewa daga baccin, daga chan waje taji ana bubbuga gangan taji
ana fadin. "Wadugaga na jiran Mairo, Mairoo Mairoo Mairo ubangijin ki na jiranki"
sai akai shiru aka cigaba da bubbuga gangan, karan kuka taji sosai da batasan
nawaye ba, sai chan taji muryan matar jiya Ladi tace "kinga Mairo karki jazamin
bala'i kitashi kibisu kutafi daga yau sai gobe fa shikenan yagama kema hankalin ki
ya kwanta, tashi kibusu kinsan dai inhar kika bari gari yawaye kinsan abinda zai
biyo baya, tashi kitafi yar kirki" muryan Mairo taji chan kasa tana sheshekan kuka
tace "Mama dazafi, Mama wai mesa ake mana hakane, yaushe zaku chanza wanan al'adan
eh, mama wlh nagaji yazo akashe ni din" da sauri Ladi tace "wlh, wlh zan fita nace
musu suzo su daukeki, yanda akai abin nan dake haka nima zamanina akayi dani, so
kike amana dariya adinga nunamu agari, ba bakon abu bane kowa yasan da hakan
mahaifinki ma haka, wuce kitafi kinsan zakije yomin sari anjima kinga kina dowawa
dasafe saimuje, wuce kitai" alamun tafiya taji sai taji Ladi tace "yauwa Allah ya
kiyaye sai andawo" bata karajin kukan Mairo ba ko muryanta saidai ajiyan zuciyan
dataji Ladi ta sauke taga an kashe fitila dakin yay duhu, tambaya kanta tayi to ina
aka kai Mairo, su waye masu kidan nan dasuka zo suka dauketa da daren nanne ko
asuba nema yanzu oho. Tabe baki tayi tacigaba da baccin ta.41 & 42
Littafin nan na kudi ne duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa.
_How to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki
turo evidence of payment to watsap number na 07012181461, sainai adding naki a
group din danake posting BIN ABINDA ZUCIYA KESO_
Wani bacci mai nauyine ya kwashe ta, ihun yara da hayaniya daya cika mata kunne, da
kukan yaro yasa tabude idanunta ahankali tana kallon koina, dakin yay haske sosai
sun daga asabarin sama gari yawaye dan har rana tafito, yaran duk suna zazzaune
akasa koko sukesha sai Maccido dake kusada mamarshi rikeda sandar kewo da alamu
yagama shan nashi kokon, Maman su kuma na kokarin lallashin agwai din hannunta
daketa tsandala mata ihu, bin duka yaran dakin tayi da kallo da babu kaya ajikinsu
dakin sai uban zarnin fitsari dayake yi, ahankali ta tashi daga inda take ta mike
tsaye hakan yasa Maccido ya kalleta yace "kin tashi yar binni" dauke kai tayi
tareda ballamai harara tai hanyar kofa zata fita Ladi tace "ke zonan agidanku
uwarki bata koyamiki gaida manya ba" hararanta Rahima tayi tawuce tafita abinta
tana kalle kalle har lokacin tana sanye da kayan uniform din rehab dinan da hulanta
akai, tafiya kawai take tana kalle kallen mutanen garin daga ta wuce wanan bukkan
taga ana dakan fura yara na kuka saita wuce wanan taga ana surfe shinkafa, wanan
bukan ana tasan nonon shanu, duk inda tabi sai an bita da kallo kaman anga aljana,
wani bukkan ma har nunata ake da yatsa ana nunama wasu mutanen ita, tafiya kawai
take gudu gudu sauri sauri Maccido da tuntuni yake biyeda ita dan Ladi tace yabiyo
yaga ina zata ya kwala mata kira yana gudu. "yar binni" juyowa tayi ta ballamai
harara bai damuba ya karaso yana biyeda ita yace "ina zaki? Ko zaki kwana bazaki
taba gane hanyar barin garin nan ba kizo muje gida kiyi karin kumalo" batare data
dena tafiya ba tace "baruwan ka dani karabu dani malam" tabe baki yayi yace "saikin
dawo nidai natafi zan fita da shanaye na, inkin gaji da tafiya zaki koma gida
hanyar nan zaki mike sambal" ko kallonshi batayiba tacigaba da tafiya, tai tafiya
na kusan 30min dan tabaro wajejen bukkukokin, hango wani babban gida datayi shi
kadai ne gidan da aka gina ginin kasa data gani tunda tafito yasa tai wurin gidan
da saurinta, gidane harda kwano da zane zanen irin gidan saurantan nan a jikin
bangon, babu kowa kofar gidan sai babban barandan datake hangowa da bata ganin
mutanen dasuke wajen, ganin taki kaiwa gidan yasa ta kwasa da gudu, har zuwa gaban
gidan tana leke, ganin babu kowa a kofar gidan sai wata