Showing 36001 words to 39000 words out of 197960 words

Chapter 13 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15029

tai hadadden makeup kaman zataje biki
tasa wani nude lipstick tasaka kwalli idanuwanta sukai shegen kyau, tashi tayi
tabude wardrobe dinta wani black dogon riga ta dauko mai hannaye baby pink tasaka
dayake tai shaping rigan ya bala'in mata kyau sanan tadau dankwalin takoma gaban
mirror ta zauna kan kujera tana kokarin daura dan kwalin aka bude kofar dakinta,
dagakai tayi ta kalli kofar, Lubabatu ce itama taci gayu tasa doguwan rigan atampa
ja yay mata kyau sosai, ta yafa jan veil hakan yasa ta ballamata harara tace "baki
iya sallama bane malama" hararanta itama Lubabatu tayi tace "sabida baki koyamin ba
saisa banyiba, kuma malama kifito Dady yace sun iso kowa na falo, stop trying ki
daura gyalen nan akai, better learn how to yafa gyale da shegen kananun kitson
kanta dasukai tsufa" tamata gwalo tasowa tayi cikin fushi tabiyota Lubabatu takwasa
aguje tana dariya tai falo ganin haka yasa tai kwafa takoma daki turare ta dauka ta
fesa sanan ta yafa gyalen akanta tawuce tafita tai kyau kayan daidai ita, daga
Mummy saisu Siddiqa a falon kowa yay kyau Mummy tasaka wata doguwan riga brown irin
na manyan matan nan tai kyau sosai ta yafa mayafi na alfarma, zama tayi kusada
Mummy kaman zatai kuka tace "Mummy kinga Ya Luba tazo har dakina tana neman tsokana
na ko" hannunta Mummy ta shafa tace "yakuri anjima zan mata hukunci, kinga yanzu
bakin Abbam ku sun riga sun iso yafita shigo dasune kiyakuri kinji" gyadamata kai
tayi daidai Dady ya kwada uban sallama, amsashi Mummy tayi ta tashi daga zaunen
datake ganin Chairman mutumin jiyane yazo yasa tace "ahh Chairman kaine, marhaban
dasu lale barka da zuwa" cikida fara'a Chairman yace "barka dai Hajiya, kingafa
haka Allah ke hada zumunci komi da sanadi" dan dariya Mummy tayi tace "hakane,
bismillah ka zauna, a'a kai kadai ne ina dayan?" kafin Chairman yay magana Dady
yace "yana hanya bai dade da tashi daga wajen aiki bane yanzu muka gama waya dashi
yace gashinan zuwa" cikeda fara'a Mummy tace "ayyah to Allah yakawo shi lpy"
Siddiqa ce tafara gaidashi tace "barka da zuwa Abba ina yini" kafin ma ya amsa
sauran suka gaidashi. "ina yini Abba" ahankali Rahima dake gefen Mummy tace "ina
yini" murmushi yayi yace "sannun ku yarana, ya karatu?" atare sukace.
"Alhamdulillah" Abba ya kalla yace "what a nice family you have Masha Allah, Allah
ya rayamana" ahankali Abba yace "Ameen Ameen" Chairman yace "yaranka nakama dakai
sosai wlh, Rahima ce kadai batai kama dakaiba" yanuna Rahima dake gefen dadi dan
itakadai ce fara a yaran as auran duk black beauties ne, murmushi Abba yayi ya
kalli fuskan Rahima yace "Rahima auta" dan dariya sukayi Mummy tace "Alhaji food fa
is ready akawo ne?" da sauri Chairman yace "No no madam abarshi bayan isha'i
lokacin Sameer ya iso, sai ayi komi by then in sha Allah" hira suka cigaba dayi
kafin akira isha'i suka tashi sukai masallaci su Siddiqa kuma sukai dakin dan zuwa
yin salla, wayan Chairman dana dasuka bari akan kujera dan zuwa salla ne ya shiga
ringing, ahankali Rahima tace "Mummy ana kiran wayan abokin Abba" gyadamata kai
Mummy tayi tace "eh" ganin wayartai shiru na Abba yadau ruri yasa Mummy tace "bani
wayan nan Rahima ingani" tashi Rahima tayi tadau wayan takawoma Mummy karba tayi ta
kalli wayan Lieutenant, da sauri tace "ina ganin abokin Baban ku dazaizo ne yakira
wayan Chairman yaji shiru yakira na baban ku, tashi kije kidubo waje Rahima inkinga
bako ki shigo dashi kar abarshi a tsaye" gyadama Mummy kai tayi ta tashi daga kan
kujeran tawuce tafita, slippers dinta dake bakin kofa tasaka tai hanyar Gate tana
turo baki yau ko kadan bata hutaba, ahankali tabude Gate dinsu ta leko wani black
mota Bentley tagani pake akofar gidansu gawani mutun tsaye jikin motar da bata
ganin fuskarshi dan yabata baya fuskarshi na kallon hanya rikeda waya a hannunshi
yana dannawa yana sanye da skyblue shadda bugaggiyar gaske tundaga Gate din
takejin kamshin dayake yi, fitowa tayi daga Gate din gabaki daya ta tsaya daidai
Gate dinsu tadan daga zazzakar muryan ta tace "kaine ke neman Abban mu?" wani irin
juyowa Sameer yayi hannunshi daya sanye cikin aljihun wandonshi daya kuma yana rike
da waya faduwa gabanta yayi sosai dan taga fuskarshi sabida hasken wuta dayazagaye
kofar gidansu, kaman yanda ta zuba mai ido haka ya zuba mata ido, daure fuska tayi
ta dauke kai daga kallonshi sabida yanda yawani cikamata ido tace "me kazo
gidanmu?" daure fuska yayi yace "are you talking to me?" juyawa tayi batare data
kalleshi ba tace "ance kashigo" tabude Gate dinsu ta shiga, ahankali yabiyo bayanta
ya shigo gidan yana kallon yanda take tafiya kaman zata tashi sama har zuwa gaban
flat dinsu ta tsaya ta juyo tareda kallonshi dan tasan inta shiga batare dashiba
Mummy zatace mata ina bakon, kallonshi tayi yanda yake tafiya daidai hannunshi har
lokacin a cikin aljihu dayan kuma yana daddanna waya yana tafiya ahankali,
ashagwabe kaman zatai kuka dan ta gaji bacci kawai takeso tayi tace "ni kayi sauri
kona tafiyata wlh na barka anan" dagokai yayi ya kalleta jin anbude Gate yasa ta
kalli Gate da sauri ganin Abba ta ne yasa da sauri ta taho inda yake jikinta har
rawa yake ta kallai tana satan kallon Abba tace "uhmm sannu dazuwa, ance ka shigo
ciki" "Lieutenant" yaji Abba ya kirashi hakan yasa yajuya da sauri ganin Abba ne da
Chairma yasa yakarasa suka hade ya mikamusu hannu cikeda girmamawa yace "welcome
sir" cikeda farin ciki Abba yace "yaushe kazo Lieutenant?" ahankali yace "just now
sir" kallon Rahima dake tsaye Abba yayi yace "what are you doing outside Rahima?"
ahankali tace "Mummy tace naje na shigo dashi taga yakira wayar ka ne" cikeda
fara'a Abba yace "Allah sarki sorry masallaci mukaje munbar wayan mu aciki, kumuje
ciki" da sauri Rahima tai gaba suka biyota abaya suna hira.



Sallama Abba yayi suka shigo falon tashi Mummy tayi cikin fara'a tace "sannu ku da
zuw......" kasa karasa maganan tayi sabida sauka da idanunta sukayi akan Sameer
dayake shine ya shigo na karshe, cikin fara'a Abba yace "kinga shine Lieutenant
din, Lieutenant meet my wife the mother of my children" cikeda girmama wa Sameer
yace "barka da dare Mama da fatan na sameku lpy" wani irin murmushi Mummy tayi tace
"lpy kalau Sameer, aiko suna mai dadi shigo shigo mun barka tsaye, zoga wuri ka
zauna" tanunamai kujera zama yayi anatse looking compose fitowa su Siddiqa sukayi
harda Rahima cikeda girmamawa suka gaida Sameer. "sannu da zuwa ina yini" kallonsu
yayi fuskanshi cikeda murmushi yace "sannunku ya school" ahankali sukace
Alhamdulillah, murmushi Abba yayi yace "to Masha Allah sannunku da zuwa Chairman
and Lieutenant Sameer, this is my Family, Allah has blessed me with four daughters,
ga Siddiqa nan" ya nuna Siddiqa yace "itace babban y'ata ta farko, mai sunan
Mamana, ansamata rana in sha Allah June-July zata rubuta final exams dinta
accounting taje karantawa August ne bikinta nan da four month" cikin jin dadi
chairman yace "masha Allah, Allah ya sanya alheri" atare Abba da Mummy sukace
Ameen, Abba yace "sai Zeenatu" yanuna Zeenatu dake kusada Siddiqa yace "she is my
second daughter Zeenatu, tana 300 level a makaranta tana karanta mass communication
tace ita yar jarida takeso tazama" duk dariya akai afalon Zeenatu ta boye fuskarta
cikeda kunya, Abba yace "sai Lubabatu" yanuna Luba dake zaune kusada Zeena yay
murmushi yana kallon Zeenah yace "itace tace tanason ta gaji mahaifin ta saidai ba
Civic law ba shari'a law takeyi tana 300 level itama" kabbara chairman yayi Sameer
yay dan murmushi, Abba yace "sai autan gidan Rahima" yanuna Rahima yace "kwanan nan
ta shiga University, medicine tai applying bata samu ba sai suka bata veterinary
medicine, nace tafara shi ahaka mugani next year saitai applying change of course
hopefully zasu bata medicine din" ahankali Chairman yace "Allah ya yarda".




Wani irin kallo Mummy kema Sameer harsaida yaji ajikinshi yadago kai hada ido
sukayi wani irin murmushi tayi tace "atashi aci abinci bayan angama sai kumana
introducing kanku ko Lieutenant" gyadamata kai Sameer yayi batare daya kalleta ba,
Mummy ta kalli yaran tace "alright girls to the kitchen time for dinner" tashi
dukansu sukayi sukai kitchen, warmers da suka shiga fitowa dashi Rahima kuma ta
kwaso broken plates tana tafiya ahankali takawo tsakiyan falon dayake fankacecen
falone suka ajiye Mummy kuma tafito daga kitchen din tai corridor ta shiga ciki,
dakinta tayi tabude wardrobe dinta, wani hadadden lace dinta ta ciro na 98k da aka
mata dinkin riga da skirt blue black ne kalan lace din, agurguje ta shiga shiryawa
cikin kayan aiko sun kamata chip chip kaman wata yar matashiya ta zauna gaban
madubi hoda ta shafa tasaka wani jan jambaki sanan ta daura kallabi tafito tai
dakinsu Siddiqa, drawer su dasuke saka gyaluluwan su tajawo tabude wani hadadden
dan karamin gyalen Lubabatu blue taciro tana murmushi, yafawa tayi akafada tana
kallon kanta a dogon babban madubin su, koyan murya tafarayi agaban madubin cikin
wani murya irin na yan gayun nan tace "Lieutenant Sameer sauko kaci abinci please,
ko kanaso adafama wani special ne?" wani irin murmushi tayi tace "yes yes yayi" da
sauri tafito ta maida kofan tarufe hartakai hanyar fita ta juyo da sauri tace
"turare" dakinta takoma ta feshe kanta da turarurruka sama da shida sanan tafito
tana taku daidai kaman jimina, ahankali ta yaye labule tafito tana kallonsu ganin
duk basu sauko kasa an faracin abincin ba, dan ware ido tayi ta juyasu cikeda yanga
takaraso cikin falon tana kallon Sameer da hankalin shi kekan maganan da Abba keyi
dan zancen politics sukeyi, cikin wani irin strange new voice tace "Sameer, I mean
lieut" tawani kaurara Lieut din, tace "sauko kaci abincin ka karka biyema wayan nan
indai Abban sune zai iya kai gobe yana maganan siyasa bai gajiba" dagokai Abba yayi
ya kalleta, murmushi tayi tace "Alhaji cemai ya sauko please" kallon Sameer Abba
yayi da Chairman yace "let's all have dinner, bismillan ku" saukowa kasa Abba da
Chairman yayi hakan yasa ahankali Sameer ya sauko kasa shima tareda tankwashe kafa,
cinyoyin shi Mummy tabi dawani irin kallo kafin ta juyo ta kalli su Siddiqa tace
"oya ku matso za'ai having dinner" sanan ta kalli Rahima datai shiru ita kadai kan
kujera duktai wani kalan tausayi she is not just comfortable dandai Abba nanan ne
da wlh tuntuni tagudu dakinta, murmushi Mummy tayi tace "sorry Autana oya come have
your dinner sai kije ki kwanta bacci kikeji ko?" gyadama Mummy kai ashgawbe tayi ta
sauko kusada Mummy tazo ta zauna ta dafata murya chan kasa tace "Mummy tare zamu
kwanta ko?" girgixa mata kai Mummy tayi tace "no Autana sai bakin mahaifin ki sun
tafi, idan kin kasa baccin kije dakin yayinki ki kwanta kinji" gyadamata kai tayi
Mummy tai murmushi tace "gud now let's eat" dan satan kallon Sameer Mummy tayi
ganin hankalin shi bamaya kansu yasa cikin wata yar murya tace "me zakaci
Lieuttt?".
[6/3, 9:43 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫



_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔



✍️ M Shakur




2️⃣3️⃣
3️⃣
2️⃣ 2️⃣3️⃣



Dan juyowa yayi ya kalleta cikeda natsuwa yace "anything local meal Mama" wani irin
murmushi tayi tace "shikenan Lieut" ta kalli Rahima tace "bani plates let's serve
ko" gyadama Mummy kai tayi ta tashi, Mummy kuma ta kalli Abba tace "Abban su meza'a
zuba muku?" kallon chairman Abba yayi yace "mezaka ci Chairman" dan dariya yayi
yace "fried rice is okay" jin haka yasa Mummy tace "angama" plate din Da Rahima
tabata ta karba ta dau wani ta zuba white rice da beans agefe, sea food stew ta
zubamai dayaji sea food tasa spoon tadaura kan tray, sanan ta dau wani portable
bowl tazuba pepper soup tadaura kan mini tray din tace "Rahima dauka ki kaima
Lieut" dudda tsakanin su baifi 2 zuwa 4 feet ba saida ran Rahima yabaci ganin Abba
na wurin yasa ta dauka ahankali ta mike tana tafiya kaman batason yi tana kallon
Sameer din da bamaya kallon inda suke hankalin shi hakan zancen dasu Abba keyi,
karasawa tayi kusada shi tadan duka zata ijiyemai abincin agabanshi daidai shima ya
juyo suka hada ido, gyalen data yafane akafada ya sauko hakan yasa idanunshi suka
sauka kan wuyanta da jelan kitson kanta suka sauka awurin, turo baki tayi ta ijiye
agabanshi ta tashi tsaye, cikin wani irin murya na wanda ya cika fam kaman zai
fashe da kuka tace "akwai wani abu dakake bukata?" dan haka Abba yakoyamusu tun
suna yara inhar yay baki sukai serving na bakin su tambaye su if they need any
other thing that is how to make your guest comfortable, tsayawa yayi chak yana
kallon fuskanta, this is the first time daya bama fuskarta 1min attention, a
kumbure ganin iskanci dayake mata yasa tace "eh?" cikin wani irin yanayi nako
ajikinshi yace "me kika ce? Can't hear you?" kafin tai magana Mummy tace "kiyi
magana da kyau mana Auta bakowa kejin yar muryarki ba" turo baki tayi idanunta suka
cika da hawaye ta kallai kaman yanda yake kallonta da kyar tace "nace dawani abu
dakake so namaka?" ba yabo ba fallasa yace "get me a fork" juyawa tayi fuuu tai
kitchen dinsu, Mummy ta shiga zuzzubawa kowa na dakin abinci, dawowa tayi rikeda
fork shi kadai a hannu tuk kafin ta iso Mummy tadan Harare ta tace "haka akemaba
bako abu? Jeki daura fork din on a very nice plate ki kawo" sjarr hawaye ya zubo
mata ta mugun gaji juyawa tayi takoma kitchen din ta dauro fork din kan plate
tadawo tazo har gabanshi ta ijiye mai, sanan tajuyo Mummy tanuna mata kusada ita
tace "zoki zauna kici abincin ki kowa nacin abinci banda ke" zama tayi kusada
Mummy, Mummy ta shafa kanta tace "me zaki ci eh?" makema Mummy kafada tayi kaman a
idanun Abba yace "zuba mata abinci taci, so kike ciwo ya kamaki" zuba mata fridge
rice Mummy tayi dan kadan sanin bazata ci, karba tayi tadan saci kallon Abba ganin
hankalinshi nakan Abincin dayake ci yasa ta kalli Mummy dake kallonta girgiza mata
kai tayi, hakan yasa Mummy ta shafa kanta tace "please eat Rahima ko kadan ne" tai
maganan tadan saci kallon Sameer dayakai tamarin juice bakinshi yana sha anatse.
Ahankali ta shiga cin abinci kadan kadan shiru akayi dakin tsit anacin abincin,
Mummy gabaki daya tarasa sukuni bata sakan talatin cikakke bata saci yanda Sameer
kecin abinci ba baimasan tanayi ba, almost 30min suka dauka sunacin abincin sanan
aka gama su Siddiqa sukai clearing falon tass, Chairman ya kalli Mummy yace "I
really enjoy your food Madam, I must say Chief judge is lucky to have you wlh,
saisa kullum he is looking fresh" dan dariya Mummy tayi cikeda jin dadi Chairman ya
yabeta Abba yay murmushi, ahankali Sameer yace "thank you so much for having us
Sir" yadan kalli Mummy yace "it was such a nice meal Mama, I really enjoyed it"
tashi tsigan jikin Mummy yayi sabida yanda yay maganan cikin wani irin yanayi tana
kallon fuskarshi tace "Allah Sameer" gyadamata kai yayi yanadan gyara zama,
ahankali tace "to ko nagode muku naji dadi yanda kukaji dadin abincina" ajiye
toothpick Abba yayi ya kalli Chairman yace "sai asan juna ko yanzu Chairman, gani
ga Family na nan duk kun gani" dan dariya Chairman yace "ahhh what can I say, as
you all know nine chairman din NDLEA, ni family man ne, matana yarana 6, 5 boys 1
girl, my eldest son yana University yana karantan computer engineering, sauran yara
mazan duk secondary school suke, macen kuma bata fara school ba har yanzu
breastfeeding nata akeyi" Abba ne yace "masha Allah Allah ya raya mana, in sha
Allah one day I will bring all my family over mu kulla zumunci" da sauri chairman
yace "da izinin Allah kuwan" shiru akayi Mummy takosa Abba ya tambayi Sameer nashi,
kaman Abba ya shiga zuciyan ta yace "Lieutenant kaifa" dan murmushi Sameer yayi
yace "actually ahhh, well I don't have much to say" wani irin ajiyan zuciya Mummy
tasauke tana kara gyara zama tana kallonshi tsigan jikinta har wani irin tashi yake
in yana magana. cikin calmness dinshi yacigaba yace "nine first born din gidanmu,
the eldest, I have 3 brothers, mu hudu maman mu ta haifa, my Dad is late" ahankali
kowa na dakin yace "Allah ya jikanshi" dan murmushi yayi yace "Ameen, so that's all
akaina" da sauri Mummy tace "are you single Sameer, bakai aure ba?" gyadama Mummy
kai yayi batare daya kalleta ba yace "not yet Mama" da sauri Mummy tace "how old
are you? I mean shekarun ka nawane?" wani irin kallo Abba yama Mummy dan he felt
somehow datai tambayan dan tana shiga privacy nashi ne a yanzu, he already told us
abinda yakeso musani game da shi why asking him wasu questions kuma. Dan juyowa
Sameer yayi ya kalli Mummy ido cikin ido yace "39 Mama" Mummy wani ruwa yafara dan
tsiyayo mata the way he looked at her right in the eyes and say to her face he is
39 was damn sexy, goosh Sameer is hot wlh, dan murmushi tayi tabude baki zatai
magana Abba yace "yaudai kin dawo yar jarida wifey" dan dariya Mummy tayi tace
"Alhaji just wanted to know Lieutenant better ne kasan kona nema mai mata tunda
yadawo tuzuru" tai maganan tana kallon Sameer dan dagokai yayi ya kalleta kafin
yasake dauke kai, ahankali Abba yace "to Alhamdulillah, Siddiqa kutashi kutafi
dakinku ku kwanta" tashi duk sukayi Rahima ma ta tashi zata bisu Abba yakirata.
"Rahima" da sauri tajuyo ta kalli Abban, da hannu yamata alamun tazo yace "come
back here" dawowa tayi ahankali tazauna a inda Abba ya nuna mata akan kafet a
tsakar dakin duk sukai shiru a falon, tashi Abba yayi yahau kan kujera yace
"kutashi kuhau kujera please" tashi duk sukayi sukahau kan kujera harda Mummy duk
aka natsu, gyaran murya Abba yayi yace "to Alhamdulillah ina farin ciki da irin
wanan rana" ya dubi Chairman da Sameer yace "a yanzu na daukeku Family na najini,
aduniyan nan banda kowa ni kadai mahaifiyata ta haifa kafin daga baya ta rasu, gona
biyu data barimini dasu na shiga dakaina makaranta harna dawo mutumin nan da kuka
gani yau zaune agaban su, saisa dudda kudina I try as much as possible naga ina
rayuwan rufin asiri sabida nasan duk wani wahalhalu na rayuwa, banda haka kuma
randa komi zai kare wanda ba'a fata my family will be able to survive, bakomi nasa
Rahima should stay back ba inaso ka dauketa amatsayin yarka ne" yadafa Chairman
sanan ya kalli Sameer yace "Lieutenant inaso kadau Rahima amatsayin kanwarka kuhadu
kumata fada, d'a na kowa ne, mutum shi kadai baya ya kula da danshi sabida idanu
biyu kacal Allah yamai, but by the time aka hadu ana kula da yaron idanu dayawa
akanshi yaron yasan da haka saikaga ya natsu, baran muku karya ba duk cikin yaran
nan nawa dakuka gani banda fitinanniyar yarinyar, yar bala'i, da tonan fada, rashin
kunya da rashin ji kaman Rahima ba, nasan Rahima bataji wanan bazan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login