Showing 60001 words to 63000 words out of 197960 words
harara da kumburarrun idanunta, ta mugun rame sai fari
data kara kaman mara jini kitson ta ya tsufa sosai dan gashin gaban kanta yasoma
zarewa yana warware kanshi yana kwanciya dan tanada coily hair daman sosai kaman
gashin jaririya, hulan kanta ta gyara batare data kalletaba hakan yasa Nurse din
takama hannunta, ahankali take tafiya dan batada karfi ko kadan cikinta daman tunda
aka fara mata detox dinan ya hargitse kaman ba nataba, agaban wani daki taga sun
tsaya da aka rubuta visit a sama sanan nurse din tasa hannunta tabude kofan, karan
bude kofa da Sameer yaji yasa yadago kanshi yana rike da waya ahannu, tundaga kan
crock shoe kafarta yake kallo har zuwa wandon da rigan dayamata yakuma dan mata
yawa wani irin kyau tarame bana wasaba kafin ahankali yasauke idanunshi kan
fuskarta dayay ja tsabagen kuka kaman jini zaifito, idanunta sun kumbura sunyi
suntum suntum sunyi jaajir gashin idanun duksun tattare looking so moist, idanunta
sun kode, shigo da ita ciki Nurse din tayi ta kawota har wurin kujeran sanan ta
kalli Sameer cikeda girmamawa tace "welcome Sir," gyadamata kai Sameer yayi tajuya
tafita tarufo musu kofa, tsayawa tayi awajen atsaye batare data dagokai ta kallai
ba sai kallon takalman kafafun ta takeyi takasa hada ido dashi, kallonta yayi from
head to toe sanan ya mayarda kanshi kan wayanshi yacigaba da danne dannen wayanshi,
takai almost 20min atsaye bata zauna ba, batace uppan ba, ga kanta akasa kafin
taja wani uban ajiyan zuciya tafashe da kuka sosai tasa hannunta akan idanunta
tanayi kaman zata shide, dago kanshi yayi ya kalleta yanda take kukan kaman wacce
aka zane sanan yadan tabe baki yatashi tareda daukan wayanshi da carkey daya ijiye
kan table yajefasu cikin aljihu gaban riganshi yayi hanyar kofa yabude kofan yafita
batare daya sake koda kallonta ba, da sauri tajuya tabishi tabude kofan tafito yana
cikin tafiya adan corridor taji takama hannunshi gam hakan yasa ya tsaya chak
tareda juyowa yazuba mata idanunshi dababu alamun wasa cikinsu, fashewa tayi da
kuka sosai gabaki dayan wurin ya dau karan kukan ta tace "ka maidani gidanmu, ka
kaini wurin Mummy na" yanda take kukan yasa Nurse data shiga wani office awurin
tafito tazo wajen da saurita, jin sahun tafiya yasa Rahima tajuyo tana ganin Nurse
takara damke hannunshi gam gam tana kallon fuskan shi tace "dan Allah ka kaini
wurin Mummy na kaji, please ka kaini dan Allah karka bari su tafi dani please, wlh
banson wurin nan dan Allah kaji" ganin Nurse ta iso wajen yasa takoma dayan
gefenshi talabe tana kuka sosai tana ihu kallon nurse din yayi yace "don't you have
any female security here?" da sauri tace "we have sir" "call them suzo su tafi da
ita ciki" yafada sounding a lil bit bitter, wani irin dan banzan ihu tasaki.
"noooo, dan Allah in kanama Allah ka kaini gidanmu, wlh bansan wajen nan" wani
mugun kallo yamata da idanunshi yanuna mata hannunshi, ahankali tasake shi cike da
tsoron shi tana kuka sosai tana tsaye gab dashi jikinta narawa ko minti biyu ba'a
yiba saiga Binta da Asabe tana ganin tasake damke hannunshi tana neman shigewa
jikinshi da hannu daya Asabe ta dagata sama sukai ciki da ita tana kwala ihu tana
juyowa tana mikama Sameer hannu, mugun kallo ya watsa mata yajuya yafice daga
wurin, saida yaga Dr sanan yabar Centre.
Aranan da daddare yaje yagaida Abba dayasoma jin sauki sosai, Mummy kaman zata
hadiyeshi da kallo amman tunda ya kalleta sau daya ya gaidata bai sake bata second
look ba haryay briefing Abban kan Rahima tasoma samun lafiya and she is responding
to treatment, Abba yaji dadi ranan, yaji dadi wani sabon karfi yaji ya shigeshi har
saida yafita sallan isha'i tareda da Sameer shida rabon shi daya fita masallaci
harya manta amma news din Rahima yabashi karfi.
Wasa wasa Kwanaki nata tafiya, yau satin Rahima uku a Rehabilitation Centre, tun
ranan da Sameer yazo yadubata babu wanda yakara zuwa yaduba ta daga gida, babu
ranan duniyan dabazatai kuka ba, and Alhamdulillah ana bata kulawa sosai ita kanta
tanajin chaji ajikinta amma tsabagen yanda ta tsani wurin da abubuwan da ake mata
aciki yasa taji babu abinda takeso kaman ta ganta a gidansu.
Yauma kaman kullum da sassafe aka tadasu suje wanka, tana cikin bayi tana wanka
taga anbude labule an shigo, baki tabude zatai ihu tana jan towel dinta danta rufe
jikinta matar datashigo tasa hannu ta rufe mata baki tareda rage murya tace
"listen to me, kina ihu Asabe zasuzo nan, so kiyi shiru ba jikinki na shigo nagani
ba ko wani abu magana nazo namiki" da sauri ta gyadamata kai tana kokarin daure
towel dinta, janye hannun matan tayi daga kan bakinta tabi boobs dinta da kallo
takai hannunta zata taba da sauri Rahima ta koma gefe hartana neman fadi matan ta
riketa tana washe mata baki, tana sosa kai, idanunta bakin kirin hakama lebenta,
tureta Rahima tayi tana turo baki tace "niki saken" sakinta matan tayi tana soshe
soshe tace "dalla sabida ina sonki ne dan kinada kyau saisa ma nace bari nazo
nataimake ki nidama last 2weeks duka duka shegen mijina bayan ya dannamin saki
yakawo ni nan, tunda nazo kullum nake ganinki kina kuka bakima kowa magana, kullum
ke kadai" tai shiru tareda daga hammatan ta tana sosawa kaman mahaukaciya, yatsine
fuska Rahima tayi cikeda kyaman ta takoma baya dan ganinta take kaman mahaukaciya,
dariya tayi ta sauke hannunta tace "kinga nan wurin kashemu sukeyi, inba hakaba
antaba raba nawa da abinda kesashi jin dadi, shaye shaye fa, inhar zasuce zasu
rabamu da shaye shaye to su rabamu da shan ruwa ko cin abinci man, ruwa baya kore
damuwa ko bakin ciki amma shaye shaye kina sha wayyooo matsala da bakin ciki bye
bye, bana wanan soshe soshen da amman sabida ban samu Cociene dina na shaka ba na
2weeks anan wurin shine nafara haka kaman mahaukaciya, kullum suyita kada kuka da
maburgi acikina dan bantan uba" tai shiru tana kwakulo hancita tana lumshe ido
tsabagen yanda abin kdmata dadi, tace "yau zamu gudu mubar gidan nan da daddare,
akwai wani supplier na saurayina kuma da zaizo ya kwashemu da daddare amota anan
baya, haurawa zamuyi kin gane, electric fence ne but zamu baza bargunan mu akai, in
kinaso zanje dake kema ki gudu amma zaki biyani dubu goma inkin yarda" da sauri
Rahima tazo kusada ita tace "eh zan biyaki Allah, Mummy na zamu kira muna fita zata
turomiki kudin, da gaske dan Allah zaki fitar dani ko karya kikemin?" murmushi
matar tamata tasa hannuwanta duka biyun tana sosa kai tace "eh kibarmin komi a
hannuna nasan wurin nan lungu da sako, nine number 00, amma sunana Shagali" da
sauri Rahima tace "Shagali?" gyadamata kai matar tayi tana sosa kunne tace "eh
Shagali sunana, yanzu wuce kifita, karfe takwas nadare nurses ke fita shift dazaran
ta dakin ku tafita kifito kawai zaki ganni kibar komi a hannuna" da sauri Rahima ta
gyadamata kai tana murmushi tace "nagode" wuyan ta ta shafa tace "kinada kyau ga
kira saisa zan taimaka miki, u look so innocent, wuce kifita kar Binta ko Asabe
sukamamu" ko damuwa ma batayi da batagama wankan da kyau ba tafito tana murmushi ta
ijiye sabulu da soap a box dinta tawuce ward dinsu.
Inkika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa, zaki biyani ranan da bakida shi.
How to subscribe
Pay 300 to 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to
my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din BIN ABINDA ZUCIYA
KESO.
Ranan har Nurses saida suka dinga mamakin ta ganin ranan ne rana ta farko da batai
kukaba, batai gardaman shan magungunan taba har akai magrib, dama ba ruwanta da
Salla dan tunda aka kawota ko hanyar masallaci bata taba biba sai agogon bango ward
din take kallo, agogon nabugawa karfe 8 dot taga nurse din dakin ta tashi daga kan
kujera, ta dau wayarta da wani littafi tawuce tafita da sauri ta diro daga gadon
sauran yan dakin suka bitada kallo hararan su tayi tace "sa'idawa mutum bazaije yay
fitsari lafiya bakuma yanzu adai rage" tabude kofa tafita tana fita tahango Shagali
awurin kofar wajen da hannu tamata alama tazo da gudu tai wajen hannunta Shagali
takama sukai wata hanya da batasan da ita ba tunda aka kawota Rahab centre, hanyar
lungu ne haka suketa gudu itada Shagali har suka bullo backyard wajen masallaci
wasu mata guda uku tagani awurin suna fitowa tace kowaya tsugunna Rahima tahau
kansu ta dane kan fence, tsugunawa sukayi Shagali tasaki hannun Rahima data rike
tace "hau bayansu ki dirka kijiramu" hawa bayansu tayi amma dudda haka batakai
tsawon ginin ba dan bata da wani tsawo hakan yasa Shagali tahau ta cincidata sama
ta taka bargon dasuka shimfida kan electric fence din ta mike tsaye gabanta na
faduwa hango uban tsawon ginin dasuke cewa ta dirka ga wajen daji duk ciyayi, da
sauri murya kasa kasa gudun kar ajisu Shagali tace "wai bazaki dirka ba sai an
kamamu wai babygirl?" fashewa Rahima tayi da kuka tana neman tsugunnawa dan tanada
fear of height tace "am scared bazan iyaba" wani irin tunkudata shagali tayi aiko
ta kwala uban ihu tafadi tipp akasa tasaki kuka sosai, hawa fence din Shagali tayi
ta dirko sauran ukun ma suka diddirko kasa kana ganinsu kaga kwararrun yan duniya,
sanan Shagali ta tashi ta daga Rahima dake kuka sosai ta kakkabe mata jiki tace
"sannu kinji oya mu gudu mota na chan gaba" gudu sukahau yi Shagali na rikeda
hannun Rahima dake shirin suma tana kuka kaman yarinya karama, sundan yi nisa
Rahima ta zube akasa dan karfin ta yakare hakan yasa sauran suka tsaya suna tsaki
sukace ce "wai mesa kika dauko wanan yar yarinyar shagali? Sai bata mata lokaci
take" cikin jin haushi shagali tace "sonta nake baruwan ku, kuma dai naga taimaka
muku nayi tomena cewa me yasa na daukota" ganin kaman suma tayi yasa Shagali ta
dagata tagoyata abaya sukahau gudu kusan na na 45min sanan suka kai titi aiko saiga
wata yar akwalan mota datai parking ita kadai akan hanyan da motoci basawani
guduwa, da sauri wani mutumin yafito daga motar yabude musu baya suka shiga daya
cikinsu ta shiga gaba, Shagali ta zauna kusada Rahima tace "bani ruwa in kanada
shi" ruwa yamiki mata yace "Shagali ta Shagulgula dama ashe zan kara ganinki yau
akwai holewa kenan" dariya shagali tayi tace "jamuje Bala" kunna motar mutumin yayi
yaja itakuma ta debo ruwan ta watsama Rahima kan fuska hakan yasa tabude idanunta
ganinta amota yasa tace "mun gudun?" fuskarta shagali ta shafa tace "eh mungudo
yanzu zamuje musha dadi abinmu da sassafe saimu kaiki har gidanku ki kwaso mana
kudade ko" turo baki Rahima tayi tace "yanzu zaku kaini" ahankali Shagali tace "a'a
sai safiya zamuje yanzu sun riga sun kira yan gidanku kina zuwa za'a maidake gwara
kibari gobe kinji" ahankali ta gyadamata kai tai shuru ko kadan she is not
comfortable dasu haka taga sunkai wani uncompleted building a cikin wani anguwa da
duk gine gine ne da ba'a gamaba, ya kashe motan suka fiffito Shagali tafito da ita
tana tafiya ahankali suka shiga gidan rawa suka hauyi suna ihu mutumin ya shiga
shigo musu da gorunan coke yana basu daidai biyu Shagali ta karba tazo inda Rahima
ke zaune ta mika mata tareda kashe mata ido daya tace "ga coke, amma coke dinan
yaji hadi nake gaya miki, so kisha kadan dan harkan manya ne you are too small for
this, yanzu ma nabaki ne dan nasan kinyi kewan abin" karba tayi tarike tana
kallonsu suna rawa sosai kaman ansaka musu waka suna rawa suna shan coke din harda
mutumin daketa shafe shafe da Shagali, dauke kai tayi ta makure a bango ta kunshe
ido har saida taji shiru sanan tabude idanun ahankali, ganinsu tayi duk sun baje
akasa suna bacci suna munshari, kasa koda runtse ido tayi sabida sauro awurin ga
kukan dasuke yi na bala'i, haka tazauna idanunta biyu ita kadai har asuba, sai
wuraren asuba sanan tabude coke din dataji already marfin abude ne takafa abaki dan
kishi takeji, wani shegen daci da dadi taji hakan yasa ta yatsine fuska tacireshi
daga bakinta, sai bayan ta hadiye sanan taji wani dadi a bakinta kaman tasha bitter
chocolate hakan yasa tadauka takafa abaki tanasha tana wani irin sauke ajiyan
zuciya saida ta tada goran sanan ta yar tana yatsine fuska sai chan kuma tafara jin
dadi, murmushi tayi kafin taji wani mahaukacin bacci na dibanta daganan kuma ba
tasake sanin inda kanta yakeba.
39.
Wuraren 8 na safiya namijin yafara tashi ya bubbuga Shagali dake kusada shi yace
"Shagali kutashi mutafi kafin masu gini suzo su ganmu anan" da sauri ta mike ta
bubbuga sauran kawayen nata dake kwance gefenta kafin tai wurin Rahima dake bacci
ta akasa ta bubbugata da hannu tana kiran sunanta. "Baby, Babygirl" bude idanu
Rahima tayi kadan takara maidawa tarufe su tace "niki barni bacci" da sauri Shagali
tace "baidai yar yarinyar nan ta shanye duka wanan mix dinba? Na shiga uku na
lalace" kwashewa da dariya sauran matan sukayi daya daga cikinsu tace "da ke zata
jira saikin cemata ta shanye sanan zata shanye, angayamiki sabon shigace, tunda
kikaga yar yarinyar nan a gidan nan aito kinsan ta kware kan harkan, nidai tattara
ta mutafi mota mubata ruwa kota iya bude ido tanuna mana gidansu mukaita tabamu
kudi" dagata Shagali tayi suka jata har mota suka sata cikin mota duk suka shiga
Shagali tadau ruwa ta zubamata a fuska sanan takafa mata goran ruwan a baki tana
watsa mata a fuska, dan kurba tayi, bude ido tayi kadan, Shagali ta jijjigata da
sauri ganin tabude ido tace "ke inane gidanku zamu maidake gida mu karbi kudi mu
wucene" cikin maye tace "uhmmmm gidanmu, wurin Mummy na?" da sauri Shagali tace "eh
inane gidan?" washe baki tayi tace "gidan Alhaji Sambo, number 1 Sambo Street GRA
nanne gidan muuuuuu" tai wani uban ihu, da sauri direban yadauki hanyan itakuma
tacigaba da bacci tana surutai har saida sukakai layin data fadi, baki Shagali
tabude tace "ashe yar gidan masu kudi ce" a daidai address din data fadamasu yay
parking, ruwa Shagali takara kwara mata a fuska tace "bude ido ke mun kawoki gida,
ga gidanku nan" ahankali tabude idanunta dudda dishi dishi take gani bai hanata
gane Gate din gidansu ba da sauri takara bude ido ta tashi tana tangadi tace "Mummy
na, laaaa gidanmu" ta shiga neman abin bude kofar mota, budemata Shagali tayi tace
"kiyi sauri ki kawomana kudin muna jiranki anan" gyadamata kai tayi tafita tana
washe baki hartana fadi kasa ta tashi tsaye tana kakkabe jikinta tana kallon Gate
dinsu, wani irin tura Gate din tayi Gate din yay kara kaman za'a balla hakan yasa
gateman yafito da sauri yace "waye anan?" ganin Rahima ne yasa yay gum dan yasan
zata iyamai rashin mutunci, ahankali Rahima ke tafiya tana tangadi tana kallon ko
ina kafin cikeda murna ta kwala wani uban ihu. "Mummmyyyyyyyyy naaaaaa!"
Gabaki dayansu suna zaune a dakin Abba suna hira dan yau Abba yaji sauki sosai, jin
murya kaman na Rahima ta kwala ma Mummy kira yasa duk sukai shiru Abba yace
"sainaji kaman an kirak....." "Mummmyyyyyyyyy naaaaaa" Rahima tasake kwalama Mummy
kira tana juyawa da sauri Mummy da Abba suka tashi Mummy tace "kaman muryan Auta
na, meya faru ba 6 month kacemin zatayi a rehab ba ko an sallamota ne?" tai maganan
tana bude kofa Abba biye da ita da sauran yaran duk sun kosa suga Rahima ce da
gaske, sake kwalama Mummy kira Rahima tayi tace "Mummmyyyyyyyyy" da sauri Mummy
tabude kofan falo tafito tai turus ta tsaya ganin Rahima sanye da uniform din rehab
dayay datti sosai barin ma kasan wandon dakejan kasa dukta tattake shi, babu hijabi
ajikinta sai hula, Abba yabi ta gefen ta yafito tareda saukowa daga dakalin
barandar yana kallon Rahima kaman amafarki, ganin Abba yasa Rahima tafashe da
dariya cikeda maye tace "laaaaaaaa Abba kadawo kaman tsoho wlh" tai maganan tana
karasawa gabanshi inda ya tsaya churr kirjinshi na bugawa hudu hudu, hannu tasa
akan gemunshi da fura fura ya cika tace "tsoho ne kai, kudi, bani kudi Abba" tai
maganan tana tura hannunta a aljihun gaban jallabiyarshi tana lumshe ido kaman
wacce bacci ke shirin tafiya da ita, warin da Abba yaji kaman na giya kona menene
daga bakinta da numfashinta yasa yadan kawad dakai saikuma yadago kai ya kalleta
cikin wani irin yanayi kaman wanda zai fashe da kuka, cikin raunanniyar murya mai
nuna tsantsan ciwo yace "Rahima ya akayi kika dawo gida?" kyalkyacewa da dariya
tayi cikeda maye tace "uhmmmm gudowa mukayi dasu Shagali, nahau kan gini nai tsalle
nafadi tippppp akasa hahahahahha" ta kwashe da dariya kafin ta kama hannun Abban
tace "Abba fitsari nakeji wlh tiles din bayin nan yay kal kal yau ka wanke ne?" tai
maganan tana sakin hannunshi tsugunnawa tayi agaban Abba batare data cire wando ba
tasaki fitsari awurin tana wakan fitsari "siiiiiiiiiiiii, fitsari futu futu, Mama
da Baba suna kallona yayyyy yafitooo, agayara agayara fitsari zai shiga gidan
takalmin Abba" tai maganan tana bin fitsarin datasaki da kallo dake gangarawa zai
shiga takalmin dake kafan Abban ta tana washe baki cikeda mugun murna, wani irin
juyawa Abba yayi cikin tsan tsan fushin daya dade baiyi irinshi ba yay ciki da
sauri Mummy tabishi abaya ganin a yanayin daya juya yashiga daki tace "Alhaji kaga
mezakayi eh? Kaga bakada lpy bakadade da farfadowa ba, so calm down and relax nasan
duk inda Sameer yake rehabilitation centre sun riga sun kirashi, kabari ya iso ya
mayar da ita please mijina karkamata wani abu, dan Allah kaji Abban su" ko kallon
Mummy baiyiba tsabagen bacin rai yafada dakin Rahima yay wurin wardrobe dinta
yabude kaman zai karya kofofin, babban akwatinta nasama yaciro ya yar akasa tareda
budewa Mummy tabude baki tana kallonshi tace "Alhaji me haka? Koranta zakayi daga
gidanne? Ina zata? Watake dashi aduniyan nan banda mu?" wajen kayan sawanta Abba
yabude yadinga jido uban kayan da baisan iya yawan su ba da kalansu ba ya watsa
akan akwatin haka yadin ga kwasan kayanta duk wanda hannunshi yasauka kai saiya
jawo ya wurga a akwatin har akwatin ya cika yamaida akwatin yarufe yaja trolley
yafito ya shiga dakinshi, drawer shi yabude yaciro wrappers din yan dubu dubu guda
biyar yadauko car key duk mummy nabiye dashi tace "innalillahi wa innailaihi
raji'un, Alhaji, Abban su Abban su please talk to me my hysband dan Allah kaji,
koran Rahima zakayi ne?" fitowa falon yayi yanajan akwatin batare dayabi takan
Mummy ba Mummy biye dashi sukayi hanyar fita daga falon inda su Siddiqa dake gaban
daki suka tsaya suna kallon Rahima, Mummy ta kwalama Siddiqa arude tace "Siddiqa
kuzo kuga abinda babbanku yayi, baban ku yahado kayan Rahima a akwatin koranta
zaiyi? Ina yakeso taje? Hannunka baya rube ka yanke kayar, addu'a zamu mata, addu'a
makamim mumina, ka dauka Rahima itace jarabtar wanan Family namu, and I assure you
babu abinda ya gagari Allah, dan Allah mijina karka korata instead ka maidata gidan
Rehabilitation din" wurin kofa Abba yayi batare da maganganun Mummy sun shiga
kanshi ba, da sauri Siddiqa ta tare Abban su Zeenatu ma haka duk suna kuka dan basu
taba ganin mahaifin su yay fushi hakaba, ahankali Siddiqa tace "Abba mekakeyi ne
ina zaka kai Rahima? Eh talk to me Abba na" cikin wani irin Kunan rai ya kalli
Siddiqa yace "tashi daga gabana"