Showing 90001 words to 93000 words out of 197960 words
daura ki dauka haka Allah ya kaddara, saina dawo"
yadau car key shi dake kan center table yafita binshi da kallo Mummy tayi kafin
tafashe dawani irin kuka, bata taba sanin zata dawo gida ta tarar da wanan bakin
news dinba kaman zata mutu takeji, zuciyanta yay mata daci da zafi, Rahima ta auri
wanda takeso wlh bazata yardaba, ita Rahima harta isa tai kishi da ita inaaa!
57....
Fashewa da kuka Mummy tayi taci kuka harta godema Allah, ranan haka tawuni cikin
kunci da bakin ciki, gawani kishin jaraba dake cinta kaman zata hadiyi zuciya
tamutu, hatta y'ay'anta kasa gane kanta sukayi. Wanan kenan.
Yana zaune a office dinshi har yamma baimasan a ina zai kwana yauba dan yan
interior company nan nagidanshi a auna nan a auna chan anata kawo kaya, he is so
worried akan Ummi dake fushi dashi, knocking kofarshi akayi hakan yasa ya kalli
kofan tareda rufe system dinshi yace "common in" bude kofan akayi Noor ne da
Muhammad suka shigo duk sunamai murmushi saikuma yaga matayen su rikeda yaransu a
hannu sunci gayu hakan yasa yatashi kafin yaga Mu'az ya shigo rikeda wani cake da
aka rubuta happy birthday ajiki da happy married life ga uban balloons, dan zaro
ido yayi like wats all this, maida kofan Nabila tayi tarufe Mu'az yakaraso ya ijiye
fine cake din kan table dinshi tareda kunna fireworks din hakan yasa dukansu
sukahau mai waka. "happy birthday to you, happy birthday to you, Happy birthday to
Yayan mu, happy birthday to youuuu, hip hip hurray" sukahau tafi, murmushi yayi
yazagayo hannu yasa yakarbi Princess daketamai dariya Nabila tace "ina yini Ya
Sameer" ahankali yace "lpy lau" sanan ya kalli jaririyan Fadila ya shafa kumatun ta
yace "babygirl you came to my office today" duk dariya akayi Fadila tace "happy
birthday yayan mu, ina yini" ahankali yace "Alhamdulillah" sanan yanuna musu dogon
kujeran office din yace "ku zauna" sanan ya kalli Noor da Muhammad dake tsaye yace
"ku zauna" zama sukayi kan kujeran dake gaban table yanunama Mu'az stool yazauna
shima kafin ya koma kan kujera ya zauna rikeda princess yay murmushi tareda kallon
cake din yace "I've forgotten yau birthday dina ma" yasake murmushi sanan ya kalli
Noor yace "thank you guys" akadanyi shiru, ahankali Noor yace "Yaya Sameer, I came
here we all came here not just for this" ya nuna cake, yace "Ya Sameer tun ina dan
karami I watch how you live your life akan gaskiya dayin abubuwan gaskiya, one
thing dana sani kanka haryau har gobe shine you don't just do things anyhow kome
kayi I know akwai reason behind it, Ya Sameer ko prostitute today kace zaka aura I
will support you dan nasan kasan me kakeyi, I trust my brother and I stand with you
in every step you take, worry not okay, Ummi zata sauko itama I assure you this"
ajiyan zuciya yasauke yana kallon cake din kafin ahankali yace "there's more to wat
am doing ku kannai nane dole ma sanar daku, banso iyaye susan maganan dan ba
hurumin mu bane mutona mata asiriba is left for Abban su should find out dakanshi"
labarin Rahima yashiga basu tatas, duk dakin dama Fadila da Mu'az sune masu saurin
kuka saida sukayi, Sameer yace "I just see Rahima kaman kanwar mu su Asiya and
Yusra, I look at the whole case like look at Princess, ga babygirl all of them are
children nobody knows tommorow, lemme save this girl dan nima inada kannai da
y'ay'a mata, and if by saving her from that wicked is by marrying her am ready to
do it, shikenan" tasowa Mu'az yayi da sauri yafada jikin Sameer yahau kuka,
ahankali Sameer yay patting bayanshi yace "kaga nahanaka kuka u see princess namaka
dariya" dagokai yayi ahankali ya kalli yayan nashi yace "Ya Sameer I want to be
like you when I grow up, u truly have a heart of gold" kanshi Sameer ya shafa yace
"stand up jeka zauna awurinka" tashi yayi yakoma yazauna, Muhammad ne yace "to
yaushe zakaje ka daukota daga rehab? Inyazo ta dinga zuwa as an outpatient saisu
dinga bata appointment" ajiyan zuciya Sameer yasauke yace "Ummi tace nadaukota but
yau ana zuba funitures, am planning gobe zan daukota" gyadakai Muhammad yayi da
sauri Nabila tace "Ya Sameer ni banma gantaba but Allah yadauramin sonta already
and I promise you zamu riketa as a sister kuma amana batare any stigmatisation or
abu makamantan hakaba ko Fadila" gyadamata kai Fadila tayi tana share hawaye,
Nabila tace "but inaso ka daukota da safe, ka kawota gidana ko Fadila, we call mai
lalle da saloon agayara mata kai, da daddare saimu kaita dakinta, we have to make
it special I think we should throw a party ko baby" ta tambayi Noor, kafin yabata
amsa Sameer yadan yatsine fuska yace "No banson party, banson anything noise"
tasowa Fadila tayi tazo wajen Yaya Sameer din tace "bamu kudi, we need to get kayan
dazata sa ready gobe" Nabila najin haka ta taso itama tazo tace "yauwa kin tunamin
yarinya ranan bikin ta bazata saka tsofaffin kayaba, Ya Sameer akwatinta fa" dariya
Noor yayi yace "yauwa ku damai dan yayanmu zai iya ya share komi babu ruwanshi"
yanda sukamai chaa aka yasa yadau wallet dinshi yabude yaciro Atm card yamika musu
yace "gashi, pin 5474" ihu duk akayi cikeda murna Noor yace "ehen let's cut cake
and feed yayan mu is his birthday" yanda sukamai hayaniya a office yasa yace "wai
ya akayi aka barku kuka shigo Barrack dinan?" da sauri Mu'az yace "cha musu mukayi
we are lieutenant Sameer Simran Sameer family and today is your birthday we are
giving you a small surprise" girgixa kai yayi suka shigo gutsuro cake suna bashi
har yasamu da magrib ya tarkatasu suka tafi.
Washe gari!
Daren jiya bakaramin fada Mummy da Abba sukayi ba, tun yana ganin abin nata shirme
harsaida yace mata waito me danna auramata Sameer me eh, shima yamata kacha kacha
ganin ya shareta hakan kuma zaifi jawo mata olla dan tanason jin information daga
gareshi yasa tasameshi safiyar yau tabashi hakuri sanan ta tambayeshi ya ake ciki
yanzu, yace mata kampanin interior sungama saka mata kaya duk wani kayan bukata
data sani tundaga kan kitchen dining labulalye da sauran su sun saka, dama
quotation din dasuka min nakomi was 11.9m, nabasu 8m, to inaso anjima zan basu
sauran kudin, Sameer yacemin zaije Rehab Centre yadauko ta da daddare zanje gidan
nafadi mata dakaina na aurar da ita" da sauri Mummy tace "zamuje tare nai kewan
yarinya na" dan shiru yayi kafin yace "no tafiyan namiji daban naku na mata daban,
idan uba yatashi zaije gidan yarshi shi kadai yake zuwa" shiru Mummy tayi kafin ta
gyadamai kai tace "shikenan gobe ni naje naduba gida idan da gyare gyare nayi" kudi
Abba yaciro dayawa yabama Mummy gashi kimata siyayya sanan yafito tareda kwallama
Siddiqa kira tafito yace "yauwa kije dakin Rahima ki tattara yan kayanta zan kawo
miki babban trolley na, da school books dinta kihada komi kikai motana, make sure u
pack anything dakikasan tanaso fa" da sauri Siddiqa tace "to Abba" ta shiga dakin
shikuma Abba yashiga dakinshi yafito dawani babban jakan Lv yashiga dakin yabama
Siddiqa tahau aiki, ganin batasauri yasa yashiga tayani gwanin ban sha'awa Abba is
just so happy, jiya harda sallan dare dan gani yake Allah gata yamai daya bama
yarshi dake shaye shaye kamilin namiji irin Sameer.
***
Wuraren 11 na safe yay parking motarshi agaban rehab din batare da security sun
bari yay parking acikiba ya leko yace "Sir sorry, we are celebrating 20yrs
anniversary yau saisa kowa anan yake parking you can come in sir" kashe motar yayi
yafito Mu'az dake taredashi shima yafito yana sanye da kananun kaya, shikuma Sameer
na sanye da uniform yay wani irin asirtaccen kyau ko mesa oho, sai kamshi yakeyi,
rufe motar yayi suka shiga ciki shida Mu'az dake biyada shi, compound din yagani an
gyara anyi decorating da balloons black and golden, ga tables da chairs da aka zuba
awajen all patient dinsu maza da mata zazzaune suna shan drinks wasu nacin abinci
wasu kuma nacin snacks gawani soft music natashi, all the patients looks very happy
sai hira ake, dan the only thing dake joining maza da matansu is sport randa za'ai
sport other than that kuma babu saiyau da aka fitoda kowa sabida 20yrs anniversary
da Hope Rehabilitation centre ke celebrating, ahankali yake tafiya yana kallon
koina kaman eyes dinshi is searching for someone, chak ya tsayar da tafiyan
dayakeyi hango Rahima dayayi dake zaune itada wani fair guy da naman idanunshi
kenan so black tsabagen shaye shaye, tana sanye da uniform dinta na rehab saidai
kanta babu kodan hulan nan data saba sawa kuma anbata taki sawane sabida an mata
tsifa an wanke mata kan dama ance mata yau za'a kawo mai kitso tamata, an mata
parking gashin aka bata wani pink ribbon takama gashin dashi tasaki jelan gashin
dayakai har tsakiyan bayanta bakin dukya kanannade abinku da coily hair, bakaramin
kyau tayiba sabida gashin mutane dayawa maza da mata anata mata magana sabida yanda
tai kyau tai kaman wata little angel irin yaran yan gayun nan, tai mugun kyau,
damasu biyune kadai a table dinsu tana rikeda cocktails a cup da straw keciki tana
zuka shikuma yagama cin rice yana goge baki yana kallonta dan yarinyar ta masifan
burgeshi kaman yasace ta yakeji yasakin mata murmushi yace "finally yau munsami
normal food munci, amma kullum aita bama mutum abincin magani ewwww" yatabe baki,
kyalkyacewa da dariya tayi ya mugun bata dariya dudda batasan guy dinba ita kadai
ke zaune yazo yasame ta yazauna ya ijiye abincin shi yana shi yahau mata surutu.
Wani irin abu Sameer yaji yadaki kirjinshi ganin yanda take hirada wani daketa
kallonta kaman zai hadiye ta kanta ba hula iska na kada gashinta, ahankali yashiga
dunkule hannu kirjinshi namai wani irin zafi.58.
Agurguje
Da sauri Mu'az yakama hannunshi yarike gam yana kallon inda Sameer din ke kallo
yace "Yayan mu itace Rahiman?" gyadamai kai Sameer yayi ahankali batare dayabar
kallonsu ba, baki Mu'az yasaki yana kallonta baisan lokacin dayace "wow! My Godddd!
She is so beautiful wlh" wani haushine Sameer yaji yatasomai da sauri yajuya yay
cikin office din Dr dan inyaje wajen zai iya abinda he might regret yashiga yamai
bayani zaidau Rahima zasu dinga dawowa as an out patient, gyadamai kai Dr yayi
sanan yabashi katin next appointment din Rahima ya kwalama Asabe kira da sauri ta
shigo, yace "bring all Rahima's things, and come along with the Rahima" gyadamai
kai tayi yajuya tafita Dr kuma yacigaba da hira da Sameer dake amsa shi dai dai dan
jiyayi ranshi yawani yi masifan baci, almost 8 minutes suka bata sai aka turo kofan
dakin Asabe ne rikeda katuwar jakar Sameer na sojoji da kayan Rahima ke ciki sai
Rahima dake bayanta ganin Sameer zaune kan kujera a office din yana magana da Dr
dawani mai kama da Sameer din saidai ba sosai ba yasa taji gabanta yafadi da sauri
ta saukar da kanta kasa, hannu Sameer yamikama Dr tareda tashi yace "thank you Dr
saimunzo" sanan ya kalli Asabe yace "where is her hijab?" yamata pointing Rahima da
yatsa batare daya kalletaba, hannun Rahima Asabe takama tace "wanan ko anbata
hijabin bata yarda tasaka hakama hula duk suna cikin jakan nan" dagokai ahankali
Sameer yayi ya kalleta kaman tasan kallonta yake itama tadan dago kai ta kallai
hada ido sukayi da sauri ta sunnar da kanta, ahankali ta tsugunna tabude jakan
hijabin dake saman kayan ta dauka ta zage zip din tareda zura hijabin, hannu Mu'az
yasa yadau jakan ahankali yace "let's go" juyawa tayi tafita tareda Mu'az shikuma
Sameer biyeda su, hakanan gabanta ke faduwa ganin a dawo ansake daukan ta again ina
za'a kaita, bayan motan Mu'az yabude nata yana kallon fuskarta yace "shiga" shiga
tayi ahankali tazauna batare data kalleshi ba ya maida kofan yarufe shikuma ya
shiga ciki yazauna already Ya Sameer harya tada motan Mu'az narufo door dinshi yaja
motar, tafiya sukai sosai sai kallon hanya take tai shiru har zuwa wani anguwa
dabama tasan anguwanba duk zaman ta a Abuja, anguwan na yan gayune gidajen hadaddu,
agaban wani gida Sameer yay horn mai gadi yabude musu ya shiga gidan, awajen
parking taga sunyi parking, Mu'az yafito yabude mata baya ganin batada niyyan fita
yace "fito Rahima" ahankali tafito su Nabila dake jikin window itada Fadila suna
leke atare sukace "woww, Baby zokaga matar Ya Sameer she is so beautiful wlh"
Fitowa Rahima tayi ta kalli Mu'az cikin siriruwan muryanta tace "inane nan?"
murmushi ya sakin mata yace "gidan Ya Noor ne nan" da sauri tace "Ya Noor? Wayeshi"
ahankali yace "muje ki ganshi kanin Ya Sameer ne" ganin Sameer haryay flat yabarsu
wajen yasa yace "muje kigani" ahankali take binshi duk tajita wani iri a daidai
bakin kofan taga wasu kyawawan mata sun fito da saurinsu sukayo kanta. "Oyoyo
Rahima" saiga wasu maza guda biyu suma su fito dataga suna kama da Sameer sosai
saidai yafisu kyau da tsayi da cikan jiki duk antsaya ana kallonta ganin yanda ake
kallonta yasa da sauri ta matsa wajen Sameer batai wata wataba takama hannunshi
tarike gam idanunta nataruwa dahawaye, wani mahaukacin shewa suka shigayi ganin
yanda takire Sameer shiko wani kunya yaji da sauri ya karbe hannunshi ya shiga ciki
itakuma su Fadila sukai bedroom dinta da ita inda makeup artist kezuwa, karasawa
wajen fridge Sameer yayi yabude yadau ruwa yabude bottle din yadan kurba sanan ya
maida marfin yarufe ya kalli kannin nashi dake wani kallonshi yace "lemme go back
to the office" da sauri Noor yarikemai hannu yace "wlh baxaka tafiba, boys oya" to
his biggest surprise gani yayi ganinshi drag him to Noors bedroom sanan suka rufe
kofa wani kallo Sameer yamusu Noor yadan sosa kai yace "Yaya munsanar da friends
dinka kai aure munmayi inviting some to dinner damuka hada muku by 5 anjima sai
bayan magrib mutafi gidanku, yanzu su Nabila za'a fara gyara amaryan ka" shiru
kawai yayi yana kallonsu baice musu komi ba, yanaji yana gani suka hanashi fita.
Rahima kawai binsu take da dara daran idanunta tana gani aka shiga gyara mata kai
wani gyara dabatama san kanshi ba, mai lalle namata hadadden gaske, aka kunna fanka
banda AC dakin sabida lallen yay yabushe da wuri, duk wani shirin Amarya da ba'a
rasaba saida suka mata harda wankan turare sanan akasa tai salla duk sukai salla,
wuraren 5 makeup artist tataho aka shiga yi mata makeup nafitina aka gama tsaf wani
irin kyan datayi kaman balarabiya sanan akasa tasaka wani white gown sky blue
dayasha stones yana jamata kasa sosai sanan aka mata dauri, Fadila ta jawota takai
ta gaban madubi tana murmushi tace "kinga yanda kikai kyau kaman fatalwa kuwa"
kallon kanta Rahima tayi kafin ahankali takalli Fadila tace "mesa kuketa min
kwalliya haka?" dariya dukansu suka kwashe da sauri Nabila tazo wajen rikeda
Princess tace "ki tambayi Ya Sameer, bari kiga mu shirya Fadila" shiryawa suka hau
yi cikin wani hadadden kaya dasukai anko itada Fadila, sunacikin shiryawa Noor yay
knocking yace "baby all set fa" da sauri tace "we are coming out yanzun nan Baby"
music sukaji yana tashi daga compound shiryawa sukai tsaf sanan suka fitoda Rahima
dasuka rufemata fuska da net suka fito tsakar gida da ita Ya Sameer suka gani zaune
kan wani royal chair yana sanye da wata bugaggiyar shadda sky blue anko shida
Rahima, ga wasu friends dinshi da su Noor sukai inviting saikuma su kannenshi da
sukasha white shadda da some few friends da matayen su, basu da yawa but gwanin
tsari zaunar da Rahima kusada Sameer sukayi, aka shiga party ga abinci dan masu
girki aka bama kwangilan girki ga drinks, Rahima dai kallonsu take ganin anamata
abu kaman wasu ango da Amarya, Sameer yariga yafadi musu baya rawa so basu damai ba
su suka dinga shirmen su daga baya suka dauko Rahima dataki tai rawan, kallonsu
kawai Sameer yake ganin yanda family dinshi are so happy da auren shi dudda ga
yanda auren yazo zaiyaji inama Ummi was here yasan da abin yafi haka haduwa......
Wuraren Magrib aka gama sanan yasa aka dakatar da wakan suka fita masallaci, SU
fadila sukai ciki da Rahima suka chanza mata kaya zuwa wani fine lapaya bayan sunsa
tai salla sanan suka hada mata wani nagani tasha da kyar yana dawowa ya shiga mota
yace afito da ita zasu tafi Abban ta na hanya, fitowa da ita sukayi, sukasha ta
shiga gaba Sameer yaja motar zuwa gidanshi, gidane nagani nafada danya tsaru sosai,
horn yayi wasu sojoji guda biyu taga sun budemusu Gate Sameer ya shiga da motan ya
kashe yafito, ahankali tabude itama tafito tana kallon ko'ina saida ta zagayo sanan
yafara tafiya binshi ta shiga yi har zuwa cikin gidan, innalillahi heaven shine
furnitures din da aka zuba mata, duplex ne gidan hadadden gaske komi yahadu tsayawa
bada labarin gidan bata bakine, horn dasuka ji yasa yace "sit Abban ki ne yazo"
fita daga dakin yayi hakan yasa ta zauna ahankali tana tunani dakuma fargaban
haduwa da Abban nata, sallaman Abban ta dataji yasa ta dago kanta da sauri suka
hada ido da Abban dake kallonta, bakinta nadan rawa rawa tace "in...ina wuni Abba"
zama yayi kan daya daga kan kujeran Sameer yazauna akasa ganin Sameer yazauna akasa
yasa ta kallai sai itama ta zauna ahankali akasa, gyaran murya Abba yayi anatse
kafin yafara da salatin Annabi ya kalli Sameer yace "Sameer kai d'a ne dakowani
mahaifi inhar Allah yabashi irinka to ya godema Allah, you are a treasure dat
personally I cherish, And Alhamdulillah for knowing in this life and Alhamdulillah
da mutum kaman kai mai hankali ilimi yazamo miji ga yardana haifa, koma mezan
fadama kariga kasani, kuma komame zan fada maka awanan daren you've already done
that even more Sameer dan cewa zanyi ga Rahima nan matarka kariketa amana but
kariketa amana tun kafin ma tazama matar taka, da ayau zanfadi namutu I will be at
peace because nasan mutum kaman natare da y'ata kuma zai riketa amana, Allah yamaka
albarka Sameer, Allah yabuda maka kofofin samu, sanan Allah ya azurtaku da zuri'a
dayyaba Allah yabiya maka bukatunka na alkhairi Sameer" ahankali Sameer yace "Ameen
Abba" juyawa Abba yayi ya kalli Rahima da tunda taji Abba yacema Sameer Rahima
matar shi taji kirjinta yamata nauyi, ahankali yace "Rahima! Ayanda kika taso da
rawan kai aure kan natsar da yara irinku saisa namiki zabi zabin kuma Sameer ne, na
daura miki aure da Sameer jiya misali 9 nadare, ga sadakin ki nan" yaciro wasu kudi
dake envelope ya ijiye agefenshi kan kujera, yace "inaso ki natsu Rahima ki tuba,
yanzu ke matar aure ce ki zubar da duk wata dabi'unki na banza, nina fadama Sameer
makarantan ma yahanaki zuwa at all, yacemin zaki cigaba amma saikin chanza nan da
next year, Rahima ni mahaifin kine kuma mahaifi baitaba tsanan abinda ya haifaba
saidai ya hukunta abinda ya haifa idan yaron yay badaidai ba, duk wani abu dana
aikata akanki sabida halinki ne, wanan auren da namiki shine last chance din
danabaki, Rahima inhar baki zauna a auren ki ba kin natsu kin zubar da halayen nan
naki na banza ba to ki rubuta ki ijiye saidai ki nemi wani uban da wasu yan uwan
dan zanma cireki daga cikin yayana ne, kuma you know what I can do, ga mijinki nan
kimai biyayya, yi