Showing 84001 words to 87000 words out of 197960 words
yafada ne dan karna
maidata kauye yakaita rehab" wata zuciyan yacemai karka yarda harsai kaga sunzo
anjiman shida yan uwanshi da isha'i sunzo adaura auren sanan saika yarda, tayaya ma
mutum kaman Sameer zai auri Rahima, haka Abba yazauna ya kwance ya kulla ya kwance
ya kulla shi kadai yakasa yarda cewa Sameer zai auri Rahima.
Har cikin Rehab din ya shiga sanan yafito yana kallon yanda take kuka har lokacin,
ya zagayo yabude mata kofa yace "come out" fitowa tayi tana goge kwalla dasuka kasa
saina zubowa yace "idan kikai mistake din sake guduwa daga nan wlh sainabar
mahaifinki ya maidake kauyen" girgiza mai kai tayi cikin kuka da sauri tace "wlh
bazan gudu ba, dan Allah banso na koma kauyen nan" tasake rishewa da kuka, dauke
kai yayi yace "follow me" office din likitan dayamata registration receptionist
takaisu likitan na ganinta yay dariya yace "oyoyo our run away patient, munsan zaki
dawo all your things are intact, gadonki ma haka" yana maganan ya kwalama Asabe
kira. "Asabe" da sauri Asabe ta shigo sanye da kayan security dinta, Rahima yanuna
mata dake gefen Sameer tana share hawaye yace "take her, let her change to uniform"
shigowa tayi tai wajen Rahima tareda kama hannunta tace "mutafi" binta Rahima tayi
tana waigen Sameer da yabisu da kallo tana kuka sosai mara kara Asabe tarufo musu
kofan, kallon Dr Sameer yayi yace "hope babu wani matsala and she's not too late?"
da sauri Dr yace "not at all Lieutenant, babu wani matsala ai patient naguduwa haka
is not new, adawo dasu and we continue with the treatment, burinmu subar shaye
shayen kawai" gyadakai Sameer yayi yace "take extra care of her please, asamata ido
sosai, like I don't even mind nai extra payment inhar zaku sata on 247 watch"
ahankali Dr yace "you can count on that, basai ka biyaba, normally wayanda suka
gudu aka dawo dasu anama chanza musu daki, dakin daza'a mai dasu bazama su dinga
fitaba all treatment nasu anan ake musu sunda bayinsu awajen and security da nurses
dake kula dasu basa barin wajen, karka damu I assure you baxaka ji bad news din da
kaji da ba" gyadakai Sameer yayi tareda mikamai hannu suka gaisa yace "thank you
Dr, I'll be on my way now" "alright Allah kiyaye hanya" wucewa yayi yafita tareda
shiga motarshi yarufe yafita daga rehab din yadau hanyar dazai kaishi gidan Baffa
shi gabanshi nadan faduwa, wayarshi yaciro while driving yay dialing number Baffa
yakara akunne, ringing daya Baffa yadauka cikeda girnamawa Sameer yace "barka da
rana Baffa" daga tachan bangaren Baffa yace "barka da maraice dai Sameer, abinda
yay karfe biyar da rabi ai yay dare" gyadamai kai Sameer yayi kafin ahankali yace
"Baffa kana gidane ko wajen aiki inaso nazo na ganka" cikin yanayin magana na manya
Baffa yace "too ni gani a gidanku nazo nemanka kaima kana nemana, kazo nan gida
kawai ina jiranka, gani nan tareda mahaifiyar ka da kannenka shigowan su kenan ma
sun taso daga wajen aiki" ajiyan zuciya Sameer ya sauke yace "to gani nan zuwa"
kara gudun motarshi yayi harya shigo anguwarsu dake nan sabuwan GRA, horn yayi aka
budemai mota tun kafin yay parking Mu'az yafito dagudu yazo wajen parking space din
ya tsaya, parking Sameer yayi murmushi kan fuskarshi yabude motar yafito da gudu
Mu'az yazo yace "oyoyo Ya Sameer" yafada jikinshi, kanshi Sameer ya shafa yace "how
you?" dagowa Mu'az yayi ya kalleshi ashagwabe yace "fine Yayan mu, Yayan mu I miss
you wlh tunda nadawo kai tafiya bakanan, ya hanya?" ahankali Sameer yace "lpy lau"
sanin Mu'az cikashi zaiyida surutu yasa yace "Baffa na falo ko, let's go"
Suka wuce, sallama yayi suka shiga hadadden falonsu inda Baffa da Ummi kadaine ka
falon Ummi kan dogon kujera Baffa kuma sanye da manyan kaya kan 1siter suna hira
saisu Noor da Muhammad dake dining dukansu suna sanye da suits sunacin abinci
alamun daga aiki suke, shigowa falon yayi anatse yakarasa inda Baffa yake cikeda
girmamawa yadan duka yace "ina yini Baffa" murmushi Baffa yayi yace "lpy lau
Sameer, kadawo lpy yanzu mahaifiyar ka ke cemin kaje gombe wani aiki aiko naga news
din ashe kaine behind it, you are good my son haka akeso mutane kuma irinsu
Wadugaga Allah yakara kara tona musu asiri aduk inda suke adoron kasan nan, sukuma
yaran Allah ya saukesu lpy Allah yabasu lpy" atare kowa na dakin yace "Ameen" tashi
yayi yajuyo ya kalli Ummi data zubamai ido kaman tana kallon TV ganin dukya rame
mata kusada ita yazo ya zauna ahankali yace "ina yini Ummi na" murmushi tamai tace
"andawo lpy soja" gyadamata kai yayi, Noor da Muhammad ne suka shigo falon har inda
Sameer din yake kusada Ummi sukazo, Noor yace "sannu da zuwa Ya Sameer ina yini"
murmushi yamai yace "lpy lau Noor, ya office" fine yace yana zama kusada shi
Muhammad dake tsaye dan kujeran tacika yace "ina yini Ya Sameer kadawo lpy,
harkadan rame wlh, ni saisa bazan iya aikin soja ba" murmushi Sameer yayi Ummi ta
harareshi tace "lazy kawai" dariya yayi yakoma kan kujeran Mu'az yake zaune ya
zauna. Ummi ta dubi Sameer tace "go and freshen up Baffan ka wajen ka yazo" girgixa
kai yayi yace "nima akwai maganan danake so naida Baffa, anjima I will freshen up"
ganin haka yasa Baffa yatashi yana gyara babban riganshi yace "okay bismillah muje
sama" tashi Sameer yayi yabishi sukai sama, dakin marigayi mahaifinsu suka shiga
Baffa yazauna kan kujera shikuma Sameer yazauna akasa, zama Baffa ya gyara yace "I
hope magana zakamin kan zancen da I am sure kasan shine yakawo ni gidan nan this
evening" dagokai Sameer yayi jin anbude kofa Ummi ce ta shigo dan takasa hakura so
take taji koyasamo matarne, waje tasamu tazauna tareda gyara zama, Baffa ya kalli
Sameer dayasake maida kanshi kasa yace "go on Son gani ga mahaifiyar ka we are
listening" ajiyan zuciya ya sauke tareda fuzar da iska gabanshi nafaduwa ahankali
yace "Baffa nasami wacce zan aura!" babu wanda yay expecting wanan maganan daga
bakin Sameer, wani irin murmushi Ummi harshi Baffa sukayi, kafin suce wani yace
"Baffa ina neman alfarma daya" da sauri Baffa yace "mecece alfarman Son?" kanshi
akasa yace "inaso yau dinan zamuje kudauramin aure da ita I've already promised
babban ta from now zuwa lokacin isha'i zamuzo" shiru duk akai a dakin kafin Ummi
tace "wanan wace irin magana ce haka? Bikin ka damuke muyi nagani nafada, babban
d'ana my first son is getting married kazaci karamin biki zanyi ne eh Sameer"
ahankali Sameer yace "that will all come later Ummi, dan Allah Baffa yau dinan
nakeso a daura auren" Baffa ne ya wurgomai tabaya yace "why are you so in a rush to
get married kaida ba auren kakeso ba, why are you pressuring us muje a daura auren
this night?" Baffa ya wurgomai tambayan yana kallonshi, faduwa gaban Sameer yayi
yay dan shiru yakasa magana Ummi tace "badakai ake magana ba Soja" dan dagokai yayi
ya kalleta kafin yamaida kanshi kasa ahankali, Murya chan kasa yace "sabida inaso
na taimaki yarinyar ne" da sauri Baffa yace "taimako? Taimako? Wani irin taimako
kuma, Sameer wacece wanan yarinyar dakake so ka aura?" shiru yayi gabanshi nafaduwa
baya karya kuma baima iya karyan ba, and koda family shi will find out anything
akan Rahima yafiso su faraji daga bakinshi, but yasan his family bazasu yardaba.
"Sameer Simran!" Ummi takira full name nashi dan ayanda yakeyi yafara sa tana tsoro
itama tace "ba tambayanka abu Baffan ka yayiba" ahankali ya sauke ajiyan zuciya
yace "she is Rahima a drug addict" atare daga Ummi har Baffa suke kallonshi, cikeda
kokonto tsabagen son ta gasgata abinda kunnuwanta suka jiyomata tace "yar shaye
shaye kake nufi Sameer?" gyadamai ma Ummi kai yayi batare dayabari sun hada idoba
yace "yes tana shaye shaye, yanzu haka tana rehabilitation centre, inaso na aureta
because I want to help her, inaso na taimaki rayuwanta, change her duk tabar shaye
shayen tadawo yarinyar kwarai natsassa, I want to do jiha......." "are you mad
Sameer?" Ummi tadakama Sameer wani mahaukacin tsawa tace "Sameer anya maganganun da
akeyi akanka ba gaskiya bane kuwan, anya bakada aljanu?" girgixa kai yayi yace
"Ummi lafiyata kalau, I know what am doing, taimakon ta zanyi" "kaci uwaka da
taimakon" tabugamai uban dakuwa da hannu cikin fushi sosai tace "for good 39yrs
yanzu Sameer fama mukeyi dakai kayi aure kaki, kanenka duksunyi aure sun hayayyafa,
yanzu da mukai pressuring naka ganin u are not getting any younger, Baffan ka
yabaka 30days kafito da wacce zaka aura, dakaga 30 days din sun cika shine kazo
kana cemana yar shaye shaye zaka aura Sameer, nice zaka auroma sirika yar shaye
shaye, shaye shayen natama haryay worse and dangantata da rehabilitation centre
shine zaka auromin?, wasa kake yaro, gwarama kafito da wacce zaka aura kabar
maganan wanan yar shaye shayen dakakeyi" Ummi ta shiga masifa shiru yayi yanajin ta
harsaida tagama tai shiru sanan ya dago kanshi ya kalli Baffa daya tsareshi da ido
dahar yanzu baicemai komiba sanan ya kalli Ummi kafin yace "am sorry Ummi and
Baffa, ita nakeso na aura idan kuma bazaku barni ba shikenan bazan iya ja da
maganan ku ba amman saidai nahakura da auren har abada" yakara she maganan
ahankali, tashi Ummi tayi cikeda fushi tafita daga dakin abakin kofar dakin ta
tsaya ta kwalama su Noor dake hiransu akasa kira. "Noor, Muhammad, Mu'az kuzonan,
you guys should come and talk sense to kan yayan ku, ni yayanku zai auroma yar
shaye shaye, kuzo kumai magana" tashi yaran sukayi duk atsorace this is the first
time sukejin fadan Ummi da Sameer karara sukai sama duk dakin suka shiga Ummi
tanuna musu Sameer dake zaune akasa kanshi akasa tace "kunga yayanku ko Noor yazo
yana cemana yar shaye shaye zai aura da tsabagen shaye shaye ya taba kwakwalwanta
har aka kaita rehab dan ai wayanda brain dinsu yatabu ne sabida shaye shaye ake
dangantasu da rehab kunga wanku wai itane zai auro, kuma da daddaren nan yake so
aje wajen babanta adaura auren" ganin yanda Ummi keyi yasa Noor yace "Ummi calm
down ki zauna please" zama tayi kan kujera tana kallon Sameer din, Noor ya zauna
akasa kusada yayan nashi sauran ma suka zauna ya kalli Baffa yace "Baffa menene me
yake faruwa?" shiru Baffa yayi baice komiba yana kallon Sameer din, gyaran murya
yayi yace "Sameer me kake cewa inhar muka hanaka aurenta saidai ka zauna ahaka
bazakai aureba?" ahankali Sameer yace "Baffa ita kadai ce wacce raina keso ya aura
badan komiba sabida inaso nai jihadi na taimaki rayuwanta, inkuma kun hanani bazan
muku gardama ba amman ni bazanyi aureba kuma dan banda wata wacce nakeson kuma na
aura" cikin wani irin yanayi Baffa yace "haka kace?" shiru yayi Baffa yadakamai
tsawa yace "I said haka kace Sameer?" gyadama Baffa kai yayi ahankali batare
dayabari sun hada idoba hakan yasa Baffa ya karkada kafa yace "good" ya kalli su
Noor yace "kumutashi muje masallaci ankira magrib muyi sallan magrib daganan mu
wuce muje mu dauroma yayanku aure" da sauri Ummi ta tashi tsaye tace "Baffa!" hannu
Baffa ya daga mata yace "kibarshi Sameer ba yaro bane yanada shekaru arba'in ba
daya, Sameer yasan difference tsakanin right and wrong, sanan yasan in yan uwanshi
sun yarda da abu dakuma in sunki, duk yasani, da ace shi yarone kaman su Noor da
Mu'az da zamu iya hanashi amma yariga yawuce wanan stage din yasan meyake yi, if he
choose this path dudda kin nunamai bakiso yace zaiyi ki barshi ba karamin yaro bane
shiba, ni waliyinshi ne am only going there na sauke nauyina da hakkokina
amatsayina na kanin mahaifinshi kuma mahaifinshi banda haka kuma babu komi, duk
yanda yayi daidaine Allah bada sa'a" da sauri Sameer yace "Baff...." hannu Baffa
yadagamai yace "I've given you that chance na magana and you've said wat u wanna
say dan haka tashi mutafi banson jin wata magana daga gareka" shiru yayi yakasa
tashi, "katashi mutafi nace!" ahankali yatashi yakasa daga ido ya kalli Ummi datake
binshi da kallo cikin tsantsan bacin rai gaba Baffa yayi yakalli su Noor da duk
suka tsaya yace "kumuje" binshi duk sukai abaya suka fita Sameer kaman kwai
yafashemai aciki kasa fita yayi ya tsaya awajen kofa kafin ahankali yajuyo ya kalli
Ummi suka hada ido baki yabude zaiyi magana Ummi tace "banson ji just go Allah bada
sa'a" tai kwafa, zaiyi magana Baffa ya kwalamai kira daga kasa da sauri yafita duk
ranshi badadi yasame su, batare da Baffa ya kallai ba yace "kira baban yarinya kace
muna hanya" gyadamai kai yayi ahankali kannenshi sai kallonshi suke yaciro waya yay
dialing number Abba.
Abba na zaune a dining su Siddiqa sun ijiyemai abinci yakasa shi expecting call din
Sameer kawai yake yakira yacemai wasa yake yay hakane dan karya kaita kauye yaji
wayanshi na ruri, da sauri ya dauka yakara a kunne, kafin yay magana Sameer yace
"Abba Baffana yace nafadamaka we are on our way" Abba couldn't believe abinda
kunnuwan shi suka jiyemai yama rasa mezaice da kyar ya tattaro yan kalaman bakinshi
yace "Allah yakawo ku lpy" katse wayan Sameer yayi Baffa yace "kumu tafi" fita
sukai daga dakin, sukai wajen Gate Baffa yaciro kudi masu yawa yamikama Mu'az yace
"kaje tsallaken titi kasayo goro da sweet, kaje da gateman yatayaka dauka, kasamemu
a masallaci" gyadamai kai Mu'az yayi yana kallon fuskarshi Baffa yawuce yafita
yaran biyeda shi.
Kasa yarda Abba yayi da kyar ya lalubo number babban aminin shi Baban Aisha
yakirashi yacemai yazo yanzu dan Allah, sanan yakira Chairman din NDLEA duk sukace
mai gasunan zuwa, tashi yayi ciki dan ya shirya.
Akusan tare su Sameer da abokan Abba suka iso, shima Abba daman yashirya yaci gayu
yana hango motoci yafito daga gidan ahankali yana kallon kowa yama kasa yarda,
gaggaisawa aka shiga yi shi kanshi Sameer saida yay mamakin yanda Baffa bai nunama
Abba komiba saima wani gaisuwan mutunci da aka shiga yi kaman ansan juna da dadewa
gabaki daya sanan Abba yanuna musu masallaci yace "mu shiga, Bismillan ku yanzun
nan aka idar da isha'i nariga na sanar da limamu zuwanku kumuje" atare aka dunguma
aka shiga masallaci.
Zazzama akayi limam yafara gabatar da huduba kafin ya daura aure tsakanin Sameer
Simran Sameer da Rahima Sambo Rikadawa, inda Baffa yaciro sadaki dubu dari da
hamsin wanda sune kudin dake jikinshi yabiya mai Abba yakarba sadakin shafa fatiha.
Sanan aka shiga gaishe gaishen farin ciki Sameer kanshi akasa yana zaune kawai
shikadai yasan me yakeji, Mu'az yakawo sweet da goro limam yadeba yace za'a rabama
jama'a gobe sauran Abba yasa gateman dinshi yay gida dashi, su Siddiqa na zaune a
falo sukaga gateman na shigowa dasu goro, Zeena ne tace "na menene?" washe baki
yayi yace "Alhaji yace nakawo gida nabarshi masallaci dawasu manyan mutane" yay
maganan tareda juyawa yafita daga dakin.
Tattaunawa aka shigayi inda Abba yamasu Baffa introducing kanshi, sosai Baffa ya
yaba da hankalin Abba ashe babban mutum ne kawai dai irin iyayen nanne dat are so
unfortunate Allah yabasu yara marasa ji, ko kadan bai nunama Abba komiba har
wajejen goma suka tashi aka shiga sallama aka tafi, ahankali Sameer ke biye dasu
suka tafi Abba nadaga musu hannu, sanan Abba yakoma gida ranshi fess, kaman anmai
kyautan aljanna, falonshi ya shiga yana murmushi Luba tace "Abba goron nan da sweet
na miye?" murmushi yayi yace "don't worry my daughters I promise kaina sai mamanku
tadawo sanan zan baku good news din" duk washe baki sukayi ganin Abba na farin
ciki, yace "zan shiga study room dina, inkun gama ku kwanta" yay maganan tareda
juyawa yafita yay study room dinshi, bude dakin yayi ya shiga ya zauna tunane
tunane yake fall ranshi sanan ya kunna computer dinshi, wani page na italian world
ya shiga kafin yadau number wajen da sauri yay dialing number da sauri yakara
akunne saiyay magana. "I want full house furniture na royal Italian"...... Washe
baki kawai Abba yakeyi yana wasu bayanai da banso kuji😛
[6/30, 10:17 AM] Marsy😘: 57....
Fashewa da kuka Mummy tayi taci kuka harta godema Allah, ranan haka tawuni cikin
kunci da bakin ciki, gawani kishin jaraba dake cinta kaman zata hadiyi zuciya
tamutu, hatta y'ay'anta kasa gane kanta sukayi. Wanan kenan.
Yana zaune a office dinshi har yamma baimasan a ina zai kwana yauba dan yan
interior company nan nagidanshi a auna nan a auna chan anata kawo kaya, he is so
worried akan Ummi dake fushi dashi, knocking kofarshi akayi hakan yasa ya kalli
kofan tareda rufe system dinshi yace "common in" bude kofan akayi Noor ne da
Muhammad suka shigo duk sunamai murmushi saikuma yaga matayen su rikeda yaransu a
hannu sunci gayu hakan yasa yatashi kafin yaga Mu'az ya shigo rikeda wani cake da
aka rubuta happy birthday ajiki da happy married life ga uban balloons, dan zaro
ido yayi like wats all this, maida kofan Nabila tayi tarufe Mu'az yakaraso ya ijiye
fine cake din kan table dinshi tareda kunna fireworks din hakan yasa dukansu
sukahau mai waka. "happy birthday to you, happy birthday to you, Happy birthday to
Yayan mu, happy birthday to youuuu, hip hip hurray" sukahau tafi, murmushi yayi
yazagayo hannu yasa yakarbi Princess daketamai dariya Nabila tace "ina yini Ya
Sameer" ahankali yace "lpy lau" sanan ya kalli jaririyan Fadila ya shafa kumatun ta
yace "babygirl you came to my office today" duk dariya akayi Fadila tace "happy
birthday yayan mu, ina yini" ahankali yace "Alhamdulillah" sanan yanuna musu dogon
kujeran office din yace "ku zauna" sanan ya kalli Noor da Muhammad dake tsaye yace
"ku zauna" zama sukayi kan kujeran dake gaban table yanunama Mu'az stool yazauna
shima kafin ya koma kan kujera ya zauna rikeda princess yay murmushi tareda kallon
cake din yace "I've forgotten yau birthday dina ma" yasake murmushi sanan ya kalli
Noor yace "thank you guys" akadanyi shiru, ahankali Noor yace "Yaya Sameer, I came
here we all came here not just for this" ya nuna cake, yace "Ya Sameer tun ina dan
karami I watch how you live your life akan gaskiya dayin abubuwan gaskiya, one
thing dana sani kanka haryau har gobe shine you don't just do things anyhow kome
kayi I know akwai reason behind it, Ya Sameer ko prostitute today kace zaka aura I
will support you dan nasan kasan me kakeyi, I trust my brother and I stand with you
in every step you take, worry not okay, Ummi zata sauko itama I assure you this"
ajiyan zuciya yasauke yana kallon cake din kafin ahankali yace "there's more to wat
am doing ku kannai nane dole ma sanar daku, banso iyaye susan maganan dan ba
hurumin mu bane mutona mata asiriba is left for Abban su should find out dakanshi"
labarin Rahima yashiga basu tatas, duk dakin dama Fadila da Mu'az sune masu saurin
kuka saida sukayi, Sameer yace "I just see Rahima kaman kanwar mu su Asiya and
Yusra, I look at the whole case like look at Princess, ga babygirl all of them are
children nobody knows tommorow, lemme save this girl dan nima inada kannai da
y'ay'a mata, and if by saving her from that wicked is by marrying her am ready to
do it, shikenan" tasowa Mu'az yayi da sauri yafada jikin Sameer yahau kuka,
ahankali Sameer yay patting bayanshi yace "kaga nahanaka kuka u see princess namaka
dariya" dagokai yayi ahankali ya kalli yayan nashi yace "Ya Sameer I want to