Showing 186001 words to 189000 words out of 197960 words

Chapter 63 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15033

shegen zurfin ciki da taurin kai shi adole soja zaima ijiye batun
sojane atoh, ganin 10min din data dibanmai aranta yacika baimata maganan ba yasa
tai gyaran murya tace "ammmm Sojana nakira kane kan batun Rahima" wani irin ajiyan
zuciya ya sauke da saida Ummi taji karan ijiyan zuciya ya kalleta batare dayay
magana ba, anatse Ummi tace "dama nakiraka ne kawai dan karna tauye hakkin ka
amatsayin ka na mijinta" tai dan shiru sanan tace "abinda zan fadimaka shine zan
maida Rahima makaranta, inaso tadinga zuwa kullum tareda direba sabida sun fara C.A
wai sunma gama C.A yanzu suna shirin rubuta exam ne, banso yarinya tai wasting time
gwara tacigaba da zuwa makaranta abinda, koya kagani?" Ummi tamai tana kallonshi,
jiyayi ranshi ya mugun baci da batun makaranta ko kadan baimaso takoma makarantar,
ganin yanda Ummi ta tsareshi da idanu yasa ahankali yace "dama naso tabar school
dinne tunda vet ne, inyaso next year zata sake waec tai applying for medicine" da
sauri Ummi tace "inaaa hakan gaskiya bazai yuba Sameer, so kake yarinya taita zama
agida har next year? Gwara dai tacigaba da vet din ahaka no education is a waste,
banda hakama experience ne da zaman gida kwakwalwanta yayta dodewa gwara tacigaba
da zuwa vet din ahaka har zuwa next year tai applying wanan medicine din kawai
shine" kasa magana yayi ganin Ummi bamata shirya bashi matarshi ba yay shiru
kirjinshi har tafarfasa yake, ganin yakasa cewa komi Ummi tace "direbana zai dinga
kaita kullum randa kuma bai sami daman zuwaba sai tahau adaidaita" tai maganan
danta kuleshi sosai, cikin dan fushi yace "ni matana bazata hau motar hayaba" yanda
yay maganan saida Ummi tabude baki ta kallai, shi kanshi baisan lokacin da maganan
tafito ba, cikeda ban mamaki Ummi tace "to dannan me kakeso matar naka tahau tunda
bakason motar haya?" murya chan ciki yace "zan turo wani direbana sojane shi zai
dinga zuwa yana kaita" ahankali Ummi tace "to angode shikenan, tashi katafi wurin
aikin ka" tashi yayi ahankali yacire pillow ya ijiye kan kujeran daya tashi akai
yajuya yafice da sauri, dan dariyan manya Ummi tayi tace "zakaci gidanku ne dan
banzan yaro"
[23/07, 10:12] Aishat Muhammad: 99




Ganin har 9 bai aiko da direban ba yasa Ummi ta danna mai kira, dauka yayi kafin ma
tai magana yay magana ciki ciki yace "yana hanya" ya katse wayan murmushi Ummi tayi
ta kwalama Rahima kira. "Rahima, Jewel wai kinshirya kuwa?" saukowa da sauri Rahima
tashiga yi, tana sanye dawata hadaddiyar doguwan riga mai ruwan toka ta yana
hadaddiyar gyalen rigan fararen kafafunta cikin wata black flat shoe, hannunta
rikeda wata yar jaka da littafai ke ciki tana tafiya ahankali harta karaso kasa
tana murmushi Ummi na binta da kallo dantai bala'in kyau kaman ba itaba, murmushi
Ummi tamata tace "har an shirya kenan sudai Siddiqa sungaji da jiranki sunyi
tafiyan su a binsu" murmushi tayi tace "Ummi sune sun fiye iya saurin shiryawa
barin ma Ya Luban nan" dariya Ummi tayi daidai zatai magana sukaji an danna uban
horn da sauri Ummi tace "yauwa tashi ga direban da Soja yaturo miki chan shizai
dinga kaiki sanna yadawo ya dauke ki" gyadama Ummi kai tayi ta nannada gyalen
akanta looking so decent tace "to Ummi bye" hannu Ummi tadaga mata tace "Allah
kiyaye hanya" Ameen tace tawuce tafice tako tarar da direban yana sanye da kayan
sojoji yana tuka wata hadaddiyar mota, yana ganinta yafito da sauri cikeda
girmamawa yace "good morning madam" yay maganan yana bude mata kofar baya, ahankali
tace "good morning" sanan ta shige yamaida kofar yarufe ya shiga gaba yajata
sukabar gidan har zuwa school, har gaban department dinta yakaita ita abinma yabata
mamaki yanda yasani tasan hala Ya Sameer ne yafadi mai.


Saukowa tayi ahankali tana kallon ko'ina tana tunani rabon ta da school harta
manta, ahankali tashiga tafiya har zuwa gaban department dinsu.




Ajinsu, bude kofa tayi ta shiga duk an zazzzauna kaman lecturer ake jira duk an
kafeta da idanu chan karshen class tayi tai zamanta tareda sauke ajiyan zuciya dan
tafiyan nan datayi jitayi ta bala'in gaji, ko 3min batayi da zamaba wani lecturer
ya shigo ajin, lectures yamusu na 2hrs 30min sanan yay using sauran 30min din
yamusu test, tadanyi kokari a test din ba laifi sanan ya karbi scripts din tatas
yawuce yafita, yan ajinma suka shiga fita yatsine fuska tayi jin tawani irin gaji
kafafuwantama kaman kumbura sukayi, tashi tayi ahankali ta kalli kafafunta ganin
sunyi suntum yasa abin yabata mamaki tadauki jakarta ahankali tafara takawa sosai
taji tagaji komi nata ciwo yake bamatason taje department dinsu Siddiqa har zata
fita taga students suna dawowa hakan yasa takoma itama takoma chan kujeran ta ta
zauna danta lura wani lecturer ne yazo, zama tayi ahankali tawani irin bala'in gaji
shigowa lecturer yayi yamusu 40min test sanan yashiga ymisu lectures danso yake yay
covering, almost 3hrs yadauka tanaji musu lecture tun tana ganewa hartazo bata
ganewa gabaki daya jitayi ma zazzabi zazzabi na rufeta da kyar suka samu lecturer
yafita shima sabida yanda dalibai keta cemai zasuje suyi salla ne wuraren 2:30
yafice sanan tadauki jakarta ta mike da kyar ta iya ta tsaya jikinta wani shegen
ciwo yake mata dabama tasaba dashiba haka tafito tana tafiya ahankali kaman wacce
kwai ya fashewa aciki, masallacin department dinsu ta lallaba ta shiga, sanan tai
bangaren bayin mata, wani irin wari dataji yasa cikinta yawani murda tahau kwarara
amai a corridor bayin kafin ma tashiga ciki sai sannu ake mata, amai sosai tayi
sanan wata sister ta taimaka mata tabata pure water ta karba ta kuskure bakinta
sanan tafito ahankali tana nishi alwala ta daddage tayi sanan tawuce ta shiga
bangaren mata zama tayi ta jingina da bango tana nishi inda tanada waya data kira
Ummi, kuma yau dinma mantawa tayi data taho da wayar Ummi dan da wayar Ummi take
wuni a wurin ta, wani irin mugun zazzabi takeji bana wasaba, almost 3min tayi sanan
ta gyara zamanta tai salla azaune sanan tadan kwanta tana lumshe ido ko minti biyu
batayiba wani irin bacci mai shegen dadi ya kwasheta awurin, har akai la'asar bata
tashiba dayake bangaren matane ba'a wani cika shigowaba, har akai magrib bacci take
bacci mai bala'in nauyi da dadi danko kiran sallolin da akeyi bata jisuba.



Tun 4 Soja direban da Sameer yaturo mata yake gaban department dinsu, dan Sameer
yacemai by 4 zai dinga zuwa yana dauko ta kullum, ganin har 5 tayi yasa yafito daga
motar yataka har zuwa ajinsu dan saida ta shiga ajinsu yaga shiganta dazu sanan
yawuce yatafi wanan kuma order Sameer ne, har gaban class dinsu yaje yaga babu kowa
aciki, mamaki abin yabashi yace to tuntuni suka gama lectures ne tawuce ta tafi
gida kokuma taje siyo wani abu ne, tunanin haka yasa yace bari yakara mata another
30min.
Ganin 5:30 baiganotaba yasa ya dannama Oganshi kira, ringing daya biyu Sameer ya
dauka, cikeda girmamawa ya sarama Sameer kaman yana gabanshi yace "Sir hudu daidai
tamin a school din but banga madam ba, right now ma ina gaban ajinsu but babu kowa
acikin ajin kaman sun tashi" dan jim Sameer yayi ranshi adan bace kosun tashi waya
bata izinin bin motar haya bayan tanada mai zuwa daukanta, akufule yace "am coming"
katse wayan yayi yakira Ummi, ahankali yace "Ummi ahhhh tadawo?" da sauri Ummi tace
"wacece kuma ahhh?" ahankali yace "Rahima tadawo?" da sauri tace "a'a bata dawoba,
su Siddiqa sun dawo suncemin dasuka gana saida suka biya ta department dinta sunga
wai ana musu lectures" cikin dan fada yace "babu kowa a ajinsu yanzu, wayace ta
biyo Public transport ni matata bazata dinga hawa public transport ba, wayace
ta......" tsareshi Ummi tayi tace "ni kake ma bala'i dannan ko matar taka?" murya
chan kasa yace "ni bada ke nikeba" ya katse wayan, saiyau yake dana sanin rashin
bata waya, dama sabida shaye shayen yasa yaki siyamata waya dan zata iya takira
Mummy ko wani yabata, tashi yayi azuciye yadau car keys dinshi tareda danna ma
direban kira yace yatafi kawai maybe tana hanyan dawowa ne sanan ya shiga mota
yafito daga Barrack din yana neman hanyar gida yana isowa gida ana sallan magrib,
masallaci ya shiga yay sallan magrib.



Kaman an tsikareta da allura firgigit tafarka tana kallon ko ina ganin yanda gari
yay duhu yasa taji wani irin tsoro yakamata tunda tafara school dinan bata taba
kaiwa ware haka a makarantar nan ba, ga zazzabi dataji tanaji sosai kotakan tayi
la'asar da magrib ma da akayi batabi ba ta sunkuci jakanta tareda rikewa a hannu
tana gyara dan mininin gyalen ta aka tafara tafiya ahankali tafito gajiya takeji
sosai kaman wacce tun safe ke aikin dako, fitowa tayi tana tafiya ahankali tana
kallon ko'ina harta karasa gaban department dinsu inda ake parking motoci ta nemi
wani dan dakali ta zauna jin bazata iya kara tafiya ba koda nan da chan ne dan
tagajin bala'i, gashi department dinsu shine karshen makarantan kodaga department
dinsu Ya Siddiqa zuwa nata a lafiya lau ma bata iya trekking sai wanan dabamata da
lafiya, ajiyan zuciya tasauke tana sauraron yanda jikinta ke daukan zafi tama rasa
mezatayi yasa kawai tafashe da kuka, ita gashi ba lafiya ballema tacigaba da tafiya
har gate tasami abin hawa yakaita gida, daga masallacin su zuwa parking space kaman
an mata dukan tsiya, ga shegen zazzabi dake nukurkusan ta tana rasa takamaimen
abinda ke mata ciwo ita kawai ta bala'in gaji komi na jikinta ya sage saikuma zafin
jiki sosai. "Assalamu Alaykum lafiya baiwar Allah kike kuka?" da sauri tadago
jajayen idanunta tadago kanta, wani dan saurayi ne yana sanye da normal jeans da
riga sai wasu manya manyan text book a hannunshi, ganin ta tsaya kallonshi tana
kuka sosai yace "I said lafiya kike kuka?" cikin kuka sosai tace "banda lafiya tun
dazu naje mosque sai yanzu natashi dare tayi, bansan tayaya zan koma gidaba kuma
bazan iya doguwar tafiya ba" jin yanda take kuka yasa tabashi tausayi, ahankali
yace "gashi nikuma shigowa na makarantan kenan nazo nai TDB ne sabida exams din
dake gabanmu, tashi to na rage miki hanya kona kaiki sick Bay ne?" da sauri ta
girgiza mai kai tana share kwalla tace "ni gida zani" "to tashi muje" ahankali
tafara yunkurin tashi ganin kaman ma jakan littafan nata nauye sukemata yasa yamika
hannu ya karbe jakan daga hannunta sanan ta iya sauka daga kan dakalin tana biyeda
shi har zuwa yar motarshi mai kyau ba laifi, bude mata gaba yayi ta shiga da zauna
ahankali tareda lumshe ido, ganin ko kofar takasa ja yasa yarufo mata kofar sanan
yakoma mazaunin direba yazauna yace "inane gidanku?" ahankali tana sauke ajiyan
zuciya sabida dan tafiyan nan datayi tace "GRA" ita har mamaki take saikace wacce
zata mutu ai dazu agida ba haka takeba daga dan wahalan nan datasha na zaman
lectures a aji shine ko tafiya na neman gagaranta komi tayi ta gaji.



Sosai gaban Sameer ke bugawa, ita kanta Ummi tun abin baiwani dameta ba dan
acewanta keke napep tabi har abin yadameta ganin ana kiran sallan isha'i ba Rahima
babu alamunta.
Kasa natsuwa Sameer yayi dudda Ummi nacemai hala keke napep din baya gudune yawuce
ya shiga motarshi kawai soyake yabita school din yasake duddubawa da kyau, tada
motar yayi yay reverse yazo daidai bakin anguwarsu zai fita kenan wata mota na
danno kai, bin motar yayi da kallo sai yaga kaman Rahima yagani ciki tana dan
murmushi, hakanan yasami kanshi dayin kwana yabiyo motar abaya, adaidai kofar
gidansu yaga motar tai parking, wani irin bugawa yaji kirjinshi nayi hakan yasa yay
parking anesa da gidansu ya kashe motar yana kallon motar datai parking agaban
gidansu.



Ahankali guy din yabude mazaunin shi ganin zazzabi nukurkusan Rahima take sosai dan
batada karfi ko kadan, rike da jakanta a hannu yafito yamaida kofan yarufe, sanan
ya zagayo ta bangaren Rahima, ganin kofa zai bude tasa ya rataye jakan nata a hannu
kaman yanda mata keyi sanan yasaka hannu yabude mata kofar cikeda tausayinta yace
"fito, zaki iya fitowa?" gyadamai kai tayi ahankali tanadan kakalomai murmushi
sanan tadaddage ta daga kafarta tafito da guda daya, kafarta kawai Sameer yahango
yagane Rahima shine dan bai kashe wutan motarba, innalillahi wani irin tafarfasa
kirjinshi ya shigayi kaman zai mutu, ganin wani kato yakawo mai matar shi gida
harda rataye jakarta a hannu cikin wata irin zuciyan bala'in bala'i yabude motarshi
yafito ko tsayawa maida kofar yarufe baiyiba yana tafiya kaman irin lion King dinan
dayay fushi sosai ya tunkaresu daidai lokacin Rahima takarasa fitowa ta tsaya tana
murmushi ahankali tace "nagode, Allah saka da alhairi" murmushi shima yasakin mata
ya salubo jakarta daga kafadar shi zai mika mata kenan yaji an fizgoshi before
yamasan me yake faruwa yaji saukan mari din gomasha kota ina akan fuskarshi, wani
irin razanannen ihu guy din yasaki da karfi da saida yaja gateman dinsu yafito da
gudu tace "kai lafiya, waye nan"
Azuciye yasa duka hannayenshi ya shakemai wuya kaman zai kasheshi yace "uban me
kake min da mata? Kasan wacece wanan dahar kake sagale jakarta a kafada? Kasan
wacece, kasan matar Lieutenant general? Uwar ina ka kaimin mata tun dazu meka mata?
Me kukayi? Inbaka fadimani gaskiya ba yau saina kashe ka?" yay maganan yana sakin
shi ganin tana tarin mutuwa tareda wani irin wurgashi bayanshi ya bala'in bugu da
gate din karfen gidansu, kaman ma ya karye guy din yay kasa warwas zai koma
wajenshi da sauri Rahima dake kuka sosai taji wani irin karfi yazo mata tasha
gabanshi tace "Ya Sameer dan Allah karka kara dukanshi, dan Allah kaji, Ya Sameer"
shima shigowa gateman yayi yace "yallabai amai afuwa dan Allah ko ahakama ya daku
kaga kaman suma yayi, dan Allah ayahakuri yallabai" wani irin fizge Rahima yayi ya
wurgata gefe ganin haka yasa gateman ya kwasa da gudu yay cikin gida dan yataba
ganin fushin Sameer sau daya kan Mu'az lokacin fara makarantar Mu'az kenan yadawo
hutu daga ABU saida Sameer ya sumar dashi, duksun taru su kwace shi harda su Noor
ina sun kasa saida Ummi tazo, kiran Ummi yayi da gudu dagashi har Ummi dake gyara
hijabi suka fito, ganin yanda Sameer kecin uban wani yaro da fuskarshi tai subi
subu ga jini bakida hanci antaru a kofar gidan ana kallonshi ankasa mai magana ga
yaro kaman ma yasuma ga Rahima zaune akasa tana uban kuka yasa da sauri tai wajen
Sameer hannunshi tarike gam tace "Sameer, Soja, Soja kai look at me, bar yaron nan
haka, sakeshi, sakashi nace" cikin muryanshi dabata iya fita sosai tsabagen fushi
yace "Ummi I want to kill him, nobody dare look at my wife, my property, nobody on
this earth ya isa ya kusanci gonata, inhar nabi ta wanan gonar babu mahalukin daya
isa yace zai bita wlh, inkuma kace zakabi saina salwantar da rayuwanshi, uban me
yakemin da mata harda daukan jakanta? Murmushin uban me yake mata yana kallon min
mata eh? Ummi wlh wlh wlh saiyasan yay babban kuskure, kai Bala bani ruwa saiya
farfado sanan naci uwar ubanshi" ganin Sameer yahaukace tuburan yana neman yay
kisan kai yasa tarike mai dayan hannun cikin calm voice tace "Sameer dubeni kaga,
kalleni nace, Sameer kalleni kaga" cikin masifaffun jajayen idanunshi ya kalleta,
ahankali calmly tace "kasake shi kabarshi haka, ba mamaki ragema matar naka hanya
yayi, sakeshi nace kaji yaron Ummi shi, ragema Rahima hanya yayi ko Rahima" cikin
kuka sosai Rahima ta gyadama Ummi kai, daidai lokacin bala ya kawo ruwan, fizge
hannunshi Sameer yayi daga rikon da Ummi tamai ya fincike botikin karfen kafin Ummi
tace me Sameer ya juyemai duka ruwan sanyin aka ihuu guy din yayi awahale boot din
kafarshi Sameer yasa yawani irin take bakinshi babu tausayi ihu daga Ummi har
Rahima sukayi Ummi batasan lokacin data daga hannu ta kwarama Sameer mariba tace
"haka kadawo mugu mara imani sakeshi Sameer sakeshi" "baza'a sakiba" Sameer yafadi
ahaukace tsabagen kishi abinda baitaba yima Ummi ba kenan atarihin rayuwan shi,
zama Ummi tayi akasa ta rirrike bawan Allah dabata saniba tana kuka sosai tace
"shikenan Sameer hada dani kadaka dan bazan tsaya inga kana dukan yaran wasuba ba
gaira ba dalili angaya maka baida gatane, uban me yamaka sabida yadawo da matarka
kaganta cikin motarshi ka tsaya kaji hujjan shi? Katamvaye su, jibi yanda kake take
yaro da wanan kafirin takalmin naka, haba Sameer abinda zama soja ya mayar dakai
kenan mara imani? Bakada imani Sameer, wlh ka kara daga daidai da hannu daya ka
dake yaron nan ban yafemaka ba duniya walahira wlh kuwa Sameer" wani irin ihu yayi
kaman zai rufe Ummi da duka yace "Ummi!!!" cikin kuka tace "dokanni kawai basaika
min wanan uban tsawan ba" rawa hannunshi suka shigayi yawani irin dakan Gate din da
hannunshi sanan yajuya ya kalli Rahima dake masifaffen kuka yawani irin dagata ya
fizgeta sukai ciki, kwalama Ummi kira tayi tana tutturjewa. "wayyo Allah na Ummi
zai kasheni" Ummi bata wani damu dana Rahima ba na yaron nan tafi damuwa dashi amma
saida tadaga murya tace "inkaga dama karkai mata rai mai bakin zuciya kawai
tambadadde" sanan ta kalli direban ta tace "fito da mota mukai shi asibiti, Bala
daukomin jakata, ka shiga dakina zakaga jakan akan gado" ciki bala yayi da gudu
shida baitaba shiga dakin Ummi ba yau condition yasa zai shiga fitoda mota direba
yayi nan bala da direba suka daga yaron daga jikin Ummi, Bala yace "subhallahi
kaman yanada karaya jibi yanda kafarshi ke lilo" fashewa da kuka sosai Ummi tayi
tace "na shiga uku da halin Sameer zaija a kullemu wlh wlh nagaji, kiran Baffan ku
zanyi nagayamai ina dalili, idan wani yama Mu'az wanan dukan am sure bazai yarda ba
amma shine yakema dan wasu, d'a yafi d'a ne iyye?" "kiyakuri Hajiya, wlh haka
sojojin nan suke, ba daman suga matayen su da wani, basa tsayawa suji hawa balle
suji sauka kashinka yabushe kawai, saisa yanzu duk haukan gayu da yan karya ko Yaya
soja sukaji kinada shi bama mijina tattara wa suke su matsa gefe basu shirya a
aikasu lahira ba" cikin kuka sosai Ummi tana gyara kan yaron kan cinyarta tace "to
ina dalili en, habu yanzu ya kashe yaron nan uban me zaicema Allah? Ina gayawa
Sameer nasha fadamai bafa koda yaushe ake biyema zuciya bafa, zata iya hallaka ka
wlh, ina dalilin wanan zafin zuciya yaron nan dududu nawa yake? Daga ganima kodai
Mu'az ya girmamai ko suzo shekaru daya, haba dan Allah" Ummi yacigaba da kuka sosai
har sukakai asibiti..........



Yanda take kuka tana kwalama Ummi kira kojinta Sameer bayayi, key yaciro yabude
falonshi yajefata har tana bugewa da kujera yamaida kofar dakin yana kallonta wani
irin mugun kallon da baitaba mata irinshi ba, hannunshi yadaura kan belt dinshi
yana kwancewa ganin haka yasa tafashe da kuka sosai ta tashi da gudu tai corridor
dinshi ta tsaya gaban bedroom dinshi zata bude taji kofar a kulle daidai ya iso
wajen hannunshi rikeda belt yana kallonta, make wa tayi ajikin bango jikinta na
kyarma tace "dan Allah kayakuri Ya Sameer dan Allah" shigowa corridor yayi yazo har
jikin bango datake makewa ya fincikota yadawo da ita falo yana rikeda ita idanunshi
sunyi ja, yace "ina kikaje? Ubanme kikeyi a gaban motar yaron nan kinamai murmushi,
ya sagale jakan ki a kafada, uban me kukeyi? Ina yakaiki tun dazu ina kukaje? Meya
miki? Look at your body kin saka wanan gyalen dako wuyanki baigama rufewa ba your
chest and back outside kina juyama maza dashi su sabida suyi sha'awar ki

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login