Showing 75001 words to 78000 words out of 197960 words

Chapter 26 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15038

loose it, cikin Gombe ya shigo hakan
yasa yadau wata hanya bata barin garinba ta shiga cikin garin yana gudu, acikin
wani babban hotel yay parking mai suna Swiss Resort, Gombe.

Jacket din sojojin dake kan kafarshi batare dayasaka ba yadauka ya daura akan
jikinta dan white shirt din daya bata is too transparent yace "put this on" sanan
yafito daga motar babu riga ajikinshi yabude boot din motarshi kasan cewa baya rasa
kaya a Booth dinshi yasa yabude wani leda wata white t shirt yaciro yasaka yamaida
boot din yarufe ya zagayo ta inda take har lokacin tana kuka gashin kanta yay busu
busu yace "wipe those tears and come out" share hawayen tayi tafito ahankali yabi
yagaggun crock shoe din kafarta da kallo wani irin bala'in tausayi yaji tabashi he
wish Abba zai ganta ahaka yaga irin halin daya jefa yarshi da kanshi ciki, maida
kofar motar yayi yarufe yace "follow me" yay gaba tana biye dashi abaya, ahankali
take tafiya dan kaman zata fadi takeji she is totally unwell ne, reception din ya
shiga yanuna mata wani kujera yace "sit here" gyadamai kai tayi ta zauna ahankali
tareda kwantar da kanta kan hannun kujeran juyawa kawai yayi yay wajen receptionist
din yamusu booking daki ya karbi key yadawo inda take yana kallon yanda ta lumshe
ido ahankali yakira sunanta yace "Rahima" ganin bata bude idoba yasa yadanyi
tapping hannunta, bude idanunta dasukai jajir tayi ta kallai ganin she isn't well
at all idanunta sunyi ja sosai yasa yamika mata hannu yace "let's go" ahankali
tamikamai hannu ya riketa ta tashi tsaye da kyar sukai stairs har zuwa dakin
dayakarban musu, bude dakin yayi ya suka shiga, dakin hadadden gaske gawani makeken
gado dayaji farin bargo mai shigen taushi, hannunta yakama har zuwa bathroom yabude
ya shigar da ita ciki har zuwa wajen wanka yace "shower I will be right back"
gyadamai kai tayi yawuce yafita tareda rufomata kofan ya sauka kasa yaje wajen
receptionist din yace "I need a Dr please, call Dr for me, and do you have any
boutique around?" gyadamai kai tayi tace "yes sir, third floor boutique din yake,
will call d Dr for you right away" lift ya shiga yatafi 3rd floor wani babban
boutique ne hakan yasa ya shiga wasu fine dogayen riguna yasaimata guda uku sai
simple gown mai spaghetti hand guda biyu, daya orange daya black ash color, yadau
mata cream, sai takalmi da kai tsaye yasaimata 37 dan yaga batada kafa, sanan shima
yasai t-shirt da wando, yabiya kudi akamai packaging nasu yafito sanan yakoma
dakinsu, har lokacin tana bayi bata fitoba, kayan ya ijiye mata kan gado sanan
yawuce yafita daga dakin yakoma motarshi ya zauna, hannunshi yamika yadau wayarshi
ya shiga saka wasu nambobi kafin yay dialing number, kusan ringing uku aka dauka,
cikin wanan voice din nashi na nuna babu wasa aciki yace "This is Lieutenant Sameer
Simran Sameer I want to speak to Governor of Gombe state please" yay shiru kafin ya
janye wayan daga kunnenshi, ko minti biyar ba'a daukaba same number daya kira
yakirashi back hakan yasa yay picking.....




Takai almost 15 minutes wanka take da ruwan zafi da sabulen data gani a bayin wanda
hotel ya ijiye musu, tadau shampoo da hotel din ya ijiye musu ta jujjuye akan
kitsontadaya tsufa sosai yafara warwarewa dan dama dogayen kalabane dudda bata wani
iya wanke kaiba tarage dauda kan sanan tasake wanka tai brush data dade bata samu
tayiba dan hotel sunyi providing nasu da new brush da tooth paste sanan tadau towel
ta daura akirji tadau wani karami ta daura akanta dan ya tsane ruwan tafito tana
sauke ajiyan zuciya kanta najuyawa, dan kadan tabude kofa ta leka ganin babu kowa
adakin sai TV dake aiki shi kadai yasa tafito dasauri tsigan jikinta na tashi,
ledan data hango akan gado da bakin kaya yadan leko haka data gani akan gado cikin
leda yasa tabude kofan tayi kan gadon, ledan tadaga ta zazzage kayan wanan mai
spaghetti hand din orange color idanunta suka sauka akai dan bazata iya saka sauran
manyan dogayen rigunan ba, da sauri tadauka tasaka babu komi acikin jikinta rigan
kawai tazura kaman ya aunata rigan yamata kyau sosai yakara haska fatarta, anan
kasan dakin ta yarda towel din data cire dan batada karfin komawa bayi ta ijiye
gawani mahaukacin sanyin dataji tafaraji sosai hakan yasa tahau kan gadon taja
bargo ta kudundune sosai tana sauke ajiyan zuciya ko minti daya ba'ayiba bacci yay
awon gaba da ita mai nauyin gaske.



Tareda Dr da receptionist din takiramai yadawo, Dr magidanci ne sosai dudda ba
lallai ya haifi Sameer ba but Rahima kam ya haifeta, yana rike dawani dan babban
kit da kayan aikinshi ke ciki, dan knocking kofar dakin Sameer yayi dan yasan
yabarta tai wanka kafin yabude kofan ahankali ya shiga Dr biyeda shi yakafa mata
idanu ganin baccinta take shrarawa ga towel akasa daga chan ta cikin gadon kuma
kayan dayasayo musune bata mayar cikin ledan ba, maida idanunshi yayi kan fuskanta
daya kara yin ja sosai kaman allergies din yakaru sai pink lips dinta dayay jajir
shima na irin mai zazzabi, towel din data daura akanta yadan zame kasa hakan yabama
gashin gaban kanta daman fitowa sun tattare and all coiled up kaman na karaman
baby, kallon Dr yay yace "common in" shigowa Dr din yayi yana kallon Rahima dake
bacci yace "is she the patient?" gyadamai kai Sameer yayi yakarasa gaban gadon ya
daga towel din dake kasa ya shiga bathroom ya ijiye sanan yafito ya zauna kan
kujera ya kalli Dr yace "kaduba ta" karasawa jikin gadon Dr yayi yabude kit dinshi
dake kasa yadauko wani dan tocula yarike hannun yana kallon yanda fuskar nata yay
wani strange red kaman jini yataru a fuskan yajuyo ya kalli Sameer da hankalinshi
kekan TV yay wanan zaman nashi looking well compose and serious yace "yallabai
yarinyar nan is her skin reddish haka kokuma bahaka bane?" yatsa Sameer yadan kada
yadan kalli fuskarta kafin ya kalli Dr yace "she's not this reddish, just normal
fair girl" gyadamai kai Dr yay yamaida hankalinshi kanta ya kunna torchlight dun
dayake rikedashi yadan duka
yaja naman idanunta yabude idanunta ya haska da tocula hakan yasa tabude shanyayyun
idanunta da sauri jin haske a kwayan idanunta, cire hannunshi Dr yayi daga fuskarta
yace "sannu kin tashi, tashi ki zauna naduba ki, am a Dr, and am here naduba ki,
sorry kinji tashi ki zauna muga" ahankali ta tashi ta zauna tana dafe kanta da
kaman zai fadi akasa ta janye bargon daga jikinta, yanda Dr yaga tana rike kanta
yasa yace "sannu" yay maganan yana dauko stethoscope da abun auna bp ya makala
yakama hannunta yadaura ajijiyanta, wani irin tashi tsigan jikinta yayi hakan yasa
tawani irin sosa wuyan ta cikeda gajiya da yanda tsigan jikinta ketashi ahankali Dr
yace "sorry kinji" yadan juyo ya kalli Sameer dayay kaman baya jinsu idanunshi kan
wayanshi dayake duba wani sako yace "officer yarinyar nan is suffering from chronic
allergies she came in contact with kodai something da jikinta bayaso kokuma wani
abinci taci da jikinta is trying to reject, and she is having maleria, akwai kuma
yunwa tattare da ita, zan samata ruwa yanzu sabida karfin ta yadawo zanyi allura
ciki dazaisa tadawo normal, sanan zan rubuta maka wasu magunguna da bandasu anan
you should go and get them for her tasha sanan taci abinci and tasha fruits, anjima
da daddare zan dawo nasake dubata in drip din yakare nacire mata" gyadamai kai
Sameer yayi batare dayace komiba, Dr ya tsugunna yadauko wani drip ya sagale shi a
jikin kan gado ya tsaya chak, sanan yadauko allura, tana ganin allura tabare baki
takoma cikin gado da gudu tana kuka tace "dan Allah karkamin allura, in kanama
iyayen ka karkamin kaji" kallonta Sameer yayi itama cikin kuka ta kallai tana
girgiza kai hakan yasa towel din kanta yakarasa warwarewa yafadi akan gadon tace
"dan Allah kar amin allura" dan dariya Dr yayi yace "opisa wanan kanwar takane ko
Hajiyar ka zance anyi raguwa anan" yay maganan yana dan rage tsawonshi a gabanta,
yamika hannu zai kamo hannunta takase komawa chan karshen gadon da sauri, wani
mugun kallo Sameer yamata yace "give him your hand right away" gyadamai kai tayi
kirjinta na bugawa sosai tana goge hawaye da dayan hannunta, tadawo inda take zaune
ahankali ta zauna, hakan yasa Dr yakarbi hannun yana murmushi ganin yanda take kuka
yace "yauwa muga hannun ahankali zan miki" sake bare baki tayi tace "to kabani
magani wlh zansha Allah amma karka samin alluran nan ajikina" ta karbe hannunta ta
boye hannun abayanta tafashe da kuka sosai tace "dan Allah kabarshi kabani magani
zansha wlh wlh please" hada ido sukayi da Sameer wani mugun kallon dayamata yasa ta
bashi hannunta tareda runtse idanunta da karfi, daure hannun Dr yayi da igiya
sabida yasami vein sanan ya soka allura ahankali dudda hannunshi babu wani zafin
kirki amma saida ta kurma ihu tace "Mummy, wayyo Mummy zafiii" dan dariya Dr yayi
yace "a'a kace yar Mummy ce, saisa kikeda wanan uban rakin, to angama" bude
idanunta tayi tana kallon hannun da Dr yamata fixing drip.
[6/30, 10:15 AM] Marsy😘: 48.....
Dr yadauko prescription sheet na hospital nashi yarubutamai magungunan sanan ya
hada jakan yarufe yatashi yana gyara zaman eye glasses din idanunshi hakan yasa
Sameer yatashi yamikamai hannu yace "thank you Dr" murmushi Dr yayi yace "bakomi
saina dawo dubata anjima da night, makesure taci abinci yanzu dan saitaci abinci
zata iyashan drugs dinan dazaka bata" ahankali Sameer yace "in sha Allah" sanan Dr
yamusu sallama yawuce yafita tareda mayar musu da kofa yarufe, komawa Sameer yayi
yazauna kan kujeran dayake kai yadaga land line din yakira hotel kitchen din dan
kusa da landline din an rubuta various number places a hotel din kaman su
reception, kitchen da bar, da sauransu, ringing daya kitchen din suka daga yace "I
want fruit salad, anddd" yay shiru yadaga kai ya kalleta har lokacin hawaye take
sharewa tana kallon hannun da aka makala mata drip din sai kawai ya dauke kai yace
"fried rice with water, the one that's not cold" ya maida wayan ya ijiye, wayarshi
ne dake kan jikinshi ya shiga ringing da sauri yadaga wayan ganin Ummi ne yasa
yatuna bai sanar da ita bazai dawo gidaba kuma inba tafiya ba koyaje wani
assignment a outside Abuja ba, baya taba fashin kwana agida, dudda Ummi na bacci da
wuri amma yarasa ya akayi duk in bayanan take notising koda baidawo gida da wuri
bane tasani, ajiye landline din yayi yadaga wayan yana kallo, answering call din
yayi ahankali yace "Ummi na" yanda yafadi Ummi na saida Rahima tadago kai ta kallai
cikeda mamaki dama wanan masifaffen sojan na ragema wani murya haka haladai
mamanshi ne.


Cikeda dan bacin rai Ummi tace "I call to ask you one single question, just a
question Sameer" dan faduwa gabanshi yayi dagaji yasan Ummi tai fushi dashi sosai,
tace "na lura kasoma zama man of your own yanzu Sameer, you feel kai keda kanka you
have the right to do duk yanda kaga dama, naji kuma nagane Sameer, tambayata itace
incire idanuna ne akanka kawai na zuba maka ido?" shiru yayi yakasa amsata hakan ya
mugun tunzurata ta dakamai tsawa. "answer me Sameer, nace in cire idanuna ne akanka
na zuba maka idanu, dan I see no reason dazan dinga damuwa akan ka, sabida ka
rainani Sameer kaga ka girma saika tashi bazaka kwana agidaba kuma kaki kira ka
sanar dani eh Sameer and inama magana you kept mute kaman wanda yahadiyi dalma"
cikeda damuwa ahankali yace "am sorry Ummi, please" tashi yayi akan kujeran yadan
juyo hada ido sukayi da Rahima da tunda yafara wayan take kallonshi kaman yauta
fara ganinshi harara ya balla mata yawuce yafita daga dakin, ya sauka chan kasa,
garden din Hotel din yashiga yazauna kanwata kujera mai kyau tashan iska shi kadai
awurin yasake dialing number Ummi din danta kashe cikin fushi jin baya amsata,
saida wayan ke gabda katsewa ta dauka tai shiru batare datai magana ba hakan yasa
cikin kwantacciyan murya irin ta lallashi yace "am sorry Ummi na, dan Allah
kiyakuri kinji" cikin fushi tace "ban neman hakurin ka, just tell me kana ina yanzu
haka?" dan jim yayi 1st policy din rayuwan shi shine baya karya ko zaka kasheshi
baya karya, instead of yay karya to gwara yay shiru kawai yaki baka amsar tambayan
ka koda zaka tsinemai ne. "kana jina kai shiru Sameer?" ahankali yace "ina Gombe
Ummi, am sorry I was on my way coming back home da magrib jiya issue came up da
dole I had to attend, Ummi am sorry karkiyi fushi dani kinji" cikin kakkausan murya
Ummi tace "mekaje yi a gombe Sameer?" dan jim yayi kafin yace "aiki ne, anjima
kadan zaki gani a news Ummi, news din will be a all kafafun yada labaran duniya"
dan ajiyan zuciya tasauke tadamu da situation din Sameer saisa any abu nashi yake
tadamata da hankali, jin tai shiru batace komiba yasa yace "I am sorry, rushing to
the place nake saisa I couldn't call you nafada miki zanje aiki Ummi, kiyakuri
kinji, kinyafe min?" ajiyan zuciya ta sauke tace "naji nayafema Allah maka albarka"
murmushi yayi yaji wani sanyi aranshi tace "yaushe zaka dawo?" ahankali yace
"tommorow or next tommorow" "okay daman Mu'az yadawo gida dazun nan wai ASUU sunje
warning strike na 2weeks" gyadakai yayi yace "eh yafadamin yamini text, tunda
yadawo gida tell him nace yaje farm house yataya su ishak aikin dana sasu" ahankali
Ummi tace "tom zan gayamasa gamashi nan ya shigo yana jinka tunda yadawo yadaman
wlh Sameer danai magana yace wai shine Auta haka autanni keyi, am fed up fa, ni
yakoma school yazauna yajira su gama warning strike din tunda just 2weeks ne
yafimin" dan murmushi Sameer yayi yace "put him on the phone Ummi" kafin ma Ummi
tabashi wayan Mu'az ya fizge jin Sameer yace abashi, cikeda murna yana wani irin
murmushi yace "Ya Sameer ina yini" yay maganan yana tashi daga kusada Ummi yay
dinning da gudunshi Ummi tabisu da kallo tana murmushi tanason yanda yaranta keson
junansu duka saisa ko kadan batama Sameer fada agabansu shima Mu'az shigowan shi
kenan yanzun nan duk fadan datama Sameer ba a idanunshi bane.



Ahankali Mu'az yace "good morning Ya Sameer" anatse Sameer yace "morning kiddo, why
are you disturbing Ummi?" kaman zaiyi kuka ashagwabe yace "Ya Sameer nifa kudi
nakeso tabani waidan nace tabani Atm card dinta shine wai ina damunta bazata
bayarba zan emptying account dinta" ahankali Sameer yace "tome zakai da kudi?"
ashagwabe yace "aski zanyi fa, sanan da gyaran farce" gyadamai kai Sameer yayi yace
"alright will transfer money for you, but kadena damun Ummi at her age bata bukatan
damuwa sai kwanciyan hankali daga wajenmu, karka bari takara kawomin irin wanan
complain din am I clear" gyadamai kai Mu'az yayi kafin ya saramai ya buga kafa
akasa yace "Crystal clear Sir!" da sauri Ummi tace "wlh kafasamin tiles saika kawo
kudin gyaran su" daga tachan bangaren Sameer yace "bama Ummu wayan" da sauri ya
kaima Ummi wayan ta amsa ta kara a kunne yace "okay Ummi namai magana, inya kara
damunki just let me know" hararan Mu'az din daya daura kanshi kan cinyarta tayi
yana daddanna waya abinshi tace "balm din kafafu na yakare Soja, na aika su Noor da
Muhammad basu samomin ba wlh, duk pharmacy dazasu babu" gyadamata kai yayi yace
"idan zan dawo zan tahomiki dashi" murmushi tayi tace "shikenan nagode, Allah yay
albarka, kome zakayi kadinga yi tsakani ga Allah kaji, abinda akayi tsakani ga
Allah, Allah yafi sanya albarka cikinshi, Allah yay muku albarka gabaki daya, Allah
ya tsaremin ku aduk inda kuke yakare min ku" ahankali dagashi har Mu'az dake kwance
sukace Ameen sanan yace "saina kira anjima Ummi bye" "bye Son" katse wayan yayi
yatashi daga Garden din yawuce cikin hotel din. Dakinsu yabude ya shiga kwance
yaganta kan gadon tana bacci hankali kwance ta lulluba da bargo, tray da aka aiko
musu abinci kusada gadonta yabi da kallo, tsugunnawa yayi yabude yaga ko kadan bata
taba rice dinba sai bowl na fruits wanda yaga gane na fruits ne sabida chunks of
pineapples dayagani acikin bowl din da fork kenan shi kawai tasha, maida rice din
yay yarufe yatashi yasa hannunshi ahankali yadau kayan shi daya saya a boutique din
dake hade da nata yabude bathroom din ya shiga ya maida kofan yarufe, wanka yayi
yacire uniform dinshi ya kwashe farin riganshi da jacket dinshi datai hanging
abayin yajefa cikin wani dan mini basket sanan yay wankan yadade yana wanka ya gama
tsaf ya shirya cikin jean da rigan daya saya da suka mai kyau sosai sanan yafito
rikeda basket din, yadau wayanshi, wallet da prescription note din yasaka a aljihu
yadau car key yafita, saida yabiya laundry hotel din yabasu uniform din nashi dan
su wanke mai sanan yafita ya shiga mota ya kunna wani gidan mai yafara zuwa yasha
mai sanan yafito ya shiga gari dudda baiwani san kan gombe sosai ba gaban wani
shago ya tsaya dayaga ana dinka hijabi yasai guda daya maroon mai hula da hannu
sanan ya koma mota yacigaba da tafiya saida yaga wani babban pharmacy sanan yay
parking ya shiga yasa yo duka magunguna ciki harda na wanda zata shafa a inda
kuraje ya feso mata da kuma reddish din allergies din sanan yafito ya shiga wani
super market another set od cloth yasaima kanshi da takalmi itama yasai mata
takalmi sanan yawuce yakoma mota ya ijiye komi sanan ya shiga wani masallaci that
is at the road side yay sallan la'asar yafito ya shiga mota yaja awani eatry ya
tsaya yaci abinci sanan yaja mota yakoma hotel din, har lokacin tana bacci ajiye
komi yayi yadau kayayyakin sawa su yasa a wardrobe din hotel din sanan ya zauna ya
cicciro magungunan daya siyo mata yana karanta leaflet dinsu, maganin maleria ne
dakuma na allergies din sai multuviate dazai bata apatite yakuma sa taci abinci,
aijiyewa yayi yatashi yafita.[6/30, 10:16 AM] Marsy😘: 49&50




Bayan sallan magrib suka shigo Hotel din tareda Dr din sunadan taba hira, knocking
Sameer yayi tana zaune kan gado rike da rice din dazu data kasaci mugun yunwa
takeji but dukta yanda taso ta chusa abincin acikin tane takasa sai kallonshi take
akan kafafunta knocking da akayi yasa ta dago kanta batare datace komiba dan batada
karfin magana bata dade da tashi daga baccin bama, bude kofan Sameer yay ahankali
suka hada ido ahankali ta saukar da kanta kasa duk in suka hada ido sai gabanta
yafadi juyawa yayi ya kalli Dr yace "come in" shigowa Dr yayi yana kallon Rahima
yace "iyye patient ke kadai wanan delicacy din ba tayi?" dan murmushi tayi batare
data dago kantaba yakaraso gaban gadon yace "to kishi abincin mana" girgixa mai kai
tayi tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace "nakasa ci" cikeda
damuwa Dr yace "ahh sorry bakida apatite ne, don't worry tunda yanzu kin tashi
akwai magun gunan dazaki sha zaki sami apatite nan da zuwa gobe zaki warke ok,
mezakici yanzu?" murya chan kasa kaman wata marainiya tace "sliced fruits" dan
juyowa Dr yayi ya kalli Sameer dayay kaman baya jinsu yace "call the kitchen
officer akawo mata fruits, she can't take those drugs on empty belly" landline
Sameer yadauka ya shiga kiran su shikuma Dr yajuyo ya kalleta yace "ban

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login