Showing 129001 words to 132000 words out of 197960 words

Chapter 44 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15035

kyau, jinin dayagani har kan white zanin gadon sosai yasa
yay wata yar gajeren salati. "innalillah!" ahankali yadaura hannunshi kan fuskarta
yay tapping yakira sunanta da muryanshi da bata fita tsabagen zafin ciwo. "Rahima,
Rahima" ganin ko motsi batayi ba yasa yay kokarin tashi daga kan gadon, kasa tashi
yayi yakoma ya kwanta a yana sauke ajiyan zuciya sanan ya lallaba yana dafa bangon
gadon ahankali yatashi, masifaffen jiya yake gani bana wasaba da kyar yake iya bude
idanunshi hango boxer dinshi dayayi akasa yasa yajawo da kafarshi yadauka ya mike
tsaye da kyar yasaka sanan yafara tafiya ahankali yana dafa bango haryakai kofa jin
kofan akulle yasa ya murza key yabude kofan yafita yana layi yana ganin dishi
dishi, da kyar yake tafiya haryakai parlour sama, wayarshi yadauka sanan ya kwanta
kan dogon kujera ya lumshe ido yana numfarfashi, da kyar ya iya yasake bude ido
yadaga wayan yabude ya lalubo number Ummi yakira, ringing daya biyu ana uku ta daga
cikeda natsuwa tace "Assalamu Alaykum Soja na" takirashi sabida tahakura tadena
fushi dashi, da kyar Sameer ya iya bude baki yace "Um......mi....." yakasa magana
yay shiru, faduwa gaban Ummi yayi tunda take bata tabajin muryan Sameer hakaba, da
sauri ta tashi daga falon dan Mu'az na wurin kuma bata cika son yin personal magana
da Sameer agabansu ba, dakinta ta shiga ta mayar da kofa tarufe kafinma tazauna
tace "Sameer, menene naji muryanka haka are you okay?" cikin muryan wanda zazzabi
mai zafi keci yace "baaa.....banda....lpy Ummi, pls......come to.....my house....."
yay maganan gabaki daya ararrabe, mayafi Ummi taja arude dan duk cikin yaranta
Sameer ne kadai bai cika ciwo ba, kuma duk in ciwo zai kamashi mai mugun zafi yake
tun yana yaro saisa duk cikin yaranta bata kaunar ciwon Sameer, da sauri tace "to
soja na, am on my way, yanzun nan kaji" tai maganan tana katse wayan tadau purse
dinta da wayanta tana gyara mayafi ta fito da sauri Mu'az ya kalleta dan Ummi
hardly go out yace "ina zaki Ummi" batare databi ta kanshi ba tace "ina zuwa, kasa
mai aiki tai tuwon shinkafa da miyar agushi sabida Sameer" tawuce tafita daga dakin
tana kwalama direban ta wanda Sameer ya ijiyemata na fitanta kira dan Ummi bata
driving sabida ciwon kafarta, mota ta shiga yajata zuwa gidan Sameer.


Sojojin datagani agaban gidan Sameer dayawa yasa gabanta ya shiga faduwa meya sami
Sameer dinta, sabida sojoji sun tsayar dasu yasa tabude baya tafito da sauri
sojojin na ganinta sukahau gaidata dan yawa cin su sunsan Ummi tun daren award
dinsu Sameer, cikin gidan Ummi ta shiga batare databi takan gaisuwan suba, tabude
kofa ta shiga ciki da sauri, ganin babu kowa a falon kasa yasa ta kwalama Sameer
din kira. "Sameer, Soja" tahau kan stairs tana kiranshi hartakai last stair case,
hango Sameer datayi akan dogon kujera dagashi sai boxer akwance yasa tai wajenshi
da sauri tana kiranshi. "Sameer innalillahi" tai kanshi adaidai kanshi ta tsaya
takai hannunta tadaura kan fuskarshi dataji da bala'in zafi tace "Sameer, open your
eyes am here son" tai maganan tana shafa fuskarshi, ahankali yabude idanunshi
dasukai jajir yadaura su akanta yana ganinta dishi dishi, Murya chan kasa yace
"Ummi" da sauri Ummi tace "na'am Sameer, meke damunka, tashi na taimaka maka ka
shirya muje hospital" dan lumshe ido yayi sanan yabude cikeda ciwo yamata pointing
dakin Rahima ahankali yace "Rahima Ummi" da sauri Ummi takalli kofar dayake
nunamata tajuyo ta kallai tace "wat Rahima?" murya chan kasa cikeda ciwo yace
"Ummi, pl......s h.....elp her...." yay maganan yana fitar da numfashi da kyar.



Ganin yanda yay magana yasa gaban Ummi ya mugun fadi ahankali ta ijiye purse dinta
da waya kan hannun kujeran tai hanyar dakin, bude kofar dakin tayi ahankali kaman
mai tsoro gabanta na faduwa idanunta suka sauka kan fuskar Rahima dahar lokacin a
lumshe, wani mummunan faduwa gabanta yayi tana kallon fuskar Rahima bakinta narawa
sosai tace "S....a......Safa", takai kusan 2min adakin ganin kaman bata numfashi
yasa ta shiga dakin da sauri tai gaban gadon takai hannunta kan fuskar Rahima
tashafa ahankali hawaye nataruwa a idanunta bin jikinta tayi da kallo kafin tasa
hannu ta yaye bargon jikinta jinin datagani yasa tai salati tadan koma baya.
"innalillahi" saikuma ta matso kusada da Rahima ta kara bubbugata ganin batai motsi
ba yasa ta shiga kalle kalle adakin goran ruwan datagani kan makeup mirror taje ta
dauka da sauri ta debo ruwa ta yayyafa mata amman batai motsi ba, ganin haka yasa
da sauri tajuya tabude kofa tafito bamatabi takan Sameer dake kwance har lokacin ba
tai kasa, kitchen dinsu taje tabude ta shiga store direct, albasa ta dauka tadau
wuka hannunta narawa sosai ta bare ta yanka albasan taraba shi biyu sanan tafito
daga kitchen din tundaga kan stairs tafara jin kakarin aman Sameer, da gudu bamata
damu da ciwon da kafafunta keyi ba tai saman ganin Sameer na amai kaman zai shide
yasa tai wajenshi, albasan data yanka ta ijiye takama shi tadaga tana salati.
"innalillahi wa innailaihi raji'un, Sameer da wanne zanji da matarka ko kai, eh
sannu muje nakaika bayi" baimasan tanayi ba amai kawai yake kwarawa, da sauri
tasake shi tadau wayarta number Noor taciro mai non Sameer dudda Sameer yabashi
6yrs dan lokacin data haifi Sameer tana school agidan baban su Sameer tai makaranta
saida tagama school duka sanan ta haifi Noor, shi he's 34, sai Muhammad nada 31,
sai Mu'az dakeda 25. Ringing daya yadaga yace "Ummi are you missing me" bata tsaya
amsa tambayan shiba tace "Noor kana ina?" "ganinan tuki nake wajenki zanzo naci
abinci" da sauri Ummi tace "kayo kwana kazo gidan yayanka Sameer ina wurin, Soja
baida lpy sosai, zoka taimaka mai yay wanka saimu tafi hospital yi sauri dan Allah
amai yake" da sauri Noor yace "subhallahi, ganinan zuwa Ummi" to tace tawuce kasa
tana hawa benen da kyar ruwa tadauko agora tadawo wajen Sameer zubama tayi ya
kuskure baki ta sharemai wuyan shi daya bata sanan tasake kwantar dashi dan yasoma
ficewa hayyacinshi, tabar aman kasan sanan tawuce dakin Rahima bayan tadauki
albasan data yanka.
[08/07, 19:51] Aishat Muhammad: 79




Wajen gadon Rahima tayi gabanta nafaduwa sosai albasan data yanka takai jikin
hancinta ta shafe ajikin hancin nata kafin ta danne albasan daidai wajen, almost
2min Rahima ta shiga wani irin tari na wanda baida karfi ko kadan ajikinshi, da
sauri Ummi ta dagota ta zauna kan gadon tasa kanta akan cinyarta jikinta mugun zafi
tana kiran sunanta. "Rahima, Jewel, Jewel" Ummi takira sunanta adan dimauce ganin
yanda takeyi kaman zata mutu, da kyar ta iya bude idanunta dasukai jajir tadaura su
kan Ummi, ajiye ta kawai Ummi tayi tacire mayafinta ta ijiye nan kan madubi tabude
bayin ta shiga ruwan zafi tahada mata sosai sanan tafito tazo gaban gadon Rahima na
kwance yanda ta barta ko motsin kirki bata iyawa sai nishi take kaman zata mutu
bama ta iya kuka, wani mugun tausayi Ummi taji tabata da sauri takama hannuwanta
tace "sannu, sannu Jewel, sorry, zomuje na kaiki bayi" ahankali Ummi ta dagata tai
kasa tsayuwa Rahima tayi kaman Ummi ta daga paper haka takeji tabi gadon da kallo
tana buga salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un Sameer zai kashe yar mutane"
jinin data gani ya bala'in bata tsoro, tsayar da Rahima tayi da kyar sanan takama
hannunta tadaura a bayan wuyanta sanan takai hannunta gefen cikinta tarike ta gam
tajata, kasa daga kafa Rahima tayi sai jini daya shiga bin kafafunta yana gangarowa
kasa da yawa salati Ummi tayi dan ta tsorata tace "innalillahi wa innailaihi
raji'un, you are bleeding kar jininki ya kare, zauna" mayarda ita kan gado Ummi
tayi gabanta nafaduwa da sauri tajuya tai wajen kayan Rahima data gani a akwati
anan kasan dakin ta shiga dubawa pant taciro da pad da Allah yataimaketa tagani
sanan tadauko wata yar doguwan riga tadawo wajen gadon, hannunta narawa sosai
tahada mata pad guda biyu jikin pant din sanan takama kafafunta tasaka mata tawuce
bayi da sauri towel tadauka ta tsoma a ruwan zafin data hada tafito dashi tazo
kafafuwa ta dasuka baci da jini ta shiga sharewa jin muryan Noor yana kwala mata
kira yasa tace "help Sameer to his room ya shirya we are going to the clinic now
ina zuwa ganinan fitowa" tai maganan tana share mata jinin saida tagama tass sanan
takoma bayi ta wanke towel din tass ta ijiye tafito, doguwan rigan tadauka ta zura
mata sanan tasake komawa akwatin ta nemo wani karamin hijab tazo ta saka mata sanan
tadan dagata ta janye zanin gadon daya mugun baci ta shiga bayin Rahima ta saka a
washing machine tafito tana kallon yanda katifar itama tai stain but batada lokacin
gogewa, juyawa tayi tafice, ganin Sameer da Noor basa falon yasa tai dakin Sameer
tun kafin tabude kofa takejin kakarin aman Sameer alluran was way to much for him,
over dose Mummy tamai sosai hakan yasa wanan mugun ciwo yakamashi yahade mai da
zazzabin dayake yi da safe.

Da sauri tabude kofa ta shiga hango Sameer da Noor dake rikeda shi tayi abayinshi
yana kwara amai kaman zai sume Noor namai sannu, da sauri tai bayin cikeda mugun
damuwa tace "har yanzu bai dena aman ba Noor" hannunshi Noor yamika mata yace "Ummi
rikeshi dan zai iya fadi ina zuwa" rikeshi Ummi tayi gabanta nafaduwa sosai idan
akwai abinda ta tsana shine taga yaranta na rashin lpy, wardrobe dinshi Noor yaje
yadauko mai wata simple t-shirt dinshi Black mai v- neck sai wando da belt yadawo
bayin lokacin aman ya tsaya towel yadauka yajika ya share mai baki da wuya da kirji
daya bata sanan ya rikeshi da taimakon Ammi suka iya sakamai rigan, sanan yasaka
mai wandon suka fito daga bayin Noor suka fita dashi waje bai gani wlh sai magana
dayakeji sama sama his eyes are blur amota sojoji sai yimai sannu suke ganin ogansu
ba lpy, a motan shi Noor yasashi zai shiga Ammi tace "muje ka dauko matar, saura
ita, itama ba lpy" da sauri Noor yace "subhallahi" ya kalli sojojin dasuka zagaye
gaban motan yace "stay here dashi" sanan yabi Ummi sukai cikin gidan suka hau
stairs sukai small palor abu yataka dayaji yay kara hakan yasa yadaga kafafunshi
tareda kallon kasa ganin syringe yasa ya tsugunna ahankali yadauka yana kallo ganin
dan ragowan ruwan allura mai kala baki baki, da sauri Ummi tace "alluran miye wanan
kuma?" tashi Noor yayi saikawai yajefa syringe din cikin aljihun shi yace "I don't
know" dakin Rahima Ummi tabude suka ta shiga yana biyeda kallo daya yama katifar
yadauke kai da sauri, karasawa wajen Rahima dake wani irin nishi Ummi tayi tace
"innalillahi this girl is in pain, zoka dauketa Noor mutafi" ahankali Noor yataho
yanda yaga tanayi yaji wani irin mugun tausayinta aranshi dan shi mutum ne yabada
bala'in tausayi yafi all the four of them tausayi, Ya Sameer kuma yafi dukansu
jarumta da courage dan baya mantawa da Baban su yarasu shi kadai ne baiyi kukaba ya
daure sanan ya jagoranci komi dashi da Baffa sukama Abban su wanka, shi Muhammad
kuma is very simple, Allah ya yishi da bala'in saukin kai sai Mu'az, Mu'az very
innocent ga shegen surutu akun gidansu kenan, daukan Rahima yayi ahankali yaji
jikinta kaman wuta yawuce yafita daga dakin Ummi biyeda su harsuka sauka kasa,
kofar falon Ummi tarufe tazaro key daga bayan kofan ta kulle kofar da key tasa key
acikin purse dinta sanan suka tafi, abaya ya kwantar da Rahima Sameer kuma ya zauna
agaba amma ya kwantarmai da kujeran ya rurrufe kofa itakuma Ummi takoma motarta
direba yajasu sojojin na dagamusu hannu suka tafi.




Babban clinic dinsu, wani private asibiti da family su duka ke amfani dashi Noor
yatafi, dayake an sansu da mai asibitin abokin Abban su Sameer ne kafin yarasu aka
karbe su akai emergency room da Sameer, Rahima kuna aka shiga da ita wani daki Ummi
tabisu shikuma Noor yabi Sameer.

Yanda Rahima ke nishi yasa da sauri aka shiga mata fixing drip aka samata oxygen
sanan babban likitan dake dubata ta kalli Ummi tace "meya sameta haka Madam?" tana
maganan idanunta suka sauka kan riganta daya jikeda da jini da sauri Dr ta yaye
rigan tace "My God she is bleeding, wat happen to her" batare da Ummi tabari sun
hada ido ba tace "I think she had a tea" da sauri Dr dayake musulma ce tace
"subhallahi, take her to tea theater girls" tama nurse din magana tana kwance
agogon hannunta tana zare zobunan ganin Yanda Ummi tayi yasa takamota suka fito
daga dakin kujera ta nuna mata tace "just sit here your daughter will be fine okay
am coming" tai maganan tana wucewa theater, Noor ne yadawo wurin yazauna kusada
Ummi data mugun damu yace "ina suka kaita Ummi?" ahankali Ummi tace "theatre" dan
jim yayi baice komiba, chan Ummi tamika mai wayanta tace "nemomin number Baffan
ku?" karban wayan Noor yayi ya shiga binciko number yace "Ummi da ba'a kirasu ba
banso kowa yasani" girgiza kai Ummi tayi ahankali tace "Baffan ku mahaifin kune
idanda mahaifinku nada rai adole yazonan ko Sameer danshi ne kuma shi mahaifinku
yaba amanar ku" dialing number Baffan Noor yayi yamika mata takarba takara akunne
ta sanar da shi yanama kan hanya ne yace mata bari yay kwana yazo.

Wani likita ne yafito yana share zufa da towel da sauri Noor yatashi Ummi zata
tashi Noor yace "Ummi please ki zauna kinsan yawan tafiye tafiyen nan might result
to a problem" ahankali Ummi tace "to amma ya Sameer din?" murmushi Dr yamata yace
"sweet mother kenan bamu da kaman ku your son is fine" sanan ya kalli Noor yace
"you are his brother right?" gyadamai kai Noor yayi hakan yasa Dr yace "come with
me" binshi Noor yayi har zuwa office dinshi yanunama Noor wajen zama sanan yakarasa
ya zauna yana cire lab coat din jikinshi, yace "we were lucky to stabilise his
condition wlh inda ace kunbar shi baku kawoshi hospital ba daya rasa ranshi dan he
took overdose na sex arousal inducement injection, and daban daban aka hada masu
karfin bala'i dasukafi karfin jininshi, maza sun kasa gane cewa amfani da wanan
abin baida kyau kaga kaman su Viagra da sauransu dasuke karama mutum karfin sha'awa
kaji kana bukatar mace duk sunada illa, zakai having sex dinfa kagama but zai sakin
maka mugun zazzabi da ciwon kai wasu har rayukansu magungunan nan ke costing nasu,
barinma shi daya hada kala kala daban daban Allah he is lucky Allah yace yanada
sauran kwana aduniya saisa kuka kawoshi on time, yanzu mun tsotse all maganin daga
jikinshi sanan munyi stabilising nashi, sai magungunan dazan rubuta maka da you
will have to get them for him" gyadamai kai Noor yayi ahankali dudda kam yaga
alluran a kasan dakinsu but yakasa gasgata Ya Sameer can do something like that,
mezaiyi da sexual inducement drugs, gaskiya ba Ya Sameer akwai dai wani abun akasa.



Karban prescription sheet din yayi yafita daga office din yay pharmacy yasayo
magungunan yakaima Dr, Dr ya karba sanan yafito yadawo wajen Ummi ya zauna, ganin
anyi la'asar yasa yawuce yafita la'asar yayo a masallaci sanan yafito yadawo cikin
asibitin yazauna kusada Ummi.



Dr data duba Rahima ne tadawo daga theater ganin Ummi da Noor yasa tace "please
kubiyo ni zuwa office dina" tashi Noor yayi da taimakon shi yadaga Ummi ta tashi
tana takawa da kyar sukai office din Dr, kujera ta nuna musu, zaunar da Ummi yayi
sanan ya zauna dayake ta sansu sosai dan she is use to the family tace "Mummy who
rape that girl? Innalillahi wa innailaihi raji'un baida zuciya ne eh, baida imani
ne ina imanin shi yaje, me yarinyar nan tamai yay raping dinta harda tear........"
da sauri Noor yatashi yafita dan bazai iyajin sirrin yayan shiba ko kadan he finds
it disrespectful yafita tareda rufo musu kofa yay hanyar dakin da aka kai Sameer
din.

Cikeda tsantsan damuwa Ummi tace "yanzu yatake?" ahankali Dr tace "I've stitch her
yanzu, yanzu zan baki magungunan da za'a sayo mata dan ta warke da wuri sanan
tahade, tear datasamu ne yasa she was seriously bleeding but yanzu mun tsayar da
bleeding din, and tanada maleria 2+ shima we are treating her on it bayau zatabar
hospital dinan ba sai munga tasami sauki sanan zata dinga sit Bath konan da anjima
ne idan ta farka sai anmata, Mummy zaki iya kina mata ko nasama miki nurse dazata
dinga mata" ahankali Ummi tace "zandinga mata" rubuce rubuce Dr tayi tamikama Ummi
tace "ga magungunan da za'a sayamata yanzun nan" karba Ummi tayi ta tashi tafito
ahankali Noor tagani zaune inda suke yana ganinta yatashi yarikota yazo ya zaunar
da ita sanan ya karbi takardan yaje phamarcy magungunan ta dayawa harda drip daban
daban da allurai yadawo yakaima Dr sanan takoma wajen Ummi ya zauna saiga Baffa
yashigo reception din da sauri Noor yatashi karasowa Baffa yayi wajen yana gyara
zaman babban rigan jikinshi yazo wajensu cikeda girmamawa Noor yagaidashi amsashi
yayi yace "ina Sameer din? Meke damunshi? Me ake bukata kayi komi?" gyadamai kai
Noor yayi yace "nayi" da sauri Baffa yace "muje na ganshi" yin dakin sukayi dudda
ba'a barsu sun shiga ba but suna hangoshi yana kwance karin ruwa akemai a duka
hannayenshi, haka suka juya suka koma wajen Ummi.
7




Suna asibitin har isha'i, sallan isha'i sukayo suka shigo ciki har lokacin Ummi na
zaune a reception dudda tai salla suka karaso wurin Baffa yace "Noor dau mahaifiyar
ku ka kai gida bazata iya zaman jinya ba, Mu'az yazo yazauna da Sameer din kai
kawuce gida wajen iyalinka" da sauri Noor yace "Baffa zan zauna dashi please karka
hanani" dan jim Baffa yayi saikuma yace "tom, shikenan ka zauna bari naje na ijiye
mahaifiyar taku agida" da sauri Ummi tace "natafi Rahima fa" cikeda tausayinta
Baffa yace "akwai nurses around sanan ga Noor, kinsan ke bakida lafiya Dr yace
miki kidinga hutawa, gobe za'a iya kiran mahaifiyar yarinyar tazo ta kulada ita" da
sauri Noor yace "bama sai ankirasu ba Nabila tazo gobe" yay maganan dan Sameer
already told them about Mummy su Rahima wani kallo Baffa yamai yace "Nabila mai
karaman yarinya ne zatazo jinya baridai Allah yakaimu gobe zamuga me ai faru, tashi
muje" daga Ummi Noor yayi yafito da ita har wajen motar Baffa yasata abaya zama
tayi ahankali sanan ta kalli Noor cikeda damuwa tace "dan Allah Noor ka kula dasu
da kyau kaji, in Yayanku yatashi ka kirani nai magana dashi" gyadamata kai yayi
cikeda tausayinta yace "to Ummi karki damu he will be fine" maida kofar yayi yarufe
Baffa yashiga yaja motar suka fita daidai lokacin wayan Sameer dake aljihunshi
yadauki ruri, kallon wayan yayi ganin Abba ajiki yasa yadanyi mamaki waye kuma
Abba, har wayan takatse bai dauka ba sai akira nabiyu yadauka yakara akunne kafin
yay magana Abba yakira sunanshi. "Sameer" ahankali Noor yace "baida lpy kaninshi ne
Noor" da sauri Abba yace "subhallahi meke damunshi?" "zazzabi ne kawai munama
hospital yanzu" salati Abba yayi cikeda damuwa ya tambayi Noor address din asibitin
tareda fadamai zaizo gobe in sha Allah, komawa ciki Noor yayi yana waya da Nabila,
dakin Rahima yafara zuwa ganin Nurse aciki datace mai ita zata kula da ita yasa
yafita daga dakin yayi dakin Sameer zama yayi yana kallon fuskan Sameer din yana
waya da Nabila ahankali kafin suyi sallama.




**
Kiran sallan assalatu yasa Sameer yabude idanunshi dasuka mai mugun nauyi ahankali,
sosai yaji ciwon kan dayakeji yaragu sosai sai dan tashi zuciya, hannunshi ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login