Showing 12001 words to 15000 words out of 197960 words

Chapter 5 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15062

✍️ M Shakur


9️⃣
&




Gabaki dayan goran tsumin ta shanye sanan tadawo daki tana kallon yar kyakyawan
yarinyar ta dake baccinta hankalinta kwance bayi ta shiga tayo wanka tafito salla
tayi tana idarwa princess itama natashi daga baccin, daukarta tayi ta shiga bata
nono tana azkar saida tasha ta ture sanan ta dauketa wanka tamata tafito ta
shiryata kafin ta dauketa suyi kitchen golden morn tahada mata tabata, yarinyar ta
shanye sanan tadawo ta shirya cikin English wears gabanta sai faduwa yake tana
fargaban ciki, sau hudu jiya Baby na releasing a ciki, in ciki ya shigafa
innalillahi baby na neman mata iskanci wlh yanzu yazatayi kuma yahanata planning,
bude kofa dataji anyi yasa tadago kai dan ganin ko waye, yarinyar na ganin baban ta
ta daga hannu sama alamun yazo yadauke ta tace "daaaa daaa" cikin gwarancin ta
daukanta yayi yace "yes my gurl oyoyo, Dady is here" fita yayi da ita daidai Ya
Sameer da Muhammad da Mu'az sun shigo gidan dukansu sanye da fararen jallabiyoyi,
da sauri yakarasa wajen su Ya Sameer yamikama princess dahar tafara tsalle tanaso
tafita daga hannunshi taje wajen Ya Sameer dan tagane shi tsaf hakanan yanada farin
jinin yara, karbanta yayi anatse yace "oyoyo princess" murmushi Muhammad yayi
harda sauke ajiyan zuciya yace "Please ku kaima Ummi ita, bari naje nayo wanka
nazo" hararan shi Muhammad yayi irin kar tasan kar dinan dariya yayi yajuya bayan
yama Muhammad wink da ido, Sameer na ganinsu yayi kaman bai gansu ba yajuya yawuce
abinshi rike da princess a hannunshi, ganin Yayan su yay tafiyan shi yasa Muhammad
yadubi Mu'az yace "bisu mana kutafi wurin Ummi nima bari naje na daukoma Ummi
little" makemai kafada Mu'az yayi yace "a'a wurin Mum Little zani akwai abinda zata
bani" zaro ido Muhammad yayi saikuma ya zubamai harara yace "bacci suke yanzu
kadaisan jiya we came back late, bi Ya Sameer" yajuya da sauri tsaki Mu'az yayi
yajuya yay flat din Ummi abinshi yabude kofa ya shiga, Ya Sameer yagaji zaune
kusada Ummi data karbi Princess daga hannunshi yana rike da karamin cup na lip tea
da aka dafa da na'a na'a yana sipping yana kallon news da ake nunawa a channels
television news gabaki dayan hankalin shi na wurin, zama yayi kan kujera ranshi
abace Ummi data bishi da kallo tace "kagama shirya kayan naka Mu'az bayau kace zaka
koma school ba" tashi yayi yace "Ummi nisai anjima zan hada, zan jira sai Baffa
yazo sanan zan tafi, Ummi am hungry angama hada breakfast?" "a'a ba'a gamaba saidai
in zakasha tea yayanka gashi chan dining kaje kadebo" turo baki yayi yatashi yaje
kan dinning din ya zauna yazuba a cup yana sha yana satan kallon yayan nashi dayaga
his eyes are so fix to the telivison.
Takwas na safe aka gama news din hakan yasa ya ijiye mug din ya mike yace "lemme go
and shower Ummi" gyadamai kai Ummi tayi hakan yasa ya fice Ummi tabishi da kallo
intace bata cikin damuwa she's lying akan batun Sameer.



Wuraren 10 gabaki dayansu suna zaune afalo ana hira banda Sameer da tun dazu
dayabar dakin bai dawoba sanin ya kwanta bacci safe ne kasancewan yau asabar yasa
Ummi bata tura Mu'az yataso shiba tadau killace abincin shi akula gudun karyay
sanyi, sosai ake hira gwanin ban sha'awa, horn dasukaji anyi yasa Nabila tace "Ummi
su Baffa ne halan"

Bude Gate Mai gadi yayi wata sienna ta shigo gidan, parking motar tayi wani
magidanci sosai dan duk gemunshi furfura ne yafito daga motar yana sanye da manyan
kaya, wata mata itama tafito sanye da wani hadadden lace, bude motar matar tayi
wasu yara haka guda hudu suka fito yan mata guda uku duk suna sanye da dogayen
rigunan atampa iri daya, sai namiji da bazai wuce 8yrs Bilal ba yana sanye da
shadda, babban su at least zatai 22 Asiya, sai mai binta da zatai 19 Yusra, saita
uku dakenan 15 Amra, suna fitowa daga motan duka yaran suka kwasa da gudu sukai
flat din Ummi kafin ma sukarasa Ummi tabude kofa cikeda murna aiko saikan Ummi
barinma Bilal yace "oyoyo Ummi" sun kusan kada Ummi, rungume su tayi tace "oyoyo
yarana" ku shiga ciki ga yayyunku chan ciki, sakinta sukayi suka shiga ciki da
sauri daidai lokacin matan da mijin sun iso rungume juna sukayi da matar tace
"barka da zuwa Maman Asiya" cikeda farin ciki Maman Asiya tace "barkan mu,
congratulations fa promotion din Sameer Allah yasa mucigaba da daukaka haka, Allah
kuma yay albarka" Ameen Ummi tace daidai lokacin su Muhammad da Nuru da Mu'az sun
fito dan dukawa sukayi cikeda girmamawa suka gaida tsohon. "Baffa barka da zuwa,
ina kwana" kansu yashafa cikin muryan wanda yadan manyanta yace "kutashi, kutashi"
tashi duk sukayi yay murmushi yace "Nura ya wurin aikin naka da iyali dafatan
bawani matsala ko" murmushi yayi ya girgixa kai yace "babu Baffa" Muhammad ya kalla
yace "kaikuma fa Muhammadu" ahankali yace "Alhamdulillah Baffa komi lpy lau" Mu'az
ya kalla yace "dan yaro ya makaranta" jin ya kirashi da dan yaro yasa ya kumbure
yace "lpy lau" kwashewa da dariya akayi sanan Baffa yakama kunnenshi yace "kumu
shiga ciki" shiga falon sukayi har Yusra da Asiya sun dauki su Princess su Nabila
suka gaida Baffa da matar su sanan hayaniyan yadan lapa, dan gyaran murya Baffa
yayi bayan ya kalli kowa sanan ya kalli Ummi yace "ina Sameer?" Mu'az Ummi ta kalla
tace "jeka taso Yayan ku Mu'az kacemai Baffan ku ya iso"




Falonshi yabude ya shiga babu kowa a falon sai TV dake aiki, bedroom dinshi Mu'az
ya shiga da sallama, babu wani haske sosai a dakin but yana iya ganin yanda yake
baccin shi peacefully, babu riga ajikinshi sai wani kwantaccen Black gashi dake
kwance akan huge kirjin nashi yabude kaman zai fashe tsabagen gyming, karasowa
gaban gadon Mu'az yayi murmushi kwance yadan bubbuga gadon ahankali yakira
sunanshi. "Yaya Sameer, Ya Sameer wake up" ahankali yabude ido dan baida wanan
mugun nauyin baccin, ganin Mu'az yasa yabude idanu da kyau da hannu yamai alamu
menene? Ahankali Mu'az yace "Baffa ne yazo ya tambaye ka shine Ummi tace nazo
nakiraki" dan lumshe ido yayi kafin ya yaye bargon jikinshi hakan ya bayana gajeren
wandon dake jikinshi daya fito da murdaden kafafunshi, tashi yayi yazauna tareda
daura hannayenshi akan fuskarshi almost 1min yay ahaka sanan yazare hannu ya kalli
Mu'az dake kallonshi yace "lemme shower, kace musu ina zuwa" gyadamai kai Mu'az
yayi yajuya yafita shikuma yatashi yay bathroom, wanka yayi yasake brush sanan
yafito ya shirya cikin wani milk yadi mai shegen laushi anmai dinki jumper, sabida
mugun respect dun dayake bama Baffa ne yasa bazai iya zuwa wurinshi da kananun
kayaba, links din hannun riganshi ya makala sanan yadau agogon shi yadaura a wrist,
yadau manyan turarukan shi kusan kala 9 ya feffesa nan dakin yadau kamshi mai
shegen dadi tazura3 takalmi, bakaramin kyau kayan sukamai ba dan cup cip sukamai
sun mugun fito da surarshi dakuma tsayin shi that is the first thing dake
attracting you to him, bude kofar falonshi yayi yafito yana kallon tsakar gidan
yanda ko ina looks so neat, anatse nan yake tafiya irin ta maza har falon Ummi da
sallama ya shiga falon Ummi daya cika da mutane sai cin snacks ake, ganinshi yasa
duk kannenshi suka shiga gaidashi da matayen su amsasu yayi da murmushi kan
fuskarshi kafin ya tsugunna yadauki Princess dahar ta rarrafo da gudu tazo gabanshi
murmushi yamata yaja kumatun ta hakan yasa ta kyalkyace da dariya sanan ya shigo
dakin yakarasa gaban Baffa cikeda girmamawa yadan duka yace "barka da zuwa Baffa"
sanan ya kalli Maman su Asiya yace "Mummy ina yini" cikeda so tasakar mai murmushi
tace "dana naji abin farin cikin dayasameka Allah ya sanya alkhairi, Allah ya shiga
tsakanin ka da makiya, congratulations kaji Sameer yanzu abinda yarage maka kawai
shine aure" gyadamata kai yayi kawai batare dayace komiba, glass cup din ruwan Swan
dake hannun Baffa ne ya ijiye kan dan stool din gabanshi ya mike tsaye yana gyara
babban rigan jikinshi yace "come with me Sameer" yana maganan yay hanyar stairs,
tashi Sameer yayi kafin yabama Ummi daketa kallonshi Princess yace "am coming Ummi"
gyadamai kai tayi bayan ta karbi Princess data sandara ihu sabida batason ya
ijiyeta, murmushi yadanyi ya shafa kanta yace "sorry am coming okay" tashi yayi yay
hanyar stairs Asiya tabishi da kallo kaman idanunta zasu fado kasa.



Upstairs yayi yabude wani daki dakenan a gyare tsaf saiga hoton wani tsoho da
Sameer ke kama dashi sosai da alamu dakin marigayi mahaifin sune, riganshi yadan
daga zai zauna akasa Baffa yanuna mai kujeran dake facing nashi yace "zauna anan"
yanda Baffa yamai maganan yasa yagane Baffa is very serious today hakan yasa
ahankali yazauna kan kujeran kanshi akasa, gyara zama Baffan yayi yadanyi gyaran
murya cikin wani irin yanayi na kamala yace "Sameer" anatse yace "na'am Baffa" dan
ajiyan zuciya ya sauke yace "ina matukar farin ciki da wanan karin girman daka samu
awurin aikin ka, sanan ina maka addu'a Allah yacigaba da kara daukaka ka Sameer
Allah kuma yama albarka" ahankali yace "Ameen Baffa" shiru dakin yayi Baffa ya
tsareshi da ido yana kallonshi tundaga kai har kafa yanda kanshi ke kasa ya natsu
yana jiran yaji mezaice, ahankali yace "Sameer dago kanka ka kalleni yau magana
nakeson nayi dakai sosai" dan dago kanshi yayi ya kalli Baffa nashi, cikeda natsuwa
Baffa yace "da ace tayaka murnan saban matsayin dakasamu kawai nazoyi da tun afalo
zan maka gaban kowa amma banyi ba nasa muka shigo nan dakin mahaifinka" dan shiru
Baffa yayi sanan yace "Sameer kasan duk duniyan nan bakada wani mahaifi daya wuce
niko" gyadamai kai yayi hakan yasa Baffa yacigaba "dukanku hudun nan kome zai
sameku aduniyan nan dole nine zan tsayamuku, Sameer da mahaifinka yarasu da wayanka
da komi kuma kaga yanda ya dinga maimaitamin narike ku amana narike ku amana"
yasakeyin shiru yana kallon Sameer din dayasake maida kanshi kasa sanan yace
"Sameer shekarunka talatin da takwas(38), kokuma namace sheakrun ka talatin da Tara
(39) dan watan jibi zaka cika shekaru talatin da tara, shekarun ka arba'in babu
daya Sameer amma bakama maganan aure, bamaka da niyyan aure, bamaka da sha'awan
aure, sa'oin ka da kuka taso tare sunada yaran dasun isa aure, amma kai ko agefen
jikinka eh yaron nan, yau nazone nai magana dakai Sameer kacire wanan kunyan da
shiru shurun, da zurfin cikin da miskilancin nan kamin magana, Sameer kafada min
meke damunka? Kanada wata matsala ne dabaka fadamana ba gudun kar hankalin mu
yatashi?" yay shiru yana jiran amsan shi yana kallonshi, girgiza mai kai yayi yace
"a'a Baffa" cikin wani irin yanayi na damuwa Baffa yace "karkaji kunyana ka boyemin
gaskiya ni ubanka ne taruwa za'ayi a rufama juna asiri mu nema maka magani batare
da kowa yasani ba, kafadamin Sameer kanada wata matsala ne?" sake girgiza mai kai
yayi yace "a'a Baffa" shiru Baffa yayi yana kallonshi kana ganinshi kaga damuwa
karara akan fuskanshi yay shiru yana kallonshi, sunkai kusan 3min sanan ya numfasa
yace "Sameer" ahankali yadago kanshi ya kalli Baffa yace "na'am Baffa", babu kunya
danya lura dole ya ijiye kunyan nan ya tuhumi yaron nan da kyau, Baffa yace "banso
kamin karya Sameer, kafadi mini gaskiya Allah najinka yana kuma kallonka a sama"
ahankali yace "kanajin sha'awa Sameer kokuma bakajin sha'awa ko kadan?" he wasn't
expecting such question daga Baffa dan bakaramin kunya tambayar yasa yajiba hakan
yasa yakasa magana sai kanshi dayasake saukarwa akasa, kiran sunanshi Baffa yayi
babu alamun wasa yace "am talking to you Son answer me now, kanajin sha'awa ko
bakaji?" kanshi nakasa ahankali murya chan kasa kaman an tursasashi yay magana yace
"I....in...aji Baffa" cikin tsantsan damuwa Baffa yace "to mesa bakason kai aure
kadauke ma kanka duk wata sha'awan, kasami natsuwa Sameer? Jibeka kullum shiru
shiru kullum kai kadai kunshe adakinka in badai kaje wurin aiki ba, kodai neman
mata kakeyi ne Sameer saisa baka sha'awan aure?" da sauri ya girgiza kai yace
"Baffa ban taba neman mataba" shiru Baffa yayi yana kallonshi ya yarda baya neman
nata dan duk cikin yaran wanshi Sameer yafi dukansu natsuwa ga hankali banawasaba,
ga kunya da kawaici, idan yace lamarin Sameer baya damunshi yayi karya, ahankali
yace "Sameer nagaji da samaka ido, nidai aduniyan nan nasan babu abinda zai hana
lafiyayyen d'a namiji, mai aikin yi dayake da means din ciyar da mata dari bama
dayaba aure sai in baida lpy ne, nagaji da sama ido Sameer kullum kara zama tuzuru
kake dazaran ka shiga 40 kuma kafita ma daga tuzuru kadawo Babawo, Baban gida,
jibidai Nuru kaninka da matarshi Nabila da yarsu gwanin ban sha'awa, jibi Muhammad
da matarshi Fadila da yar yarinyar su gwanin ban sha'awa, kana ganinsu kaga mazajen
dake tattare da natsuwa suna samin natsuwa wajen matansu hankalin su kwance kullum
ka gansu cikin fara'a da raha suke, Mu'azu ma jibi yanda yake tasowa dazaran yagama
makaranta sai aure shima bazan zuba maka idoba kaita zaman gida kaki aure ba har
kaninka suzo sugama aure kai kana nan kana gauranci, enough is enough, tunda dai
kaki fadimani gaskiya kace lafiyanka kalau ka saurareni da kyau kaji" yay dan
shiru sanna yace "nabaka nan da kwana 30, wata daya Sameer nabaka, wlh wlh inhar
wata dayan nan suka cika bakacemin Baffa ga wacce nakeso anemamin aurenta ba nizan
maka aure, kuma kowana aurama don't complain nagayamaka" ganin yanda Baffa kemai
magana azafafe kaman zai rufeshi da duka yasa yace "ayaha kuri Baffa" "don't tell
me nayakuri, inkanaso in hakura kaje kai aure Sameer, kasan sau nawa mahaifiyar ka
ke kuka tana zudda hawaye kan kin auren ka? Kaga tashi kabani wuri nan da 30days
zamu sake zama nabiyu, get ready for kowa nahada ka da ita, sanan anjima zan aikoma
da rubutu inma iskokai ne kehanaka auren zamu koresu ne da izinin Allah, tashi
katafi" tashi yayi ahankali idanunshi harsundan chanza kala sun soma ja yazura
takalmin shi yafice, tunda yafara saukowa daga stairs din kanenshi kowa ke
kallonshi barinma Ummi data zubamai idanu, gyara fuskarshi yayi yakarasa saukowa
ganin zaiyi hanyar fita yasa da sauri Ummi tace "Son" juyowa yayi yace "na'am Ummi
na" tasowa Ummi tayi takaraso har inda yake hannunshi takama tace "muje dinning kai
breakfast, bakai breakfast ba" baison yamata musu hakan yasa kawai yabita kujera
tajamai ya zauna tashiga bude warmers sukuma yan falon suka cigaba da hiransu, tace
"me zaka ci? In zubama biryani rice kokuma bread rolls da tea?" murya chan kasa
trying to hide damuwan shi yace "bread rolls Ummi" zubamai tayi ta hadamai tea
sanan ta turamai gabanshi, sanan tadau spoon ta mikamai ya karba tareda sakin mata
murmushi yace "thank you Ummi" kanshi ta shafa in a very loving way irin son da da
uwa dinan tace "ka cinye fa, karka rage okay, bari naje naga Baffa ku" juyawa tayi
tahau kan stairs shikuma yahaucim dudda bawani dadi abincin kema bakinshi ba dan
baida apatite.



Tasowa Asiya tayi da sauri tazo dinning din ganin Ummi tai sama, kujeran kusada shi
taja ta zauna tana murmushi tace "Yayan mu good morning" dan juyowa yayi ya kalleta
shidai arayuwan shi yanason kanenshi, murmushi yamata yace "morning Asiya, Ya
school?" yay maganan yanakai mug din tea bakinshi looking compose as usual, kaman
zatai kuka ashagwabe tace "school fine Yayan mu, kullum akemana C.A, kullum" batare
daya kalleta yace "that calls for working hard more right?" washe mai baki tayi
cikeda jin dadi ganin yau yana mata magana sosai tace "right Ya Sameer" murmushi
maidan sauti yayi yacigaba dacin abinci ahankali sai kallonshi takeyi yanda yake
kurban tea din kadai is breathtaking, yanayin komi da aji bada garaje ba, ita kanta
batamasan mesa take kallonshi hakaba kaman zata cinyeshi, juyowa yayi ya kalleta
sabida yanda jikinshi yabashi ana kallonshi hakan yasa tai murmushi tareda
wayancewa da sauri tace "Ya Sameer kaga my friend is getting married ending of this
month kuma wai Mummy bazata mini ankon ba, Ya Sameer zakamin plssss" gyada mata kai
yayi hakan yasa tai ihu tareda tashi daga kan kujeran tana rawa, murmushi yayi
yatashi daga kan kujeran plate din abincin ya nuna mata yace "take those to the
kitchen kizo side dina later" da sauri tace "to Yayan mu nagode" karasowa cikin
falon yayi yana kallon Mu'az dake buga game awaya, kafin yakaraso inda yake yace
"Mu'az" da sauri Mu'az ya ijiye wayan dan duk in Ya Sameer ya kirashi har cikin
ranshi yakeji da sauri yace "na'am" karasowa gabanshi yayi hannunshi daya cikin
aljihu yana kallonshi yace "what time did you suppose to leave for school?" cikeda
dan yanayin tsoro Mu'az yace "by 3 yayan mu zantafi" ka wuce kaje kafara shiryawa,
tashi Mu'az yayi da sauri yay hanyar dakinshi daidai lokacin Princess tararrafo
tazo har inda yake tsaye ta kama kafanshi tanaso ta mike tsaye, murmushi yayi ya
tsugunna ya dauketa yaja kumatun ta ahankali yace "princess" kyalkyace wa da dariya
yarinyar tayi tana shafa dogon hancinshi hakan yasa su Nuru dukansu suka kwashe da
dariya, hararan su yayi kafin ahankali yace "let's go out they're watching us
princess"



_Dear VIPs na_
_this book is combination of storyline 2&3 which most of you chosen, when most of
you keep selecting 2 da 3, i was like what is VIP if I can't give my VIP what their
heart yearns? I was like okay 2 and 3 u guys are up, that's all what VIP is all
about grant them what heart dinsu yearns for and liked._

_Dear VIPs na_
_life is all about making your Very special people(VIP) feel special, feel involve,
feel worthy and feel muma munada daraja, treat them with respect and take them on a
cruise of nishadi da farinciki, this book *chasing the heart cravings* kunshi komi,
dan kowa na book din yabi abinda zuciyan shi keso, e.g ni yanzu nabi abinda
zuciyana keso nake muku book ko? Haka kuma kunbi abinda zuciyan ku keso kukai
joining VIP dan bakusan jira right? So come with me lemme give u on a journey of an
unbeatable experience, and feelings that is mind blowing and out of this world cus
this novel is blockbuster_

_subscription is 2k ba dan komi ba, I buy data, I sit and type always, power bank
for always having chargi for regular updates and other pete pete matsala that your
2k can help me taushe it. I love you VIP na, and I am forever grateful of your
support 🙏🏽 cheer to good live, endless friendship and love!!_

_pay 2k into my account 3107021073 aisha Muhammad first bank, send evidence of
payment to my watsapp number 07012181461 so I can add you to VIP group, as of now
this is VIP comment section_


_Happy Salla VIPs 🥂_[6/3, 9:41 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫


_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔


✍️ M Shakur




1️⃣1️⃣
1️⃣
1️⃣

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login