Showing 132001 words to 135000 words out of 197960 words

Chapter 45 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15043

kalla
dayaga ana karamai ruwa on both hands sanan yaga Noor zaune kan plastic chair
yadaura kanshi jikin gadon yana bacci dan lumshe idanu yayi yana kokarin tuna
abinda yafaru dashi kafin yabude idanun da kyar, hannunshi yadaga yadaura kan Noor
ahankali sanan yadaga, ahankali yatashi da kyar ko'ina ajikinshi namai wani irin
ciwo yadanja jikinshi ya jingina da gado, motsin da Noor yaji yasa yabude idanunshi
ganin Sameer ne yatashi yazauna yana cije lips tareda dafe kanshi dayadan saramai
yasa yace "Ya Sameer katashi, sannu meke maka ciwo, bari nakira Dr" yajuya zai fita
hannunshi Sameer yarike da sauri yajuyo yace "menene meke maka ciwo Ya Sameer?"
yatsine fuska yayi cikeda dauriya da jarumta irin tashi yace "am fine, I want to
shower jikina ba dadi" ahankali Noor dayaji kaman zaimai kuka dan yasan dauriyace
kawai yace "sannu bari nakira Dr acire maka drip din" yajuya yafita ko minti biyu
ba'a yiba yadawo tareda Dr Sameer, kasancewan Dr yasan Sameer sosai yace "Soja
antashi wai sannu an jijjiga file din sojoji, meke maka ciwo yanzu?" dan murmushi
Sameer yayi yace "nothing just wanna shower" da sauri Dr yace "yes zakafijin dadin
jikin ka, sannu" yay maganan yana ciremai, ahankali ya sauko da kafafunshi kasa duk
suna kallonshi sanan yasauka daga kan gadon ahankali dan lumshe ido yayi da sauri
tareda dafa goshin shi dan jiri yakeji da sauri Dr yarikeshi Noor ma haka, Dr yace
"I think kabar wankan nan sai anjima jiri baigama sakinka ba" dan yatsine fuska
yayi ya cije lips cikin muryanshi dake tattare da ciwo yace "I can manage, Noor
help me to the toilet ka kawomin kaya?" rikeshi Noor yayi yace "yes akwai some of
new kayanka dana karbo daga wajen tela amota na dakuma few English wears" bayin
yabude suka shiga yamai setting hot water sanan yajuya yafita tareda rufomai kofa.



Kaya Sameer ya shiga cirewa bayin very clean dan asibitin masu kudine sosai, rataye
kayanshi yayi a hanger sanan yabi gabanshi da kallo ganin alamu alamun jini, runtse
idanu yayi yana tunanin abinda yafaru, ahankali yasa hannu ya kunna hot shower ya
shiga wanka komi nadawo mai fresh a brain dinshi, saida yagama wankan tass sanan
yay wankan tsarki yay brush da sabon brush da asibitin suka ijiye musu abayi da
sabon toothpaste sanan yadau sabon towel yadaura yakira sunan Noor da muryanshi da
bata fita da kyau. "Noor" da sauri Noor yay gaban bayin yace "ganinan Yayan mu, na
shigo bayin?" ahankali yace "give me soft cloth marasa nauyi" wata faran polo shirt
Noor yadaukan mai da dogon trouser sanan yaje gaban bayin yace "gasunan Ya Sameer"
murya chan kasa yace "come inside" bude kofan ahankali Noor yayi ya shiga yabashi
kayan ya kwashi wayanda yacire daga kan hanger yafita dasu ya linke ya ijiye cikin
jakan kayan, almost 5min yadauka sanan yafito daga bayin yana tafiya ahankali yay
wani irin mugun kyau yadan fada, tashi Noor yayi da sauri yariko shi ya zaunar
dashi gaban gado yana kallon fuskanshi yace "sannu Ya Sameer, are you hungry
maizanje nasayo ma?" girgiza ma Noor kai yayi yace "am not hungry I want to observe
salat" da sauri Noor yace "OK" dadduma dayake tareda kayan daya dauko daga mota
yaciro ya shimfida mai zama yayi ahankali dan jiri shiyafi damunshi yay sallolin
azaune sanan yahada dana asuba da aka tada a mosque din hospital, saida yay azkar
yatashi daga kan dadduman yahau kan gado, fitowa daga bayin Noor yayi yazo yay
salla akan nashi dadduman yana idarwa ya tashi yajuyo yana linke dadduman yana
kallon Ya Sameer din dayaga ya lumshe ido kaman wanda yay zurfi a tunani yay shiru,
ijiye dadduman yayi yazauna akan kujera hannun Sameer yakama yarike ahankali yace
"Ya Sameer menene, tunanin me kake?" bude idanunshi dasuka danyi ja yayi yadaura
kan Noor, murya chan kasa kaman wanda baiso yace wani abu yace "where is
my......wife?" maida kanshi kasa Noor yayi yace "tana hospital dinan itama" bude
idanu da kyau Sameer yayi ya kalli Noor dayadan dagokai yana kallon Sameer din,
kallon da Sameer yakemai yasa yace "batada lpy ita.....ma".
[09/07, 12:33] Aishat Muhammad: 80.




Lumshe ido back Sameer yayi yasa hannunshi akan saman goshin shi murya chan kasa ta
yanda ko Noor baijishi da kyau ba yace "subhanallah" yakai almost 10min ahaka bai
bude idanunshi ba sai chan yazare hannunshi daga kan goshin yabude idanunshi dasuka
chanza kala yadaura su akan Noor dake kallonshi saukowa yay daga kan gadon dudda
yanajin jiri sosai but ya dake batare daya kalli Noor ba yace "take me to her room"
tashi Noor yayi daga kan kujera yabude kofa yafita ahankali Sameer yadaga kafa
yafito kana ganinshi kasan yanajin jiki shima ganin yanda yake tafiya yasa Noor
yadena sauri yajirashi har suka karasa wajejen dakin datake, suna shigowa corridor
dakinta suka farajin ihunta da kuka sosai. "dan Allah kubari haka, zan mutu zan
mutu zafi wayyo Allah na Abba....." chak Noor ya tsaya batare daya karasa zuwa
wajen dakinba ahankali yace "ga dakin chan Ya Sameer room 9D, bari nai waya da Ummi
nafadi mata meza akawo mana.." baima jira amsan Sameer ba yajuya da sauri yafita
daga wurin, Sameer yakai almost 3min tsaye a wurin yana sauraran ihun datake yi
jikinshi yay wani irin sanyi yaji wani sabon zazzabi na neman lulubeshi, ahankali
yadaga kafa yakarasa har zuwa gaban dakin dayake kofan arufe ne but akwai wani dan
gajeren glass ajikin kofan ta sama inka leka ta wajen kana iya hango na cikin dakin
hakan yasa ya leka babu kowa adakin sai gadonta dayaga has been stain with blood
dayake farin zanin gadone saikuma ihunta dayakeji dakuma maganganu mata, wata tace
"sorry, yanzun nan za'a gama ki daure kinji" bude kofan bayin akayi yaga Dr Bisola
dan yasan almost all the hospital Dr tafito daga bayin tazo ta dauki wasu allurai
tana hadawa a syringe lumshe ido yayi ya daura kanshi jikin kofar cikin wata murya
mai rauni yace "omg, what have I done? Menayi haka" karan sake bude kofan bayin
dayaji dakuma kukanta sosai yasa yadaga kai Nurses biyune yaga sun fito daga bayin
sun dauki Rahima dake daure da towel idanunta sunyi jajir sun kumbura kumburin da
baitaba ganin sunyiba duk uban kukan datake yi ga uban zufa a goshinta tsabagen
zafin ruwan zafin datasha, tsawa Dr ta daka musu dan bata tolerating nonsense tace
"my friend ku saukar da ita, idan bata taka kafa tai tafiya ba how will the
stitches heal kunzaci mace tasamu tear is a joking mata ne, I know it hurts but you
have to help yourself kinji patient sauko kizo namiki allura" saukar da ita sukayi
yanda yaga tai ihu tama kasa ijiye kafafunta tai baya zata fadi yasa dawani irin
sauri yakoma baya kaman an tureshi ranshi ya mugun yimai daci, dawani irin sauri ya
juya kaman ana ingizashi jiri na dibanshi yay dakinshi budewa yayi ayanda yabude
kofar yasa Noor yadago kanshi da sauri fadawa gado yayi ya kwanta yana nishi fast
yana dunkule hannu kaman ya kashe kanshi dan haushi yakeji.




Ahankali Noor yatura hannunshi cikin aljihu yaciro syringe din jiya daya dauka ya
ijiye daidai wurin fuskar Sameer, bude ido ahankali Sameer yayi jin kaman hannun
mutum kusada shi, ganin Noor ya ijiyemai syringe yasa ya kade syringe din da ido.

Sosai Noor ya sassauta muryanshi yace "I don't judge you Ya Sameer cus nasan kome
kayi you have a reason for doing that, but abinda kayi this time I know ni kaninka
ne baidace nacema komiba but I have to dan kayi ba daidai ba, I have a daughter dan
duk wanda yama y'ata abinda kama yarinyar chan sainasa an kullesa wlh sanan naraba
auren danba sonta yakeyi ba" yay shiru zuciyarshi na tafarfasa yace "for God sake I
don't know you to be someone that even fancy about sex to be precise talk more of
using sexs abubuwan, Ya Sameer how could you inject yourself da alluran saka su
saka mugun karfin sha'awa dake fitar da mutum daga hayyacin sa just because you
want to have sex kasan mekama kanka sanan kasan mekama matarka?" yay dan shiru
sanan yace "Dr Momodu yace you were lucky, and kwanakin ka na gaba we could have
lost you, dan alluran tamaka karfi mugun karfi you took overdose saisa kadinga amai
mugun zazzabi ya saukar maka har bakasan inda kanka yakeba saida suka zuko alluran
daga jikin ka kaman yanda ake zuko guba ko in yaro yasha kalanzir haka aka maka
jiya, all this akan sex kai you think bakada karfin kanka ne dazakai amfani da
eternal substance, inda yarinyar mutane ta mutu me zakace? Ya Sameer this girl was
bleeding yesterday kaman wacce ta haihu, you gave her tear, or sabida kaga ubanta
yanuna maka yagaji da halinta ne yasa you think you can molest her like that kaman
wata slave dinka, you rape that girl Ya Sameer, fiyade kama.........." kasa karasa
maganan yayi sabida mugun marin da Sameer ya daukeshi dashi, hannunshi yadaura akan
inda ya marai ya kalli Sameer din idanunshi sunyi jajir, cikin mugun fushi Sameer
yace "watch it Noor! Watch your tongue, don't cross limit" ahankali Noor ya saukar
da kanshi kasa batare dayace komiba, dafe kanshi Sameer yayi kirjinshi namai zafi
yace "you think I just marry that girl to abuse her? How could you such hurtful
words akaina Noor?" shiru yayi kafin cikin wata sassanyar murya yace "you think I
got married to that girl hakanan ne? You think I got married to her just to save
her from her step mum, just to save her from illicit drugs?" cikin wata irin murya
dake tattare da broken heart yace "Well you are right, duk gaskiya kafadi ba
karyaba Noor, but there's more, there's more dat I keep to myself, I didn't just
marry Rahima because of all you've mentioned dudda hakan ne, I got married to her
because I love her, I love her sosai, ina sonta so da tushenshi is tausayi, and I
can't rape anygurl on this planet ballema wacce nakeso" yay shiru yana shafa
goshinshin shi sanan yazare hannun ya ijiye yadan fuzar da iska yace "ada ina ganin
ba hurumina bane na fayyace ma Abba komi kan matar dayake tareda shi this time ta
taboni I just have to" yasake yin shiru sanan yace "there's something I haven't
told all of you Noor, kaga Maryam step Mum din Rahima......." nan yashiga bama Noor
labari tun ranan data fara rungume shi da Rahima tai shaye shaye a gidansu har zuwa
abinda yafaru yau tatas. "innalillahi wa innailaihi raji'un, Ya Sameer matar nan ko
shaidan saiya sara mata omg why didn't you tell baban su Rahima?" ahankali Sameer
yace "kunya nikeji, inajin nauyin yima Abba irin maganan nan, tayaya zan fadi mishi
Abba matarka na nemana how Noor? Maganan tamin girma dayawa, tausayinshi nikeji
he's so old wat if news din yabashi heart attack eh? Yafadi yamutu wat will I tell
his daughters? Girgiza kai yayi yace "I can never tell him but I will deal with
Maryam so........" kasa karasa maganan yayi sabida bude kofa da akayi yaga Abba
sanye da doguwar farar jallabiya da hula akanshi, hannunshi rikeda charbi da key
mota da alamu daga masallaci yawuto nan, ganin inda Sameer yake kallo yasa Noor
yajuya da sauri ya kalli bayanshi ganin Abban su Rahima tsaye idanunshi sundan
chanza launi yasa yatashi da sauri ya mikamai hannu cikeda girmamawa yace "barka da
zuwa Abba, ina kwana" ahankali Sameer yasaukar da kanshi kasa, wata irin murmushin
karfin hali Abba ya kakalo yamikama Noor hannu yace "Noor barka da safiya Noor,
yamai jiki" da sauri Sameer yasake dagokai ya kalli Abba jin yanda yakira sunan
Noor anan yakara tabbatar da cewa Abba heard all conversation dinsu da Noor dan
baisan sunan Noor ba, "Son" Abba yakira sunan shi yana zama akan plastic chair da
Noor ya ijiyemai, kallonshi Sameer yayi ahankali yace "Abba" hannunshi Abba yamika
dake rawa sosai ya shafa kan fuskar Sameer din yace "sannu son ya jiki?" yay
maganan idanunshi na sauka kan syringe din da yaji suna magana akai, ahankali
Sameer yace "naji sauki Abba" murmushi Abba yayi yace "to Allah kara sauki, daga
masallaci nawuto nace bari nazo naduba dan nadamu sosai, Allah ya kara lpy, Allah
yasa kaffara ne, ina Rahima?" ya tambayeta ahankali dan he really wants to see her,
kasa magana Sameer yayi sai Noor da ahankali yace "tana chan dakin" dan mahaifinta
ne bazasu iyamai karyaba, tashi Abba yayi ya kalli Sameer yace "Allah yakara lpy
Son, sai nazo kara dubaka" ya kalli Noor yace "muje kai kaini inda Rahima take"
tashi Noor yayi suka fita tareda Abba har zuwa dakin da Rahima take yabude kofar
dakin Rahima na kwance idanunta a lumshe a lullubeta da bargo mai kyau dan sanyi
takeji ana mata karin ruwa, da sauri Abba yace "subhallahi dukansu ne ba lpy dama"
gyadamai kai kawai Noor yayi, Abba yakarasa gaban gadon zama yayi kan plastic chair
wajen yakama hannunta dayaji bala'in zafi sanan yakira sunanta ahankali. "Rahima,
Auta" kaman daga sama cikin zafin zazzabi Rahima taji muryan Abban ta bude idanunta
dasuke buduwan mata da kyar tayi tadaurasu akan Abba dake rikeda hannunta yana
kallon fuskarta, ganin Abba yasa tawani irin fashe da kuka sosai ko'ina na jikinta
na girgiza da sauri Abba yadaura hannunshi kan fuskarta yace "stop crying, u are
strong, dena kuka dena kuka kinji" da sauri Noor yajuya yafita ya maido kofan
yarufe tausayi suke bashi.



Hannu yasa ta share mata hawayen dasuka kasa dena zuba, cikin wata irin murya
dabata fita sosai tace "Abba" da sauri Abba yace "na'am menene Rahima kirjin ki na
bugawa dayawa ki kwantar da hankalin ki u will be fine kinji, haka maleria take"
cikin wata irin murya Rahima tace "Abba da gaske Mummy na ta tsaneni itama? Tace ta
tsaneni, ta tsani abinda yayini sanan wayan nan mutanen dasuka biyoni wai uta
tasasu suyi raping dina sanan su yarda ni na mutu, wai uta tabasu kwangilar, bata
taba sona ba, me akeyi da yar kishiya, Abba da gaske Mummy na tafadi haka ko
mafarki nikeyi?" all this maganganun datake yi inda ace Abba baikai kunnenshi
saitin bakinta ba da bazaiji ba, hannu yasa yasake gogemata hawayen dake zubowa
yace "da yaushe kikaji Mummy ki tafadi haka?" cikin wata murya kaman tamaison suma
tace "Ya Sameer tafadi ma haka babu kaya ajikinta ta rirrike shi tanacemai......"
saikuma tai shiru tafashe da kuka, for the first time Abba yaji Allah yabashi
courage akan anything zancen Mummy, ahankali yace "metake cewa?" cikin wata irin
murya tace "wai tanason shi maisa ya aureni, wai saiya sadu da ita" tafashe dawani
kuku, cikin son ya kara tantance abinda yaji Sameer yafadi ma Noor na cewa ya auro.
[09/07, 12:40] Aishat Muhammad: 81




Rahima sabida he wants to save her from her step Mum, ahankali yace "listen to me
Rahima stop crying, kinga yanzu mun shirya and you've already promised me bazaki
kara shaye shaye ba, inaso kifadi mani ranan damuka dawo mukaga kina shaye shaye
yan makarantan ku su Chris ne suka kawo miki?" girgixa ma Abba kai tayi tana nishi
tace "a'a, adakina kan drawer nagani" dasauri Abba yace "towa ya shigo dakin ki ya
ijiye awurin?" shiru tayi hawaye nafita daga idanunta batare datai magana ba, da
sauri Abba yace "tell me" ahankali tace "amana Abba ba zaka fadima kowaba?"
gyadamata kai Abba yayi batare dayace komiba ahankali tace "Mummy nane!" yanda
takira sunan saida yasa yasake maimaita sunan yace "Mummy ki, ya akayi take baki
kayan shaye shaye without my knowledge?" shiru tayi batacemai komiba saidai da
wayau da wayau da inda extracting info daga bakinta yana tareda ita yana shafa mata
kai hartai bacci sanan yatashi yawuce ya shiga motarshi yatafi kirjinshi na
tafarfasa, yawuce gidan Sameer, dudda sojojin sunso hanashi shiga dan Sameer baya
gida but he came there as a lawyer and he need their maximum support, yariga ya
lura akwai CCTV agida so CCTV footage yay request yabi sojan har zuwa dakin sojan
ya kwafemai CCTV footage din na 1week ago awani flash da Abba ya bayar sanan yamusu
sallama tareda yimusu godiya yawuce yatafi gida, baima shiga flat dinsu ba study
room dinshi ya shiga ya kulle kofa yaje gaban table dinshi ya zauna ya makala flash
dinshi jikin desktop din ya fara kallon footage din gidan gabaki hada har zuwa
falon sama da falon kasa sukenan inda mai CCTV dinke capturing, Sameer shine kadai
keda CCTV dakin Rahima dan a pad dinshi yake kallon wanan.
Daga ranan da interior din suka fara kawo kaya yafara kallo yana wucewa har zuwa
ranan dayaga Mummy tazo, yaga lokacin da Rahima tabude daki rikeda gyalen Mummy ta
sauka kasa sanan yaga Mummy tafito waje tayi hanyar dakin Sameer ta tsaya gaban
dakin taja riganta kasa tafito da nonuwa da kyau, ahankali Abba yace "innalillahi
wa innailaihi raji'un" sanan yacigaba da kallo yaga tabude dakin Sameer tafada
bayan andau lokaci sai gashi Sameer yafito yana dukanta ga Rahima tazo tana kuka
tanacema Rahima ta sadu da Sameer Allah ya isa, da wasu maganganu kala kala harya
gama kallon abinda yafaru ranan yana relating abun da abubuwan da Mummy ta dinga yi
ranan ko bata kwana gidaba tai karya, banda haka dayace ya aurama Rahima Sameer
yatuna haukan datayi, cigaba da kallon video yayi har zuwa jiya, dafarko dai yaga
Sameer baida lpy yazo ya kwanta sai chan Mummy ta shigo gidan da jaka a hannunta
tana tafiya kaman barauniya ta shige dakin Rahima, sai chan ka Rahima tafito tasaka
hijabi ta sauka kasa, sai chan ga Mummy tafito rikeda allura haka yadinga kallon
komi har zuwa inda Mummy ta dane bayan Sameer ta rungume shi babu kaya ajikinshi
yana kiran sunan Allah, wani irin bugawa da kirjin Abba yakeyi saida yay pursing
abin ya shiga karanto ayoyin Al Qur'ani koyasami karfi da jarumta, yadade ahaka
sanan yadago kanshi yacigaba da kallo haryakai inada yazo yafitar da ita daga
gidan, abu yaji yana gangara a idanunshi da sauri yakai hannu yataba yaji hawaye ne
sharewa yayi da sauri, baitaba sanin bada zuciya daya Mummy ke zama dashi ba, tasha
yin abubuwa da dama dayakamata ya zargeta akai amma baya iyawa gani yake ya za'ayi
ya zargi matarshi, ranan datake tarayya da ita yaji takira sunan Sameer saida ya
kwana da abin aranshi saikuma yazo ya kauda abin, inda ace baiga abubuwan nan da
idanunshi ba dabazai taba yardaba, idanunshi yasake sharewa sanan yatashi ahankali
ya shiga bayin dakin yadauro alwala yazo yay sallan walha sanan yatashi, wayarshi
yadauka yakira number babban yayan su Mummy wanda yake amatsayin abokinshi Alhaji
Bashir, dansu uku maman su ta haifa shine babba sai Mummy sai kanwar su dake aure a
Suleja, irin yanayin yanda yaji maganan Abba yasa yace "ganinan zuwa yanzun nan dan
Allah Alhaji koma menene ayahakuri akai zuciya nesa" katse wayar Abba yayi yadauko
wani jotter dinshi mai kyau da byro yay wasu rubutu aciki sanan ya linke yajawo
sabon envelope yajefa aciki yarike yasake zama awurin almost an hour yaji horn din
mota hakan yasa yatashi yafita, da fara'a ya shigo da Alhaji Bashir har falo su
Siddiqa cikeda murna sunata gaida Baffan su wucewa Abba yayi corridor, key yadauko
daga dakinshi yafito yasaka akofar yabude kofar dakin Mummy, zaune yaga Mummy
dataci gayu sosai kaman ba itaba da hankalinta ya gushe jiya saida safen nan tadawo
daidai. Murmushi tayi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login