Showing 42001 words to 45000 words out of 197960 words
2️⃣5️⃣
Takai minti biyar kanta nakan guiwanta kuka take, Murya chan kasa yakirata.
"Rahima" dago kanta tayi ta kallai idanunta sunyi jajir sosai yace "what happen to
your mother? Mesa kika tsaneta?" wasu sababbin hawayen ne suka shiga zubomata tasa
hijabin kan fuskarta tana gogewa hakan ya bayyana da rigan dake jikinta sosai,
ahankali yace "ba kuka nace kitasani agaba kinamin ba, what happen to your Mum?"
share fuskanta tayi tass sanan ahankali tace "basa tareda Abba, ranan data bar
gidan Abba was ranan datamin shegen duka, bansan mena mata ba tagama waya a phone I
was watching cartoon a falo kawai tazo tahauni da duka tabugani da bango sai ihu
nake, yanda take dukana yasa gateman dasu Mummy da Siddiqa had to come to my rescue
but taki bari suyi saving dina tace musu ita ta haifeni ko kasheni tayi ita ta
haifen, ganin nasoma finding breathing difficult tun ina kuka ina cemata Mummy
yakuri nakasa yasa Mummy tai maza takira Dady dake wurin aiki ga abinda ke faruwa,
kafin Dady yadawo bana gani da kyau ma, but I could barely hear muryan Abba yana
cemata takashemai yarinya wlh saiya daureta agidan yari, and I heard Mummy saying
zai iya tunda ma ya daure ubanta, yabata saki kota wurgani arijiyan nan, daganan I
don't know what was happening, nasan nabude idanuna naga Mummy nacemin dagayau ita
ba mahaifiyata bace that ita in as much as she is concern ko za'a kwana ana
tambayanta bata taba haihuwa ba, she is not my mother and I am not her mother, ta
tsaneni da duka zuciyanta sanan ta tsani mahaifina da duka zuciyanta bani ba ita
har abadan ta juyar dani bansan meya faruba but I felt sharp pain a hannuna kota
burgeni ne oho, all I know is natashi daga bacci naganni a ICU da Abba da Mummy
sunsa wanan kayan da ake shigowa ICU dashi, ansamin wani abu awuya ga dauri a
hannuna da kafana nasan duk ita tamin dukan dan I tot nama mutune, nayi rayuwa
almost for a year asibiti gida asibiti gida, karyan datamin sau uku ana sake
ballawa ana gyarawa daga baya ma na hausa Abba yakaini akamin daurin dan na asibiti
yakiyi, I use to ask Abba ina Mummy na cikin fushi zai cemin karna kara tambayanshi
ita, Mummy was my only friend, ita kadai kesona duk intaga ina kuka she will always
come to me dress me up and take me to shopping, saloon and ice cream shop, she give
me anything danace inaso kafin ma nafurta, she love me love da Mamana bata taba
nunamin ba, she always put me to sleep deep down my mother na raina, lokacin da
Abba yasaimin waya na labe adakina the first person dana fara kira was my Mum cause
na had dace number ta tun ina yarinya, I....I......called.....her" tafashe da kuka
sosai, murmushi tayi irin mai ciwon nan muryan ta na rawa sosai tace "ta daga wayan
tacemin hello, saida hawaye ya zubo daga idanuna after six years rabona da ita naji
muryan ta ranan for the first time, fashewa nayi da kuka ahankali, cikin kuka nace
mata Mummy ina kikaje kika barni? Mummy why did you leave me is Rahima" fashewa
dawani irin kuka tayi da kyar ta iya tsagaitawa tace "kasan menene she really
forgot me, could you believe she was asking me wai wace Rahima waye Rahima, bandamu
ba dan I was so excited nace mata is me, Rahima her daughter, her bulbulyoyo cus
that's the name the name she use to call me with da ita yarinya, tsaki tayi tace
she don't know me ta katse wayan, da sauri nakira ta back harsau uku bata dauka ba,
she picked ana hudun I said Mummy ahankali, wani irin ihu tamin dat ni mahaukaciyan
wani gari ne zan dinga kiranta Mummy, she hates me, this should be the last time
dazan kirata ta zageni stupid girl. I carried my eyes out, subsequently haka nake
kiranta once in a while dan kawai naji sanyi araina she always cursed me, the last
time I called her was ranan nan dana shiga rest room, I told her to come and get me
she said is should rot a headquarter dinku for all she cares stupid gurl, I felt
pain I regret calling her nima, my mum is a bad person wlh she don't deserve to be
a mother, she is heartless, cruel, wicked, and a dev......." " is okay!" Sameer
yafadi ahankali yana kallon yanda take kuka, saida tai kusan na minti goma sanan
yace "all this are not enough reason yasa kiyi embarking on shaye shaye ba, cause
it will ruin your life and kill you, duk problem din dakike dashi always face Allah
ki gayamai, you are too young to understand some situations and circumstances in
this life, stop believing drinking this and that shizai sa ki manta da damuwanki,
ki natsu and concentrate on your studies wata rana zaki zama wani abu da Maman ki
zata dinga nunaki a TV tace dats my daughter" dan murmushi tayi tasa hannu ta goge
hawayen daya zubomata tace "wlh bazata taba cewa haka ba" girgiza kai tayi cikin
wani irin yanayi na mugun ban tausayi cikin murya mai raunin gaske tace "ta tsaneni
sosai, sosai" wani iri Sameer yaji zuciyanshi tamai he is not a weak hearted person
dawuya yanunama abu yataba shi amma saida yaji tabashi tausayi, koma menene tayi
koda shaye shayen ne her mother baikamata tabata wanan treatment da tsanan ba, and
Allah will definitely ask her dan this small girl is hurt, ahankali yace "tashi
kitafi kicema Abba ina jiranshi anan" gyadamai kai tayi ta tashi tawuce yabita da
kallo, saida takai bakin kofa hartasa hannu zata bude kofan yakira sunanta
ahankali. "Rahima" ahankali ta dago jajayen idanunshi ta kallai gabanta yadan fadi,
Murya chan kasa yana kallonta in the eyes yace "don't cry again okay" gyadamai kai
tayi very slow tawuce tafita daga dakin, samun kanta tayi da tsayawa ta goge
idanunta tass sanan tawuce tai flat dinsu, Abba da Mummy kadai tagani a falo kafin
ma Abba yay magana Mummy tace "kin dawo ina Sameer din?" ahankali tace "yana study
room" ta kalli Abba tace "Abba yace yana jiranka a wurin" da sauri Abba yatashi
yafita, tahowa tayi ahankali ta zauna kusada Mummy dake binta da kallo kafin
ahankali ta daura kanta kan wuyan Mummy ta shige jikinta, ahankali Mummy tace
"maganan me kikayi da Sameer? Me yagaya miki?" murya chan kasa tace "kan drugs" da
sauri Mummy ta dagata tace "me kikacemai to? Hope baki tonamin asiri ba?" girgixa
mata kai tayi, hakan yasa Mummy tace "to meya saki kuka idanunki sukai ja?" maida
kanta jikin Mummy tayi tace "fada yamin" shiru Mummy tayi tana hamdala dudda dama
tasan Rahima bazata taba tonamata asiri ba but she was worried tazaci aure Abba
yake kokarin hadawa tsakanin Rahima da Sameer din dan wlh ko zasuyi tsiya da Abba
bazata yardaba, babu yar da Sameer zai aura agidan nan dan she has goody goody
plans akan Lieutttt.
Bude study room din Abba yayi ya shiga da sallama kusada Sameer ya karasa ya zauna
yace "Sannu da aiki Son, ya kukayi da ita?" dan ajiyan zuciya Sameer ya sauke yace
"acikin all maganganun da nai da Rahima, 90% of her problem dana lura shine she is
missing her Mum" da sauri Abba yace "her Mum kullum fa tana makale da mamanta" dan
kallon Abba Sameer yayi yace "I mean her Biological Mother" shiru Abba yayi kaman
an dauke nepa ya tsaya chak yana kallon Sameer, ahankali Sameer yace "Abba ina
mahaifiyar Rahima? What happen between you two? Mesa batazuwa ganin Rahima ko
Rahima bata zuwa ganinta, mesa Rahima don't know anything about the whereabout of
her Mum? Rahima is not a small gurl anymore don't you think she deserves to know
something akan inda maman ta take?" Sameer dukya koromai tambayoyin yana kallonshi
yanda yay shiru yana kallonshi, ahankali Abba yasa hannayenshi ya shafe fuskarshi
kafan me shafa addu'a ya fuzar da iska tareda dago kanshi ya kalli Sameer yace "ni
nasan in as much as Rahima tasha nonon mahaifiyar ta dole ta tambayeta dole kuma
tai kewanta watarana komin ko irin soyayyan damuka bata, tsakanin uwa da y'a sai
Allah, Allah kadai yasan irin bond din dayay creating tsakanin su" yadanyi shiru
tareda fuzar da iska yace "mata na biyu ne da, wanan Mummy dakasani Lieutenant ba
ita tahaifi Rahima ba, yaranta uku dani, Siddiqa, Zeenatu da Lubabatu, Rahima dayar
matata mai suna Safa ce ta aureta, bafulata na ce yar gombe but anan Abuja duk aka
haife su, Rahima kadai muka haifa tare muka rabu" Abba yay shiru looking so much
worried, ahankali Sameer yace "mesa ta tsani Rahima Abba, what happen between
them?" girgixa kai Abba yayi cikin wani irin yanayi yace "matsalan Safa bada Rahima
bane, danine, nita tsana sama da komi aduniyan nan shine tsanan data mini ya shafi
yarda muka haifa nida ita, am sure batada wayanda ta tsana aduniyan nan kaman ni da
Rahima" cikeda mamaki Sameer ya kalli Abba yanaso ya tambayi more question amma
bayaso yay intruding into Abba's privacy hakan yasa yay shiru, dagokai Abba yayi ya
kalleshi yace "Sameer na dauke ka amatsayin my first son zan fadamaka komi" yadanyi
shiru sanan ya nisa yace "Safa is from a very very wealthy home, iyayen ta are
super rich, mun hadu tanaso na sosai nima ina sonta she don't mind a lokacin inada
mata da yara uku lokacin banma riga nazama judge ba amma ta aureni, uwargidana
tarigata haihuwa ta haifi Lubabatu kafin after two yrs itama muka haifi Rahima bata
kara haihuwaba, munada almost 8yrs da aure nazama judge tafi kowa murna, she loves
me sosai, ana haka munada 11-12 yrs da aure a lokacin Rahima was just 12yrs a case
come to my table EFCC suna charging her father and her mother akan money laundering
da fraud, innalillahi bantaba shiga matsala irin na lokacin ba hankalin Safa
yatashi she refuse to believe iyayen ta yan damfara ne suna damfaran turawa and to
tell you the truth her parent were guilty dan sabida surukai nane I took my time
nai investigating case din to the core nagano gaskiya they're really guilty of
their act, I was on a hot sit, gefe daya in laws dinane iyayen matana data haifamin
beautiful daughter gefe daya yan damfara ne, Safa kullum ba dare ba rana kuka
takemin akan nama iyayen ta rai karna yanke musu hukunci dazaisa suje gidan yari,
tunda nafara aiki in this my profession bantaba take gaskiya nabi karyaba, dudda
inason Safa I had to do the right thing nai sentencing nasu to 10yrs life in prison
da fine worth 350million dollars, ranan Safa takusan karaman hauka a court dan
taje, haka aka tattare mamanta da baban ta aka fito in front of that court
mahaifiyata tace mata inhar ita ta haifeta, inhar ita yar halas ce yarsu, sanan
yarta data dauketa aciki na wata tara babu abinda zata kara zama tayi da mutumin da
kuma yar wanda ya tura iyayenta gidan yari na tsawon shekara goma, dagayau bata
bashi, inhar tacigaba da sonshi to ita ba yarsu bace aka jasu akai mota dasu, mota
Safa ta shiga tayo gida, the next thing was Mummy su Siddiqa da masu gadi sun
kikkirani waiga Safa zata kashe Small Rahima of 12yrs, she knows ina mutuwan son
Rahima she can get to me inhar ta tabamin Rahima shine ta shiga dukan yarinyar nan,
wai ta tsaneta ita ba mahaifiyarta bace tadena kiranta da Mummy harna iso nasamu
Rahima kaman ma tamutu, I was angry nakusan dukan Safa amma na daure dan I can
never hit my wife I told her ta kashe min yarinya itama saina kaita gidan yari
kaman yanda nakai iyayenta, shine ta daga Rahima ta bugata da jikin rijiya Rahima
ta sume warwas, I had to slap the hell out of Safa, takama rigana ta barka so kawai
take nabiye mata muyi dambe dan she was pain yanda na sentencing her parent to
jail, tace min wlh inban saketa ba saita kashe Rahima right this instant inyaso
taje wajen iyayenta duksu hade a prison, at long last saida nabata saki biyu sanan
tarabu dani nadau Rahima Mummy su Siddiqa tabini da sauri muka kaita asibiti tama
yarinyar nan karaya uku, wuya, hannu da guiwwa" yay dan shiru sanan ya nisa yace
"Sameer kaga Mummy su Siddiqa nan, abinda tamin in this life banjin akwai wata mace
dazata taba iyamin ba, saisa I can give that woman the whole world bandamu ba, ita
tatayani kulada Rahima tabata motherly love, to the extend tazo taso Rahima sama da
nata yaran, bata taba barin Rahima tai lacking abuba, kafin nama Rahima ita tamata.
"
_ina bin book dinan daki daki, sannu sannu bata hana gobe zuwa, hope u guys are
enjoying it VIPs_💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
2️⃣6️⃣
6️⃣
2️⃣ 2️⃣6️⃣
"I thought sabida Rahima was still a small girl then lokacin da whole incident din
yafaru tamanta da komi bazata wani damu da zance mamanta ba, but today am hearing
something da bantaba expecting ba, and bansan yanda zan bulloma lamarin ba cus
nasan maman ta don't want anything to do with her, ta tsani Rahima all because of
me, banmasan inda take yanzu hakaba dan nasan government sun amshe gidansu anyi
auctioning da other property nasu all together, so I have no idea inda takoma, all
I know tundaga ranan bansake samunta awayaba, kaman blocking dina tayi, and I don't
think mahaifiyar Rahima nama nan Abuja, dan inda tananan nasan one way or the other
bazata taba boyun mini ba, saimun hadu kokuma sai anganta anfada mini" shiru yayi
yana sauke ajiyan zuciya sosai Sameer yaji yabashi tausayi, ahankali yace "okay a
ajiye wanan a one side Abba, I think, though I don't know what is between yayinta
da ita, but she has this perception cewa Mummy kadai kesonta kuduk baku sonta, I
think all what Rahima needs is love, in aka jata aka sata ajiki she will be able to
manta da komi and zata dena shaye shayen and live happily like kowani girl in her
age" gyadamai kai Abba yayi yace "hakane Sameer, bazanma karyaba Sameer all my
children ina sonsu sosai ma kuwa, bana daukan wanan kyautan princesses dinan da
Allah yamin da wasa, bansake ma Rahima fuska ne sabida Rahima ta taso da zafin kai,
rashin ji da rashin kunya, original rashin kunya ma ba fake ba, as small as you are
seeing this Rahima rashin kunya takema kowa, tama yayyinta bata basu respect, she
is so spoilt ko banmasan yaya zan maka bayani ba saisa kaga banwasa da ita hakanan,
yayyinta su Siddiqa suna sonta suma sosai amma rashin kunyan datake musu yasa
kullum fada suke, ta tasasu agaba da tsiwa, Rahima batajin magana Sameer" dan
murmushi yayi yace "in sha Allah komi yakusa zama daidai Abba" yay maganan yana
kallon agogon bangon dakin ganin shadaya na dare yasa yace "I think I should get
going dare yayi Abba, in sha Allah gobe zanzo, Allah yabamu sa'a" Ameen Abba yace
yatashi suka gaisa har Gate Abba yarakashi dayake a kofar gidansu yake parking,
motarshi ya shiga Abba yadaga mishi hannu shima ya dagamai yana murmushi yawuce
yafita, ahankali yake driving har zuwa gida, budemai gate mai gadi yayi ya shiga
yay parking yana kallon flat din Ummi takashe wuta yasan tai bacci ne dan inda
batai bacci ba zai hango haske adakin, flat dinshi yayi yabude shashin shi ya
shiga, rage kayan jikinshi yayi yawuce ya shiga bathroom shidai yanason yawan
wanka, wanka yayi yafito daure da towel a waist da dan karami towel a hannunshi
yana share kirjinshi har zuwa kan gado, zama kan gadonshi yayi yadauko mac book
dinshi yabude, Skype ya shiga yakira wani contact mai suna Abuddar, yana gyara
zama, ringing biyu yayi aka amsa, wani fuskan mutum ne fari kyakkyawan gaske yanada
gemu da saje sosai gadan furfura kadan kadan agemun yana zaune kan wata kujera
sanye da lab coat da alamu likita ne, kafin ma Sameer yay magana mutumin yace "you
are late yauma ko" dariya Sameer yayi da baicika ma kowa irin dariyan ba ya ijiye
karamin towel din hannunshi agefe yace "sorry Buddy, something came up ne I had to
attend to it" dan hararan shi mutumin yayi cikeda tuhuma yace "what came up?" dan
yatsine fuska Sameer yayi yace "is a long story, anyway ina kitten bakazo da ita
office ba?" girgixa mai kai yayi yace "No I left her da Mum dinta at home, barna
takemin wlh, Ya aiki?" ahankali Sameer yace "fine" shiru sukadan yi kafin dayan
yace "Buddy am so worried about you, I talked to Ummi today fa" da sauri Sameer ya
dafe kanshi cikeda gajiya da case din yace "not again! Are we still on this topic
Ayaan? Why is Ummi doing this to me? goosh!" yadafe kanshi yana fuzar da iska kafin
cikeda damuwa yace "am sick of this, I'm not a baby, for godsake nasan menake yi,
am not a small boy daza'a dinga daukan decision akaina, marriage is for better and
for worse so anytime am going into it, I have to make sure am ready you know" ganin
yanda yake masifa ranshi duk yabaci yasa Ayaan yatashi daga kan kujeran dayake kai,
lab coat din jikinshi ya cire ya koma ya zauna tareda natsuwa ya rungume
hannayenshi akirji yakira sunanshi ahankali. "Sameer" dago jajayen idanunshi Sameer
yayi tareda janye hanunshi daga kan goshin shi ya kallai irin kallon nan na wat
again, ahankali Ayaan yace "listen to me Buddy" yadanyi shiru kafin yace "Sameer we
grew up together, shekarun mu daya, attended the same primary school, secondary
school and university, inda I go for medicine and you go for civil engineering,
look at me today Sameer, am no more that Ayaan that think of himself only, no! Am
now a family man, anytime am thinking I think for myself and my family, na auri
Bilkisu na, look at me I have four kids, four Sameer" yanunamai yatsun shi guda
hudu, yace "four dinma dan ina child spacing, da yanzu maybe inada six or five
children, banda komi like my Family now, anytime natashi daga hospital nakoma gida
I meet my wife looking all glamorous waiting for me nadawo, gefenta are my kids
looking super neat playing or watching cartoon waiting for Papa to come home, ina
zuwa my wife and children feed me, subani abinci, I eat and play with the children
for a while kafin najata muyi daki and leave the children a falo suna kallon
carton, we go to our room and have sex Sameer, yes sex" yay maganan looking serious
yana kallon Sameer din kaman yanda yake kallonshi shima anatse, yace "I