Showing 135001 words to 138000 words out of 197960 words
cikeda kissa tace "Abban su ina kwana? Natashi naga kofa a
kulle na kira su Siddiqa wai kaika kulleni" daga bakin kofar dakin ya tsaya batare
daya amsa maganan taba yace "kizo falo, Alhaji Bashir yazo" yana maganan yajuya
tashi tayi gabanta na bugawa uku uku Abba baitaba mata magana hakaba aranta tace
"to kodai yagane wani abune jiyan?" falo tafito ta tarar da Abba harya zauna a
babban kujera kusada yayanta, saikuma su Siddiqa data gansu zazzaune akasa,
murmushi tayi tareda washe baki cikeda girmamawa tace "Yaya kaine agidan mu yau,
ina kwana" cikeda fara'a yace "Alhamdulillah Maryama, ya yara dudda na gansu jibi
yanda yar tatsitsiyar nan ta girma" yanuna last born dinta Luba, dariya Mummy tayi
tace "aikam sai tsawon kafa Luba keyi" Alhaji Bashir yace "yanzu Alhaji ke fadi
mini auren Rahima ya akayi baki sanar da niba" daure fuska tayi saikuma tace "muma
haka muka jinshi kawtsam" "to Allah ya sanya alheri yabasu zaman lpy" shiru tayi
bata amsaba Abba daduk yake lurada ita yace "Ameen" sanan dakin yay shiru, hannu
Abba yatura cikin aljihun rigan jallabiyan shi yaciro envelope sanan yabama Alhaji
Bashir yace "gashi nan" da sauri Alhaji Bashir ya karba yana kokarin bude envelope
din yace "na menene Alhaji" ahankali Abba yace "karanta kaji" ciro paper yayi ya
warware yana gyara zaman gilashin idanunshi yace "ni Abdullahi Sambo Rikadawa na
saki Maryam Adam saki biyu!" atare kowa na dakin ya kalli Abba harda yaran da Mummy
datake kallonshi babuko kyafta ido, cikin dan tashin hankali Alhaji Bashir yaciro
hulan kanshi yana fifita kanshi yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Alhaji,
Alhaji menene nagama karantawa yanzun nan, after 27th yrs of marriage shine zaka
rabu da matarka, meya faru haka? Meya faru that is so serious like this that dayasa
ka saki Maryam har saki biyu eh? Ga three beautiful daughters dasuka girma a
tsakanin ku, wah happen?" shiru Abba yayi yana kallon yaranshi mata yanda sukai
zuru zuru kowacce hawaye fal idanunta kodan darajansu bazai taba tonama Mummy asiri
ba, kodan sabida su gwara kawai suyi rabuwan arziki" ahankali Abba yace "Alhaji
Bashir wasu abubuwan babu amfanin fadinsu, sanan wasu abubuwan gwara an barsu
batare da an fadiba ko dan darajan wayan nan yaran" yanuna su Siddiqa sanan yace
"na sake ta saki biyu amma dalilina nayin hakan bazan iya fadamaka ba Alhaji
Bashir, kayakuri" Abba yay maganan ahankali gwanin ban tausayi, wani irin murmushi
Mummy tayi dama tunanin yanda zata bullomai ya saketa take dan bataso yasami heart
attack a hannunta kodan darajan shi na uban y'ay'anta, kuma tasan yanda su Siddiqa
keson ubansu, mikewa tayi tsaye tana kakkabe riganta ta kalli Yayanta tace "Yaya
bari nadan hado kayana nadauko mayafi mutafi" ta juya zatai corridor wani irin
mahaukacin tsawa Alhaji Bashir yadaka mata. "Maryam, come back here, mijinki ya
sakeki you didn't show at atom of remorse ko damuwa, kin tashi u dare tell me bari
kije ki dauko mayafi eh Maryam" cikin fushi Mummy ta kalli Abba dake kallonta tace
"I guess Sameer da yarka sun fadi maka komi, eh nine nakoyama Rahima shaye shayen,
sanan kaga ranan daka kirani kace naje NDLEA nadauko Rahima ranan nafara ganin
Sameer, aranan kuma Allah ya jarabce ni da mugun sonshi, tuntuni nake tunani ta
yanda zan bullomaka danka sakeni nasamu na auri Sameer amman narasa banso heart
attack yakamaka ka mutu, kai bakaga Sameer ba dan Allah, handsome, black young
looking young man, ba irinka ba 5min man....." shiru tayi ganin Abba yafara tari
yana dukan kirjinshi da sauri daga yaran har Alhaji Bashir sukai kanshi, rikeshi
Alhaji Bashir yayi yace "bani ruwa Siddiqa" da gudu Siddiqa tai dinning takawo ruwa
Alhaji ya karba yabude yabama Abba yadan kurba sanan tarin yalafa, Mummy tawani
ballamai harara tai ciki tace "now am free like a bird, babu any guilt akaina,
yanzu ne zan BI ABINDA ZUCIYA KESO, now is the right time to CHASE MY HEART
CRAVINGS babu aure akaina babu nauyin kowa akaina, Alhamdulillah" tafada dakinta ta
shiga hahhada kayayyakin ta a akwati saida tagama tsaf sanan tajawo akwatin falo
takalli Alhaji Bashir tace "Ya tashi mutafi" sanan takalli su Siddiqa dake kallonta
Zeena takasa hakuri tafashe da kuka, murmushin yake tayi tace "yara bazaku taba
gane wani hali nake ciki ba sai randa Allah yadaura muku son wani akanku, duk yanda
zanbi sainabi na mayar da Sameer nawa cus ina sonshi sosai, yafi babanku komi, yafi
babunku....... " Luba ne ta tashi cikin fushi tace "karki kara hada Sameer da Abban
mu Mummy, karki kara" tashi Siddiqa tayi tace "today is the last day zaki kira wani
banza chan kice yafi ubanmu Mummy, our father is our number one hero" Zeenatu ko
daduk tafisu zuciya tace "Mummy I hate you wlh sosai, I wish keba mahaifiyata bace"
Alhaji Bashir dake tareda Abba yace "kina ganin yanda abinda kikace yake neman yasa
kirasa yayanki da girman ki da hankalin ki zakisa yaranki su tsaneki?" tabe baki
Mummy tayi tace "inhar kan Sameer ne ba y'ay'a ko kaine banki narasa ka ba, Sameer
yafimin kowa aduniyan nan sonshi daga Allah ne, ina masifan sonshi ko Allah yasani"
sosai duka yaran suka fashe da kuka sosai, kuka bana wasaba kallonsu tayi tace "iya
gaskiyata kenan bazanyi karya danku soniba, inason Sameer so dazaku taba iya ganewa
ba, and I don't mind sacrificing jinina inhar zan sami Sameer nabarku lpy, Abban
kuma" tai maganan tana kallon Abba dayau ne yake ganin asalin true colors din Mummy
tace "I hope zaka iya rayuwa babuni, Allah yabaka zuciyan jure wanan heart break
din, koba komai banso yarana su rasa ubansu dasuke mugun so abun zai musu yawa koba
hakaba, so be strong kaji, nagode da sakina dakayi, sai anjiman ku".
[11/07, 17:34] Aishat Muhammad: 83
Ficewa tayi daga gidan abinta, kasa dagakai Alhaji Bashir yayi ya kalli Abba ko
yaran, saiyaji inama bai hada jini da Mummy ba, kasa magana yayi yana sauraron
yanda su Siddiqa ke kukan tsuma rai sosai, yakai almost 10min azaune sanan ya kalli
Abba da idanunshi sukai ja sosai yace "Alhaji bari nabita danna lura Maryam bata
cikin hayyacinta ina zuwa" yawuce yafita cikeda bala'in kunya batare daya jira
amsan Abba ba, yanda yaran ke kuka yasa Abba yaji they're really breaking his
heart, ya daure amma suna neman susa yakasa daurewa tashi yayi daga kan kujeran yay
wajen Luba data kifekai ajikin kujera last born din Mummy, ahankali yasa hannu
yadagota cikin wata low voice yace "zonan Lubabatu, come here" yadagota tareda zama
kan carpet, tasowa Luba tayi ahankali cikin wani irin kuka tana kallon Abba tace
"Abba sabida Ya Sameer Mummy tarabu damuko, Abba zuciya na zafi sosai, Mummy is a
terrible woman Ab......" hannu Abba yadaura kan bakinta yakai dayan hannun yana
goge fuskarta yace "stop using harsh words akan mahaifiyar ki, is okay stop crying,
ya isa, ya isa kinji" fadawa tayi jikin Abba ta daura kanta kan kirjin Abba,
dagokai Abba yayi ya kalli Zeena dake kusada Siddiqa duk suna kuka suma, hannu Abba
yasa yakirasu alamun suzo duk zuwa sukayi suka hadu ajikin Abba kuka kuka kuka suke
kaman wani gidan makoki, da kyar Abba yasamu sukayi shiru, murmushi yamusu yace
"kunsan mene, kutashi kuje kuyo wanka kuzo mufita" dudda basuda raayin fita haka
Abba ya tursasa su suka fice just to take the issue out of their heart.
Karfe 9. Ummi ta shigo asibitin tareda Mu'az dake rikeda wasu manyan basket guda
biyu na kulolin abinci ke ciki suka shiga, dakin Rahima suka farayi, ahankali
tabude kofar dakin ta shiga tana kallon Rahima dake bacci ga karin ruwa ana mata,
ahankali tasa hannu ta shafa kumatun ta sanan ta taba saman goshinta dataji zafi
sosai, cikeda damuwa ta dagokai ta kalli Mu'az tace "ijiye basket daya anan,
saikakai daya dakin Sameer, muje" tai maganan tana tashi ijiyewa Mu'az yayi yawuce
yafita Ummi biyeda shi har zuwa dakin Sameer, sallama tayi tareda bude kofan Sameer
na kwance kan gado dudda ba bacci yakeba ya lumshe ido kaman bacci yike, Noor kuma
na zaune yana danna waya, jin anbude kofa yasa Noor yajuyo da sauri ganin Ummi
yasa yatashi da sauri yace "ina kwana Ummi" karasowa tayi cikin dakin tana
kallonshi tace "sannu Noor kaima dukkabi kafada, zokai break saika tafi gida kaje
kai wanka ka shirya katafi aiki inka tashi da yamma saikazo" tai maganan tana zama
kan kujera tana kallon Sameer shikuma Mu'az ya ijiye kulan abinci yana gaida Ya
Noor yana kallon Ya Sameer.
Matsawa Ummi tayi jikin gadon sosai tana kallon fuskan Sameer din, hannunta takai
ta daura kan goshin shi jin akwai zafi har lokacin saidai ba kaman na jiyaba yasa
ahankali takira sunanshi. "Sameer" wani irin nauyin Ummi yakeji nauyin dabai taba
jin yana mata irinshi ba tunda yafara girma saisama yaki nuna kaman idanunshi biyu,
juyowa Ummi tayi ta kalli Noor tace "yaci wani abune Noor? Mai likita yace?" "dazu
ya shigo yamai allura gida biyu, Ya Sameer yacemai wai ya sallameshi, although Dr
yace sai yaji sauki sosai zai sallamai" juyowa Ummi tayi ta kallai tace "ni narasa
me hadin Sameer da bayason asibiti, naga Dr dazai sallameka a asibitin nan batare
dakaji sauki ba, Allah kawo Dr ai ina nan har dare" sanan ta kalli Noor tace
"kaikuma nace kazauna kai break ko ga abinci nan" ta kalli Mu'az dahar lokacin
Sameer yake kallo tace "lafiya kakemai irin kallon nan kaman kanamai kallon karshe,
bani flask dinan nahadamai shayin dana yomai nasan yanason shayin" dukawa Mu'az
yayi yadauki flask din yabama Ummi ta shiga hadamai shayin dayasha kayan kamshi
sosai sanan tadau cup din ta ijiye kan drawer dakin kota gane idanunshi biyu yadai
kasa kallonta ne sabida aika aikan dayayi oho hakan yasa kawai ta mike daga kan
kujeran ta kalli Noor dake cin chips da soyayyan kwai tace "bari nakoma wajen
Rahima, yi maza kawuce katafi aiki, Mu'az ka zauna da yayanka inya tashi kabashi
shayin dana hadamai yasha" tawuce tafita, tsaf Noor ya cinye abincin shi sanan ya
tashi kan Mu'az ya shafa yace "lemme go kiddo, take care of him" yanunamai Sameer
sanan yaciro atm card dinshi yabashi yace "idan ana bukatan anything use it, order
than that ka kashemin ko biyar saika biya dan baka riga kasan zafin nema ba" kaman
Mu'az zaiyi kuka yace "Ya Noor please mana kagafa daman nafada maka laptop dina ya
lalace kaki bani kudin gyara kaga saina cire" hararan shi Noor yayi yace "katabamin
ko biyar kaga aidai zanga receipt din anything daka sayako you will see, katuna pin
dina ko" gyadamai kai Mu'az yayi yana batarai sosai, dan dariya Noor yayi yace
"okay to kacire just 1k nabaka" da sauri yace "wlh banson 1k" dariya Noor yayi yace
"rainuwa ko toka lashe nidai natafi" saida yaga yafita daga dakin sanan ya hararai
kafin yajuya zaije ya zauna, Sameer yagani idanunshi biyu da sukadan kode irin na
marasa lafiya, da sauri yay wajen Sameer din kaman zaiyi kuka yace "Ya Sameer
katashi?" gyadamai kai Sameer yayi yana kokarin tashi ya zauna taimakamai Mu'az
yayi yazauna sanan yamika hannu ya dauki cup din shayin yakai bakinshi ahankali
tareda lumshe ido, he just wish zai iya ganin Rahima and hug her right now, ajiyan
zuciya yasauke yarasa me kemai dadi, bude kofa akayi hakan yasa yadago kai Ummi ce
ta shigo tareda Dr Sameer, hada ido sukayi da Ummi da sauri ya sudda kanshi kasa,
cikeda tsokana Dr yace "Lieutenant, andan girgiza file din sojoji fa, Good morning
yajikin" yay maganan yana makala stethoscope a kunnenshi dan yaduba Sameer, sanan
yashiga dubashi yace "how are you feeling this morning? Any pain any complain?"
girgiza mai kai Sameer yayi ahankali yace "no, I am fine" murmushi Dr yayi yace
"good" Ummi na tsaye a gefen Dr tana kallon yanda Dr ke duba Sameer, saida yagama
dubashi sanan yace "inka gama shan shayin kasha magangunan ka zaka karajin karfi
sosai" gyadamai kai Sameer yayi ahankali yace "please discharge me I will continue
the treatment at home" da sauri Ummi tace "a'a Dr karka sallamai saiya warke tass,
Sameer baicika ciwo ba yayi kuma wlh yana girgiza shi" dan murmushi Dr yayi yace
"Hajiya amai hakuri a sallamai soja ne fa, and is natural duk sojoji basa son zaman
asibiti, kunya suke wai soja dasu agansu kwance gadon asibiti kaman wasu mata" dan
murmushi Ummi tayi tana kallon Sameer din da kanshi ke kasa, murmushi tasake yi
tace "to shikenan likita duk yanda kayi, nidai bari nakoma wajen y'ata" tai hanyar
kofa da sauri Dr yace "yauwa Hajiya I've been wanting to ask, Dr Bisola tasameni
akan other patient din dakuka kawo mana kan she was raped haryakai ga stitches and
you people are not ready to take the case up akama shi" yay maganan kai tsaye dan
duk basusan Sameer yay aureba, dan murmushin yake Ummi tayi tace "ai Soja nakan
case din already amma kama mutumin" tai maganan tana kallon Sameer da kanshi ke
kasa, cikeda jin dadi Dr yace "good job Lieutenant Sameer is high time munfara kawo
all this rapist to justice, haba that girl is too small and pain din yamata yawa
wicked rape aka mata ko a rape din" juyawa Ummi tayi tafita ahankali ta maido kofan
tarufe shikuma Mu'az dama tuntuni kanshi ke kasa, Dr kuma yagama yan firarraki6da
Sameer da baya wani bashi amsan kirki yawuce yafita da sharadin zai dawo karfe daya
in temperature shi ya sauka zai sallamai.
Lumshe ido yayi ya kwanta yarasa me kemai dadi ahaka har azahar Dr yazo ya sallamai
dudda bawani jin sauki yayiba kawai baison zama a asibitin ne, fitowa sukayi Mu'az
yatafi sayo magungunan da Dr yakara rubutamai, ahankali yake tafiya yay hanyar
dakin da Rahima ke ciki to kofar yafara tsayawa ya leka tana zaune babu dan kwali
akanta sai rigan asibiti tana kuka sosai hannunta rikeda cup na yogurt mai sanyi da
Ummi tabata, tai wani irin shegen kyau da haske, idanunta sun kumbura sosai kaman
zaka taba hanunnka ya lotsa ciki, gashin kanta na shining an mata kalaba guda daya
da duka gashin saitai kaman wata yar bararojiya me kikazo saya garin magani, tana
zaune amma ta wawware kafa kaman anmata kaciya, bazaima iya defining abinda yakeji
ba but he feels kaman yaje yay hugging nata tight and be listening to yanda take
kuna ahankali hartai bacci ahaka, she can't believe he caused all this pain for
her.
Ahankali yadaura hannunshi kan door handle ya murza tareda bude kofan ahankali ta
shiga, karan kofan dasukaji yasa duk suka dagokai, hada ido Rahima tayi da Sameer.
Wani irin kwalla razananan ihu tayi daseda yatsorata Ummi dake zaune awajen kan
plastic chair, tawani irin yarda cup din youghrt dinda takesha tana zabura tana
kokarin mikewa tana kuka sosai tana kallon kofa tana mika hannunta tana kokarin
jawo pillow ta rufe fuskarta dan wani irin mugun tsoron Sameer taji Allah yasaukar
mata kaman taga ogan doddanni dan gani take kamar zekara yimata abinda yamata ne,
yanda tafashe da kuka tana jan duwaiwai baya tana kokarin tashi takasa tana kallon
Sameer din yasa Ummi tasaki salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un" tai juyo
ganin Sameer ne tsaye ajikin kofa yasa taji ranta yabaci, cikin fushi tace "what
are you doing here? Please kafita, you know you caused all this so kafita akwai
tsoro tattare da yarinyar nan karkasa jininta ya buga" Ummi tafadimai babu alamun
wasa, ahankali yajuya tareda bude kofan yafita yarufo musu kofa, hakan yasa Ummi
tai wajen Rahima dake kuka sosai tace "ya isa Rahima, dena kuka nakada shi, kinga
kin zubar da yogurt dinki, na zuba miki wani?" girgixa mata kai Rahima tayi tana
kuka sosai hakan yasa Ummi tace "to shikenan stop crying share hawayen ki" hannu
tasa tana share hawayen sanan ta kalli Ummi ahankali tace "bazai dawoba?" gyadamata
kai Ummi tayi tace "I promise bazai dawoba" ajiyan zuciya ta sauke cikin yar
siriruwan murya tace "tsoronshi nikeji sosai" wani irin mugun tausayinta Ummi taji
tace "ina zuwa" juyawa tayi tafita daga dakin Sameer tagani tsaye tareda Mu'az tace
"har an sallame ku dinne?" gyadamata kai Sameer kawai yayi batare dayabari sun hada
idoba Ummi tace "to shikenan, Mu'az gida zaka wuce dashi saisun warke tatas sanan
zasu koma gidansu" ahankali yace "to Ummi" sanan tawuce takoma ciki sukuma suka
wuce suka tafi gida.
[11/07, 17:35] Aishat Muhammad: 84
Bayan sati daya!
Rahima tasami sauki sosai dan wani irin kyakkyawan kulawa akeyi da ita a asibitin
nan bana wasaba, kullum Ummi na wurin ta tun safe har dare, dafarko tazaci Ummi bad
person ne amma saitaga Ummi na bala'in jida ita tana sonta, sanan kullum saita bata
wasu magunguna a yogurt tasha, dinkin da aka mata yaji sauki sosai dan yanzu in
zatai pupu da fitsari batajin zafi, batawani jin zafi a wurin ta warke fess da
magunguna ake bata da zaisa ta hade taciki fast sanan tai healing fast, Abba yazo
yadubata kusan sau uku harda su Siddiqa tazo dudda bai fadamata komi kan rabuwanshi
da Mummy ba, duk zuwan dazaiyi baitaba haduwa da Ummi ba, Sameer sau biyu kacal
yazo yadubata daganan bai karaba dan bala'in kunya take bashi agaban kannenshi ko
gaban waye ihu zata kurma inta ganshi kaman taga dodo tun yan uwansu banda Noor
basu ganeba har sunzo sun gane hakan yasa baisake lekawa asibitin ba dudda ranshi
na mugun yimai kwadayin ganinta, ga tunaninta dayake kaman bashiba, hakanan yanzu
baya wani iya baccin dare da kyau, dazaran yarufe ido sift jikinta zai dingaji
anashi yafadima Dr Ayan yacemai wai soyayya mai karfi yake mata.
Yau Sunday tun safe aka sallamesu, sosai taji dadin sallaman da aka musu danta gaji
da asibitin nan tagaji da komi ba, babu abinda ke mata dadi, shiryawa tayi cikin
wata sabuwar plain doguwan rigan atampa yellow and black da Ummi ta dinka mata,
sakawa tayi ko Ummi saida ta kalleta sabida yanda kayan suka mata shegen kyau bana
wasaba tayi haske sosai aciki, tana kokarin saka Black hijab din da Ummi tabata sai
kallon kalaba kwara daya na kanta take, ahankali Ummi tace "daga nan mu wuce saloon
amiki kitso Rahima, kanan na bukatan gyara, muje?" gyadama Ummi kai tayi dan itama
tulin gashin ya isheta wlh, batawani iya maganan kirki da Ummi hakanan taji kawai
tanajin nauyin matan sosai, knocking Mu'az yayi ya shigo Ummi tace "harka kai kayan
mota" gyadama Ummi kai yayi yana murmushi yace "eh Ummi" "madalla to kumu tafi,
saloon zaka fara kaimu ama Antyku kitso" gyadamata kai kawai yayi, Ummi ta kalli
Rahima tace "to tashi mutafi" sauka tayi dagakan gadon ahankali ta zura flat vine
slippers din da Ummi tabata sanan Ummi takama hannunta tarike tabude musu kofa suka
fita, ahankali take tafiya tanadan lum lumshe ido rabonta da waje harta manta,
reception suka fito wata Nurse dake zaune a gun ta kalli Rahima tace "cry cry
patient bye bye" hararanta Rahima tayi dan dukansu haka suke kiranta, dariya Ummi
tayi ba tace komiba, nurse din tace "ni kike harara zaki kara dawowa allura mai
zafi" dariya Ummi tayi tace "nurse Halima ki kiyayan mini yarinya fa" dariya Nurse
din tayi tace "Mummy sai kundawo Allah ya kiyaye" Ameen Ummi ta amsa suka wuce suka
fita, mota suka shiga Mu'az ya ijiyesu awani hadadden saloon, kanta Ummi tasa aka
wanke sanan tasa aka mata kitso shuku na 7 7 yan kananu masu bala'in kyau sanan
Ummi tasa aka mata lalle baki da ja, saitai kaman wata Amarya,