Showing 21001 words to 24000 words out of 220972 words
kada ki sake wannan KUSKUREN.!"
Tace "Rafeek wollahi ko ka yarda ko kada ka yarda ni banyi KUSKURE ba,kaine dai kake son yin KUSKURE ta hanyar nunawa duniya d'anka shege ne,,wollahi thumma billahi cikin nan ba shi da uban daya wuce ka kaf duniyar nan,ni na tabbatar cikin nan ubangiji ya nufemu da samun shi,amma kaine silar samar da shi,ina baka shawara kayi duk iya binciken da kake jin za ka iya yi,na tabbatar kai da kanka sai ka yarda bashi da uban daya wuce kai"
"Kada ki sake danganta cikinki da ni."
A zafafe kamar yadda yayi tace "wollahi sai na fad'a naka ne"
Girgiza kai yayi kamar tana gabansa yace "ta yaya ya zama nawa.!? Daga yin abu sau d'aya shi ne sai ya zama nawa.!? Da Allah malama kada ki b'atawa kanki lokaci,,ni Rafeek kike son lik'awa cikin wani ko.!? To wallahil'aziiym bazan karb'a ba,kuma har abadan duniya bana karb'arsa,can ki nema masa uban daya dace amma ni nafi k'arfin kiyi min sharri,,idan kina iyawa kici gaba da rainonsa har ranar zuwansa duniya,and ina fatan idan ya zo wata rana ko da zai tambaye ki maifinsa kiyi k'ok'arin sanar da shi gaskiya kada ki b'oye,cos duk ranar daya san gaskiya zai tsaneki a matsayinki na wacce ta kawo shi duniya,zaiji haushin kin b'oye masa gaskiya,bayan zunubin samar da shi ta mummunar hanya,zai tsaneki bayan ya gano kina sane kika yi sanadin zuwansa ta k'azantacciyar hanya,,kafin duk wannan lokacin ya zo ina so kiyi tunani,sannan kiyi kokarin tara hujjojin da zaki fuskanci d'anki da su,ta hanyar bashi gamsassun amsoshin da zasu wanke laifinki a gare shi,,kai tsaye ba sai kin yi masa k'arya ba a duk lokacin da ya b'ukaci jin asalinsa ina so kice masa shi shege ne bashi da baba..!"
"RAFEEK.!" Ta kirashi a zafafe,dariya yayi yace "mene ne.!? Wai kinji haushi.?''
"Kada ka sake sheganta d'anka,ka tuna kai kayi silar samuwarsa"
"Da Allah dakata Malama,ta ina na samar da shi ne.!?"
"Rafeek.! Kada ka yanke hukunci kan abunda baka da ilimi akansa,d'anka ne na sunnah."
"Ni ba d'ana bane,ki daina danganta ni da shi,,ke kanki kin san ba ni ne mahaifinsa ba.!"
"RAFEEK dank'a ne.!"
"Hauwa! Kada ki sake cewa nawa ne.!"
"Sai na fad'a dank'a.!"
Dariya yayi mai ciwo yace "Kina son lik'a min d'an da bashi da uba ko.!? Saboda kin maida ni mahaukaci na karb'i d'an da ban san *ASALINSA* ba.!?,k'arya ne wollahi bazan tab'a karb'a ba"
"Shi kenan Rafeek, idan har baka sonsa ni ina son abuna.."
"Dama dole ne ki so shi,tunda a yanzun ke kanki baki idan za'a tambaye ki ubansa baki san takaimaman wane ne zaki ce shi ne mahaifinsa ba,kinga kenan kece uwarsa kuma kece ubansa,dole ya zame miki ki so shi."
Sosai kalmar tayi mata muni da ciwo ta runtse idanunta jin kirjinta yayi mata nauyi tace "shi kenan Rafeek na gode,,amma ina so ka san wani abu guda"
Yace "fad'i kafin lokaci ya k'ure miki"
Daurewa tayi duk da ciwon da take ji yana taso mata,a hankali ta dafe k'asan mararta muryarta da rauni tace "Ina so ko da zuwa gaba,a lokacin daka gane gaskiya,ka tabbatar kana da alak'a da d'ana,,ka yi min alk'awarin baza ka tab'a kusantar inda muke ba,sannan ba za ka kira Yarona naka ba.!"
Dariya yayi yace "wannan shi yafi komai sauk'i"
"Na gode" tace muryarta a raunane tana fad'a ta katse wayar had'e jefar da ita,mik'ewa ta sake yi zata fita sakamakon kanta da taji ya tsananta ciwo ga k'irjinta dake mata wani irin zafi²,baya ga ciwon marar daya taso mata,tana son neman drugs da zai rage mata rad'ad'in ciwukan da suka had'e mata kai,still kuma har lokacin hawaye bai samu damar sauka ba bare ya jik'a fuskarta ko zata samu sassaucin nauyin da take ji a k'irjinta,idanunta sunyi wani irin soyewa baka ganin komai cikinsu sai zallar damuwa da tsananin ciwo,ta kama hanya zata fita a d'akin a daddafe,shi kansa d'akin ji take a yanzun ta fara kyamar zama a cikinsa,saurin rik'e kanta tayi sakamakon ganin komai yana rabewa yana komawa biyu,wani har fiye da haka,kafin tayi aune gaba d'aya d'akin ya hau jujjuyawa da ita,laluben hanya ta fara yi tana son komawa ta zauna amma abun ya gagara,dole ta tsaya guri guda tana layi kamar wacce tasha kayan maye ta bugu,kanta ta sake matsewa ta k'udundune guri d'aya,ji tayi duniyar tayi mata zafi komai ya fice mata akai,wani irin tak'ark'arewa tayi ta rik'e kanta dake shirin tarwatsewa kafin a hankali ta sulale tayi k'asa,bisa tsautsayi ta fad'o a saman k'aton cikinta a kife,tsananin azabar data ratsata yasa ta fasa gigitacciyar k'ara mai firgitarwa then ta daina motsawa jini ya fara biyo jikin kafafunta yana yiwa kansa hanya,,ihunta ya janyo hankalin maidservant d'in gidan a gurguje suka nufo d'akin,ganin halin da take ciki da jinin dake bin jikinta hankalinsu a tashe suka sanar da Hajiya halin da ake ciki,kafin wucewar wasu mintuna aka wuce da ita wani private hospital da cikin gaggawa,suna zuwa aka karb'eta,likitoci kusan biyar suka rufu akanta suna ta k'ok'arin ceto ranta,da kyar aka samu jinin dake zuba ya tsaya bayan dogon lokaci,but cike da rashin hope tsakanin rayuwa da mutuwa,Dr Fahad da ya jagoranci aikin ya nemi ganin wad'anda suka kawota da gaggawa,Hajiya hankalinta duk baya tare da ita tabi Dr Fahad dan jin abunda yake faruwa,a office d'insa ta tarar da shi tsaye ya kasa zama bcos aikin gaggawa ake son yi mata a cire cikin,tana shigowa Dr Fahad ya nuna mata guri ta zauna,a gaggauce yana kallonta yace
"Hajiya ya ya kuke ne da mara lafiyar da kuka kawo.?"
Tace "Y'ata ce" Jinjina kai yayi yace "Mijinta fa..!?" Hajiya tace "Dr zaka iya yi min duk bayanin daya dace ba sai lallai yana nan ba,shi d'in d'ana ne,a halin da ake ciki kuma baya k'asar" jinjina kai ya sake yi,then ya shiga koro mata jawabin idan har sun damu suna son rayuwar y'ar su da abunda ke cikinta lallai sai dai ayi mata aiki yanzun da gaggawa a cire shi,Hajiya bata tsaya jin k'arshen maganar ba saboda tashin hankali tace "Dr idan har zasu rayu ayi aikin na amince,ayi mata a rabata da shi" gyad'a mata kai Dr Fahad yayi sannan ya mik'a mata takardun tayi signing,a gaggauce bayan ta gama signing ya karb'a ya ajiye sanma ya fita ya bar ta a office d'in ya wuce theatre room,Hajiya tana k'arasowa bakin room d'in dawowarta daga office d'in Dr Fahad taga an wuce da Hauwa kamar matacciya,Maimunatu da ma'aikatan gidan da suka taho tare suna zaune jigum a wajen,ganin lokaci yana tafiya yasa Maimunatu bayan ta goge hawaye ta juya ta kalli maidservant d'insu tace "ina ganin da kunje gida kafin mu san abunda ake ciki,mu zamu zauna a nan muga yadda hali zai yi" da girmamawa suka amsa,mata ne su biyu y'an manya sai driver'nsu suka yi musu sallama da addu'ar neman sauk'i sannan suka d'auki hanyar komawa gida,hospital ya rage daga Hajiya sai Maimunatu dake ta addu'ar Allah ya tashi kafad'un Hauwa,suna ta zaune a ward d'in a bakin theatre room sun zuba idanunsu akan entrance jira suke suga an fito da ita,kusan awanni biyu da mintuna suka sake zuwa suka wuce har lokacin ba'a fito da ita ba,Hajiya ta kasa hak'uri ta mik'e tana zarya hankalinta a tashe,fitowar Dr Fahad yana cire mask daga bakinsa yana matsowa inda Hajiya take yasa taji hankalinta ya sake tashi,ajiyar zuciya yayi yace "Alhamdulillah! Hajiya y'arki da jikanki suna lafiya,but due to condition na yadda haihuwar yazo mata it seems nak'udan ma na dole ne akasa tayi,kwanakin EDD d'inta sun nuna sai first of next month and yanzun muna farkon month,baby'n ku ya sha wahala sosai,ya zo jikinsa babu wadataccen k'wari ina ganin kamar zamu rik'e su na wani lokaci duk da itama a halin da ake ciki a yanzun zata iya kaiwa kwanaki uku bata tashi ba,but idan an shirya su za'a wuce da shi baby unit cos yana bukatar asa shi cikin na'urar d'umama jarirai (incubator)."
"Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat..!"
Fuskar Hajiya k'unshe da farin ciki ta d'aga hannu sama tana hawaye tana jera addu'o'i,kallon Dr Fahad tayi idanunta suna sake kawo hawaye tace "Na gode Dr da wannan albishir d'in,,yanzun kam na samu nutsuwa da jin wannan labarin.."
Murmushi Dr Fahad yayi mata sannan yayi musu sallama ya wuce bayan ya sake fad'a musu za'a fito da ita yanzun babu jimawa,Maimunatu tana murmushi ta kira Abba'nsu ta fad'a masa zancen haihuwar,kafin wani lokaci ya k'araso hospital d'in shima jin abunda ya faru,yaji mamaki lokacin da yaga Hauwa kwance kamar gawa babu inda yake motsawa a jikinta,yana kallon Hajiya yace "Hajiya anya yarinyar nan da rai a jikinta kuwa.!?" Tayi murmushin k'arfin hali tace "Tana numfashi mana,ka kalleta sosai zaka gani.."
K'ura mata idanu Alhaji zakar yayi a hankali yaga cikinta yana d'agawa kad'an²,jaririn da bai gani ba nan ma ya tambaya a tunaninsa ko ya zo babu rai ne tunda yasan duk wacce ta haihu ana ganin yaronta a kusa da ita,Hajiya tayi masa bayanin yadda duk suka yi da Dr Fahad,a nan ta sanar masa su kansu basu samu damar d'aukan yaron ba an nuna musu shi lokacin da za'a wuce da shi baby unit,ya tausaya musu sosai,yayi musu addu'ar neman sauk'i,ya jima sosai shima a hospital d'in kafin suka wuce gida da Maimunatu ya rage sai Hajiya kawai a hospital.
Tsananin ciwo da wahalar da hauwa tasha a wannan lokacin fad'arsa zai zama kamar b'ata lokaci,to the extent lamarin ya zarta duk tunanin mai tunani,a hakan da take tun bayan da aka fito da ita daga theatre bata sake sanin inda kanta yake ba har aka cinye kwanaki uku tana kwance bata san ina yake mata ciwo ba,tana halin rayuwa ne ko mutuwa.? Or even ma ace tasan ta haihu duk bata san abunda yake faruwa ba,,Baby kuwa idan ya farka yayi kuka a cikin kwanakin,sai dai ayi amfani da electric breast pumper,cos hakan kad'ai shi ne solution da yaron zai samu cikakkiyar kulawar daya kamata ya samu ta wajen shayar da shi nonon mahaifiya,wanda shi ne sinadarin da zai k'ara masa kuzari da lafiya tunda yazo a wahale,,idan ya farka yayi kuka Hajiya ke zuwa ta rarrasheshi cikin nuna so da tausayawa ga wannan uwa da d'a da har lokacin basu ga juna ba,da yake a kullum tunda aka mata aikin tana under medication bayan alluran da ta sha kafin aikin da wanda akayi mata bayan anyi aikin,har a rana ta hud'u bata farko ba and babu wanda ya iya ganin kwayar idanunta,jikinta kam zuwa lokacin Alhamdulillah ya fara sauk'i duk da Hajiya ta damu sosai da rashin tashinta,a cewarta kwanaki uku Dr yace mata,tun tana tambayar Dr Fahad anya lafiya har yanzun bata farko ba,yana fad'a mata tayi hak'uri komai lafiya bai san dai a ina aka samo matsalar data hanata farkowar ba,but daga yanzun zuwa ko wane lokaci shi dai yasan zasu iya sa rai da tashinta,Hajiya dai taji zancen Dr Fahad ne amma k'asan zuciyarta damuwa ce sosai.
Misalin karfe 3 da y'an mintuna na dare Hajiya tana tsaye saman abun sallah tana kai kukanta ga Ubangiji akan al'amuransu ta farka,idanunta suka fara motsawa a hankali kafin ta fara k'ok'arin bud'e su da kyar,yadda jikinta yake a d'aure bata fasa juya kanta tana kalle² ba,kud da babu yalwataccen haske yanayin k'amshin da d'akin ke fitarwa ya bata tabbacin ba a gida suke ba,tunanin abunda ya kawo su nan d'in ta fara,bayan ta gama y'an tunanukanta bata gano komai ba ta tab'e baki a hankali tana k'ok'arin tashi ta zauna,zafin da taji a gefen cikinta yasa ta sakin marayan ihu da ya kaiwa Hajiya sak'on ta farka,,muryarta dishi² take magana tana kira taji ko akwai mutum kusa da ita ya taimaka mata,Hajiya dake zaman tahiya da sauri ta k'arasa ta sallame sallah,ko addu'ah bata jira tayi ba ta taso da sauri tayi gurinta tana fad'in
"Alhamdulillah.! Hauwa'u kin farka.!? Sannu kinji Allah yayi miki albarka,ya kara muku lafiya.!" Juya kanta tayi tana kallon shade d'in Hajiya dake tsaye kusa da ita tace
"Hajiya zanje toilet.."
Da sauri Hajiya ta amsa mata,ta taimaka mata suka je tayi fitsari ta wanke bakinta suka dawo,saman gadon ta sake zama bayanta jingine jikin pillow Hajiya ta fita ta dawo da nurse ta dubata ta fita,sannan ta had'a mata tea ta bata,tana gama sha muryarta har lokacin bata fita sosai tace
"Hajiya me muke yi a hospital.!? Mene ne ya same ni a ciki na naga anyi min d'inki.!?"
Hajiya tace "haihuwa kika yi,amma aiki suka yi miki." Idonta ta d'an bud'e sosai ba kamar da farko ba data tashi da suke a shanye tana kalle² a d'akin,ganin babu jaririnta da aka ce an ciro mata a hankali ta sauke idanunta hawaye suna gangarowa cikin muryar kuka tace
"Hajiya ya mutu ko.!?" Ido Hajiya ta zaro tana kallonta tace "waye ya fad'a miki haka.!?" Tace "Hajiya ai to ban ganshi ba.!"
D'an murmushi Hajiya tayi tana dafa hannunta tace "kada ki damu daughter yaron ki yana nan a raye,an sashi dai a na'ura ne saboda yazo da rashin kuzari,an jima kad'an idan Allah ya kaimu zaki je kiga abunki kinji.!? Ki kwantar da hankali."
Sai lokacin taji wani irin nutsuwa ya saukar mata duk da nauyin da har lokacin take ji a k'irjinta a hankali ta zame jikinta ta amsa ta koma ta kwanta,bayan an fito a masjeed Hajiya ta kira wata nurse d'in ta sake zuwa ta duba jikin nata kafin Dr yazo,da safe Dr Fahad ya shigo duba jikin cos tun tun kafin ya k'araso hospital aka sanar da shi ta farka,yana zuwa ko zama baiyi ba a office ya shiga duba jikin,komai nata yana lafiya sai ciwon da ba'a rasa ba,hajiya ta tambaye shi ko za'a iya bata abinci kuma cos tunda ta farka tea kad'ai ne a cikinta,Dr Fahad yace "Ehh!" Za'a iya bata but ya zama mai ruwa²,sai kuma fruits da za'a k'ara mata da su,saboda wajen yin bayan gida kada ta wahala su samu matsala a aikin nata,godiya Hajiya tayi masa sosai,Dr Fahad ya fita ya barsu tana lallab'a ta,,y'an gidanmu duk da bama zaman dad'i sun je duba Hauwa da yake tana cikin halin jinya sai bata sani ba,ni kuwa tunda aka yi mata aikin naso na zauna nayi jinyarta saboda duk duniya nice tata da ya kamata na zauna da ita bayan mahaifiyar mu,itan bata raye sai ni,ni d'in kuma dana nuna zan zauna da ita Hajiya tace kada na damu naje na kula da gida na ita zata zauna da Hauwa har zuwa lokacin da za'a basu sallama,a zahirin gaskiya mahaifan Rafeek mutanen kirki ne,sun yiwa Hauwa rik'on amana,ko dai ace su suka kawota duniya iya gatan da zasu bata kenan,bare ba su suka haifeta ba matsayin suruka kawai take a gurinsu,ranar da Hauwa ta farka ranar ne farkon da kaji d'umin mahaifiyar da tayi silar zuwanka duniya,lokacin shayar sa kai yayi ta tafi ganinka,yanayin d'akin da kake ciki da yadda yake fitar da hucin zafi saboda yawan na'urori yasa Hauwa ta shiga damuwa,bayan duk damuwar da ta shigo da shi the resemblance of Rafeek in ur face as if it were being torn apart ya sake jefa zuciyarta a damuwa a lokacin da aka ciroka daga incubator aka mik'a mata kai,zuciyarta a raunane take ta kallonka,tunda ta farka take tunanin dalilin da yasa take jin ciwuka sa yawa a ranan but bata iya gano dalilin zamanta a hospital ba,amma lokacin data d'auke ka a karo na farko da niyyar ta shayar da kai yadda al'amarin ya faru ya dawo mata kamar a lokacin ne komai yake occurring,ta daure ta shayar da kai tana kallonka cike da soyayya mai tattare da tausayi take zubar da hawaye,har ta gama shayar da kai bata iya tashi ta fita ba,kana jikinta kana bacci yayin da ita kuma tana ci gaba da kuka tuna yadda komai ya faru,kula da nurse d'in dake d'akin tayi da halin da take ciki yana neman sawa ka fad'o daga jikinta tayi saurin karb'e ka daga hannunta ta mayar cikin na'ura,bin nurse d'in tayi da ido,idanunta suka sauka kan takardar dake jikin na'urar mai d'auke da sunan *RAFEEK Son* a hankali ta kai hannu ta ciro hawaye na ci gaba da zuba a idonta,nurse d'in ta bita da kallon tausayi tana tambayarta ko lafiya,da kyar Hauwa tayi shiru tana kallon rutun har lokacin tace
"Dan Allah y'ar uwa zaki iya min wani taimako.!?"
Tace "fad'i kada ki damu in sha Allah idan ina da yadda zanyi na taimaka miki zanyi"
Godiya Hauwa tayi mata tace "sunan nan nake so ki canja min"
Nurse d'in tace "Ohh! An sawa baby'n suna.!?"
Hauwa tace "Ehh! Ansa masa" murmushi nurse d'in tayi tace "Masha Allah,mene ne sunan.!?" Ba tare da Hauwa tayi shawara da kowa ba tace *"NURAAZ.!"*
"Wow.! But dan Allah zan iya tambayar ki.!?" Nurse d'in ta fad'a tana kallon Hauwa da kanta ke k'asa tace "fad'i tambayarki",tace" Ma'anar sunan nan da kika fad'a dan Allah zaki fad'a