Showing 3001 words to 6000 words out of 220972 words

Chapter 2 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1176

sai Annie tayi saurin rik'o hannunsa
"Zo Habibiiy ka sanar min damuwarka.. Me ya same ka jikinka yayi zafi haka..!?"
Girgiza mata kai kawai yayi,a hankali ya zame hannunsa ya shige bathroom without yace da ita wani abu game da tambayar da tayi masa.....


*#HAPPY NEW YEAR.*🎉


#Comment first
#Vote &
#Share pls.
#Real Smasher.
#Jan/1st.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                  *'DAN MACE..*
             (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

  
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

*YABON GWANI...*

Hassan Atk
Hussain Atk
Itz B.Y Ebraheem
Hayat Baba Zubair
Ku d'in ku ne gwanaye na,kuma abun alfahari na,idan har ina da mutanen daya kamata ace na ambata,a wannan dan tak'aitaccen rubutun nawa,tabbas ku ne farko,,bisa d'awainiya da kuke da litattafaina a social media,bani da bakin da zanyi muku godiya,sai dai har kullum ina yi muku fatan rabb ya saka muku da mafificin alkhairinsa ameen.

Pᴀɢᴇ 2.
#Eɴᴛʀᴇᴀᴛʏ

      Tun daya shige bathroom d'in yake tsaye k'ark'ashin shower,hannayensa dafe a jikin wall guda na katafaren toilet d'in da yaji kayan more rayuwa ya sake zurfafa tunani akan abunda mafarkin nasa yake nufi,a iya shekarunsa tabbas yasan bai kai matakin da za'a ce ya iya d'aukar irin wad'annan damuwar bane,to amma yaya ne zaiyi tunda k'addararsa tun farko a haka tazo.? Shi dai ya sani kuma har zuciyarsa ya tabbatar bawai yana damuwa da halin da yake ciki bane,abunda kawai yake damunsa a yanzun shi ne yana tsananin buk'atar son ya gane ma'anar yawan mugayen mafarkan da yake,,bakinsa ya bud'e kad'an yaja numfashi ya fesar,a fili ya tambayi kansa
    "Shin mene ne hakan yake nufi..??"
   Ya sake sunkuyar da kansa k'asa deeply thinking about his dreamt,ya b'ata lokacin da bai san adadi ba a k'asan shower ruwa yana ci gaba da sauka a saman kyakykyawan sumar kansa daya sha wani masifaffen undercut with long side swept,duk da yake yanzun ne yake kan tasowa amma sosai gyaran kan yayi masa kyau,but zuciyarsa tana cikin zullumi da damuwa wannan dalilin ya sake taimakawa wajen boy'ewar sirrintaccen kyaun da Allah yayi masa.
   "Tsayin wane lokaci zaka d'auka kana irin wannan mafarkan..?? Ya kamata ka bibiyi asalinkan idan har hakan zaisa ka samu nutsuwa,,lokaci yayi daya kamata ace ka gogewa mutane shakkunsu akan kasancewarka *MARA ASALI..!"*
    Zuciyarsa ke yi masa khud'ba da bashi shawara,a hankali ya d'an dakata da tunani,can daga wani gefen na zuciyarsa yake jin tana sake sanar masa
    "Ya kamata kayi wani abu wajen gano asalinka,idan ba haka ba..!"
    Sai yaji shiru kamar d'aukewar ruwan sama,,tambayar kansa yayi yace "If not.. What..!?"
     Kamar mai jira yayi tambayar zuciyarsa ta bashi amsa da "Har duniya ta tashi zaka tabbata ne a matsayin *MARA ASALI.!* Tare da ci gaba da amsa sunan *'DAN MACE..!"*
   Saitin zuciyarsa yayi saurin dannewa da hannunsa d'aya yana girgiza kai cikin wani matsanancin tashin hankali daya tsinci kansa sakamakon tunane² da yake fama da su ya furta
   "No..!! Bazai tab'a yiwuwa ba..! Sai na tambaye ki,,kuma bazan fasa tambaya ba,duk tsayin *ZAMANI* zan jira na sani,,sai na sani..! Wollahi sai na bibiyi asalina,sai na san *WANE NE ASALIN MAHAIFI NA.!"*
    Ya k'arashe maganar cikin wani irin murya mai amo dake tattare da damuwa,Annie dake tsaka da gyara d'akin tana karkad'e saman bed d'in daya tashi ta jiyo sautin maganarsa daga bathroom,tayi saurin ajiye spread d'in hannunta ta matsa jikin k'ofar toilet tana tambaya
   "Habibiiy.! Me yake faruwa..??" Shiru yayi bai yi magana ba,hakan yasa ta sake fad'in
     "Yi maza ka bud'e k'ofa habibiiy..!"
    Tana naganar tana kwankwasawa da iya k'arfinta,still taji shiru bai amsata ba sai taci gaba da kiransa,jin maganarta yasa a firgice ya juya ya kalli k'ofar,cos bai san a fili yayi maganar ba
   "Yanzun mene ne zan fad'awa Annie ta yarda da ni..?"
    Ya tambayi kansa yana k'urawa k'ofar idanu kamar mai neman amsar a jikin door d'in
    "Yalla habibiiy open the door..!"
   Annie ta sake fad'a tana bubbugawa,jikinsa duk yayi wani irin sanyi a hankali ya janyo towel ya d'aura a waist d'insa sannan ya nufo k'ofar yana b'ata fuska,har lokacin Annie bata daina dukan k'ofar ba tana ci gaba da kiran sunansa
     "Please habibiiy open it for me.."
    Bud'e k'ofar yayi ya tsaya a tsakiyar hanya hannayensa d'age a sama ya dafe both side na hanyar wucewa,bayan ya sake had'e rai wanda yayi masifar k'ara masa kwarjini yana kallon Annie data tsare shi da idanu tana masa kallon tuhuma yace
     "Annie..! What's happen..?"
    Kallon rashin fahimta ta bishi da shi kafin ta kamo hannunsa tana ja da fad'in
      "Wuce muje..!"

      "Annie stop..! Kin kira ni,and u know ban gama abunda nake yi ba..just leave me na k'arasa zan zo.."
   Wani kallon k'asan ido Annie tayi masa tace
   "Na fara wasa da kai ko..?? Zaka wuce muje ko sai na b'ata maka.?"
  
      "I'm sorry Annie.!"
   Ya fad'a yana sake kallonta yaji ko zata yi magana,but sai yaga ta b'ata rai,a hankali ya fara jan k'afafunsa yana binta har suka isa gefen bed,zaunar da shi ta fara yi then ta zauna closer to him,bayan ta rik'o saman shoulder d'insa d'aya fuskarta tana bayyana damuwa tace
   "Dear.! I knew kana cikin damuwa,musamman a kwanakin nan,kuma kasan ina kula da duk motsinka,duk canjin da zan gani a tare da kai ina ganewa farin ciki ko akasinsa,but why don't u tell me ur worries..? Kaga dai daga mu sai kai,bamu da kowa,duk duniyar nan mu kad'ai kake da muma kuma haka,kayi hak'uri Yarona,har kullum nasan bazan gaji ba wajen fad'a maka,duk halin daka tsinci kanka ciki ka kasance mai tunawa da ubangiji,sannan duk abunda ke damunka kada kaji tsoro ka fad'a min,,idan ina da yadda zanyi kasan zanyi ba don komai ba sai dan na making rayuwar ka ya zama different da na sauran mutane,duk da nasan a yanzunma akwai bambancin.."
   Ajiyar numfashi Nuraz yayi then ba tare daya kalleta ba yace
   "Annie..! I was dreamed,,ban san kuma me yasa ba yanzun all the time na kwanta bacci sai nayi ta fama da scary dreams,ina jin tsoro kada wani abu ya faru da ku..!"
 
    "Don't feel terrible habibiiy,ko mene ne zai faru kasan ina tare da kai,,kai dai kayi k'ok'ari ka kasance mai yawan kai kukan ka ga Ubangiji,shi kad'ai zai isar maka a cikin dukkan lamuranka,,in sha Allah babu abunda zai faru.."
    Rau² yayi da idanunsa kamar mai shirin zubar da hawaye yana ci gaba da kallonta,Annie dake ta kallonsa da tausayawa tayi saurin cupping fuskarsa a tsakanin palms d'inta tana sake tsurawa fuskarsa idanu
       "Don't cry habibiiy please..!"
    Yadda tayi magana da fuskar damuwa yasa Nuraz d'in saurin girgiza mata kai a hankali yana ta k'ok'arin mayar da hawayensa yace
   "Bazan yi ba Annie,,kema kada kiyi kinji.!?"
   Kai ta girgiza masa tana shafa kansa gently,yadda yake jin dad'in shafar da take masa a hankali ya zame yayi d'ai² a jikinta yana sakin wahalallun ajiyar zuciya,shafa sumar kansa taci gaba da yi in a calmness way zuciyarta fal tausayinsa,bayan wani lokaci tayi zaton yayi bacci ta gwada kiransa,a hankali ya amsa still idanunsa a kulle,d'an jimm Annien tayi kafin tace
    "Maza ka sanar da ni abunda yake faruwa ka ji ko..?"
   D'agowa yayi ya kalleta da lumsassun idanunsa yace
     "Annie what should i tell u..!?"
  Tana kallonsa tace "about ur concerns" Rau² ya sake yi da ido yana fad'in "But Annie i told u am sacred,ina jin tsoron abunda ya faru ya same ki.. Ni ban san yaya zan iya fad'a miki ba,besides kuma ina jin tsoron rayuwa ba tare da ke ba,,tun farko ban san kowa ba sai ku,bani da kowa,ina kike so naje idan na rasa ku.?"

   K'ura masa ido Annie tayi ko k'iftawa babu kafin ta tattaro jarumta tace "No habibiiy this is not for real,,abunda ka gani it's just a matter of dreamt,, shirmen mafarki ne,mafarki kuma baya zama gaskiya."

   Saurin katse ta yayi "Ni dai Annie ki bar tuno min, ko son maganar ma ba na yi"
   K'wafa tayi kad'an ta ture kansa tace "D'aga ni to,sai kaje can ka ji da damuwarka tunda baza ka fad'a ba"
   Yadda fuskarta ta nuna taji haushinsa har ta fara k'ok'arin mik'ewa ta bar masa d'akin da sauri ya rik'o hannunta yace "I'm really sorry Annie,, but believed me ina jin tsoron wani abu ya same ki ne..I have seen it in my dream"
   Yanayin fuskarsa kad'ai ya isa bayyanar da gaskiyar abunda yake fad'a,Annie da taji baza ta iya jurewa ba sai tayi saurin dawowa ta rungume shi tana shafa shi gently
    "It's ok habibiiy,, kada ka damu ka ji,ina tare da kai.. In sha Allah babu abunda zai faru,keep on praying Allah zai tsare ka"
  
   "Annie to kiyi hak'uri..!" Ya d'ago kansa daga jikinta yana kallonta,kai ta girgiza masa tace "Ehh! Zan hak'ura amma ka fara sanar dani abunda ke yawan saka damuwa,,idan kayi haka ni kuma promise zan hak'ura"

    "Annie amma fa.."

     Saurin rufe masa baki tayi tana fad'in "I told u zan hak'ura,but ka fara fad'amin,idan ba haka ba kuma zamu samu sab'ani tunda haka kake so"
    Kansa yayi saurin girgizawa kad'an yace "Shi kenan Annie zan fad'a" tiryan² ya fara d'auko mata labarin irin mafarkan da yake yi from da root har ya dire shi k'arshe inda ya farka babu jimawa,shirun da Annie tayi ta zuba masa ido tana sauraro har ya k'are bata fargaba,sai shi da yaji shirun nata yayi yawa ya dan girgiza ta "Annie baki ce komai ba" a d'an firgice ta kalle shi tana fad'in "Ahmn! Habibiiy" sai kuma tayi shiru,kallonta yaci gaba da yi ba tare da yayi magana ba,a hankali yaga ta mik'e tsaye kamar mai neman abu cikin kame² ta juya da sauri zata fita tana fad'in "Idan ka shirya maza ka fito kayi breakfast lokaci yana tafiya."

   K'ura mata ido ya sake yi har ta kai bakin k'ofa,still ba tare da ya amsa ta ba yana kallo tasa k'afa ta fice daga cikin bedroom d'in ba tare da ta ce masa komai ba,bayan fitar ta bai daina kallon hanyar da tabi ba,tunani da lot's of tambayoyi dake shak'e a zuciyarsa suka fara zuwa masa without limit
   "Me yasa bayan taji damuwata zata tafi..?"
  Ya tambayi kansa,idanunsa ya d'an juya cikin salon tunani yana dafe chin d'insa da duka hannayensa,a fili ya sake cewa
    "Ko dai bata fahimci abunda nake nufi ba.?"
     Zuciyarsa ce tayi saurin katse shi
   "No! Amma taji ai kuma tabbas ta fahimta,,the way take acting ya nuna akwai wani abu,shin kai baka ga yadda tayi bane.? Ya kamata kayi k'ok'arin finding abunda take maka hiding since.!"
   Jim yayi yana tuno yanayin fuskarta,damuwa bayyane akan fuskarsa yace
   "There must be something hidden,,her face point that out.. After taji komai,then ta juya ta tafi without tace min komai,,,shin mene ne hakan yake nufi.?"
   Juya kansa yayi kad'an cikin salon son takura kai akan lallai sai ya gano ko mene ne yake shirin faruwar,bai d'auki dogon lokaci a zaune ba bayan fitar ta yayi maza ya mik'e,jallabiya yasa mai gajeran hannu ya biyota,can k'asan zuciyarsa yana sake fad'in
   "Tabbas.! By God grace saina gano duk abunda kuke b'oyewa.. Zan gane da yardar Allah.."
    Dai² ya ratso cikin katafaren parlor'n da yake d'auke da wasu irin shiryayuun royal chairs masu matuk'ar kyau masu kalar royal blue and gold,iya gani da kushen mai hassada sai dai ya kalla ya had'iye saliva's amma ba dai yace zai tofa wani k'azamin magana game da tsarin gidan ko mammalakansa ba,yake tafe yana sake zurfafa tunani akan lamarinsa da Annie,har ya iso tsakiyar parlor'n ba tare daya farga ba,sai da Annie dake shigowa tace
       "Kaii.! Lafiya kuwa kake tafe kana tunani har ina magana baka ji..!?"
     Saurin kallonta yayi daga inda yake a hankali ya girgiza mata kai yace
     "Yeah! Am fine"
  Wani kallo Annie ta bisa da shi bayan ta tab'e baki tayi wucewarta zuwa kitchen ta barshi tsaye a tsakiyar chair's,tsintar kansa yayi da kasa zama,haka nan yaji yana son shiga ya ganta and ya duba yaga yaya take.

     Lokacin daya shiga d'akin a kwance ya isketa tana bacci,da alamun kamar bata farka ba har lokacin,gefen gadon ya k'arasa bayan ya d'an yi jimm a kusa da ita yana kallonta da tausayawa ya rik'o hannunta slowly yana murzawa,lokaci guda yanayin damuwa ya bayyana saman kyakykyawar fuskarsa,ya jima sosai a kanta yana ta kallonta ba tare da ta san ya shigo ba,kamar wanda ake tursasawa dole yana ta kallonta ya bud'e bakinsa da kyar
    "Lolly.! I dunno how things suke tafiya min a haka cikin kwanakin nan,ina yawan yin mafarkin abubuwa marasa dad'i suna faruwa,,but na san ba akan komai ne hakan yake faruwa ba face ciwon ki da a kullum da tunaninsa nake rayuwa,,tun bayan dana mallaki hankali na nake cikin damuwa,a duk lokacin dana bud'e idanuna na ganki cikin wannan yanayin ina tsintar rayuwata cikin k'unci,ban san mene ne zanyi na cire ki daga wannan k'angin ba,ina son ganinki cikin lafiya kamar kowane d'an adam mai y'anci,,but i don't even know mene ne zan aikata da zai sa ki dawo kamar kowa farat d'aya.. Ina sonki sosai kuma ina tausayinki,,,Ku biyun nan ku ne kad'ai duniyata kuma dangina,bayan ku ban san kowa ba,,ciki har da mahaifina,ban san wane ne shi ba,yaya yake.? A ina yake.? Duk ban sani ba,ban san komai game da shi ba,even his name ban sani ba,and u know ina son sanin abubuwa da dama game da rayuwata,but ban san mene ne dalilin da yasa kuka kasa sanar dani ba,,shin ina mahaifina yake ne..?? Ina son sanin wane ne shi.? Mene ne ya faru dake bayan samuwata.? Jikina ya jima yana sanar dani akwai damuwa a cikin rayuwarmu,,ina son sanin komai.."
    Shiru ya d'anyi yana sakin numfashi,jikinsa duk ya sake yin sanyi,a hankali ya kai hannunsa ya goge hawayen da suka gangaro masa yaci gaba "All i wish a rayuwata shi ne na ganki kinyi rayuwa kamar kowa ne bil'adam mai y'anci,, sai dai ban san yaya zanyi ba ko ta yaya ne hakan zai kasance.. Duk irin sonyayyar da nake miki a matsayin mahaifiyata,na san ban isa na cire miki wannan larurar ba,,ina tsananin sonki,soyayya irin wacce baki bazai iya fad'a ba,ina miki so irin na tsakanin d'a da mahaifiya,ina sonki da dukkan zuciyata,,ana ahabbuk Mamah.. Ahabbuk.! Ahabbuk-thtiir.!"
     Kansa ya sauke a hankali zuwa saman jikinta yana ci gaba da sauke hawayen damuwa da ajiyar zuciya masu nauyi,Annie dake tsaye bakin k'ofa tun d'azun ta gama jin kalaman da yake furtawa ita kanta bata san yaushe hawaye suka fara gangaro mata ba da sauri ta juya ta bar wajen tana ci gaba da hawaye masu d'umi da k'una,kitchen ta shige ta kulle kanta a nan tayi kuka har ta godewa Allah,bayan wucewar wasu mintuna still tana zaune ta buga tagumi take tunanin anya ta yiwa Nuraz d'in adalci da taja baki tayi shiru har tsayin wannan lokacin.? Shin tsayin wane lokaci ne zasu d'auka tana b'oye masa asalinsa.? A yanzun shekarunsa da hankalinsa ya kai ace yasan wane ne shi.? To amma ta ina zata fara sanar masa.? Shiru tayi tana sake zurfafa tunani har zuwa tsayin wani lokaci kafin ta yanke shawarar abunda take ganin shi ne yafi mata dai².

    Yana kwance a jikinta bayan tafiyar Annie Dr Waseem ya shigo d'akin da sallama bcos lokacin daya kamata ya dubata yayi,har ya k'araso kusa da shi bai san ya shigo ba sai da ya tab'a shi
       "Hello handsome..!"
      A d'an tsorace Nuraz ya d'ago duk da ya fahimci muryar waye,cikin dabara ya goge idonsa sannan ya waiwayo ya mik'awa Dr Waseem hannu bayan ya k'irk'iro murmushi
      "Welcome Dr."
     Suka yi musabaha Dr Waseem yana sake tambayarsa
      "How are u,,nd how was the patient.?"
   
    "Alhamdulillah." Yace yana sake kallonta
   
      "Allah ya k'ara mata lafiya" Dr Waseem ya fad'a yana maida hankalinsa kanta,Nuraz ya amsa da "Ameen" d'akin yayi shiru,Dr Waseem ya wuce kusa da ita ya fara shirin duba jikin nata,,Annie ta sake dawowa a karo na biyu bayan sun gaisa da Dr Waseem,ba tare da ta kalli Nuraz dake mak'ale da hannun mahaifiyarsa ba tace
      "Habibiiy! Zo maza ina son ganinka yanzun ka kyale Dr yayi aikinsa.!"
   Tana fad'a bata jira ba ta juya ta bar wajen,kamar bazai tashi ba ya fara binta da kallo har ta fita kafin ya mik'e ya bita yana jin zuciyarsa duk babu dad'i,a parlor ya tarar da ita zaune ta dafe chin d'inta da duka hannayenta biyu,tana ganin fitowarsa da sauri ta nuna masa kusa sa ita tace
   "Sit" babu musu ya nemi guri ya zauna yana d'an kallonta but k'irjinsa yana ji kamar ana kwala masa abu ta ciki,nan da nan ya fara ji yayi masa wani irin nauyi,idanunsa ya runtse yana d'ora hannunsa a dai² saitin zuciyarsa slowly ya shiga karanta
   "Allaahumma inniiy a'uzhu bika minal-hammi walhazan,wal'ajazi walkasal,walbukhli waljubni,wa'dhala'id-dayni wa'ghalabatir-rijaal."
   A hankali² yana ta maimaitawa har ya fara jin k'irjinsa yana sanyi,damuwar da yake tare da ita ta fara yayewa,ci gaba yayi da maimaitawa har tsayin lokacin da yaji ya dawowa nutsuwarsa tamkar dama can wani abu bai faru da shi ba sannan ya dakata yana sake fuskantar Annie da itama shi d'in take kallo tun d'azun ganin yayi shiru da idanunsa a rufe.....
   
 
   #Posting wannan karon yana wattpad da yardar Allah,but idan na ga babu voting zan ajiye na koma whatsapp & facebook kamar last novel.

   
   
#Vote,
#Comment &
#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

  

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login