Showing 9001 words to 12000 words out of 220972 words

Chapter 4 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1173

ya tsokani wancan,kullum haka ake yini abu guda,idan har kaji baki ya huta tofa sai dai idan dare ne ya zagayo kowa ya kwanta hak'ark'arinsa,a nan d'inma gurin kwanciyar bawai ina nufin za'a yi shi lafiya bane,dole sai an yada hali kafin baccin,wani lokaci idan ta d'auro cikin baccin ma sai an daki juna,,rayuwar gidanmu ta kasance rayuwa ce ake yinta kowa yana ganin hanjin kowa,zaman lafiya yayi mana k'aranci,kowa tak'amarsa shi kad'ai Babarsa ta haifa,kasancewar duk matan da suka shigo daga haihuwa d'aya ne zaman yake k'in dad'i wata ma bata haihuwar sai kaga an tafi,tafiyar da babu biko bare kome,,kowa shi kad'ai ne bashi da d'an uwa duka a cikin gidan,idan aka cire mu ni da mahaifiyarka da muka kasance ciki d'aya kuma baba d'aya,komai namu mun kasance tare muke yinsa tun tasowar mu duk da tsakani na da ita akwai nisan shekaru biyar (5),bata tab'a raina ni ba,tana bani girma na a matsayin yayarta,yadda ta d'auke ni take girmama ni a matsayina na y'ar uwarta da muka fito ciki d'aya,yana b'atawa sauran y'an uwanmu rai,a ganinsu ta yaya zamu kasance masu had'in kai al'halin duka gidan kawuna suna a rarrabe.? And duk wanda zai neme mu da fad'a bama kulawa daga ni har Hauwa,wannan hali ne wanda mahaifiyarmu ta d'ora mu akai,duk abunda zasu ce idan zasu kwana suna magana bama tanka musu,,kafin Allah ya yiwa mahaifiyarmu rasuwa tayi iya kokarin da zata iya na ganin ta had'a kawunanmu gaba d'aya,ganin lamarin ya gagareta ta hak'ura ta zubawa sarautar Allah ido,Innar mu mace ce mai hak'uri da kauda kai,ta rasu lokacin Hauwa tana da shekaru uku a duniya,,to da yake a gidanmu bamu samu wadataccen muhalli ba,kasancewar duka d'akuna guda hud'u ne,babanmu d'akinsa daban,matar babanmu ma haka,sai ya zama mu mata gaba d'aya muna d'aki guda,sauran d'akin kuma na y'an uwanmu ne maza,,a duka tashinmu halin babanmu guda biyu yake burgeni kuma nake matuk'ar so,duk da nasan da yawa mutane sukan yi mamaki da wannan halin nasa,amma agare mu ba abun mamaki bane,duk da kasancewar muna da yawa a gidanmu hakan ko kad'an baisa ya gagara ciyar damu ba,a kullum rana yadda ake d'ora tukunya a sauke sau uku a ko wane gida da suke jin suna da rufin asiri,muma haka nan ake yinsa a gidanmu,safe,rana da dare duk lokacin da mutum ya b'ukaci abinci zai same shi,,amma batun girmamawa ga juna ko soyayya irin ta y'an uwantaka wannan ne babu shi,haka ko a b'angaren karatu ma dai² gwargwado baba yana iyakar k'ok'arin sa wajen ganin mun wadata da ilimi,sai dai mu d'in a wannan fannin ba kowa ne hankalinsa ke kan karatun ba,duk wanda aka ce yau mahaifiyarsa bata cikin gidan mahaifinsa dole ne rayuwarsa ta samu nakasa dole ne kuma kaga bambanci da ratuwar wanda yake tare da tasa mahaifiyar,mahaifiya ita ce tushen tarbiyya ga ko wane d'a,shin mu da bamu da iyaye wane ne zai ce muyi ko mu bari.? Duk wacce baba zai auro wani lokaci sharrin yau da gobe ke sawa ya rabu da ita,dan har ga Allah babanmu mutum ne da yake da saurin yarda da magana,sannan duk duniya idan har kana son ganin b'acin ransa ka tab'a masa y'ay'a,a wannan lokacin na tabbatar duk yadda kuke da shi lallai za kuyi hannun riga,,ganin abunda muke so shi muke yi yasa itama matar gidan da aka auro take zaune da mu bata tab'a hana mu,idan ana hayaniya bata tab'a cewa mu bari,hasalima sai dai ta kad'e zaninta tayi wucewarta d'aki ta barmu nan,idan muna iyawa mu kashe juna ko mu hak'ura wannan duka ruwanmu ne,wad'annan dalilan yasa gaba d'aya kowa abunda ransa ya so yake yi,makaranta zuwanta sai wanda yaga dama ko yasa kansa,duk safiya baba zai sa mu shirya mu fita saboda yana ganin hakan shine babban gatan da zai mana a rayuwa,zuwa kuma ya rage na mai niyya,iidan ka ji baka iyawa kana fita daga gida zaka iya wucewa gararinka,idan ka daidaici lokacin tashi ka biyo ayari a dawo tare,,ruwanka ne kuma rayuwarka ce.

     Lokacin da baba ya fara harkar bin y'an siyasa,sai ya zama babu ruwansa da wani binciken muna zuwa ko bama zuwa duk da a bayama ba damuwarsa kenan ba,shi dai yasan duk k'arshen term zai biya school fees na gaba d'ayan mu,wad'anda suke zuwa da wad'anda basa zuwa,damuwarsa shi ne a tattara masa shaidar biya na gaba d'ayan mu a bashi,shin mutumin da aka bawa shaida kamar haka ta yaya ne ma zai san wanda bai je ba.?
   Life goes on,,bayan tsayin shekaru da muka shafe still rayuwar gidanmu yana a yadda yake babu wani sauyi,kullum abu biyu ke yawo a tsakani dad'i/kishiyarsa da rashin watar zaman lafiya,,cikin hukuncin ubangiji a dai² lokacin dana kammala secondary school Allah ya kawo min mijin aure daga cikin y'ay'an abokan Baba,,tunda aka tsayar da ranar aurena nake cikin damuwar barin gida,a zahiri kuma ba wai ina damuwa bane saboda zan tafi,sai dan a wannan lokacin duka damuwata ita ce Hauwa,tunani na a kullum yadda zan tafi na barta,saboda ban san yaya rayuwarta zata kasance ba bayan bana gida,na san matar babanmu bata kula da kowa a baya ba da yake cikin gidan bare yanzun nayi tunanin za'a fara,tak'amarta kuma shi ne bata haifa ba,babu wanda zata raina sannan baba ya nuna fifikon soyayyar mu akanta,shi yasa tunda ta shigo gidan bata tab'a cewa muyi wannan mai kyau ne,ko mu bar wannan bashi da kyau,tunda aka tsaida ranar aurena hankalina ya kasa kwanciya,,but a wannan lokacin Hauwa tayi abunda ni ya kamata ace nayi,kasancewarta mai k'ananun shekaru a kaina,kamata yayi ace ni zan kwantar mata da hankali,amma abun mamakin shi ne ita da ake ganin bata da cikakken hankali ita take kwantarmin da hankalina,a duk lokacin da zata ganni cikin damuwa takanyi k'ok'arin taga ta sanya murmushi akan fuskata,har Allah ya kawo lokacin aurena,aka yi biki lafiya aka kai ni d'akina,a daren daya zama daren farko na rabuwarmu da Hauwa,ya kasance ni ina kukan rabuwa da ita a karon farko tun bayan tasowar mu,itama tana kukan shiga sabuwar rayuwar da babu ni a cikinta,a hakan ina kallo y'an gidanmu suka wuce suka barni,naji babu dad'i sosai duk da ba zaman lafiya muke yi ba,amma ganinsu kad'ai a tare da ni nasan zai bani kwanciyar hankali,,tsakanin gidan mu da gidan da nake aure babu nisa,but mu a gare mu a wannan lokaci gani muke kamar an gama nisanta mu da juna,bayan y'an rakiyar amarya sun watse ango ya shigo d'akin amarya.."
   Shiru Annie tayi tana sauke numfashi da kallon Nuraz sannan taci gaba
    "A bisa tsarin addini komai angona yayi min,na tabbata mijina na sona haka nima ina sonsa,kasancewar mutum ne shi daya dace da burin kowace y'a mace,,bayan komai ya lafa,duk wata hidima an k'are,aurenmu ya samu wasu kwanaki haka nan sai nayi nufin tuntub'ar babanmu akan maganar ko zai bari Hauwa ta dawo gurina dan a yadda na kula da ita cikin lokacin tana cikin damuwa da takurawar y'an gidanmu,amma kuma idan na tambaye ta duk lokacin da ta zo gurina bata iya sanar dani sai dai tace min komai lafiya,ni dai haka nan duk lokacin da zata fad'amin haka nakan ji ban gamsu ba,shi yasa lokaci guda nayi nufin samun babanmu da batun,mijina ya bani goyon bayan na karb'o ta ta dawo hannuna,cike da wannan k'arfin guiwa da sa hannunsa muka je tare har gaban Baba da maganar,duk da a d'ar² muke bcos bamu sani ba zai amince ya bamu ita ko bazai amince mana ba mu dai gamu nan a probability....
   
   
   
   
   
#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*


*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2


Pᴀɢᴇ 4.
#Sᴏᴜʀᴄᴇ

Mun samu Baba a gida,bayan mun shiga mun gaisa da y'an gidanmu,muka samu Baba da batun,lokacin da muka gabatar da buk'atar mu ta son tafiya da Hauwa amma sai da amincewarsa,bai nuna mana komai ba yace muje zai yi tunani,idan zai iya bamu ita to,,ni dai tunda naji ya ce haka jikina yayi sanyi,dan Baba mutum ne shi kaifi d'aya,idan zai yanke hukunci da k'arfin guiwarsa yake zartarwa a take,haka ma idan bazai yi ba a take yake yankewa,but matuk'ar kaga yana abu kamar baya so,tabbas there's something behind,idan anyi sa'a kana da saurin fahimta ka gano dalilinsa na k'in amsa maka kai tsaye yace bazai yi ba ko akasin haka,jiki babu k'wari muka yi sallama da Baba muka tafi,,kwana biyu tsakani muka ji shiru and there's nothing in return akan maganar,mijina ya sake tuntub'ata ko zan sake tunawa Baba maganar irin ace ko mantawa yayi.? Gudun kada nace wani abu shima ya ga laifi na,tunda ni dai na fahimci Baba bazai bamu ita ba,na amsa da "Toh" amma a zahirin gaskiya nasan Baba bai amince zai bari Hauwa ta bar gida ba,,lokacin da na je gida mun gaisa da Baba kafin nayi masa maganar ya haumin fad'an akan wane dalili zan d'auko masa mijina nace muna so ya bamu Hauwa.? Tunaninmu bazai iya kula da ita bane ko yaya muke tsammani.? Ni dai nayi shiru na kasa cewa komai,k'arshe bayan ya gama fad'an yace "kuma kinji na fad'a miki ko da wasa bana son a sake min irin wannan titsiyen,ni ba lusarin uba bane da zan d'auki y'ata na bada ita zuwa wani gida al'halin nasan ba aure nayi mata ba,duk hak'k'in dake kaina dai² gwargwado ina rok'on Allah ya bani ikon kamanta saukewa,daga yau bana son a k'ara min maganar za'a tafi da ita wani gida,ban amince da barinta gidan nan ba" ni dai tunda yake fad'an kaina ke k'asa kuma har ya gama banyi ko tari ba,sai dana tabbatar ya gama na bashi hak'uri,nuna min yayi babu komai,daga nan ban samu damar shiga gida ba nayi masa sallama na wuce gidana,,da na dawo mijina ya ganni ni d'aya ya tambayi ina Hauwa? Na bashi hak'uri sannan na fad'a masa Baba yace muyi hak'uri da karb'ar Hauwa,duk dai yadda muka yi da shi sai na gyara batun cikin sanyin kalamai na fad'a masa ta yadda ba zai zargi komai ba,duk da yaji rashin dad'i amma haka ya gwada min babu komai muyi hakur'in,,a b'angaren Hauwa kuma zamanta a gida gashi nan dai za'a ce,tun bayan barina gida rayuwa ta fara yi mata wahala,wani abun a lokacin da nake gida duk da ba shiga harkar y'an gidan muke ba,sukan raga mata ko don ganin idona,to amma da yake yanzun bana nan kuma an ganta yarinya ce k'arama duk wanda ya deb'o cin mutuncinsa sai ya sauke kanta,haka nan dai take ta hak'uri da duk abunda za'ayi mata,har lamarin ya fara neman fin k'arfin shekarunta,bayan wani lokaci ta yanke shawaran sanar dani halin da take ciki,ta zo muka yi maganar da ita ta fad'a min duk halin da take ciki,sai na ji ban ji dad'i ba,to amma yaya zanyi tunda Baba baya so nayi masa maganar ya bamu ita,shawaran da kawai na bata shi ne daga ranar idan ta dawo daga makaranta ko wani gurin zuwa,ta daina zama a gidan tunda ganinta a tare da su shi yake janyo mata shiga damuwa da wahala,na bata damar idanma bata da shi ta dunga zuwa gidana tana yini,a take tace min A'a Baba ya hana ta yanzunma bai san ta zo ba,ina jin haka dabara ta zo min,nace to me zai hana ta dunga shiga gidan su k'awarta Maimunatu tana zama can idan ta dawo daga school,idan yaso sai tayi zamanta a nan har lokacin islamiyya yayi,which means ita da gida dai sai idan taji tana son yin bacci ta koma. Tace min "Ehh! To yaya wannan shawarar d'in dai ina ganin zaifi koh.?" Nace mata "haka nake tunani,kuma ina ganin ko Baba ma idan ya sani ba zaiyi fad'a ba" tace "haka nima nake gani,tunda dai ai ina kusa da gida,kuma duk abunda za'a fad'a masa ma ba lallai ne ya yarda ba ko.?",tun bayan tafiyarta sai ya zama daga wannan ranar idan sun dawo daga boko sai tayi wucewarta gidan su Maimunatu duk da ba makaranta d'aya suke yi ba amma zaman unguwa d'aya da had'uwarsu a islamiyya aji guda yasa suke k'awance sosai duk dama Hauwa ta kasance tana yin baya² da shiga sabgogin mutane,lokacin data fad'awa Maimunatu zata na zuwa gidansu,sosai Maimunatun tayi murna dan ita har ga Allah tana matuk'ar k'aunar Hauwa,itan ce dai da bata bada fuska ba yasa ko itama da kanta tayi baya² da ita tunda ta san ba'a k'awance dole,,cikin hukuncin ubangiji sanda Maimunatu ta fad'awa Hajiyar su hauwa zata dunga zuwa tana zama a nan,Hajiya ta amsa mata da k'arfin guiwarta bcos Maimunatu ita kad'ai ce y'arta mace,daga Yayanta sai ita su kad'ai suka mallaka,da taga tana murna itama tayi maraba da zancen,cikin tak'aitaccen lokaci rabin rayuwar Hauwa ya koma gidansu Maimunatu,idan ta fita tun safe ba ita zata koma gida ba sai dare lokacin kwanciyarta bacci,da safe ta sake shiryawa ta tafi makarantar boko,k'arfe 3:00pm sun tafi islamiyya,su da samun zama sai misalin 6:00pm idan sun taso daga islamiyyar yamma,rayuwarta ta koma gaba d'aya ta koma gidan su Maimunatu,,bayan b'illowar wannan al'amari na rashin zama tsakanin y'an uwanmu,idanunsu da hankulansu sai ya sake dawowa kanta,aka fara kai tsaiguminta gurin Baba akan tana tafiya yawo ba'a ganin k'afarta sai dare,abincin gidanma bata ci,maganganu dai barkatai haka aka cakud'e su,wani abun ma k'irk'irarsa suka yi suka fad'a,tun Baba bai fara tanka musu ba,sharrin yau da gobe ya janyo har ya fara tuhumar inda take zuwa tayi dare,a karon farko lokacin da ta sanar masa gidan Alhaji zakar labbo take zama,ta kawo masa dalilinta na yin hakan,ya gamsu kuma tun daga nan bai sake d'aga maganar ba,sai da aka sake soko mata sharrin k'arya tayi masa wancan lokacin,idan ta fita ba gidan Alhaji zakar d'in take zuwa ba,tana dai fakewa ne da can d'in a matsayin garkuwa,amma a zahiri yawon ta take tafiya,kwararo² babu inda ba'a santa ba yanzun saboda gantali,,ranar da aka kawowa Baba wannan maganar saboda zugashi da aka yi ya fusata sosai,maganar tayi masa zafi da yawa,ba tare da yayi bincike ya tabbatar da gaskiya ba yayi duka wa Hauwa,bayan nan ya yanka mata warnings masu tab'a zuciya akan ko da wasa ya sake ganin k'afarta a waje sai ya karairaya yasa an hura wuta da su,,a wannan ranar Hauwa tayi kuka sau babu adadi har taji tamkar hawayen idanunta sun k'are,yanayin maraici,damuwa da kad'aici ya sake mamayeta,cos a wannan lokacin bata da wani da zata sanarwa taji sanyi,ni d'in da muke sharing damuwarmu ban jima da zuwa ba,ita kuma Baba ya ce ko da wasa yaga k'afafunta waje sai ya sab'a mata,dan haka ta rasa mafita,a haka ta ci gaba da daurewa ta zauna cikin habaici da gori,makarantar da zata d'auke mata kewa itama ya hana zuwanta saboda a baya na fada maka Baba yana da halin yarda da abunda za'a fad'a masa,and baya damuwa da binciken gaskiya,kullum tana zaune gida ga damuwa ga kad'aici sai cin ranta suke,a gefe guda ga takurawar y'an gidanmu,,duka da yake ba shekaru gareta ba sai ta kasa yin wayon ko wani ne ta fad'awa yazo ya sanarmin halin da take ciki,,bayan kwana biyu da faruwar al'amarin Hajiyar su Maimunatu ta kula da rashin zuwanta tasa Maimunatun ta shiga ta duba ko lafiya bata ganinta cikin kwanakin.? Bayan zuwan tan suka d'an keb'e a d'aki duk dama an samu su ido,a hakan tayi iya kar k'ok'arinta cikin bada sallahun azo a fad'a min halin da take ciki ko Allah zaisa na rok'i Baba ya kyaleta taci gaba da zuwa makarantar,ta kwashe duk abunda yake damunta ta zayyanawa Maimunatu,tana kuka Maimunatun na taya ta har ta gama bata labarin abunda ya faru,Maimunatu tayi mata alk'awarin in sha Allah zata yi duk k'ok'arin da zata iya ta zo ta sanar min,Hauwa tayi mata godiya suka fito tare,da ta rakota bakin k'ofa suka sake tsayawa a nan suna ci gaba da y'an maganganunsu,kafin suyi sallama aka samu wani cikin y'an gidanmu ya kaiwa baba gulmar ga Hauwa can ta fita,babu b'ata lokaci Baba ya zo ya iske su zaure suna magana,nan d'in ma bai tsaya bin ba'asi ba ya korata gida bayan ya sauke mata kyawawan rankwashi masu shiga jiki,Maimunatu na kallon yadda take kuka,ta fice tayi gidansu da yanayin damuwa,,bayan komawarta gida bata iya fad'awa kowa ba har Hajiya data aikata,kuma ko da ta dawo ta tambayeta ce mata tayi tana lafiya daga haka bata sake cewa komai ba,,yanayin rayuwar gidansu Maimunatu rayuwa ce da suke yinta a sauk'ak'e,yanayin mu'amalar su da zaman takewarsu sun kasance suna gudanar da rayuwar su tamkar abokai tsakanin iyayen da y'ay'an,idan suna tattare da damuwa iyayen suna jansu a jiki su ji damuwarsu,itama Hajiya mahaifiyar sun a lokacin data kula da yanayin da Maimunatun ta shiga cikin kwanakin,haka ta sata gaba da tambayar lafiya take ganinta cikin damuwa.? Tana ta tambayarta da damuwa a fuskarta,tana lallab'ata saboda tana so ta sake sosai sannan taji mene ne ya kawo sauyin da aka samu,zuwa lokacin kasancewar damuwa tayi mata yawa sai bata sake b'oyewa mahaifiyartan ba ta zayyana mata komai da yake faruwa da Hauwa,,Hajiya ta shiga damuwa ta rarrashi Maimunatu sai da ta kwantar mata da hankali,and ta bata albishir idan Alhaji ya dawo zata san yadda tayi aka nemawa Hauwa'r sassauci,cos tana ganin lallai rayuwarta a cikin gidan akwai hatsari,sannan su da suka sani baya daga cikin hak'k'in mak'otaka kana ganin b'arna tana faruwa ka rufe baki ka zuba ido,dole tana bukatar inda zata zauna ba tare da tsangwama ko takurawa ba,ya dace ace itama ta zauna ne kamar ko wane d'a da yake k'ark'ashin iyayensa cikin y'anci,,sun gama maganar a ranan bayan Abba'nsu ya dawo tayi masa bayanin abunda ta ji daga bakin Maimunatun,shi kansa yayi mamaki sosai ace irin haka tana faruwa,abunda ya sanarwa Hajiya shi ne bai san yaya zai yi ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login