Showing 6001 words to 9000 words out of 220972 words
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
Alkhairin Allah ya kai miki uwa ta gari *Hajiya Maryam Alhassan (Oum Feedy & I)* ina mik'o gaisuwa,da addu'ar fatan alkhairi gare ki,Ubangiji ya raya zuri'ah,ya albarkaci rayuwarsu.
Pᴀɢᴇ 3.
#Tʜᴇ Bᴇɢɪɴɴɪɴɢ
Duk abunda yake idanunta na kansa,duk da niyyarta da farko data kira shi,ta shirya yi masa nasiha ne akan damuwar da yake sawa kansa cikin kwanakin,but ganin da tayi masa a yanzun da maganganun da yake yi lokacin data shiga d'akin,yasa taji duk guiwoyinta sunyi sanyin da har tana ji a ranta baza ta iya sake b'oye masa komai dan gane da rayuwarsa ba,,sun d'auki lokaci zaune shiru babu wanda yayi magana tun zamansu ko wannensu da tunanin da yake zuciyarsa,fitowar Dr Waseem yana tambayar Annie abincin da aka dafa mata ya taimaka wajen dawo dasu cikin hankulansu,jikin Annie a sanyaye ta kira maidservant d'insu Bareerah dake taimakonta ta b'angaren kulawa da gidan ta kawo masa ya karb'a ya wuce,hannun Nuraz ta rik'o cikin nata a hankali bayan sun kasance su biyun tana sauke nauyayyun ajiyar zuciya tace
"Samahniiy ya ibniiy..!"
A d'an dake ya kalleta yace "Annie what's going wrong kike neman yafiya ta.?? Ni mene ne kika yi min,a iya sani na tun dana taso ni baki tab'a min komai ba.. Daya wuce kyautatawa."
Hannunta tayi saurin d'orawa saman lips d'insa tana girgiza masa kai tace
"Skutiiy habibiiy.. Kada kace komai.!"
"Annie.! Stop this drama,ni na san baki yimin komai bafa."
"A'a habibiiy kada kace haka,,tabbas a gareka na kasance mai laifi,kai ne dai da baka san na aikata hakan ba kake k'ok'arin nuna min bani da laifi a gurinka,,but idan har baka yafe min ba tabbas ban san yaya zanji a rayuwata ba,ban san ina zan kai girman hak'k'in ka akaina ba."
Ajiyar zuciya yayi ya sake damk'e hannunta a nasa fuskarsa bayyane da damuwa yace
"Annie.! Dan Allah ki bari,nifa babu abunda kika yimin,,idan ma akwai ni ina so ki k'addara a ranki tun kafin kiyi na yafe miki,bcos baki cancanta da zama a sahun wad'anda za'a ga laifinsu ba idan sunyi KUSKURE..I knew KUSKURE ne ba don kina sane ba.."
Sai da tayi murmushin samun sukuni ta shafo gefen fuskarsa sannan tace
"Shukhraan'kthiir habibiiy,,sai dai sam fa ba yadda kake tunani bane.."
"Uhn!" Yace yana sake zuba idanunsa akanta,kallonsa itama ta sake yi tace
"Je kayi breakfast tukun kazo,akwai maganganun da nake son muyi da kai a yau idan rabb ya nufa."
"Really Annie.!?" Tace "Haka nake tunani idan rabb ya ara mana lokaci!" A hankali ya jirkita kansa gefe sannan yace "Okay" ya tashi ya nufi dining,Annie nata kallonsa har ya fara bud'e warmers dake gurin,shi yayi serving kansa,bayan ya zauna ci kawai yake amma sam baza ka tab'a gane yanayin dake kan fuskarsa ba,kad'an yaci ya ture plate d'in da mug daya had'a tea,ya taso ya dawo kusa da ita yana fad'in
"Annie na gama.."
"Uhn!" Tace,,haka nan tunda ta amsa ya tsinci kansa da sake nutsuwa idanunsa a k'asa yana ta addu'ar Allah yasa ko mene ne zata fad'a masa a dai² lokacin yazo masa da sauk'i kuma ya kasance alkhairi,muryar Annie ta katse masa tunani data kirashi
"Habibiiy.!" A sanyaye da irin muryar data kira shi yace "Na'am Annie",jim tayi kafin tace
"I want to tell u something,,though i know it's extremely ugly.. But ina fatan baza ka k'arawa kanka damuwa ba bayan kaji abunda zan fad'a."
Gabansa yaji ya fad'i da sauri ya d'ago ya kalleta yana marairaicewa "Annie.! Please idan dai zai tada mana hankali kawai ki barshi ba sai kin fad'a ba,ni banga amfanin ace a yanayin da muke kuma muna sake sharing wani damuwar ba,kawai a hak'ura ba sai kin fad'a ba,dama haka Allah ya nufa.."
"Ya zama dole ka sani habibiiy,,wajibi na ne na fad'a maka,ko dama ace na b'oye maka a yanzun,dole ne wata rana nan gaba kad'an kai da kanka ka sake tambaya,wannan dalilin yasa tun kafin zuwan lokacin na yanke shawaran sanar da kai,ni na huta da dako kaima ka huta tunani da damun rayuwarka akan son binciko gaskiya."
"Amma Annie.!"
"Kayi shiru ka saurari abunda zan fad'a,idan na gama kaji koma mene ne daga nan sai ka yanke hukunci,, amma kada kace na bari,a yau na riga nayi niyyar sanar da kai ne bisa umarnin zuciyata ba tare da ka tambayeni ba."
Ajiyar zuciya yayi yace "Shi kenan Annie,tunda har kin yanke hukunci,Allah yasa hakan ya zama mafi alkhairi a gare mu."
Shiru gurin ya d'auka for a while kafin Annie ta sauke dogon ajiyar zuciya tace
"HABIBIIY.! Nasan ka jima kana bibiyata da son sanin wane ne asalin mahaifinka.. A ina yake.? Wanene shi.?"
Kai ya gyad'a yace "Ehh! Annie but u already told me he was pass away"
Kai ta fara gyad'awa a hankali cikin wani yanayin damuwa muryarta tana rawa tace
"Tabbas na fad'a maka haka a bayan saboda wani dalili nawa,duk da na san this is not true habibiiy.."
Da mugun mamaki yace "But Annie kefa kika ce haka.?" Kai ta gyad'a tace "I knew a baya na fad'a maka cewa ya mutu ba don komai ba sai don ina son ka nutsu ka cire shi a cikin rayuwarka kamar yadda ya yanke ka daga jikinsa,,but a yanzun kuma ina sake shaida maka he's alive.."
Wani gagarumin gumi ne ya fara yanko masa,yana ci gaba da kallon Annie da mugun mamaki yace
"Annie! Kin san abunda kika fad'a.?"
Kai ta gyad'a tace "yeah! I knew,kuma ina cikin nutsuwa ta ne nake sanar da kai mahaifinka da kake damuwa da son sanin wane ne shi yana raye..!"
Kamar bai yarda da abunda kunnensa yake jiyo masa ba yace "Annie.! Yana raye fa..!?" Tace "K'warai yana raye bai mutu ba,abunda nace kenan..!"
Zuba mata idanu yayi ko k'iftawa ya kasa yi,mamaki kwance akan fuskarsa na abunda yaji,haka nan duk sai ya kasa motsawa but ya tsinci kansa dai da cewa
"Annie.! Idan har yana raye kamar yadda kika fad'a a ina yake..?? Kuma wane ne shi.!?"
"Zan sanar da kai yanzun da izinin Allah.. Saboda haka ka saurare ni kawai.."
Nutsuwarsa gaba d'aya ya sake tattarawa ya mik'a ta gurinta duk da yana cikin rud'ani,a hankali ta kalleshi sannan ta fara da cewa
"Mahaifinka ya kasance wani hamshak'i,wanda zan iya ce maka duniya gaba d'aya ta san da zamansa,shahararsa matsayi da yake da su kad'ai yasa shi mallakar lasisin shiga duk k'asar da yaso a lokacin da ya so.. Duk da na tabbatar ba lallai ne duk wanda zan fad'awa ya yarda da abunda zan fad'a ba kai tsaye,but wannan itace gaskiyar kuma ita nake shirin zan bayyana,,,mutum ne shi shahararre da duniya ta aminta da shi,haka nan shahararsa ba iya nahiyarmu kad'ai ta tsaya ba,sai da ta had'a da zagaye duniya,al'ummah ta sanshi ta yarda da ingancinsa,duka wannan maganar da nake yi ina yinta ne akan mutum d'aya tilo,bak'ar fata jinsinmu da ya fito daga Africa,,,ba kowa nake nufi ba face mahaifin da yayi silar zuwanka duniya wato *SUPERIOR."*
A mamakance a kuma razane ya d'ago yake kallonta bayan mik'ewa tsaye zubur da yayi,,bakinsa da duk wata gab'ar dake jikinsa tana aiki banda kyarma babu abunda yake sakamakon abunda yaji ta ambata yace
"Annie is he my Dad..!? Shi ya haifeni kike son cewa..??"
Tace "K'warai wannan mutumin shi ne asalin mahaifinka."
Wani murmushi ya saki mai ciwo yana kad'a kai alamun abunda yaji bazai tab'a faruwa ba yace
"Impossible! Annie ace kamar wannan mutumin shi ne Daddy na,,kin san wane ne shi da kike dangatashi da ni..?? Abeg.! Annie stop this drama,mutumin fa da kike magana baya zama k'asar nan,shi da ahalinsa sun jima basa nan,idan ya shigo ma within k'ananun hours yake barinta,me zai had'a mu da shi.? And how zai zama mahaifina.? Annie! Ba sai kinyi haka ne zan fahimci asalina ba,yau idan kika ce min bani da mahaifi wollahi Annie i will accept my fate a duk yadda yazo,zanyi hak'uri cos haka ubangijina yaso na kasance,Annie even a bite wollahi ban tab'a tsammanin irin wannan furucin daga gare ki ba,but for the sake of Allah nake rok'on ki,ki rufa mana asiri dan girman Allah Annie mu zauna a matsayinmu please..! Na amince na yarda da k'addara,please and please ki bar maganar nan ma kawai ya wuce.. Na hak'ura da sanin ko ma waye mahaifin nawa.."
Hannayensa ya had'e cikin rashin sanin abunda zai sake fad'a ya runtse idanunsa,Annie dake ta kallonsa da tausayi ganin bai yarda ba tace
"Habibiiy..! Did i tell u such things a baya can..??"
Yayi saurin girgiza kai alamun A'a,tace "why yanzun kake neman k'aryata ni..?"
Idanu ya zaro yasa hannunsa d'aya ya dafe bakinsa d'ayan kuma ya d'ora shi akansa yace "Annie! Ta ina na isa nace kinyi k'arya.?"
Had'e rai tayi tace "gashi yanzun mun fara."
Da sauri ya rik'e ta yana marairaicewa yace "I'm really sorry Annie idan har abunda nayi yasa kinyi tunanin na k'aryata maganarki,ki gafarce ni wollahi bazan sake ba.."
Duk sai ya koma abun tausayi cikin k'ank'anin lokaci jikinsa ya d'auki wani lalataccen rawar tsoro,a hankali tana d'auke kanta gefe tace "It's okay!"
Kallonta yayi yana langab'ar da kai yace "kin hak'ura.?"
Ta gyad'a masa kai kawai,shi dai Allah ya sani tun da yaji sunan mutumin da tunaninsa yake kawo masa ko a mafarki hanya bata isa ta had'o su ba bare a gaske ace suna da wata alak'a ya shiga tashin hankali,d'agowa yayi da kansa dake sunkuye a karo na sau babu adadi yana jinjina kalmar mahaifinsa ya kalleta fuskarsa har lokacin da alamun rashin yarda da abunda yaji,tambaya yake shirin watso mata kafin ya kai ga yin hakan tayi saurin tarar numfashinsa
"Ina so ka saurare ni a yanzun,,cos na riga na san abunda kake shirin tambaya ta,tun kafin muzo wannan gab'ar na shirya domin sanar da kai wannan muhimmin sirrin,,dan haka idan kaji wani abu daya shige maka duhu bayan na gama kana iya tambayata,ni kuma zan sanar da kai asalin yadda aka yi hakan ya faru da yardar Allah.."
Ajiyar zuciya yayi ba tare da yace komai ba yana ta kallonta,idanunsa,zuciya da jikinsa duk jinsu yake kamar sun daina motsawa sosai ga wani irin tsoron da yake jin yana taso masa a rai,Annie da ta kula da halin firgicin da ya shiga ta dafa kafad'arsa tana fad'in
"Kada ka damu habibiiy,ko mai zai zama dai² da yardar Allah,,sannan ni a yanzun abu d'aya kawai nake da buk'ata daga gare ka,shi ne ina so kayi min *ALK'AWARI* bayan kaji labarinka daga gare ni,ina so ya zama ba zaka tab'a sawa ranka damuwa akan abunda ya riga ya wuce ba.."
Kai ya girgiza mata a hankali sai dai bai ce mata komai ba,kamar mai tunani itama Annie tana kallonsa ta ci gaba da fad'in...
"Abunda ya faru..!"
*FLASHBACK...*
*(The beginning of the story).*
*"RAFEEK ZAKAR LABBO* shi ne cikakke kuma asalin sunan mahaifinka,wato *CHIEF ECONOMIST* kamar yadda kaji na ambata a farko ne,sai dai kamar yadda na sani ne kuma kaima ka sani a yanzun al'ummah gaba d'aya tafi kiransa da *SUPERIOR* kuma shima wannan sunan yake amsawa,wannan suna ne da zan iya ce maka ya samo shi ne tun bayan da d'aukakar sa ta bayyanar da shi a duniyar shahararru,,asalin iyayen Rafeek ba y'an garin Kano bane,zama da yanayin canjin gurin aiki irin na ma'aikatan force ya kawo iyayensa garin Kano,Allah ya had'a mu mak'otaka da su,tun kafin su haifeshi har zuwa bayan haihuwarsa muke zaune tare da su cikin unguwa d'aya,asalisu sun kasance Fulani ne su da suka fito daga jihar *YOLA*,,Mahaifin Rafeek Alhaji Zakar Allah yayi masa rufin asiri da dukiya dai² shi wanda duk wani bawa da yake neman rufin asiri a gurin ubangiji ya samu kamar wannan a iya cewa ya more,kasancewar iyayen Rafeek tun a wancan lokacin suna da arzik'in su dai² su,mahaifinsa Alhaji Zakar ya kasance mutumin k'warai daya rik'e muk'amai da dama a cikin hukumar su ta *CUSTOMS* kafin Allah ya kaishi matsayin *ASSISTANT COMPTROLLER* a b'angaren d'amarar tasu,daga nan ne kuma bai sake yin gaba ba saboda ajiye aiki da yayi (ma'ana yayi retire).
Duk wanda ya san su yasan mutane ne su na gari masu mutunci da ake zaune da su lafiya,tun farkon zuwansu kafin a samu mahaifinka,babu wanda zai zo yau yace sun tab'a yin ko da musayar yawu,haka ko bayan haihuwar Rafeek zuwa tasowarsa babu abunda ya canja,,a d'abi'u irin na yarinta ko wane yaro zaka ga da irin abunda tunaninsa da ra'ayinsa yafi karkata akai,ko nace muradinsa da idan ya girma zai so ya zama,,a wancan zamanin lokacin da shekarun Rafeek suka yi dai² da wannan stage bayan tasowarsa cikin hukuncin ubangiji,ya kasance gwani wanda yake da burin ganin ya nemi na kansa a k'ok'arinsa na ya wadata kansa ta inda ko ya girma ba zaiyi kukan rashi ba,,sab'anin sauran yara sa'anninsa da zaka tarar dole sai sunje gida suna y'ar murya suke samun biyan buk'atunsu,,sau da yawa a wannan lokacin tun bashi da shi,da y'an kud'in makarantarsa da yake ragewa yake siyo y'an k'ananun kaya da basu fi karfin aljihunsa ba a shaguna yana siyarwa a k'ofar gidansu,yau da gobe aka ce a gurin ubangiji tafi k'arfin wasa,akan wannan hali da mahaifinka ya d'auka mutane suka fara yi masa kallon shirmen yarinta yasa shi yin hakan,yayin da shi a gare shi bil'hak'k'i ya d'auki al'amarinsa,lokaci² idan ya samu yan kud'ad'ensa ba tare da yayi shawara da kowa ba zai je ya siya yan abubuwan da suke da rangwamen kud'i,kama daga kan sweet,chewing gum,biscuit da sauransu,ba don komai ba sai dan ya tallafi kansa ta hanyar neman halal d'insa and ba tare kuma da ya jira anyi masa a gida ba,and ba dan ya rasa gata ko idan yace ayi masa a gida za'a gagara yi masa ba,sai dan yana so ne ace wata rana shima ya dogara da kansa,,,tun a farkon lokacin daya fara wannan sana'a a lokacin da jama'a suke kan yi masa dariya,sam bai d'auki hakan wani abu ba,ya maida hankali sosai wajen ci gaba da siya yana siyarwa,had'e da nunawa mutanen dake masa dariya,dariyarsu bai dame shi ba,duk da wasu a ciki sukan yi masa izgili ta hanyar tsallake shagunan unguwa zuwa gurinsa,to idan sun zo d'in ma dai mai makon su jira ya basu,su da kansu suke d'auka suna masa wasa da kayan sana'a,idan yayi magana suci gaba da dariya suna tsokanarsa da fad'in maganganu marasa dad'i,abun ya fara damunsa a rai ya fara tunanin daina sana'ar tunda ita take kawo masa wulak'anci,sai kuma yayi tunanin shin idan ya bari d'in gurin waye zai dunga samun kud'in b'atarwa da biyawa kansa k'ananun buk'atu na yau da kullum.?? Wannan tunani yayi masa jagoranci wajen yin watsi da al'amuran mutane yaci gaba da bin shawarar zuciyarsa,and ya d'ora daga inda ya tsaya,,a lokaci guda yana sana'arsa kuma yana ci gaba da karatunsa,kullum cikin ranakun markaranta da safe zaije makaranta,da yamma kuma zai zauna gurin sana'ar sa,duk da tun farkon fara wannan d'abi'a tasa mahaifansa sunyi iya yinsu akan ya bari tunda komai na rayuwa akwai a gida amma sai yace shifa sam su kyale shi yayi,to ganin ba dainawar zai yi ba yasa suma kansu suka hak'ura suka zuba masa idanu tare da binsa da fatan alkhairi,,,bayan wani lokaci da fara sana'ar tasa Allah ya sake bud'a masa,lokacin da Alhaji zakar ya fahimci da gaske yake son yin sana'ar ya bud'e masa shop a nan jikin gidan,raba d'aya nasara ta kwankwaso masa k'ofa daga zube kaya saman tabarma ya koma babban container,yayi farin ciki sosai lokacin da yayi gamo da canjin da ya samu daga ubangiji,,akan haka rayuwarsa ta fara kullum cikin samun bud'i daga ubangiji akan harkar kasuwancin sa."
Dan kallon Nuraz Annie tayi da yake ta kallonta tace "wannan duka ina tsakuro maka labarin abunda ya riga ya faru ne a tak'aice,kafin mu gangara kan asalin alak'ar data had'a mahaifanka. "
A hankali gyad'a mata kai alamun ya gane,Annie taci gaba
"Asalin alak'ar mu da juna,,,mun kasance tsakaninmu da mahaifinka neighbours ne mu kamar yadda na fad'a tun farko,mun taso cikin unguwa d'aya a cikin line guda,gidajen mu basu da wani nisa tsakani,hasalima sun kasance suna kallon juna,but mun samu bambancin tsagi,ina nufin mu muna wannan gefen suma gidan su mahaifinka suna d'ayan hannun,kasancewar mu a haka na tsayin shekaru yasa babu yadda za'ayi ace bamu san juna ba,duk wanda yake cikin line mu ko da jiya ya zo mun san juna mu da shi,mun kasance mu da kowane gida kamar y'an uwan juna.
Gidan mu a gaba d'aya line ya kasance shi ne gidana farko da yafi kowanne tara mutane,bisa wannan dalilin yasa a kullum ba'a rabo da yin fad'a da y'an gidanmu,saboda yawanmu da jaye²n fad'a irin namu yasa muka yi fice a unguwar,dalili yawanmu kuwa shi ne babanmu yayi aure²,wannan yasa adadin y'ay'ansa muka kai ashirin maza da mata,to kuma dai da yake ba'a samu macen data zauna ba a cikin matan daya aura sai mahaifiyarmu,wacce ta zauna tare da shi tsayin lokacin har Allah ya karb'i rayuwar ta tana gidan,bayan mutuwarta sai wata bazawara daya sake aura,idan aka cire wad'annan matan biyu a tarihin gidan mu da aure²n babanmu sune kad'ai matan da suka zauna sama da shekara guda,duk wacce ta zo bata wuce haka,,sannan a yadda muke rayuwa gidan mu ya kasance yana da matsaloli,amma abu na farko daya nakasa gidanmu shi ne rashin had'in kai sai rashin wadataccen muhalli,wannan sune suka bawa gidan tallafin da kullum a kowace safiya yake kamar gidan haya,da zaran gari ya waye za'a fara hayaniya da fad'ace-fad'ace wannan