Showing 18001 words to 21000 words out of 220972 words
"Ni dai Hajiya kiyi hak'uri amma ki daina cewa nawa.. Ni ban yi mata ciki ba."
Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ta tunda ta tsaya tayi shiru sai kallonsa take ta kasa cewa komai,maganar da yayi a lokacin yasa har bata san ta dawo gabansa ta tsaya ba she feels like the whole world where lost ta rik'o rigarsa bakinta,jikinta da muryarta suna kyarma tace "Rafeek kada kace haka,,cikin ka ne fa,kada kayi min haka,ka tuna ban san kowa ba a bayanka,,kada ka sake furta cewa ba naka ba ne..!"
Fincike ta yayi a jikinsa cikin tsawa yace "kada ki rainawa kanki hankali malama,ni nayi miki cikin nan kike son cewa.!? Tun yaushe ne rabon mu da juna.!? And tsayin wane lokaci muka zauna duka bayan aurenmu.!? It's just a week,after then na tafi na barki.. Ta yaya ne wannan zai zama nawa.!?
Lokaci guda kanta yayi wani irin bugawa da kyar take ganinsa a idanunta saboda hawayen dake shirin zubo mata,taci gaba da girgiza masa kai
"Rafeek kada kayi min haka.. Wollahi ban san kowa ba sai kai,believe me cikin nan naka ne..!"
Tsawa ya sake yi mata cike da hayaniya yace "Na rantse da Allah kika sake cewa nawa ne sai na nakasta miki rayuwa,,how za'a kalli wannan uban cikin a kirasa nawa.!? Da yaushe nayi miki shi.!?"
Gaba d'aya ya mance da kasantuwar iyayensa a gurin yake sakin layi babu kunya bare tsoron Allah,su kansu iyayen mamakin da suke bai wuce yadda ya dage yana musanta cikin a matsayin nasa ba,a yadda suka san komai ya faru su dai sun gama tabbatarwa kansu ciki nasa ne,so why shi d'in yake arguing zancen.? Why don't him accept.!? Gaba d'aya sun shiga rud'ani sun kasa gane kan maganar.
Maimunatu na gefe ta saki baki sai kallon d'an uwanta take ta kasa cewa komai tun da aka fara maganar,sai idan wani cikinsu yayi magana ta juya,ta kalli wannan ta kalli wancan duk ta zama wata speechless a gurin,yadda parlor'n yayi shiru baka jin komai sai sheshshek'ar kukan Hauwa dake tashi yasa Maimunatun k'arfin hali ta iso kusa da yayan nata,tana kallon cikin idanunsa tace
"Yah Rafeek kada kayi saurin yanke hukunci,ka daina musu akan abunda baka da iliminsa.."
Wani lafiyayyen kallon ki rufe min baki yayi mata,duk da hakan bata yi shiru ba taci gaba da magana abunta
"Gaskiya Yaya kayi hak'uri amma ni dai sai na fad'i wannan gaskiyar.."
Kallonta yake ci gaba da yi yana gyad'a kai alamun kada ta fasa,duk irin warnings d'in da yake aika mata da su through kallon da yake mata bata fasa ba ta d'auke kanta daga kallonsa gudun kada ta firgice ta kasa fad'a tace "Yah Rafeek kowa a cikinmu da muke nan ya tabbatar cikin nan naka ne,why are u still arguing.? daga gidanku fa ka kawo ta nan.. Shin a ina kenan ta samo cikin idan ba a gidanka ba..??"
Lafiyayyen mari ya tsinka mata a karo na farko,tun tashinsu bai tab'a sa hannu ya daki y'ar uwarsan da suka fito ciki d'aya ba sai yau,still yana hucin b'acin rai yake karkad'a mata hannu idanunsa jajir yace "didn't i warn u to keep quiet and watched with ur eyes!? idan baki mai da hankalinki jikin ki da min zancen ciki² ba,yanzun i will make sure to shatter ur legs.. Stupid girl.!"
Ya k'arasa da zabga mata harara,still take tsaye gabansa hannunta dafe da cheeks d'inta daya sharara mata mari,Hajiya da Alhaji zakar tunda suka ga ya mari Maimunatu suka kasa magana,sai kallonsa da suke yi da mugun mamakin abunda ya aikata,kowa cikinsu tambayar da yake yiwa zuciyarsa shi ne
"Shin idan har cikin jikin tan ba nasa bane,na wane ne kenan.!?"
Da kyar Hajiya ta had'iye wasu irin terrified saliva's tana kallon su duka da rashin fahimta tace "Rafeek ina so kamin bayanin yadda akayi kake k'aryata zamtowar ciki matsayin na ka,,amsa d'aya nake so na ji daga gareka,shin wani abu ya shiga tsakaninka da matarka ko A'a.!?"
Straightforward babu b'oye² ko kunya yace "Ehh Hajiya"
Kallon Alhaji zakar tayi sannan ta sake kallon Rafeek tace "Kamar yaya Ehh!? So nake ka bud'e baki ka fad'amin d'aya a cikin magana biyu,Ehh Hajiya wani abu ya had'a mu,ko A'a babu abunda ya faru,simple.!"
A sad'ad'e yace "Ya had'a mu." Shima k'asa² baiyi tunanin zata ji ba,jinjina kai tayi tana harararsa tace "sau nawa ne hakan ya faru!?" Bai dago ba yace "Sau d'aya" tace "lokacin a yaya ka sameta.? I mean is she verging or not.!?" Saurin kallonta yayi yaga ta tamke fuska not to look his direction ta sake cewa "da kai nake magana ka tsare ni da ido.!" A sanyaye yace "she is.." tsaki tayi tana neman gurin zama ta kallo Hauwa dake ta uban kuka har lokacin tace
"Zo nan daughter kinji,,ki kwantar da hankalinki,ni banga abun damuwa ba a nan tunda har ya amsa tambayata da bakinsa,k'arya yake yace min ciki ba nasa bane."
"Hajiya wollahi nifa ban san na wane..!"
Hannu ta d'aga masa tun kafin ya gama bata amsa tace "Shud i give u a chance to talk.!?"
Kai ya fara gyad'awa yace "Noo! But am sorry!"
D'auke kanta tayi daga kallonsa taci gaba da kallon Hauwa tana sake riritata "Don't stresses ur self dear,musamman akan abunda kika san bashi da amfani,ki dai na ajiye shi a ranki kin ji my daughter,due to ur conditions ma bana so a samu wani matsala saboda hakan kinji.!? Kin riga kin san irin condition da kike ciki a yanzun,u don't want anybody to remind u,ke ya kamata ki fara kiyayewa cos it's ur field"
Idanun Hauwa sunyi jaa ta daure tana goge hawaye tace "Toh" Hajiya tana mata murmushi mai sa nutsuwa tace "Yawwa y'ar albarka,goge hawayen ki,kuma daga yanzun ba na son na sake ganin kina kuka kinji ko.!?"
Ta sake gyad'a kai tace "Toh Hajiya,in sha Allah i won't"
Shiru parlor'n ya d'auka tsayin wani lokaci babu wanda ya sake magana,Rafeek sai bin iyayensa da Hauwa yake da kallo,so yake yayi magana amma ganin sun basar da shi a gurin ga tsoron hukuncin da zasu zartar sai ya hana shi tofa albarkacin bakinsan,bayan shafe tsayin lokaci ya fita ya bar musu parlor'n,babu wanda ya tanka masa ko ya damu da shi har ya fice,a gefen Hauwa itama yadda ta bishi da kallo kad'ai ya isa sawa ayi saurin gane ma'anar kallonta,duk da ya ta'allak'a ne bisa yanayi mai wahalar fassara,siririn tsakin da yayi escaping a bakinta tayi sauri ta rik'e shi bata bari kowa yaji sound d'in zuwansa ba,dukansu alhini suke da jimami,Hajiya mamakinta ya kasa b'oyewa dan har dare bata daina tunanin al'amarin ba.
A b'angaren Alhaji zakar da Maimunatu ma dai haka abun yake,kowa tunanin dalilin da zaisa Rafeek ya musanta cikin a matsayin nasa yake,daren ranar gaba d'ayan ahalin gidan basu iya samun bacci cikin nutsuwa ba,washe gari da safe Rafeek ya shigo apartment d'in,a parlor ya iske su cikin shirin tafiya skul sun ci uban fararen kaya,kad'an ya kalleta ya d'auke ido soundly ya saki tsakin da yasa gaba d'aya suka kalleshi,not minded ya tsuguna yana sauke kai k'asa cike da ladabi
"Hajiya ina kwana.!?" Idan ta amsa ku k'addara parlor'n da item's dake cikinsa sun motsa ta share shi a gurin dan kansa ya gaji ya zauna,har suka kammala breakfast suka yi niyyar tafiya skul babu wanda ya gaisheshi tsakanin Maimunatu da Hauwa,suna kammalawa suka yiwa Hajiya sallama sai sun dawo,ta bisu da addu'ar fatan alkhairi sannan suka fice suka barshi nan yana fama da latsa waya,,fitarsa babu jimawa ya mayar da wayarsa ya sake kallon Hajiya,so yake yayi magana amma duka ya rasa inda zai fara kamawa,fuskarta tamke kamar kokon safe and not to look at his direction tace "Me ya kawo ka nan ne.!?"
In'ina ya fara yana sake sunkuyar da kansa k'asa,kallonsa tayi ta tab'e baki "Ka ga bana ciki da iskanci Rafeek,baka san tun jiyan da haushinka a zuciyata na kwanta ba ko.!?"
Bai d'ago ba yace "Ki yi hak'uri Hajiya"
Wani kallo ta masa tace "Nayi hak'uri.!?"
Ya gyad'a mata kai,gyara zama tayi tace "To ubana na yi,,yanzun yaya aka yi ne kazo min nan ka sani gaba.!?"
A sanyaye yace "Na zo na yi muku sallama ne ina son komawa.."
Wani kallo ta bishi da shi,kusan mintuna uku tsakani kafin tace "Allah ya tsare to" daga haka ta yunk'ura zata tashi,saurin d'agowa yayi yace "Hajiya.!" Kallonsa tayi ya ji ya kasa maganar,data tambaya shi "yaya aka yi",still kasa magana yayi sai cewa yayi "babu komai ",tab'e baki tayi tace "toh tunda babu ka tashi ka wuce kada ka rasa flight ko..!?" Jikinsa a sanyaye amma idan ya tuno abunda ya faru jiyan sai yaji k'irjinsa ya cika fal da bak'in kishi,Hajiya da taga ya kasa tashi ya tafi wisely ta fara yi masa nasiha,yadda jikinsa ya nuna ya karb'i nasiharta yasa ta bishi da addu'ar fatan alkhairi,sallama ya sake yi da ita sannan ya d'auki hanyar komawa inda ya fito,,duk abunda ya faru a ranar cikin nasihohin Hajiya da tayi masa akan cikin jikin Hauwa,bayan ta k'ara da fad'in ita dai ko da ace wani abu bai shiga tsakaninsu da Hauwa ba to ta amince d'an da Hauwa zata haifa tana so ya tsaya a matsayin mahaifin cikin,duk maganganunta da nasiharta akan cikin da kula da Hauwa tayi masa shi,abunda ya janyo jikinsa ya mutu kuwa ba komai bane face nasihar data masa akan marin Maimunatu da yayi da tunatar da shi lahira,but bayan tafiyarsa tun kafin ya isa k'asar Ghana al'amura duka suka warware bisa khud'ubar da shaid'an yayi masa akan lallai ya raba Hauwa da gidansu tun kafin ta raba shi da gidan.
Tunda ya koma yake tunanin yadda zaiyi ya raba ta da gidan amma ya kasa,daya tuna ai akwai waya ya kirata ya sanar da ita sak'on sa babu b'ata lokaci ya aika mata da sak'on kira,lokacin da Hauwa taga kiransa tayi tunanin kamar yadda Hajiya ta sanar musu ne bayan sun dawo daga skul,shi yasa ta d'auka da fara'a sosai a fuskarta tayi masa sallama,ta samu ya amsa sallamar amma gaisuwa sai ya basar da ita kamar bai jiba,daurewa tayi ta sake gaishe shi still yayi banza bai amsata ba,hakan yasa ta sha jikin jikinta akan lallai ba kiran lafiya yayi mata ba,abunda bai tab'a yi ba tunda suka yi aure ranar shi yayi,ina nufin kiran sunanta kai tsaye,amsawa tayi babu damuwar komai a ranta dan ita kanta a lokacin ta gama shiryawa duk wulak'ancin da zai mata idan taji baza ta iya ba tofa tabbas za tayi tafiyarta dan bazata tsaya auren wanda yake zarginta ba,maganarsa ta dawo da ita hayyacinta
"Hauwa! Shin gidan da kike zaune na wane ne.!?"
Kai tsaye Hauwa tace "gidan surukaina.." Girgiza kai yayi kamar tana kallonsa yace "ba wannan na tambayeki ba"
"Me ka tambaya ne.!?"
Yace "cewa nayi gidan da kike na wane ne.!?" Ta sake maimaitawa kamar farko,cije lips d'insa yayi na k'asa ya sake tambaya,gane abunda yake nufi a wannan karon yasa ta bashi amsa da "gidan iyayen mijin da yake zargin naci amanarsa" duk da yaji amsar data bashi kamar yadda ya buk'ata hakan bai hana shi jin fad'uwar gaba ba,but ya dake yace "good.! Kenan ba gidan ku bane ko.!?"
Tace "Me zai hana ya zama gidanmu tunda ina da iyaye a ciki da y'ar uwa.!?"
Murmushi yayi yace "amma ta dalilin waye kika same su.!?"
Tace "Ubangiji ya azurta ni da samunsu ba tare da wayo ko dabara ta ba.!"
Yace "Bayansu kina da iyaye ko A'a.!?"
Tace "ina da su,kuma kaima ka san ina da su" murmushi yayi mai kyau yace "good.!³" yana clapping hannunsa,jim tayi tana saurarensa gabanta sai tsananta fad'uwa yake ta daure tace "me kake nufi ne wai.!?"
Sai da yayi ajiyar zuciya a hankali yace "abunda nake nufi kike son sani.!?"
Ta gyad'a kai tace "Uhn" k'wafa yayi sannan yayi shiru na wani lokaci continuously yace "tabbas nasan kina da iyaye,to amma mene ne dalilin da ya hanaki tafiya gidanku ki raini cikin ki a can!?"
"Kafi kowa sanin dalilin da yasa ban tafi ba ai tunda kai ka ajiye ni a nan,and u know ba zaman kaina nake ba."
"Okay! Zaman waye kike yi.!?"
Tace "Zamanka nake" yace "Really.!?" Tace "Sure" murmushi ya saki soundly followed by "Idan har zamana kike zan iya cewa iska na wahalar da mai kayan kara.! Ke me ya kai ki jiran abunda bazai amfani rayuwarki ba.?"
Abunda yake bakinta ta had'iye da kyar tayi yak'e da fad'in "kamar yaya.!?" Yace "ina nufin.!"
Sai kuma ya yi shiru bai k'arasa ba,sun d'an b'ata lokaci shiru kafin yaci gaba da magana cikin kaushin murya
"Ina son kiyi min wani abu guda d'aya,and not to seek favour in u" Ya fad'a da wani irin murya,cewa tayi "ina saurarenka fad'i kawai" yace "ina so ki bar gidan mu",gabanta na fad'uwa tace "ko mene ne dalilin ka na yin hakan.!?" Yace "saboda ke da kanki kin bawa kanki amsa nan inda kike gidanmu ne ba naku ba,so ina son ki tattara ba tare da kin fad'awa kowa ba ki bar gidan" murmushin k'arfin hali tayi tace "shi kenan zan tafi in sha Allah kamar yadda ka buk'ata,amma da farko ka fara fad'amin" cikin hayaniya yace "me zan fad'a miki ne.!?" Tace "saurin mene ne kake yi haka.!? Ai zan fad'a maka"
Yace "Ina saurarenki"
"Da farko ina son jin bisa shawarar waye kake son na tafi.!?" Yace "bisa ra'ayin kaina", tace "Da kyau.! To amma ka sanar da su Hajiya ka ce na tafi.!?"
Kasak'e yayi yana saurarenta yace "kamar yaya.!?"
"Kamar dai yadda kaji na fad'a" yace "dole sai na fad'a musu za ki tafi.!?" Tace "Sure sai sun sani,saboda kaika kawo ni gurinsu ka ga idan zan tafi ma bisa umarninka ne,kuma dole sai sun san zan tafi"
Yace "really.!?" Tace "sure" girgiza kansa yayi kad'an yace "but yanzun mene ne kike ganin zaisa ki tafi ba tare da sun sani ba.!?" Bata yi tunanin wani abu ba tayi masa shiru,murmusawa ya sake yi cike da mugunta yace "kina ganin idan misali yanzun nace na yanke alak'a da ke,zaki sanar musu.!?" Danne tsoron daya cika mata zuciya tayi tace "sure",tsaki yayi saboda ba haka yaso yaji daga bakinta ba,yana shirin yin magana ko me ya tuna kuma ya fasa,can ya sake daurewa yace "Hauwa!" Ta amsa "Na'am" yace "Ni RAFEEK ZAKAR LABBO a yau ina son shaida miki na yanke alak'a ta dake" cikin tsananin tashin hankali tace "me kake nufi.!?" Yace "abunda kika ji" tace "kana nufin ka rabu da ni.!?" Yace "sure",, "ka rabu da ni.!?" Ya sake maimaitawa "na sake ki nace"
Murmushin takaici tayi tace "Rafeek! Ya kamata kayi tunani kafin ka yanke hukunci,, idan ba ka tunanin baya akwai gaba fa,ka tsaya ka yi nazari."
Tsaki yayi yace "kinga Malama ni ban tambayeki wannan ba,abunda kawai nace shi ne.. Na sake ki.! Idan kin samu wanda zai iya aurenki yayi k'ok'arin zama dake da halinki kina iya yin aure.."
Yana gama fad'a ya katse kiran,,wani irin nauyi taji k'irjinta yayi mata,ta toshe bakinta tana girgiza kai,har lokacin gani take maganar sakin da Rafeek yayi mata kamar mafarki take tana farkawa zata ga a bacci hakan ya faru,da yake a zaune take cikin d'akinsa data mayar nata tun zuwanta sai ta mik'e tsaye ta fara zagaye d'akin cikin tsananin firgici da damuwa,lokaci guda maganarsa ta dawo mata
_"Na sake ki.! Idan kin samu wanda zai iya aurenki yayi k'ok'arin zama dake da halinki kina iya yin aure.."_
Zuciyarta ta harba lokaci guda bayan gano ma'anar abunda kalamansa suka k'unsa,a slow ta tsaya inda take tana dafe kanta da take jin kamar ana kwad'a mata guduma,cikin hayaniya take tambayar kanta kamar yana gurin
"Yanzun Rafeek na cancanci irin wannan hukuncin daga gareka.!? Me nayi maka da zaka min haka.!?,kana nufin ni karya ce bani da daraja.!?"
Shiru tayi kamar wata zararriya ta shiga girgiza kai
"A'a.! A'a.!! A'a.!!! Wollahi ba haka bane,ni ba karya bace,ina da mutunci na,kuma kaima ka sani,kai shaida ne akan mutunci na..!"
Shiru ta sake yi tana kallon guri guda fuskarta d'auke da murmushin takaici tace
"Me yasa zaka min haka Rafeek.!? Me yasa zaka yi zargin bani da kamun kai al'halin kafi kowa sani idan ina da shi ko bani da shi.!? Me yasa zaka ce ka sake ni.!? Me yasa zaka ce cikina ba naka bane...!?"
Wani irin shiru ta sake yi jikinta yana kyarma ta k'urawa guri d'aya ido kamar mai tunani,haka tai ta juya words d'in a cikin kanta da zuciyarta da ta cika fal da tsoro,kamar sabon kamun hauka take magana cikin hayaniya tana sake juya zancen,dai² ta kawo kan maganar cikin ta fizgo wayarta ta fara dialing number sa,rai a b'ace Rafeek ya d'auka yana daka mata tsawa yace....
#No comments,no voting,,,there's no posting till further notice... Time to posting strike.🚴🏻♀
#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
Pᴀɢᴇ 7.
#Bᴇᴄᴏᴍɪɴɢ ꜱᴏɴ ᴏғ ᴀ ᴡᴏᴍᴀɴ
"Da Allah mene zaki kirani kuma.!? Ni yanzun mene ne zanyi miki.? Muna da wata alak'a ne kuma.!?"
Ta daure tace "Rafeek ina son muyi maganar cikin ka dake jikina."
A zafafe ya tari numfashinta "Hey! Hey.!! Malama