Showing 93001 words to 96000 words out of 220972 words

Chapter 32 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1167

Allah,,ya karatu fa.!? Na san dai kina yi" tace "Alhamdulillah" dai² lokacin da suka tsaya bakin entrance,Maimunatu tayi y'an danne² tana jan su da hira,they didn't take a moment tayi enrolling sunan su,kamar daga sama suka ji k'ofar tana mentioning sunayensu and welcoming nasu,suka d'aga kai a tare suka kalli juna,Maimunatu ce a kan gaba suna binta har suka shiga cikin apartment d'in daya kusa gigita tunanin su,dukiyar da aka zuba kad'ai ya zame musu abun kallo,suna ta tafiya su wuce wannan parlor su shiga wannan har suka k'arasa bedroom d'insa inda suka tarar da Hajiya,tana ganinsu ta saki fuska tayi musu maraba cikin mutunci,Annie da Nusrah suka zauna suka gaisa da Hajiyar da tambayarta mai jiki,ta amsa babu yabo saboda ta san idan tace da sauk'i kawai fad'a za tayi,kafin kace me har an fara jera musu kayan ciye-ciye,ta ko ina maidservant ne turawa sai shigowa suke suna hidima da su,tun abun yana basu mamaki har ya daina,,a tak'aice ranar har bayan maghreb suna gidan sai kusan isha sannan suka yi shirin tafiya,Hajiya ta cika su da goma ta arziki and tasa su Clark da driver su mayar da su gida,suka yi sallama,Hajiya thanked them saboda ta ji dad'i sosai tana ta basu hak'uri da sak'on su gaisar mata da Hauwa'u,ko da suka tashi dawowa motar da aka d'auko su a zuwa ba a ita aka mayar da su ba,,lolly was sitting in the parlor wondering where Annie went sai ga su sun dawo,ta bisu da kallo bayan ta yi musu sannu da dawowa,Clark ya shigo musu da kayan da Hajiya ta basu sannan yayi musu sallama,lolly ta bisu da kallon mamakin inda suka samo shi,dai² suna zama saman armchair,looking at them again tace "Adda ni kam ina kuka jene.!? Ni dai na san babu wanda kuka sani a garin nan,amma tun yamma da kuka fita sai yanzun,nayi tunanin ko mall kuka je.." Annie tace "Who knows ko we have found out a new family ne a nan k'asar" she quickly looked at her and was surprised by the expression tace "relatives? Here.!?" Ta gyad'a mata kai tana tashi tace "Ehh! Kin san komai nufin Allah ne ai" ta jinjina kai tace "Haka ne" daga haka bata sake magana ba,a ranta take ta juya maganar and ta k'udurce duk abunda Annien za tayi ba zata sake tambayarta ba,but zata sa mata ido har sai ta gano ko mene ne take hidden mata.
     
9:00pm His car stopped at the apartment,ya fito ya rufe a hankali ya nufo entrance,duka suna zaune a parlor har lokacin suna hira doorbell tayi k'ara Annie tace "Daughter je ki bud'ewa.." Tun bata k'arasa ba tayi zumbur ta mik'e tana fad'in "Kai Annie,ni dai ba sai kin fad'a komai ba" Ita Annie dariya ma Nusran ta bata,tace "Ku ji min ja'ira,do u know what am i going to say kika tari numfashi na.!?" Tace "No Annie! But if u say so Allah na san sai kin sani jin kunya" suka sa dariya har Bareerah dake fitowa daga kitchen,dai² tana bud'e masa k'ofa Bareerah tace "Ni dai Annie ban san me yake faruwa ba,duk naga kwana biyu baby kunyar ki take ji." Annie tana dariya tace "To waye ya sani ne,ga ta nan dai tambayeta muji whether she'll say anything to u",suna had'a ido da shi yayi mata murmushi k'asa² yadda za ta ji shi yace "Hi.!" Ta bishi da kallo tace "Hello" He rolled his eyes and stood still where he was yace "how are u.!?" Tace "Uhm! Alhamdulillah" ya jinjina kai yana sakin ajiyar zuciya sannan ya fara takowa ciki,ta koma baya kad'an ta bashi hanya ya wuce ta mayar da k'ofar ta rufe sannan ta dawo tana cewa "Bareerah Aunty what are u asking.!?" Bareerah tace "Kunyar Annie naga kina ji,wai mene ne yake faruwa ne.!?" Tayi murmushi tace "Kema dai Auntyn nan ki ji ki da wani magana,kuma shi kenan ba zan ji kunyarta ba.!?" Bareerah tace "Amma da ai banga hakan ba,when did u start.!?" After she sat back tace "Yesterday" suka sake yin dariya.

Har ya wuce bayan sun gaisa da su Annie ta kira shi,ya tsaya kad'an yana jiran yaji me za tace,tana kallonsa tace "Ka je ka duba shin.!?" Ya girgiza kai yace "No,,i have no time to leave the hospital sai yanzun,amma idan Allah ya kaimu gobe i will go" tace "Ai suna gida ma yau da safe Maimunatu ta kira ta fad'a min sun koma gida" ya dawo ya zauna kad'an yace "Jikin nasa yayi sauk'i kenan.!?" Annie ta girgiza kai tace "Da sauk'i dai za'a ce amma yadda yake haka yake" lolly ta zuba musu ido tana sauraren hiran nasu,Nuraz ya tab'e baki yace "Allah ya basa lafiya" ya mik'e tsaye yana had'a kan wayoyinsa zai wuce,Annie tace "Ameen" yana juya baya k'asa² yace da Nusrah "please help and bring me some coffee" she slowly nodded tana b'ata fuska,yana barin gurin lolly ta fara harhad'e rai,Annie ta kalleta tayi dariya k'asa² tace "Ya dai madam.!?" She was quiet and did not say anything until maganar ta ciyo ta tace "Wai dama Adda shi kuka je dubawa tare da baby.!?" Annie tace "Ehh! What happen.!?" Ta tab'e baki tace "Nothing" Annie tace "A'a ki fad'a if there was" ta sake tab'e baki tace "Kawai banga amfanin zuwan naku ba ne" Annie ta tsaya kallonta tace "Really.!?" Tayi shiru bata ce komai ba,Annie ta jinjina kai tace "Allah ya kyauta,though i am not surprised da kika ce haka,amma ko babu komai ya ci albarkacin yaron mu" Nusrah tayi saurin tashi ta wuce kitchen,even before she asks herself mene ne alak'ar su Annie da gidan da suka je but she find nothing about,and as soon as she hear the conversation begins to find out,tana shiga kitchen ta d'auko coffee powder ta ajiye tasa ruwa a kettle tana tsaye har ya tafasa ta had'a masa cup d'aya tasa a saman midi tray ta d'auka ta fita,suna zaune har lokacin suna maganar ta zo ta wuce,tana shiga bedroom d'insa lokacin shi kuma ya fito daga wanka yana sanye da bathrobe,ta ajiye masa za ta fita yace "Ahmn! Baki ji ba" ta tsaya a inda take kamar wacce aka dannawa pause,yace "Thanks" ta gyad'a masa kai ta wuce a hankali tana tafiya,har ta kai bak'on entrance bai daina kallonta ba,za ta fita yace "I want to see u if u have nothing to do" hannunta rik'e da handle d'in k'ofa tace "when.!?" Yace "now if u don't mind" ta girgiza kai tace "Okay.!" Tana fad'a ta fita,quietly yayi ajiyar zuciya,he turned around and took the cup ya fara sipping,sai da ya shanye sannan ya juya ya shirya cikin kanan kaya yana gamawa ya bud'e k'ofar da zata sada shi da balcony ya fita,tsaye ya hangota jikin realer looking outward ya tsaya da mamakin when she had come,ya k'araso inda take a hankali yace "Ba dai tun d'azun kike jira na ba.!?" Ta waiwayo a hankali tana sauke ajiyar zuciya ta girgiza kai tace "A'ah" ya lumshe idanunsa ya bud'e yace "ok then can we go and sit.!?" Ta girgiza masa kai bata ce komai ba,he began to adjusting his position and placing his hand on the realer yayi shiru yana kallon sararin samaniya da tunanin abunda zai fad'a.

Tun daya zo she didn't look at him duka sunyi shiru babu wanda yayi magana,sai da taga shirun ya yi yawa tace "Why didn't u go and visited him.!?" Bai kalleta ba yace "Aiki ya min yawa" tace "Amma ko na mintuna 10 da ka je ai" yayi murmushi yace "I'll go ai" tace "when.!?" Kai tsaye yace "babu rana bare wata" tayi saurin kallonsa tace "Kamar yaya babu rana.!? Mahaifinka ne fa.!?" Ya girgiza kai yace "I know" she was silent as she looked at him,ya d'ago idanunsa daga kallon fulawowin gurin ya sauke akanta yace "Ya akayi ne.!?" Ta girgiza kai ta juya slowly ta fara tafiya daga gurin,ya bita da kallo kafin yace "Baki ji ba" ta waiwayo tana harhad'e rai,ya kalli yanayin ta yace "Me aka yi miki ne.!?" Ta girgiza kai a hankali tace "Babu komai" ya tab'e baki kad'an yace "Ko dan na ce ba yanzu ba.!?" Ta kalleshi sosai tace "No this is not" yayi murmushi yace "To mene ne.!?" Tace "Babu komai" yace "Ok then" daga haka bai sake magana ba,ta koma bakin pool ta zauna tasa k'afafunta a ciki,carefully yake watching how she had quieted duk ta had'e rai kamar ba ita ba,yayi dariya a ransa yace "Idan sai na je zai samu sauk'i ya shekara yana jinya"

*2 Month later...*

Since the incidence has taken place yau tsayin watanni biyu kenan Annie take bin Nuraz yaje ya duba Rafeek amma kullum sai kwacewa yake,kuma har wannan lokacin jikin Rafeek d'in dai ga shi nan ne,he is constantly undergoing treatment amma jiya tana nan a matsayin yau,though he came back from a long faint (suma),amma an rasa gane kansa kullum bashi da maganar data wuce a kira masa lolly da d'ansa ya nemi gafarar su,Hajiya ta gaji da kiran My son da yake ta kira Annie a karo na babu adadi kamar za tayi kuka tace dan Allah ta lallab'a Nuraz yazo,tace she would send him off if God willing,daya dawo daga hospital da dare ya iske su a parlor kamar kullum ta fad'a masa kai tsaye yace "Dan Allah Annie ki rabu da su,ni wollahi bana son ganinsa" Annie ta rasa yadda za tayi da shi,duk ta inda ta b'illo masa sai ya bi ya toshe da nashi hujjojin,even though she told him Rafeek's situation was worse than amma ya bad'e ido da toka yace "Shi bai san me zai yi musu ba da suka damu yaje" maganganun da ya farfad'a basu yiwa Annie dad'i ba,ita kanta NUSRAH they made her feel bad,but she tried to look at him,after then she simply didn't say anything ta mik'e ta bar wajen,ya bita da kallo har ta shige bedroom,daya koma bedroom d'insa ya kira ta saboda ya ga irin kallon da tayi masa,kasancewar a tsakanin kwanakin alak'arsu ta d'an fara k'wari,sai dai tak'i d'auka daya dameta da kira kai tsaye ta tura masa sak'on "Ita ya rabu da ita kawai since he is humiliating his father,what will she do to him.!?" Gabansa yaji ya fad'i he was completely unprepared ya bud'e k'ofa ya fita balcony,a dai² bedroom d'insu ya tsaya da yaga da haske a ciki yayi ajiyar zuciya cos yasan har lokacin tana nan,sai dai baya ganin komai saboda curtains d'in duk sun rufe wall glass d'in gurin,wayar ta ya sake gwada kira yana tsaye a gurin har ta katse bata d'auka ba ya koma jikin door d'in yayi knocking,Nusrah dake zaune saman bed ta juya a hankali ta kalli gurin,shade d'insa da ta gani tsaye yasa ta sauka taje ta bud'e k'ofar,yana tsaye yana kallon yadda ta had'e rai tak'i kallonsa yace "what.!?" Bata yarda ta kalleshi ba tace "Nothing" yace "Fad'a min mana" ta d'ago za tayi magana aka tab'a k'ofa za'a bud'e ya rik'o hannunta da sauri suka bar wajen,sai da suka je bakin pool sannan ya sake ta ya gyara tsaiwarsa yace "That's because i said am not going anywhere shi ne kike fushi.??" She raised her wider eyes ta kalleshi slowly ta juya masa baya tace "A'ah" yace "A'ah me.!?" Tace "babu komai",yayi murmushi yace "Kina so naje.!?" Tayi saurin kallonsa,ya d'aga mata gira yana tsare ta da idanunsa,ta d'auke kanta gefe tace "Idan ina so,kai ai baka so" he laughed and said "Uhn! I don't want to,but if u said.." Sai kuma yayi shiru yana sakin murmushi,she looked at him eagerly taji ya k'arasa amma sai taji bai ce komai ba,ta tab'e baki tace "Ai ba zuwa za kayi ba ko nace ina so" yana kallonta yace "Kice naje to ki gani" ta juya tana murmushi tace "Who am i to say to u.!?" K'asa² yace "The mother of my upcoming kid's" tayi saurin kallonsa because she wasn't hear him,yayi saurin fuskewa yace "Kin ji" tayi squeezing face tace "What is that.!?" Yayi dariyar rainin wayo yace "kice naje please" tace "Idan ka yi niyya ba" yace "A'ah! Ba idan na yi niyya za kice ba,cewa za ki yi kaje ka dubasa" ta juya ta fara tafiya tace "Saboda nice Annie sai nace za kaje.!?" Ya bita da kallo yace "Ai baki fad'a ba,da kinga abun mamaki" tace "Ni babu abunda zance,duk lokacin daka sauko daga fushin ka je ka dubasa.." Tana fad'a ta wuce za ta shige yace "Since u know the house,tomorrow u will be ready to accompany me.!" Cak ta tsaya kafin tayi saurin juyowa tana kallonsa,ya shagwab'e fuska yace "please.. Will u go with me.!?" Ta tab'e baki tace "Kaje Kai kad'ai mana" ya girgiza kai "Yace idan ba zaki ba shi kenan na fasa" ta juya tana dariya tace "No offense",dariyar shima yayi bayan tafiyarta,ya jima sosai a gurin yana mamakin kansa with the changes he has made cikin k'ank'anin lokaci.

Washe gari da yamma ya fito cikin shirinsa,ya zauna a parlor waiting for her arrival,about twenty minutes later yaga ta k'i fitowa ya gaji ya kirata,tana kwance a saman bed kiransa ya shigo,duk da ya fad'a mata tare za su je amma ita dai ta fi so yaje shi kad'ai,ta d'auko wayar tasa a hands free "u know i've been waiting tun d'azun kika k'i fitowa" ya fad'a cikin husky voice d'insa da ko wane lokaci bata sauyawa,tayi murmushin yak'e tace "What can i do for u.!?" Yace "Raka ni za kiyi ai kin san ban san gidan ba ko.!?" Tace "Ok then kace Annie ta baka address mana" ya katseta da sauri "I don't want,idan ba zaki ba,just say it out" tayi murmushi tace "Nifa aiki nake yi yanzun" yace "Wane iri.!?" Tayi shiru,yace "Ba zaki ba.!?" Tace "Ni dai kayi tafiyarka kawai ba sai na je ba" yace "Ok.!" Zai kashe wayar tayi saurin cewa "will u go.!?" Yace "Ina ruwanki da zanje ko bazan jeba.!?" Tayi shiru tana tunani,yace "Tunda ba zaki ba nima ba sai na jeba,kuma kada ki sake min maganar nak'i zuwa daga yau" tace "Za kaje ne.!?" Yace "ina ruwanki.!? I said i won't go" za tayi magana ya katse,da sauri ta diro daga saman bed tayi hanyar fita,tana fitowa ta ganshi zai shige bedroom d'insa,a ranta tace "Da gaske yake yi ba zai je ba.!?" Tayi saurin cewa "uhmm! D'an tsaya please" ko bi ta kanta bai yi ba ya wuce abunsa,,ta tsaya tayi shiru ta rasa me za ta yi bayan ya tafi,da sauri ta juya ciki a gaggauce ta sake sakarwa jikinta ruwa,ta fito ta shirya cikin atamfa Holland mai kalar sea blue,sai data gama tsaf sannan ta kira shi,yana kwance yana kallon kiran yayi mata banza,ta gaji ta tura masa text "Ka fito na shirya" yana gani ya sake yin banza da sak'on,taji shiru² bashi da niyyar kiranta,ta fito parlor nan ma bata ganshi ba,bakin k'ofar d'akinsa taje tayi knocking yana jinta yak'i tashi ta gaji da jiran ya bud'e ta tura k'ofan ta shiga da sallama,she saw him resting on top of the resting chair without any intention of getting up,,tayi shiru tana kallonsa tace "Ka taso mu tafi." A hankali ya d'ago kansa ya saci kallonta,when he saw that she was so beautiful a cikin shigar mu ta hausawa sai tayi kamar sabon aure (Amarya) bai san lokacin daya gyara zama yana kallonta ba,ta juya za ta fita yayi saurin tashi yace "Ki jira ni mana kike tafiya" taci burki a bakin k'ofa bata ce masa komai ba,ya d'auko mukullin ya fito,a tare suka yiwa su Annie sallama suka fita,tana gaba yana binta,shi ya bud'e mata ta shiga ya rufe ya zagaya side d'in driver ya bud'e ya shiga ya tada motar suka d'auki hanya,ita ta dunga masa kwatance har suka k'araso mansion,ya gyara parking suka fito ya kalli mansion d'in ya kalleta zaiyi magana sai kuma ya fasa suka wuce zuwa entrance,to the surprise of Nuraz lokacin suka fito daga mota yaga hadiman gidan sai wani girmamasu suke,he didn't even realize it until they stood in front of the glass building da zai kaisu cikin ainihin mansion d'in,nan yaji na'ura tana mentioning sunansa dana Nusrah,ya tsaya tunanin ya akayi shi da bai tab'a zuwa ba akayi enrolling sunansa as a young master.? (Ni dai na ce idan ya shiga ya tuhumin Rafeek),ya daure yana had'e rai ya bita suka shiga,sun shigo cikin parlor'n yana mata k'orafi k'asa² tana masa dariya,ta tsaya da niyyar bashi amsa ya tsare ta da idanunsa,tayi saurin juyawa za ta wuce ya fizgo hannunta da sauri ta dawo baya a tsorace ta juyo tace "What's that.!?" Ya had'e rai yace "Ki daina ganin mun zo nan fa,dan na koma ba abunda zai ba ni wahala bane" tayi shiru bata ce komai ba ta fara k'ok'arin kwace hannunta daga rik'on da yayi mata,shi kuma yak'i sakinta tace "Wai mene ne hakan,ka sake ni mana,kai ko kunya ba ka ji ne.!?" Yayi squeezing face yace "What is it.!?" Ta harare shi tace "Nima ban sani ba" yace "Kuma kike tambaya ta.!?" Ta d'auke kanta a hankali tana harhad'e rai,kamar ance ta kallo cikin parlor'n ta hango mutane zaune,da sauri ta kalleshi tace "let me go ka ga dai da mutane" ya tsuke fuska yace "Ina ruwana da su.!? Kika dame ni da maganar su Allah i will take u straight in front of them,,ko baki yarda ba na gwada.!?" ta zaro ido za tayi magana wrongly suka had'a ido da,ido ta zaro waje fuskarta cike da tsananin mamakin ganinsa ta furta "Aatif.!".....



*#😱😱😱 Jama'a mene ne ya kawo shi gidan nan kuma.!? Wayyoo Allah yasa ba....*

*#Abeg ke Smasher keep quite,,,no ur water inside oooooo...😷*


#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login