Showing 177001 words to 180000 words out of 220972 words
"Uhn! Tell me" ta had'iye saliva's da kyar saboda yadda fuskarsa ta koma tace "Dama fa ban sansu ba sosai,kuma tunda ta rasu bamu sake zuwa ba" ya gyad'a kai yana rufe computer da ya bari yace "Yanzun kuma kina son zuwa?" Ta gyad'a kai tace "Ehh!" Ya kad'a kai yace "Ok! Bari mu gani k'arshen session d'in ku yayi" tayi saurin kallonsa tace "will u..?" Bata k'arasa ba ya girgiza kai yace "Ban yi alk'awari ba" tayi murmushi mai burgewa saboda da farko da ya girgiza kai bata yi tunanin abunda zai fad'a ba kenan,da sauri ta haye jikinsa cikin murna duk da bai amsa zai kaita ba,but ta sani tunda yace idan sun yi hutu tana da tabbas zai kaita.
Kwanansu biyu da sauka a k'asar suka shirya zuwa ziyara gidan yayan Abbah,da yake tun da suka had'u a Nigeria wajen biki sun yi alk'awarin k'arfafa zumuncinsu kasancewar a bayan sun watsar da shi,wannan dalilin yasa suka shirya duka da yamma suka nufi gidan Mr Muhammad Sajid,lokacin da motocin su suka shigo harabar gidan iyalan gidan dukansu suka fito tarbarsu because sun san wane ne Rafeek,Abbah ne dai basu sani ba duk da kasancewarsa matsayin k'ani a gurin mai gidan,but yaran gidan suna samun labarinsa sosai a gurin Daddy'nsu da yake shi d'in mutum ne mai son nasa,ta nan suka samu sab'ani da matarsa,motocin su suna yin parking suka fara fitowa fuskokinsu a sake,suma mutanen gidan duk suka fito tarbarsu sun saki fuska sosai,Mom ce kan gaba tana kallon Annie da Lolly ta nufesu,cike da wayewa had'e da ilimi suka rungume juna tana sake welcoming nasu,duk sunyi farin ciki sosai da suka tarar da ita hakan,yaranta mata biyu *AFAF* da *HANNAH* suka nufi Nusrah,duk suka rik'e ta suna mata barka da zuwa,cikin sakin fuska tayi musu murmushi kamar can da sun san juna,Mr Rafeek dake kallon Dad (Yayan Abbah) suka tab'a tsokanar juna na kwanaki biyu da ba'a had'u ba,daga nan aka d'unguma ciki duka,sun shigo babban parlor'nsu da yaji alatun rayuwa aka zauna ana gaisawa,ko ina da komai fes gwanin sha'awa tsaftar Mom ya sake bawa su Annie damar sakin jiki sosai da ita,here maidservant suka fara hidima da su,da aka dasa hira here aka fara gabatar da juna,su Nuraz ana gefe an kame kamar baya nan,sai idan anyi abun dariya yayi murmushi,bayan haka ko tari ya k'i yi,ana tsaka da hiran ne Abbah ya juya ya kalli Yayansa bud'ar bakinsa yace.....
#Ina kuke masoya *REAL-SMASHER?* tofa yau ga damar ku ta samu,whoever like my story if kin/ka/kun san u are all ready to read just follow as soon as na fara updating sai dai wannan lokacin labarin zai zo da sabon salo ne kasancewarsa paid story,the story is unlike any other,so kada ku bari a barku baya,and dan Allah ina rok'on alfarma d'aya gare ku duka,duk wanda yasan he'll just follow the story for nothing other than ya b'ata min rai da wani magana akan story d'ina ya yi hak'uri please,akan *D'an Mace!* I have been hurting a lot,but na danni zuciyata ba wai don basu b'ata min ba,please and please idan kun san za kuyi min abunda zai b'ata min,dan Allah stay away from reading my stories,because ba na yin rubutu dan na b'atawa kowa,why za ku b'ata min? Abun nan babu dole sai ka yi ra'ayi za ka bi and babu wanda na takura sai ya karanta,hopefully this honor will be given to me,thank u.
Ga wanda suka shirya littafin *MAKTOUB* paid story ne saboda wasu dalilai sun sa dole zan siyar da shi,ga masu buk'ata/wanda suka shirya siyan labarin #300 ne,zan fara posting littafin cikin tak'aitaccen lokaci,da zaran na kammala *'DAN MACE* in Allah ya amince,for more enquiry za ku iya tuntub'a na ta 08085701562 or 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
Pᴀɢᴇ 48.
#ʟᴜsᴛ
Bud'ar bakinsa yace "Brother wai ina yaro na? Tunda muka zo ban gansa ba?" Daddy yayi murmushi yana kallon Mom yak'e baiwa Abbah amsa "Yaronka yayi min laifi,na tura shi Amsterdam k'arin karatu" Rafeek ya zuba masa ido yana kallo yace "Shi *AATIF* d'in ne ka tura karatu amma babu labari?" Not only Nusrah ta shiga shock da jin an ambaci sunan Aatif,hatta Nuraz,Lolly da Annie sai da suka saurara da hiran da suke yi suka kalli Daddy,suna jira suji amsar da zai bayar,yayi murmushi yace "Shi d'in fa,al'amarin yaron nan ya fara bani tsoro,na yanke wannan hukuncin,but kuyi hak'uri duka ban sanar da ku ba" Abbah ya kad'a kai yana sauraren Yayansan while Rafeek shi kuma yake sake tambayar "Tun wane lokaci ka yanke wannan shawaran?" Daddy yayi murmushi yace "Not too long" duka daga haka wani abun mamakin sai duk suka yi shiru babu wanda ya sake tada maganar Aatif d'in har suka zo tafiya,Daddy da iyalinsa suka yi musu rakiya har bakin mota,ciki kuma har a time d'in babu wanda ya canja fuskarsa duk da sanin Aatif ya fito ne ta tsatson Daddy,da za su tafi Hannah da yake ita ce babba,tun zuwan su gidan itace tayi ta shigewa Nusrah sai suka fi sabawa da ita,but ko da suka fito tafiya nan Nusrah taga salon da take yi na tafiya a gaban Nuzar kishi yayi ta cin jikinta,tunda ta tsime bata sake bada fuska ba har suka shiga mota,Nuraz ya kalleta yayi murmushi sai baice da ita komai ba,sunyi sallama bayan duka sun shiga motoci da suka zo da su driver's suka ja suka bar gidan,Daddy suna d'aga musu hannu har motocin su suka fita,it was there Nuraz ya rik'o hannunta yana k'unshe dariyar dake son kama shi,ta d'auke kai gefe ta k'i yarda su had'a ido,ya matsota sosai yana rik'o fuskarta,tayi sauri ta rufe idanunta fuskarta sam babu fara'a,yana kallon yadda tayi yayi ajiyar zuciya a hankali ya fara laluben bakinta,quickly ta bud'e ido tana tureshi,yayi still yana kallonta bai ce da ita komai ba,sai da ya bari sun shigo mansion driver yayi parking tana shirin fita ya rik'o waist d'inta da duka hannunsa ya hanata fita,fuskarsa babu fara'a yana tsareta da idanunsa ya furta "Me aka yi miki kike fushi?" Ta d'ago ido za ta yi masa fitsara taga yadda fuskarsa ta koma da sauri ta shiga hankalinta,yana sake tsare gida yace "Akan wannan abun da kike yi ina tambayarki kina ji kiyi min shiru wani lokacin saina faffalla miki mari" ta d'ago da sauri ta kalleshi jin kalmar mari a bakinsa,ya sake tsareta da ido yana fad'in "Didn't i..?" Bai k'arasa ba ta fashe da kuka tana fizge jikinta,ya lumshe ido cike da tashin hankali ya rungumota jikinsa yana fad'in "Mene abun kukan? Ke dai da hawaye suke yiwa arha kullum cikin asararsu kike" cikin kuka tace "mari na fa kace za ka yi!" Ya tab'e baki yana sakinta yace "Ba dai kina son raina ni ba?" Ta kad'a masa kai tana cewa "Har abada ba zan tab'a raina ka ba" yayi saurin kallonta yana son fahimtarta,da ya tabbatar da gaskiyar abunda take fad'a har ranta,lokaci kad'an duk kuma sai yaji bai kyauta ba da yace hakan,nan ya rungume ta yana bata hak'uri akan maganar marin,tayi luf jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Su Annie kuwa lokacin da suka k'araso motarsu yana yin parking duk suka fito suka wuce ciki kafin su tafi gidansu da suka sauka because duk sunk'i yarda su zauna gida guda da su,a nan suka wuce apartment d'in Hajiya suka dasa hira.
*****
*Ina labarin Aatif ne??*
A b'angaren rayuwar Aatif kam gaba d'aya since Nuraz yasa akayi detaining nasa a police stationt,bayan ya sa anyi freeing d'insa ko da ya fito sai ya ci layar b'ata ua b'ace b'at ko cikin labari ba'a sake jinsa ba bare gani,as Aatif ya kasance some kind of coward parson,idan ya samu wanda yafi baki da k'arfi za kuyi tunaninsa as a hero,but idan aka yi kuskure ya had'u da wanda shi kuma yake stronger than him ya kuma fishi kaifin baki sai yayi lak'was,but to that point ba kowa ne yake iya fahimtar hakan ba,sai idan wani abu ya had'a ko lamarin ya rikid'e,tun da ya samu aka bada bailing d'insa ya fito,saboda fushi da b'acin rai da Daddy'nsa yayi a nan d'in bayan ya saka shi gaba da tambayoyin sai ya fad'a masa dalilin da yasa aka rufe shi,here he explained everything to Daddyn because he was in such a state of fear of him,ran Daddy'n ya k'ara b'aci da yake bai san da maganar yana dating wata yarinya ba until then,duka laifin sai ya d'ora shi kan Mom because a times duk wani iskancin da Aatif d'in yake yi itace take d'aure masa,ranar gaba d'aya kasa gane masa suka yi,yadda ya rufe ido ya yi musu fad'a sosai,daga uwar har d'an sunyi mamakin fad'arsa a nan dai duka suka shiga no 6 d'insu,a wannan ranar bai jira ba ya tattara Aatif ya mai da shi Amsterdam da sunan k'aro karatu,bayan yayi masa warning masu zafi akan ko da wasa yaji ance yayi wani abu kuma shi da shi ne,but sai yak'i fad'a masa hukuncin,tun daga lokacin har ya fara karatun Masters d'insa idan ya samu space yace zai zo,sai Daddyn yace a'a yayi zamansa su za su zo masa idan sun samu lokaci,a haka lokaci ya dunga tafiya ba tare da sunje ba,kuma shi d'in Daddy would not let him come,after then ya fahimci Daddy yana yi masa haka ne duk cikin hukunci amma ba zuwan za su yi ba,dole tasa shi ya hak'ura ya ci gaba da zama shi kad'ai,and he did not say that he would come again,because ya san hukuncin Daddy musamman da ya san ya yi laifi,if he made such a mistake he would do more than that,batun Nusrah kuwa tuni ya manta da shi,except from time to time yana tunawa in love with her yayi sanadin zuwansa behind the bars,har aka yi auren Nusran da Nuraz he did not know because he was not in the country.
While on the side of his parents da k'annensa mata suke zaune lafiya,sai dai bayan lokaci *MR SAJID* d'in da yayi receiving phone call from Nigeria,here his father from Gombe State ya sanar da shi y'ar k'aninsa dake zaune a k'asar yayi alk'awarin nemota,saboda Allah yayi shi mutum ne da yake son y'an uwansa,nisan da suka yi ne kawai da yanayin aiki sai rashin dace da mace yake hanashi ziyartarsu duk lokacin da yaso,sai abunda ya faru tsakaninsu da d'an uwan nasa wanda shi ne yayi silar da yasa suka daina nemansa bisa umarnin Mahaifinsun,da suka samu labarin zuwansa kuma bayan lokaci har yaje ya bada hak'uri ya nemi yafiya duk sai suka manta da wancan hukuncin aka rungume juna. And then da yake shima Mr Sajid d'in ba mazauni bane that is why they have not seen each other,but suna yin waya tun lokacin da suka dawo daga Nigeria,har aka yi sabo mai k'arfi tsakaninsu,a hakan yaje Nigeria auren Abbah,later kuma suka kawo masa ziyara zuwansu k'asar,a lokacin duk Aatif yana Amsterdam.
Daga bayan zuwansu Rafeek ya fahimci dalilin Mr Sajid na tura Aatif Amsterdam shi da Abbah suka rok'i alfarma wajensa yayi waya da Aatif d'in yace maza² yazo gida yana son ganinsa,da farko da Aatif d'in ya samu kiran daga maifin nasa yayi tunanin wani abu ya samu Mom Daddy ya b'oye masa,hankalinsa duk a tashe a washe garin ya tattaro ya nufo London,da yake babu wanda Daddy yayi magana da shi a gidan ya sanarwa Aatif d'in zai zo,lokacin da ya shigo cikin gidan jikinsa duk yayi sanyi jira yake ya ganewa idanunsa abunda yake faruwa,but yana shigowa ya tarar da gidan yadda ya sanshi,ya wuce harabar gidan bai samu wani gamsasshen amsar da yake buk'ata ba,lokacin da ya shigo parlor here ya tarar da Mom zaune ta ci uban ado ita da su Hannah,ya sauke jiyar zuciya yana rufe idanunsa had'e da saita nutsuwarsa,k'annensa duka suka yi wajensa suna murnar ganinsa,haka shima d'in sai duk ya tsinci kansa cikin farin cikin zuwan,take yaji wani irin kewarsu dake damunsa ya warware,suka yi hugging juna cikin farin ciki sannan ya nufi Mom,fuskarta da fara'a sosai tayi welcoming nasa,ya kwanta jikinta yana jinsa cikin farin ciki. (Wannan kenan...)
*****
Kwana kusan hud'u da zuwansu kaiwa family d'in Mr Sajid ziyara,labarin gagarumar dinner da Rafeek d'in yake shiryawa yaran nasa wanda ya watsu cikin arean headington da wajenta tun kafin lokacin ya risko su har gida,but agaresu kam su da suke cikin gidan babu wanda ya sani sai a ranar da Allah ya nufa suka samu labarin,duka cikinsu idan aka cire Abbah babu wanda ya fad'awa abunda yake shiryawa,wani abun mamakin kuma daga garesu ko da suka ji,suka kuma ga ba shi da niyyar su sani,sai suka yi kamar basu sani d'in ba,ranar da suka cika sati biyu da dawowa,da safe lokacin duka suna zaune a parlor bayan sun gama breakfast kasancewar weekend ko wane ma'aikaci yana gida tare da iyalinsa,here Rafeek d'in yake sanar da su maganar dinner,da kuma mission d'insa na b'oye maganar,gaba d'aya sun yi shiru saboda kowa cikinsu mamaki yake yi,Lolly ta kalleshi tana b'ata rai tace "Haba Yallab'ai akan dinner kawai shi ne kake asarar k'udi?" Ya girgiza kai yana lumshe idanunsa yace "Ba asara bane,nuna farin ciki ne" tace "ta yaya kake ganin wannan zai zama nuna farin ciki?" Yace "A haka na d'auke shi,saboda haka ina so kowa ya kalle shi a haka" cikin saurin baki tace "bidi'a ne fa" yayi murmushi yace "A'a al'ada dai" ta yi shiru bata sake cewa komai ba ganin duk abunda ta fad'a sai ya kawo nasa point d'in kuma a gaban yaran,cikin rashin jin dad'i tace "Allah ya bada sa'a" ya kalleta da sauri ganin yadda fuskarta ta canja sai duk baiji dad'i ba yace "Allah ya huci zuciyar sarautar mata,idan ran gimbiya ya b'aci ayi min afuwa,a sassauta min kada ace za'a hukunta ni bisa wannan laifin,abune da aka riga aka shirya yinsa,idan lokaci guda akace za'a fasa asarar za tayi yawa right?" Ta harare shi bata ce komai ba,yana kallon yaran nasa yace "hey child ku taya ni bada hak'uri a gurin Mummy'n ku kada tayi fushi da ni",yadda yayi maganar yana yin kalar tausayi yasa su duka yin kalar tausayi,ta kallesu duka taga kamar had'in baki duk abunda yayi suma shi suke yi,lokaci d'aya sai ta fashe da dariya,yayi dariya yana clapping hands yake cewa "yes! I did it!" Ta girgiza kai tana sake yin murmushi,daga haka suka sauya yanayin zuwa hira mai dad'i,ranar kasancewar Rafeek ya samu lokaci sosai tare da su sai yaji inama zai dunga samun time su zauna kamar hakan,hira sosai irin wacce basu tab'a yin irinta ba tsayin rayuwarsu shi suka yi,Rafeek ya sake sosai cikin iyalinsa ana wasa da dariya,yadda suke tsokanar juna suna dariya abun sai yayi gwanin sha'awa.
Misalin k'arfe 2:00pm masu shirya su suka zo kamar yadda ya sanar da su,komai na Nusrah da Nuraz a ranar ya kasance special one ne,da masu shirya sun suka iso tun da suka riketa suka fara tattala ta,ko inanta sai da suka tabbatar ya karb'i gyaran da ya dace da shi,duk wanda ya santa lokacin tun ma ba'a gama ba yadda aka maida ta,tsaf zai ce ba ita bace saboda masifar kyaun da tayi,shi kansa Nuraz a nasa gefen though ba ko wane namiji ne a nan za ka gansa da make-up ba,ranar da yake special a gurin family'n sun sai mutum ya yi da gaske zai ganeshi,wani gyaran gashin da aka yi masa,special hair barber aka kawo,tsarin haircuts d'in da aka yi masa ya tafi da mutane da yawa,ciki har da journalist da suka attending event d'in,da ake hira da Barber d'in mai suna James lokacin da ake masa tambayoyi game da sana'ar san cewa yayi bai tab'a yin irin tsarin haircut d'in ba sai ranar,da aka sake tambayarsa me yasa yayi shi al'halin bai tab'a yiwa kowa ba,yace dalilinsa kawai shi ne yana so ya samu lambar yabo irin wanda bai tab'a samu ba a b'angaren sana'ar san,da journalist d'in suka sake tambayarsa dama yana da shiri ne ko ya tab'a yiwa wani? Yace ya gwada ne a kan Nuraz d'in ne saboda yana da tabbacin zai yi masa kyau,sai kuma aka yi nasara da yayi d'in al'amarin ya zarta duk yadda yayi tsammani.
Tun misalin k'arfe 8:00pm cikin arean headington ya fara yin shiru,yayin da duk wani da yake da niyyar zuwa dinner d'in a lokacin ya kasance a cikin babban d'akin taron da aka tanada domin gabatar da dinner d'in,yadda aka k'awata gurin jami'an tsaro an yi multiplying wanda suke cikin mansion d'insu,banda security cameras dake duk wani lungu na gurin,haske kuwa a ko ina tamkar rana,jama'a sai shiga da fita suke,fararen fata da bak'ak'e,manyan mutane masu fad'a aji cikin birnin London da wajenta,abokan aikin Rafeek da wanda suke business tamkar taron dan su aka yi shi,lokacin da motar su Nusrah ta samu k'arasowa wajen wani irin escort da aka shirya musu abun sai ya bada mamaki,yadda al'amarin yake sai yasa ayi tunanin wasu jinin Queen Elizabeth ta k'asar ne za su bayyana saboda yadda ake ba su girma da muhimmanci,motocin suna yin parking daga cikin wani RR (Rolls-Royce) dake tsakiya silver aka bud'e side d'aya,Nuraz ya fara fitowa sanye da wasu irin outfit masu kala da jinsin Indians,farin skinny trouser da royal blue d'in riga mai double breasted,tsayinta har guiwarsa,anyi mata wani irin ado,daga k'asan side d'aya yayi kamar paralyse,ta gaba da bayansu security ke dafe musu,cikin takun nutsuwa ya zagaya inda take bai bari kowa ya rab'eta ba ya bud'e mata,ta ziro k'afarta dake cikin