Showing 192001 words to 195000 words out of 220972 words

Chapter 65 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1209

rik'e baby'n tana kallo yace "Ma'am ya dai kika yi shiru,tunanin me kike yi ne?" Lolly ta d'ago kai tana sakin sanyayyar murmushi tace "I'm not thinking,just praying to my kid" Abbah yace "Saboda son kai tun d'azun da ke da y'arki na fahimci kun k'i yi mana kara,fisabilillah su sauran laifin me suka yi ba kwa d'aukansu su dad'e a hannunku?" Hajiya ta karb'i zancen da fad'in "Aah toh! Nima dai na kasa gane musu,gara kai ka tambaya ko za mu samu amsa" Lolly tana dariya tace "Hajiya itafa mace ce ta yaya ne baza mufi sonta ba? Beside duk sun fita girma da nauyi sai dai ita ta fisu hak'uri,kalli fa tunda suka zo duk suke kuka amma ita baiwar Allah bacci take yi" Abbah ya kad'a kai yace "ur words are true and i care more duk ta fi y'an uwan nata hak'uri",suna nan suna ta hira har aka fito da Annie aka wuce wani room d'in da ita,they both looked over the bed da aka wuce da ita,lokaci d'aya hawaye suka kawo idanun Lolly,Hajiya da ta kula da yanayin da take ciki taji jikinta yayi sanyi bcus ta san abunda ta tuna yasa ta kuka,briefly dai ranar duk Annie bacci take tun da aka fito da ita daga theatre,yaran kam da suke kuka sosai duk suka tada musu hankali,da Nuraz suka yi maganar kukan sun Dr Paredes yasa aka musu pumping breast milk,da suka ji cikinsu ya d'auka duk suka yi shiru sai a nan hankalin family ya kwanta,bayan duk su Hajiya sun tabbatar yaran da Mamarsu suna lafiya suka yi sallama da juna suka wuce gida kowa sai labarin kids d'in yake yi....



     #Really² sorry my people,wollah all these day's my phone gotta problem,but u are always in my mind.



#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*



*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2


Pᴀɢᴇ 51.
#Hɪᴅᴅᴇɴ ᴀɢᴇɴᴅᴀ

Though Nusrah ta so wucewa gidan Annie ta kwana a can,ganin Nuraz ya bad'awa idanunsa toka ya nuna sam bai amince ba,dole ta hak'ura suka wuce gida,but tun da suka shiga mota take b'ata rai har suka shigo mansion,shi kam duk yana kula da ita sai dai bai kulata ba,from time to time ya kalleta sai yayi murmushin da shi kad'ai ya san ma'anarsa,as their car parked cikin parking lot na apartment d'insu,a fusace ta rik'e murfin za ta bud'e yayi sauri yasa lock,ta waiwayo fuskarta a d'aure kamar hadarin gabas za tayi masa fitsara,kafin tayi k'ok'arin yin hakan taji ya sauke bakinsa cikin nata and began to send her a warm kisses,as much as she could try ta kwace daga irin rik'on tsaurin da yayi ma lips d'inta though ta fara enjoying but ta kasa yin hakan,sai ta fara turashi tana k'ok'arin k'wacewa bcus ba ta so ya gane,shi kam quickly ya rik'e hannayenta and let them down,zaro ido tayi ta kwace bakinta da kyar,tana maida numfashi a wahale tace "Please let's go inside" yayi murmushi ya fara warware vail that had covered her head,ta rik'e hannunsa ganin abunda yake shirin yi tana marairaicewa tace "Please ka rufa min asiri" a kunnenta ya rad'a mata "Asirinki ya jima a rufe" ta janye kunnenta daga saitin bakinsa quickly jin a yadda yake mata magana kamar wani drunkard tace "Please hayat,ka bari muje ciki,ka ga a waje fa muke and security za su iya biyowa nan" Kafad'a ya d'age alamar ko a jikinsa,ta rasa yadda za tayi da shi ya hak'ura suje ciki d'in,gashi shi sai wani cukuikuye ta yake sake yi,ta sake sassauta murya tace "please Hayat bai kamata wani ya ganmu a haka ba ka sani" ya d'ago kansa daga jikinta looking at her with his pale eyes that began to change yace "So what idan sun gani? Ke ba halalina b'ace? Su yi ta gani mana ko a kanki nake ina ruwana da ganin su ko na ce wani ya kalle mu?' Shiru tayi bata sake cewa komai ba ganin yadda yake magana ransa a b'ace,dan kansa da ya gaji da jagwal-gwalata ya bud'e musu motar suka fita.

Da safe tun da Nusrah ta tashi ta shiga kitchen ta bada order breakfast da za'a yi musu,ta koma bedroom because she was early ready,tana shigowa taga ba shi da alamar tashi and ranar ya kasance akwai aiki because it's tuesday not weekend,har ta wuce za ta shiga bathroom ta sake dawowa,saman bed d'in ta haura a hankali ta kai hannunta za ta saka cikin curly hair d'insa daya bazo saman forehead yayi caraf ya rik'o ta,a tsorace tayi y'ar k'ara bcus bata san ya jima idonsa biyu ba,murmushi ya saki mai sauti yana ware idanunsa akan fuskarta,ta kalleshi idanunta sunyi rau² kamar za ta fasa kuka tace "u scared me fa" da sauri ya jata cikin jikinsa yana hitting bayanta da fad'in "I'm so sorry wife,i didn't know u would be scared" ta tura baki gaba tana sauke ajiyar zuciya tace "kuma tashin ka nazo yi kayi wanka shi ne kayi min haka" a nutse ya juyo da ita suka fuskanci juna looking at her beautiful face ya d'an sassauta yanayin fuskarsa yana rik'e da kunnensa yace "I said i'm sorry,if baki yi ba kuma just take revenge" ya k'arasa yana rage girman idanunsa,ta kad'a kai tana adjusting bakinta tace "na hak'ura but sai ka goya ni" murmushi yayi mata mai kyau yace "shi kad'ai kike so?" Ta kad'a masa kai,yace "Oyah! Hau muje" da sauri tana washe baki ganin ya juya tayi maza ta d'ane bayansa,murmushin gefen baki yayi ya mik'e da ita a bayansa,taku uku yayi bata san me ya shirya ba taji ya silmiyota,a tsorace jin kamar za ta fad'o ta fasa k'ara ta sake cukuikuye shi,ya fashe da dariya and backed her forward,yana kallon yadda ta kulle idanunta ya zaro ido da sauri ya kai bakinsa dai² nata ya fara aike mata da wasu irin kisses,bata yarda ta bud'e idanunta ba saboda tsoron da taji,jin saukar bakinsa cikin nata ta sake rik'e shi sosai and gave him all the help. After a long period of time yana kwance jikinta suna maida numfashi,yayi mata rad'a a kunne da sauri ta bud'e idanu ta kalleshi yayi mata wink,turo baki tayi tace "Tabbb' A'a'a na yafe" yace "Please" mutsu² ta fara yi tana fad'in "A'a'a! Allah na hak'ura" yayi murmushi yace "well! Get up na goyaki" Kafad'a ta mak'ale tace "Shima ba na so" yace "really?" Ta murgud'a masa baki tace "tou ba idan nace ka goya ni tsoro kake sawa nake ji ba" ya kad'a kai yace "Ba zan yi ba yanzun" tace "Ni dai a'a'a na hak'ura" ya murmusa yana jan tip noise d'inta yace "Gud girl,dama ba na son ina d'aukar ki da yawa,idan kika saba k'uiya za kiyi" ya k'are maganar da yi mata gwalo,sakin baki tayi tana kallonsa,da sauri ya rufe mata bakin yana fad'in "rufe bakin kada k'uda ya shige" she did as he said but didn't stop looking at him,ya sake yi mata wink a karo na biyu ya tashi,rik'o shi tayi fuskarta a shagwab'e tana fad'in "Allah Bazan yarda ba wayo kayi min nace na fasa,kuma Allah ni sai ka goya ni zan hak'ura" dariya yayi mata ya rik'o k'ugunta ya matso da ita jikinsa sosai sai da k'irjinsu ya had'u yana kallon tsakiyar idanunta ya d'age gira "waye yace kice kin hak'ura?" Tace "ai wayo kayi min nace haka" yace "kada kiyi min sharri" ta kwab'e fuska tace "Allah ni banyi maka sharri ba,ai da gadon can ma yana magana zai fad'a" yayi murmushi yana yi mata kallon k'asan ido yace "Let's ask tou" ta kallesa da sauri tace "ai dan ka san ba ya magana shi yasa za kace haka" ta k'are da zabga masa harara,murmushi yayi yana sake matsarta yace "Muje dai mu tambaya,kika sani yau yayi magana" yadda yake yi yana kallon lips d'inta da sauri ta fara turashi tana k'ok'arin zamewa,yana janye hannayensa daga jikinta ta wuce tana fad'in "Shi mutum kullum abu d'aya kad'ai ya sani." Bata karasa ba taji ya dawo da ita da k'arfi,bayanta ya had'u da k'irjinsa,ta bud'e ido za tayi k'ara ya d'ora fuskarsa gefen wuyanta yana kissing da sauke numfashi,tayi wani mugun ajiyar zuciya ta fara relaxing kanta,sai da taji yana k'ok'arin zarcewa tayi sauri ta rik'e hannunsa d'aya dake zagaye da cikinta,muryarta a raunane ta furta "please ka bari na had'a ruwan wanka time yana wucewa fa,we are about to late and u know akwai office" lumsassun idanunsa ya d'ago a hankali ya sauke su kan k'aton wall clock decorated with things like leaves,idanunsa suka hasko masa 8:20am da sauri ya bud'e ido sai kuma yayi sauri ya saketa,tayi murmushi bata bari ya gani ba ta wuce bathroom,saurin binta yayi ko ruwan bai tsaya ta gama had'awa ba ya d'auketa yasa cikin tube then ya bita,ta bud'e baki za tayi magana ya tura mata harshensa ciki yana sucking da sauri ta had'iye maganarta,yana jin tayi lak'was ya zare bakinsa,a gaggauce ya musu wanka suka fito,har suka gama shiryawa bata sake attempt na yin magana ba,ya kalleta lokacin da suke fitowa apartment d'in ganin bata kulashi ba ya tallafe waist d'inta k'asa² ya furta "Mr's I" Da sauri ta fito da idanu waje a hargitse ta furta "ka sake ni kana kallon yadda security suke kallonmu fa" ya d'age shoulder alamar ko a jikinsa,ita dai duk kunya ta cikata sai mutsu² take but bai bari ta iya k'wacewa ba har ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe,ya zagaya d'ayan side d'in ya zauna,ya fara warming motar ta bud'e ido da sauri ta furta "wait please" yayi saurin kallonta irin "what?" D'innan ta kama murfin motar za ta bud'e ya watso mata tambaya "what happened?" Da sauri tace "I just forgot something" ganin za ta fita da sauri ya rik'o d'ayan hanunta,tayi saurin waiwayowa ta kalleshi za tayi magana,ya lumshe mata idanu yace "calm down everything is in the booth" ajiyar zuciya tayi sai kuma ta furta "thank u" daga haka bai sake cewa komai ba ya maida hankalinsa kan tuk'i tana zaune gefe lokacin zuwa lokaci tayi magana sai ya d'an kalleta yayi murmushi,idan kuma ya kama dole sai ya yi magana sai yace "um'um ko ehh" har suka k'araso Nuffield health maganarsa baifi a counting ba,yana yin parking ya fito ya bud'e mata ta fito,ya wuce ya bud'e booth ya sauke basket manya biyu da wani madaidaici,ta tsuguna kad'an za ta d'auki babba yayi sauri ya dakatar da ita da fad'in "um'um! Take that one wannan yana da nauyi,and na san ki da son jiki ba iyawa ma za kiyi ba" d'agowa tayi tana sakin murmushi ya d'age gira yace "what?" Tayi murmushin yak'e ta d'auki wanda yace d'in da fad'in "dama dan naji me za ka fad'a ne" ta wuce da sauri tana masa winking,yayi murmushi yana kad'a kai ya d'auki sauran kayan yabi bayanta.


Suna shigowa ward they see Bareerah coming out of the room da Annie take da alama kamar akwai wanda take nema,but har suka k'araso bata gansu ba sai da Nusrah tace "Bareerah Aunty! Who are u looking for?" Quickly ta waiwayo tana sakin murmushi tayi sauri ta matso inda suke za ta karb'i basket a hannun Nuraz tace "wollahi Abbah na fito nema,yanzun yayi waya yace suna hanya tare da bak'i,ashe basu k'araso ba" Nusrah tace "Ohh! Maybe yanzun su shigo" bata gama magana ba,Bareerah ta hango shigowarsu with about 10+ people,ta bud'e ido da sauri tace "ga su suna shigowa ma" Nusrah tace "Ohk let's wait them to come in,my hand starts to held" Nuraz kam tuni yayi gaba,Bareerah tayi dariya jin abunda Nusrah tace,tace "ke dai babyn Annie duk kin zama raguwa,anya bamu kusa samun baby ba?" Nusrah tayi murmushi shyly tace "Kai Aunty i have nothing fa" daga haka tayi gaba k'asan zuciyarta tana addu'ar Allah sa abunda Bareerah ta fad'a ya zama gaske,surely da ta kasance cikin infinite joy,haka kawai sai ta tsinci kanta da shafa cikinta a fili tayi furucin "I wish maganarkin nan ya tabbata,i know Hayat would be more than happy,dama ya fi ni damuwa da maganar cikin",tura k'ofar tayi tana sakin murmushi da sauri kuma ta mak'ale a tsaye tana kallon Annie dake jingine da bed tana feeding baby,wani k'ara tayi like a rattle da d'an gudu ta k'arasa ciki tana ihun murna,Annie ta bita da kallo tana sakin murmushi,Lolly da su Hajiya began to laugh at her for being so young,placing the basket dake hannunta towards the bed ta nufi gadon,kusa da Annie sosai taje ta zauna ta fara lek'en fuskar baby'n,sai kuma ta tab'e baki ganin ba baby girl d'in bace da fad'in "Annie! I like that baby girl" Hajiya tayi murmushi tace "sai ki yi k'ok'ari ki haifo mana" turo baki tayi tace "tou ni Hajiya y'ar k'arama da ni sai na haihu yanzu?" Hajiya glanced at her tace "kuji min ja'ira idan banda Allah bai nufa ba,ai yanzun da kin haihu ma ko kin kusa" turo baki ta sake yi tana k'unk'uni duka suka saka mata dariya,Annie tayi murmushi tana cire breast d'in a bakin baby'n tace "Don't worry baby u will not have to give birth until kin k'ara girma" ta washe baki tana dariya Nuraz da hankalinsa ke kan phone kamar bai ya jinsu ya furta "Uhn! Sai dai idan ba kya gidan ko?" duka suka kallesa,jin d'akin yayi shiru da sauri ya d'ago,yaga shi suke kallo,sai ya sauke kansa yana sakin murmushi dai² lokacin da su Abbah suke shigowa,he is at the forefront sai Baba da wasu mutane mata da maza kyawawa dasu,dukansu da suke cikin d'akin suka bisu da kallon rashin sani but no one showed it clearly until their sallama were answered,fuskar Abbah a sake yake fad'in "Bismillah ku k'araso ku zauna ga guri" dukansu dai gwanin burgewa daga mazan har matan kana kallonsu za ka tabbatar akwai jin dad'i tare da su,and idan batun naira ma ake yi itama ba bak'on su bane,bayan sun zauna and greeting each other in a friendly manner,Nuraz da ya tashi ya basu waje suka zauna ya kalli Nusrah kad'an fuskarsa a had'e ganin wani cikin samarin da suka shigo ya kura mata ido sai kallonta yake,fuskarsa babu walwala ya furta "Annie bari na lek'a office na dawo amma ba jimawa ma zanyi ba" Annie ta kad'a kai tayi masa addu'ah fuskarta a sake,har ya juya ya fara tafiya yace "Roohii! Zo muje office mu dawo" ta d'ago a shagwab'e babu kunya za tace ya barta ita dai yaje ya dawo Bareerah tayi mata ido,sai ta mik'e a hankali tana turo baki tana cewa "Hajiya mun tafi sai mun dawo" Hajiya ta raka Nusrah da ido tace "Oh! Ji min gulma,ni wannan sakaliyar matar tasa wai nan wani sabon iyayi zata ma mutane harda tura baki ita dole ba ta son zuwa ne ko me?" Lolly tana dariya tace "Kai Hajiya tou kiyi musu addu'ah,kina gani ma daga ke sai Annie kad'ai suka iya yiwa sallama" Hajiya ta tab'e baki tace "Tou Allah dawo daku lafiya,idan sun bada sallama kuma sai ku tarar da mu can gidan" Nusrah tana dariya ta d'agawa Lolly hannu tace "Bye Aunty" ta k'arasa fita a room d'in da sauri,a tsaye ta gansa yana jiranta fuskarsa cif babu fara'a,yana ganin ta tsaya rike da k'ofar bata rufe ba ya rik'o hannunta da sauri ya k'arasa rufewa,Nusrah dai ta bisa da kallon mamaki because ita dai ta san lafiya k'alau suka fito daga gida,yanzun kuma ta ga mood d'insa was changed,suka fara tafiya yana rike da ita a jikinsa,suna fita daga room d'in already Hajiya ta ga abunda ya faru ta furta "Magulmata biyu" Baba yace "A'a dai Hajiya kada ki tab'a min mata a kan idona" hajiya tace "Mata!? Wannan d'in?" Baba yace "K'warai kuwa baki ganta kyakykyawar gaske ba? Wannan da kike gani ko cikin jinsin aljanu ba za'a samu kamarta ba" gaba d'aya aka yi dariya,Hajiya ta tab'e baki tace "haba dai yo ko ni tsohuwa ma ai nafi wannan kyau" Annie dake k'ok'arin bawa Bareerah baby tace "A'a fa Hajiya ni dai kawai na gane kishi kike yi da babyna ta kwace mijin" Hajiya ta kyab'e baki tace "wane mutum,ko ta kwace ma zai dawo ne,aro na bata",bayan an tab'a barkwanci sosai Baba yayi sallama duka suka amsa,in a serious tone yace "Alhamdulillah alaa kulli halin" sai ya kalli Abbah yace yayi addu'ah,bayan Abbah ya gama kwararo addu'o'i,Baba ya waiwaya ya kalli Annie yace "MARYAMU!" Annie ta d'ago da sauri ta kalleshi,taga yana yi mata murmushi,bata san na mene ne ba kawai sai ta mayar masa,Babah yana ci gaba da kallonta yace "Kin san wad'annan bayin Allah'n?" Ya nuna mata su duka,haka Annie tayi ta kallon fuskokinsu but ta fi kallon mutum uku daga cikin matan y'an dattijai da suke zaune kusa da Hajiyar su Rafeek,kai ta kad'a a hankali bayan ta gama kare musu kallo bata gane abunda Baba yake nufi ba ta furta "A'a Baba ban gane su ba" su duka suka yi mata murmushi,a hankali Baba yace "Tou kema baki sansu ba ina kuma ga HAUWA'U?" Annie ta sake k'ura musu ido tana kallo da tunanin inda ta san wani fuskar mai kama da nasu,within thirty seconds ta bud'e ido sosai ta furta "Na tuna!" Baba ya kalleta yana murmushi yace "me za ki iya tunawa game da su?" Hawayen da suka kawo idanunta suna saukowa ta furta "Su ne da gaske Baba?" Lolly tayi saurin kallonsu ta kalli Annie tace "Annie! Su d'in su waye?" Sautin kukan Annie ya fara fitowa tana kallonsu har lokacin tace "K'annen Innarmu" a rikice Lolly tayi saurin mik'ewa tana yi musu wani irin kallo,da sauri kuma sai ta koma kusa da y'ar uwarta ta dafa kafad'arta da fad'in "Da gaske su ne

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login