Showing 210001 words to 213000 words out of 220972 words
ya dawo tunaninsa ya sauke glasses d'in,ganin Mummy'nsa ce ya lumshe his red eyes with signs of distress,Mommy ta bisa da kallon tsanaki kafin ta yi magana ya fara k'ok'arin bud'e motar ya fito,ta matsa a little bit ya sakko,tana ci gaba da kallonsa har sannan tace "lafiyarka k'alau kuwa Aatif?" Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba,sai can ya d'an k'irk'iro murmushi yace "I'm fine mom" ta girgiza kai tace "u know i won't agree,say something different than that" saurin kallonta yayi yana lumshe ido ya rik'o hannunta a little and adjusted his stance,Mommy duk ta zuba masa ido tana kallonsa jira take taji me zai fad'a,yayi shiru yana tunanin yadda zai iya fad'a mata,a hankali Mommy ta shafa kansa fuskarta d'auke da wani expression wanda a fuskar mahaifiya kad'ai ake ganinsa idan taga yaranta a damuwa tace "ko dai muje ciki muyi maganar ko kuma idan mun dawo?" Ajiyar zuciya ya sauke ya kad'a kai a hankali da fad'in "Idan kun dawo d'in" Mommy tace "alright! Maza je ka kwanta ka huta" d'an murmushin yak'e ya k'irk'ira and gave her a side hug then ya fara tafiya,Mommy ta bishi da kallon tausayi har ya shige cikin gidan ya barsu tsaye a compound,bata iya motsawa a gurin ba sai da Hannah ta matso ta rik'o hannunta,da sauri ta sauke ajiyar zuciya tace "muje kou" Hannah ta kalli Mommy tace "but Mommy kamar Yah Aatif yana cikin damuwa fa,ko za ki fasa zuwa sai mu tafi mu?" Murmushi tayi tace "No! Let's just go,he said we'll talk when we get back" a hankali Hannah ta kad'a kai tace "tou mu tafi."
Da daren ranar bayan sun dawo suna zaune Mommy ta kalli Aatif who's lying on the rug ya tada kansa da hannu yana kallon ceiling,tayi shiru tana kallon how deep he was cikin duniyar tunani tayi calling sunansa out "Aatif!" A hankali yayi blinking madaidaitan idanunsa and letting out a sigh of relief,Mommy dake kallonsa tace "wai ba da Aatif nake magana ba,kayi min shiru?" Kansa ya d'an juya yana tsuke baki yace "I'm sorry Mom" siririn tsaki tayi tace "za ka tashi ka min bayanin abunda yake saka damuwa kwanakin nan ko kuwa?" Fad'uwa yaji gabansa yayi a hankali ya mayar da idanunsa ya lumshe yana sauke numfashi,yadda yayi shiru ya rufe idanu angrily Mommy tayi k'wafa da fad'in "u are very stupid,ina magana ka kulle min ido,ni sa'ar kace ko meye ne wannan sabon iskancin kuma?" Saurin tashi yayi ya zauna zai yi magana Mommy taci gaba da fad'a "irin wannan abubuwan da kake yi su suke sawa Daddy yake ganin kamar ni nake cewa kayi,kana d'aukan alhakina da yawa fa Aatif,but ban sani ba ko soyayyar da nake nuna maka yasa kake min haka ko kuma abokiyar wasanka ka mayar da ni,ka shiga hankalinka da ni ina fad'a maka,otherwise kuma za'a ji kanmu da kai a gidan nan" tunda ta fara fad'a ya sunkuyar da kai,bai yarda ya d'ago ba sai da yaji ta yi shiru sannan ya d'ago a hankali cikin cool voice yace "I'm sorry Mom,ni ba wani abu yake damuna ba,i'm just trying naga cousin sis da Noor sun daina fushin da suke yi,i know i didn't give a damn about what had happened,wannan shi ne kawai damuwa na,after that babu komai and i'm not hiding anything from u" wani kallo Mommy tayi masa mai cike da tsantsar tausayi,kafin tayi magana aka bud'e entrance aka shigo,duka suka waiwaya suka kalli Daddy dake shigowa fuskarsa d'auke da wani irin murmushi suka yi masa barka da dawowa,ya amsa yana zaunawa next to Mommy dake saman armchair,no one expected yaji maganar da suke yi sai da yayi murmushi ya kira Aatif "Aatif" da sauri Aatif ya sauke kansa k'asa yace "Na'am Daddy" Daddy yace "sure yanzun na yarda hankali ya shiga cikin kanka,tunda har kake realizing u have made a mistake,but abunda zan fad'a maka shi ne ka samu time kaje ku zauna da su sai ka basu hak'uri,ina tunanin idan ka yi haka za su fi d'aukan lamarin da muhimmanci" nasiha sosai Daddy yayi masa and gave him more explanation of how to apologize,yayi wa Daddy godiya then ya tashi ya wuce bedroom d'insa,da ya shigo zama ya fara yi bakin bed yayi shiru remembering of their relationship with Nusrah har yadda suka rabu,lokaci d'aya wasu irin hawaye suka kawo idanunsa because he never thought that after their separation zai shiga damuwa,sai daga bayan lokacin yana Amsterdam wani irin soyayyarta yayi ta d'awainiya da ruhinsa by then lokacin da ya shirya yiwa Mummy'nsa bayanin komai har ya gama tsara yadda zai nemi Nusrah su dai²ta kwatsam sai ya samu labarin aurensu da Nuraz,a hankali ya koma ya kwantar da bayansa saman bed d'in while k'afafunsa suna k'asa,ya d'auki tsayin lokaci a hakan kafin da kyar cikin wani irin muryar damuwa ya furta "Yah rabbi kasa zab'in da kayi min a yanzun shi ne mafi alkhairi a tare da ni,ya Allah ka basu zaman lafiya su kuma,ka raya abunda ka azurta su da samunsa" yana kwance almost an hour shiru yana tunani,da yaga damuwa yana neman yayi affecting kwakwalwarsa da wuri ya tashi ya d'auka phone d'insa dake gefensa ya fara kiran line Deeja,suka yi hira sama² but basu wani jima ba suka ajiye because he's not in a good mood,but duk da hakan ya ji dad'i and ko babu komai damuwar dake mak'ale a ransa ta ragu.
*****
Cikin haka kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa,yayin da tun ana saura kwanaki biyu suna aka fara shirya k'ayataccen dinner na taron suna,ai kam nan cikin Oxford city da wajenta ya amsa aka san za'ayi gagarumin hidima,ranar event d'in kuwa duk inda ba'a san da batun bama sai da aka san da shi,da daren ranar kamar yadda aka shirya da misalin 8pm bakin hall da za'ayi shagalin ya cika da manyan mutane,masu zuwa Allah sanya alkhairi da y'an ganin k'wak'waf duk sun hallara,ni dai na kalli yawan mutane nace "ji mutane da shishshigi ba'a gayyato su bama sai da suka zo" to y'an mata kuwa dama ina ganinsu na san me ya kawo su,kun san dai karatun ba sai na ce komai ba,ba ruwa na... (Lol) daga cikin hall d'in na fara zuba ido wanda ya cika,ai kam nan na hango tawagar d'an mace fan's,su kad'ai da na gani sun cika gurin i was so surprised,ina kallon su baki bud'e nace "O'ohhh su kuma ta ina suka zo k'asar ban samu labari ba?" Ni dai ina tsaye rik'e da baki naji an dafa shoulder na,na waiwaya da sauri naga waye here my eyes fell on lil habibtiiys real Hafsy,Mamah Zee together with Teemah abdulmajid,dukansu suna kallona da wani irin murna and giving me a beautiful smile sun ci ado kamar ka sace su ka gudu,na sake baki ina kallonsu da mamakin ganinsu a gurin,ihun su ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi,a guje suka rungume ni suna fad'in "habibtiiy wollahi we miss u,daga zuwa d'aukan rahoto sai ki mak'ale a Oxford kuma? Ko dai jira kike sai Mr Noor ya aurar da Maysam sannan za ki dawo?" Nayi dariyar yak'e ina kallonsu nace "ku rufamin asiri,ina ni ina zama kuma? Nawa *HABIBIIYN* na kai shi ina?" Muka yi dariya duka ina kallonsu har lokacin cike da so,da sauri kuma sai nace "Wait a minute,ta ina kuka zo k'asar nan?" Dariya suka kwashe min da shi suka had'a baki a tare da fad'in "O'ohhh! Haba sis muna da ke zuwa UK ai won't be difficult for us and ko ba haka ba Mr Noor jirgi guda yasa aka ajiye saboda masoyansa na *'DAN MACE FAN'S"* na yi murmushi ina sake ware idanuna nace "kunji masu shi wad'anda basa tsoron talauci,yo ta ina ma za suji kyashin kud'in tunda an tara su ana kuma kan tarawa? Allah dai ya k'arawa Annabi daraja,ya kuma azurta mu,arziki mai amfani."
Alhamdulillah anyi taron suna lafiya together with ceremony na bud'e new ship owned by Mr Rafeek,an ci an sha kowa yayi farin ciki,duk da yake ba wasu jama'a ne na daban ba a gurin,family ne sai abokan aiki da kasuwanci,after the ceremony na bud'e ship followed by a dinner da aka shirya na taron suna,sosai dinner da akayi ya k'ayatar komai anyi shi cikin ilimi da wayewa,irin kyaututtuka da baby da parents d'inta suka samu kasancewar family'nta babba da ake ji da shi,labarin bai tsaya iya Oxford kad'ai ba because her grandfather and mahaifinta da suka kasance famous,wanda shaharar su tasa aka san da zamansu ba a iya single line ba duniya ma tana ji da su,fad'ar irin shagalin da aka yi a wannan daren zai kasance kamar b'ata baki,bayan an gama dinner bak'i da duka wad'anda suka samu damar halartar zuwa gurin sun koma gudajensu,gidan sai ya sake dawowa kamar da can daga su sai family,securities da maidservant da suke zaune tare,yanayin kulawar da Nusrah take samu a yanzun a gurin Hajiya da su Annie herself sai da ta san yes ta karb'i gyaran da a duk ranar da Nuraz ya bud'e treasury d'in zai kwashi ganimar da sai ya kusa haukace mata.
*FEW YEARS LATER...*
Rayuwa ya mik'a yayin da a gefen Hajiya Karima da Gwaggonta Hajiya mariya at this time da al'amura suke sauyawa ake sake samun ci gaba,su kam a garesu za mu iya cewa era d'in ci baya ne ya kama musu because tun a bayan faruwar al'amarin wancan ranar rayuwa yayi musu wani irin juyi,a hankali komai ya fara juya musu baya komai sai neman fin k'arfinsu yake,they are once again in the throes of poverty that did not have in the past,ko a lokacin da Hajiya Karima take kan zawarci duniyar take kan gara musu,uwa uba kuma yanzun da ya zama Hajiya Karima was suffering from dementia wanda ko kad'an ba ya jin magani,sannan ita kanta Hajiya Mariya d'in ba wai tana da cikakkiyar lafiya ba ne,she's helpless,malnourished,restless,damuwarta kuwa akan halin da Karima d'in take ciki sai ya janyo jininta yayi mugun hawan da ita kad'ai ma saboda stress da suka yi mata yawa,sai kaga tana surutu ita kad'ai like she had just passed by,d'an gidan da suka tsira da shi suke zaune kuma bayan lokaci unguwa gaba d'aya ta san halin da suke ciki da abunda suke aikatawa,a nan duka jama'a suka sake tsangwamar rayuwarsu,lokaci kad'an kowa ya canja musu fuska a unguwar,dama kuma ba da kowa suke shiri ba sai wanda suka zab'a,basa mutunci da kowa,Hajiya Amina ma da mijinta ya samu labari ya rabasu don yace baza ta je ta janyo masa wani masifar ba yana zaman lafiya,wannan dalilin yasa dole suka hak'ura suka siyar da gidan suka canja unguwa,a hankali lokaci yana sake tafiya hauka tuburan akan Hajiya Karima,d'an asibitin da suke zuwa shima dai tuni suka watsar because an kasa gane inda ciwon Karima yake,in less than five years duk sun zabge sun lalace,sunyi wani irin duhun da it is not possible ma for anyone ya sansu ya ganesu,abinci da sauran kayan more rayuwa duk babu,sai Hajiya Mariya taje bara take samo musu abunda za su ci,zuwa gidan su Nusrah kuwa tun bayan da al'amarin ya faru da suka yi yawon neman magani basu dace ba,at that time da things that started to become worse Hajiya Mariya tayi ta yawon zuwa neman Abbah sai ta iske labarin basa zama a k'asar ma gaba d'aya but they only came to visit occasionally,ko Binitta ma da Hajiyar ta tambaya tana ina? Get man d'in gidan ya sanar mata tana tare da su Abbah a can k'asar waje,yanzun shi kad'ai ne da matarsa da yaransa,Abba yasa ya dawo dasu nan saboda kada a bar gidan haka ya samu matsala.
Dama ita rayuwa haka take,if u sow goodness sai kayi reaping mai kyau a gaba,yayin da k'arshen duk wani mai makirci kuma if he doesn't repent ya bi Allah yadda ya dace ba,shi kam wannan kowa yasan makomarsa,here sai muce Allah ya tsare mu da munanan d'abi'u,Allah ya k'ara tsare mana imaninmu,ameen.
*****
Tsayin shekarun da suka gabata,tuni aka yi auren su Deejat da AATIF,su AFAF da KALTHOM ma duk anyi aurensu,sai dai su da yake dama Nigeria aka kaisu can suke zaune a Bauchi state,yanzun haka duka da yaransu,yayin da Aatif yake da two kids duka mata,d'aya yasa mata sunan Mummy'nsa suna ce mata Aairah sai mai sunan Mummy'n Deejat da take shayarwa ita kuma suna kiranta Beena,Kalthom also had two children but ita duka maza ne Abdullah da Abdulmalik,sai Hannah mai y'a d'aya sunan Aunty Khadijah k'anwar Inna amma suna ce mata Afreen,sai Afaf itama dake da y'arta mace da tsohon ciki,itama dai sunan Aunty Asiya ne aka sa mata amma Seeyama suke kiranta. That's how life goes on ka tashi a wani gurin sai rayuwa yayi maka changing gurin zama,su Afaf da suka tashi ba'a nigeria ba duk da yake itace asalinsu,yanzun gashi dalilin aure sun dawo zama cikinta,while Nusrah kuma da suka rayu a cikinta sai ga zaman ya mayar da su wani gurin na daban,ita ni'imar Allah dama yawa ne da ita,sai a dunga yi maka ganin ba komai ba,wata rana kuma Allah ya maida kai sarki,yanzun kam a kind of care Deejat take samu a gurin Mummy'n Aatif tun bayan da zama ya kawota cikin gidan will make u unable to determine itace ko dai wata na daban aka yi,all because of the way she regained her pride,ta bi ta rik'e family'nta da na Mr Sajid suna zumunci sosai,duk abunda ya taso kuma suna kan hanyar zuwa,sannan amincin dake tsakaninta da su Annie kamar dama can sun jima tare,sun had'a kai sun koma tsintsiya mad'aurin ki d'aya,yayin da suka rik'e yaransu a tsakiya,they forgets and forgive of all the events that take place and now everyone is in a relationship with each other.
*****
A gefen Bareerah ma dai ba'a barta a baya ba,dan a yanzun haka she was already married to a friend of Abbah,lokacin duka da ya ganta a wani zuwan da suka yi ziyara Nigeria,nan ya sanar da Abbah because a lokacin matarsa had recently died shi kuma yaji yana son yin aure saboda yarinyarsa d'aya da bai aurar ba,shi ne yayi magana da Abbah,shi kuma sai ya samu Annie da batun,da farko Bareerah ta so tak'i,but da su Annie suka sakata gaba da shawarwari tare da Lolly da Mommy suka yi mata nasiha suna fad'a mata ai she was not too old to get married,while ita a nata hangen tana ganin ta d'ebi shekaru tana tare da su a matsayin widow and she had never met any person da yace zai aureta until then,Annie dai bata yi k'asa a guiwa ba tayi ta bata examples har da kanta ma because a shekaru ma bata kai Annie ba,so here they calmed her down ta yarda karb'i batun auren,babu b'ata lokaci aka yi aurenta yanzun haka tana zaune a Kano cikin rufin asirin Allah,su Annie su suka yi mata komai na kayan d'aki,ranar da aka kaita kam da taga irin gidan da Allah ya nufeta da zama,nan tayi kuka sosai because she couldn't think of live in such a privileged and prosperous life. Tunda ta shiga gidan kuma da yake mutumin da yake aurenta yana da yaransa 5 da matarsa ta mutu ta bari,though duka manya ne ba yara ba,dan har ya aurar da hud'u ma cikinsu mata biyu da manyan yayansa maza biyu,babban duka bazai wuce sa'an Nuraz ba,da yake kuma yaran sun samu tarbiyya mai inganci sai suke ganin Bareerah matsayin mahaifiyar su,while she herself also ta d'auke su ta rik'e a matsayin y'ay'a.
*****
On Binitta's side ma dai yanzun za muce ne Alhamdulillah,because since that incident ya faru bayan dawowarta UK,their relationship with Annie da irin mu'amalar da Annie take yi mata,has attracted her to the point ta musulunta,because Annie ta kasance mace ce mai yawan alkhairi and ibadah sam baya tsere mata,a yanayin mu'amalar ta da mutane kuwa tsakaninta da duk wasu wanda suke k'ark'ashinta mutuntawa ne,babu tsana/tsangwama,or even nuna bambancin addini,wannan dalilin shi ne yasa Binitta taji lallai tana sha'awar kasancewa cikin addinin Islama,ba'a wani d'auki lokaci mai tsayi ba ta karb'i addinin gaskiya,and now her name has changed from Binitta to Fatima,itama dai shekaru biyu kenan da tayi aurenta da wani baturen k'asar,but shi asalinsa musulmi ne and she now has her daughter Fadeela.....
#In any case dai sai muce Alhamdulillah...
*#Let's meet in the final chappy...💥*
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
Pᴀɢᴇ 54.
#Fɪɴᴀʟᴇ
K'aran takun takalmin Nusrah dake tahowa za ta shiga cikin study room opposite da na Nuraz,yasa baby Maysam y'ar kimanin shekaru hud'u da wasu watanni tashi da gudunta daga kan manyan books that she was assembling and tore up a pile of papers tana wasa da su,cikin rashin sa'a kuma kafin ta kai ga b'oyewa tuni Nusrah ta hangota kasancewar the building was made of bright curtain glass,za ka iya ganin na ciki shima zai ganka,da sauri Nusrah ta zaro ido hango Maysam wacce ke sanye da jumpsuits suspender trouser na yara black d'in trouser da pink d'in riga,her hair da akai split into two was tied with a pink ribbon ta yi bala'in kyau sak yarinyar turawa,tun kafin Nusrah ta k'araso ta kwala kiran "Maysam!" In a terrified voice that caught Nuraz's attention lokacin da yake shigowa cikin apartment d'in,a tsorace Nusrah ta wuce cikin sassarfa because ba'a jima ba ta saka bookmark ta fita,a time d'in she was doing research on their part (cardiologists) wani uzurin ya fitar da ita,Maysam who was trying to hide a k'asan table jiyo muryar Nusrah tana kwala mata kira bata san lokacin da ta