Showing 27001 words to 30000 words out of 220972 words

Chapter 10 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1158

"Kika ce mene ne.!? Ba'a binne ruhinki ba.? Idan ba shi d'in aka rufe a gidan mu ba zaman mene ne kika ci gaba da yi daga lokacin dana furta cewa na yanke alak'ar dake tsakanin mu.!? Why don't u leave us.!?"
Ya k'arashe yana zare ido da d'agawar sauti,murmushi tayi mai ciwo
"Wannan kuma ba ruwanka bane,zama na ko tafiyata duk basu shafi mutum ba.."

"Sun shafe ni,,cos nan gidan mu ne kuma gidan mahaifina na asali,me zai sa ke baza ki gwada komawa naki asalin ba.!?"

Kallonsa ta sake yi ya d'aga mata gira d'aya "Yeah I mean it.! Ki gwada mana.."
Sauke kai tayi k'asa bata ce komai ba sai dai taji k'irjinta ya fara zafi,Rafeek cikin wani irin murya yace
"I knew baza ki tab'a iyawa ba,wannan gidan naku dai mai kama da village's graveyard babu yadda za'ayi na yarda zaki iya komawa cikinsa.."
Yayi mata murmushi yana shafa sumar kansa,a d'an fusace ta kalleshi
"Kada ka sake ko da wasa ka zagarmin asali na,,gidan mu it's for us ni da y'an uwana da shi muke alfahari,haka kuma naku it's urs,so kowa ya zauna iya matsayinsa,ni bance ka zagarmin asali ba,kuma naga ai nan d'in da kake magana bani na zaunar da kaina ba.."

"Wane ne ya zaunar dake idan ba son duniya ba.? Gidanku a yanzun baza ki iya rayuwa cikinsa ba,saboda kinga duniya kin shiga inda yafi naku,me zai sa ki koma can ko ba haka bane.!?"

"Ba haka bane,amma idan amsar kake nema kana iya zuwa gurin mahaifiyarka ka tambaye ta dalilin da yasa na kasa tafiya,har yanzun nake zaune muku a gida.."
A fusace tana kaiwa nan ta juya tayi hanyar fita,da sauri ya rik'o hannunta,kamar wacce aka dannawa pause ta k'ame a gurin da mugun mamakinsa
"Baki isa ki fad'a min wannan maganar na bari ki fita ba,dake nake yi so ba ruwan Hajiya ta a ciki,tunda ke kika fara dole ke zaki k'arasa."

"Sake min hannu..!"

"Bazan saki ba sai kin fad'a min abunda nake son ji.."

"Rafeek ka sake min hannu..!"

"Bazan saki ba."

"Na ce ka saki." Ya maimaita "bazan saki ba" bai k'arasa fad'a ba tana juyowa ta wanke shi da lafiyayyen mari idanunta cike taf da hawayen k'unci but sai ta kasa furta ko 'A',shi kansa a bazata yaji marin ya sauka saman kyakykyawar fuskarsa cikin wani irin b'acin rai yana kallonta yace "ni kika mara.!?"
Bata d'ago ta kalle shi ba ta juya da sauri ta d'auki d'anta tasa a kafad'arta zata fice a d'akin yayi saurin sake tare ta
"Ni kika mara Hauwa."
Still bata d'ago ba zuwa lokacin hawaye sun fara sakko mata,cikin wani irin mutuwar zuciya dana gangar jiki tace
"Ka bani hanya na wuce.."

"Ki wuce zuwa ina.!?"
Bata tanka masa ba ta d'auke kai tana goge hawayenta,hak'oransa ya datse muryarsa a k'asa ya fara mata magana cikin kaushin murya
"Though banzo da niyyar zama k'asar nan ba,dole na ne a yanzun na rabaki da asali na kafin ki gurbatamin su,,ke idan banda kaddara mai zai had'o mu da ku.? Ki duba irin bambancin dake tsakaninmu mana,sam bamu yi deserve da juna ba,har yau ina tunanin dalilin da yasa iyayena suke sonki,and ban san mene ne Abba ya gano na musamman a tattare dake ba,,amma tunda Allah ya raba mu,kije can kiyi rayuwarki,sai dai ina sake jaddada miki mari na da kikai sai ya saki shiga masifar da baki tab'a tunanin zata same ki ba,,,and then matuk'ar baki yi niyyar komawa gidanku ba,ina tabbatar miki saina wulak'anta rayuwarki,wulak'anci irin wanda baki tab'a tunanin wani bil'adam zaiyi miki shi a tsayin rayuwarki ba.."



*#Yah Allah save dis innocent soul..😢 Rafeek ya k'ullo makirci..*



#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥


*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2


Pᴀɢᴇ 9.
#Eᴠɪᴄᴛ

*Am back again.. Babu abunda yafi dad'i a duniya sama da samun masoyin gaskiya,,as u requested me to apologize to u my special friends,na yi hak'uri da yardar Allah,and if God please permits i'll continue sending u as usual,sai dai not really anywhere saboda wasu uzurori nawa,hope u people will help me in sharing,but by Allah's favor if such a problem arises again God knows the truth ba za ku sake jina ba,sai dai for those of us who are on the Wattpad software,then daga lokacin kuma i'll be out of any group,ku sani when ever i leave the group there's no coming back..Chanjin da kuka fad'a daga yanzun ya kamata na fara ganinsa if i don't see any changes kuma i will fill my trouser with air..🏃*

💕

Yana gama fad'a ya barta nan tsaye cikin halin damuwa da fargabar maganganunsa,a zahirin gaskiya tunda ya fita ya barta ita kanta ta fara tunanin komawa gida,to amma wace hanya zata bi ta sanar da su Hajiyarsa abunda ke damunta ba tare da sunyi saurin gano dalilin zuwan Rafeek ne take son tafiya ba.? Har ga Allah maganganunsa sun duki zuciyarta shi yasa tun da wuri ta fara tunanin tafiya ba tare data bari wani ya fahimci nufinta ba,but idan ta tuna Hajiya kuma sai tace "To ni yaya zanyi ne na bar gidan nan bata sani ba.?" Ko kuma "Anya idan na tafi babanmu zai kyaleni na zauna tare da su.?" Irin wad'annan tunanukan da tambayoyin sune suka fi damun zuciyarta,a gefe guda kuma tunanin kalamansa bayan muguwar damuwar da take tare da ita kafin lokacin,cikin y'an kwanaki da zuwan Rafeek gidan,a hankali al'amura suka fara sauyawa idan yana gida gaba d'aya Hauwa bata da sukuni,tun Hajiya na yi mata fad'an ta daina sa damuwa a ranta tayi hak'uri da duk abunda ya faru har ta hak'ura ta kyaleta,a b'angaren Rafeek tunda ya fahimci idan yana guri bata da sakewa sai ya maida zaman gidan kamar ibada,idan ya fita baya jimawa yake dawowa,yayin da a gefe guda b'angarensa da mahaifansa babu wanda ya san yaya suka k'are ta da su tun bayan d'an fushin da suka yi na kwanaki,lokaci guda aka wayi gari aka ga sun gyaro alak'arsu har zaman hira suke,su yi wasa da dariya abunsu kamar da,wannan dalilin yasa damuwar da Hauwa take ciki ta sake yin yawa gashi babu mai d'an shiga gurinta yanzun ya d'auke mata kewa.

Satin Rafeek biyu da zuwa gidan al'amura marasa dad'i suka ci gaba da faruwa tsakaninsa da Hauwa,a gefen iyayensa kullum cikin rufe su yake da kyawawan halayensa yana nuna musu shi d'in na gari ne kamar yadda suka sanshi kuma suke so ya kasance,ko wane lokaci yana kan kyautata musu da faranta musu sab'anin idan sun had'o hanya da Hauwa cin mutunci da muzgunawa had'e da kausassun kalamai ke raba su,a cikin hakan ba tare da sanin kowa ba ko neman shawara cikin irin rufin asirin da Allah yayi masa yayi musu Visa zuwa Saudi Arabia suyi umrah a ransa ya k'udurce daga wannan tafiyar baza su sake dawowa Nigeria ba,tafiyar duka cikin sati guda aka tsara yinta,da yake aikin kud'i ne nan da nan aka yi komai aka gama,tunda maganar tafiyar sun ta bayyana a ranar lokacin ana ta sallama da su,kafin su wuce airport Hajiya ta had'a su duka tayi musu nasiha mai ratsa zuciya,jikinsu yayi sanyi musamman Hauwa da kana kallonta zaka san tana tattare da damuwa,irin wacce da za'a tambayeta tabbas zata ce Hajiya ta fasa zuwa,aka gama sallama da su driver ya wuce da su airport,gida ya dawo daga Hauwa sai Maimunatu,Rafeek da maidservant d'insu sai mai gadi dake can bakin get,,a wannan ranar tun daya kasance babu iyayen Rafeek a k'asar,hankalinsa kwance da dare bayan an idar da sallar isha'a ya shigo gidan ya wuce su a parlor yana murmusawa,Hauwa da ta bishi da kallo haka nan take jin zuciyarta na fad'a mata lallai akwai wani bak'on alamari da zai faru da ita,lokacin bacci ya yi Maimunatu tayi mata sallama ta wuce,har suka shiga d'akin Maimunatu bata sani ba sai data juya zata rufe k'ofa taga Hauwa biye da ita,a tsorace ta bita da wani irin kallon mamaki
"Baki kwanta ba dama.?' Ta tambaya soundly muryarta da alamun tsoro,da kai Hauwa ta amsa mata ta wuce tana niyyar kwanciya a saman gado,Maimunatu tayi saurin matsowa kusa da ita tace
"Me za kiyi min a d'aki kuma yau.? Ke da kika ce d'akin mijinki,daga bayan kuma kika ce kin samu wanda ya fishi,nan ai bai wuce a kirasa kitchen ba,ke da kike da d'akunan bacci da yawa me kuma zai kawo ki nan.?"
Bata tanka ta ba sai da ta kwanta sannan tace
"Nan nayi ra'ayin kwanciya yau,idanma za kiyi shiru to,idan ba zaki iya ba kuma ci gaba,dare dai yayi kuma kin san Hajiya basa nan,idan kika damu masu gidan sa daka ki.. Ni babu ruwana y'ar kallo ce."
Murmushi Maimunatu tayi tace "Allah sawak'e wani ya dake ni yanzun,,ko Abba da Hajiya ta sun ce na girma,bare wani can a gefe yace zai dake ni.. Tabb'.!"

"Kada ki cika baki Hajiya,gara miki kija bakinki ki b'ame ki kwanta kawai,idan ba haka ba..!"
Sai tayi shiru tana sauke numfashi jin ana tab'a handle d'in k'ofa,a tare suka juya suka kallo gurin Maimunatu ta matsa jikin k'ofar da nufin bud'ewa,Rafeek ta gani tsaye sanye cikin pyjamas d'insa masu matuk'ar kyau,rigar sleeveless sai wando 3quarter farare tas da su,musanyan murmushi suka yi ga juna da d'an mamaki a saman fuskarta tace
"Yah Rafeek did u come to check munyi bacci ko wani abu kake so.!?"
Murmushi ya sake yi yana gyad'a mata kai alamun A'a ga maganarta ta k'arshen,a hankali ta sake yin murmushi tace
"Thank God.! Bayan tafiyar su Hajiya kana kusa da mu,i knew har su dawo babu abunda zai faru damu."

Yana gyad'a kai yace "Sure.!" Sai ya juya da nufin komawa yana fad'in "Good night dear" murmushi tayi tace "Allah tashe mu lafiya",yana tafiya ya amsa mata had'e da sakin wani killer smile,,Hauwa dake k'arshen bed tana sauraren dialogue d'insu kasa fahimtarsa tayi saboda yadda yayi furucin ya nuna kamar akwai abunda yake nufi kuma ba abunda ya kawo shi ba kenan,amma kuma sai ta share bata zurfafa tunaninta akai ba tayi kwanciyarta ta lullub'e jikinta cos tana da nata personal damuwar,dawowar Maimunatu kusa da ita tana kallonta da mamaki tace
"Wai ina kika baro min Yarona ne.? Kinzo kin kwanta min a nan,ya za'ayi na ganki ke kad'ai ne,ina yake.?"
Cikin muryar bacci tace "Yana gurin big sister."

"Ohh! Can zai kwana yau.?"

Tace "Ehh!" Ba tare data d'ago ba,daga haka itama Maimunatu bata sake magana ba ta nemi guri ta kwanta,,a b'angaren Rafeek lokacin da suka yi sallama da Maimunatu kasa tafiya yayi sai daya tabbatar Hauwa tana cikin d'akin sannan ya bar wajen yana sakin wani irin murmushi,tun daga ranar data fara gano nufinsa ta koma kwana a d'akin Maimunatun bcos tana tsoron ta kwanta ita kad'ai wani abu ya faru,kuma tun daga ranar bata sake barinka ka kwana cikin gidan ba,gudun kada idan Rafeek ya kasa samun dama akanta ya dawo kanka tunda yayi furucin kai ba d'ansa bane.

Kwanakin su Hajiya goma da barin k'asar duk wani muguntar daya shirya mata ya fara fito da shi fili,bamu san yaya aka yi ba lokaci guda muka ji gari duka ya d'auki maganar Yaron da Hauwa ta haifa Rafeek yace ba d'ansa bane,duk wata hanya kuma da yasan zata ji babu dad'i yabi ya tozarta ta,hatta maganar rabuwarsu tun kafin ta haifi yaron sai daya tabbatar ya watsata bayan ya nad'e ta da sharri,mutane masu jiran kad'an suka fara zaginta da aibanta ta suna Allah wadai da rayuwarta,a dai² wannan lokacin kuma again sai ga sharrin da y'an gidanmu suka yi mata tun na kafin aurenta da Rafeek d'in ya sake tasowa,mutanen dake mata kallon ta gari suka koma fad'in abunda suka so
"Tabbas biri yayi kama da mutum.. Zata aikata tunda har uban daya kawo ta duniyar ma yayi k'ok'arin bada ta sadaka.. Shi illar mutum mai shiru² kenan mak'etaci ne.. Kaji tsoron mutumin da ya cika nunk'ufirci munafikin kansa ne,ba'a jin cikinsa sai al'amari ya kwab'e.."
Sharri iri² daga bakunan mutane babu wanda ba'a yi mata ba,hatta Babanmu jin irin maganganun da ake ta yad'awa a gari yasa shi yin fushi,kuma idan baka manta ba na fada maka a baya babanmu mutim ne mai saurin yarda da magana,ba tare da ya tsaya binciken ainihin abunda ya faru ba,ya d'aukar ma kansa alk'awarin ba zai zauna da ita ba,yanatunanin zamanta tare da shi zai b'ata masa maganar takarar d'an majalisa da ya fito bcos a lokacin harka ta bud'e,,tun kafin ma tayi tunanin dawowa gida kenan ya aika mata sak'on idan ta tashi daga can gidan surukanta kada ta kuskura ta dawo masa gida ya yafe ta a duniya,yahada mu kaf ya fad'a mana duk wanda yake jin k'aramin iskancinsa a cikinmu ko ya goyi bayanta to shima a shirye yake ya sallama shi ko da zai rage shi kad'ai,zai iya hak'ura da gaba d'ayan y'ay'an daya mallaka tunda mu bamu san yana son mu ba,shi yasa muke neman tozarta shi,shi ya gaji da rik'on mu muna azabtar da shi,muna sa shi yana ta aure²,sai tarin y'ay'a kawai yake da arzik'in da yake nema ya gagara samunsa.

Cikin k'ank'anin lokaci rayuwa ta sake yiwa Hauwa zafi kaima da ake kaika gida gurina Baba yace kada a kuma kawo ka,idan so nake na zauna tare da ku hanya a bud'e take,,tafiyar su Hajiya dai² sun cika sati biyu Rafeek yasa Maimunatu ta shirya kayanta kaf,tare da maidservant d'insu yayi musu Visa zasu bar k'asar,mai gadinsu kad'ai za su bari a nan bcos yayi shirin gyara gidan,saboda yana so ne ko da zasu zo k'asar ya kasance suna da gidan da zasu sauka a cikin gari duk da a d'an zuwansa ya mallaki manyan kadarori sosai,Hauwa bata tashi sanin abunda yake faruwa ba sai a ranar da su Maimunatu zasu bar k'asar,da safe wajen k'arfe 9 taga ana fita da kayansu,cikin damuwa ta samu Maimunatu da tambayar lafiya taga ana fita da kaya.?
Maimunatu cike da damuwa ta kalleta kamar za tayi kuka tace "wollahi nima ban sani ba yanzun dai yah Rafeek yake fad'a min wai zamu yi tafiya.."
A tsorace Hauwa tace "to su Hajiya fa,yaushe zasu dawo.?"
Maimunatu ta kad'a kai tace "Ban sani ba wollahi,munyi waya da su dai Hajiya tace min wai suna U.S."
Hawaye taji suna shirin sakko mata cikin damuwa tace "Me ya kaisu can to.!? Su da suka tafi Saudiyya.!?"
Maimunatu tace "Wollahi nima bai fad'a min ba"
Sauke kanta k'asa Hauwa tayi hawaye suna bin fuskarta ta had'e kai da guiwa a hankali ta fara rera kuka,damuwarta duka a lokacin ba akan tafiyar su Hajiya bane,illa kawai tana tunanin inda zata nufa idan ya zama dole sai tabar gidan,Maimunatu ta dafata tace "kiyi hak'uri sister in-law in sha Allah nasan ko mun tafi Hajiya da Abba zasu yiwa yah Rafeek maganarki,in sha Allah tare zamu zauna dake a can"
Cikin kuka ta d'ago kanta tace "Dama idan kun tafi can zaku koma da zama.?"
Maimunatu tana share hawayenta tace "Haka dai nake tunani,kamar idan mun tafi sai dai muzo da yawo k'asar nan"
Sake kife kai Hauwa tayi taci gaba da kuka kamar an aiko ta,Rafeek ya shigo ya tarar da Maimunatu tana aikin rarrashin Hauwa,ya tab'e baki daga inda yake tsaye yace
"Kizo ku wuce kina b'ata muku lokaci,kinsan lokacin daya rage flight d'inku ya tashi bashi da yawa ko.?"
A hankali Maimunatu ta kalleshi ta girgiza kai,tana rik'e da hannun Hauwa tace "Toh sister sai munyi waya.. Zamu tafi.?"
Hauwa tana jin haka ta sake fashewa da kuka ta rik'e ta sosai tana cewa
"Sister kada ki tafi ki barni,kice su Hajiya suma su dawo dan Allah,wallahi ban san ina zani ba yanzun,Baba yace kada na koma masa gida saboda abunda ya faru,,idan kuka barni rayuwata tana cikin garari wallahi bani da kowa ban san ina zan nufa ba"
Maimunatu ta sake goge hawayenta tace "kiyi hak'uri in-law idan na tafi zan sanar da Hajiya in sha Allah kema zaki biyo mu,ki kwantar da hankalinki,kuma ai naga ga nan gidan me zai sa baza ki zauna ba,zuwa sanda Abba zai turo miki kud'in jirgi.? Kada ki damu please in sha Allah zaki biyo mu"
Rafeek yana daga tsaye ya had'e rai yace
"Wai ke ba magana nayi miki ba,i told u zaku yi missing flight idan baku yi sauri ba,kin zauna nan kina kuka kamar wata matar mamaci,idan baza kije ba ki zauna.."
Yayi wucewarsa ciki,kusan mintuna biyar ya sake dawowa,still yaga Maimunatu tana ta aikin lallab'a ta,ransa a had'e ya taso kansu duka a masife,sai da yayi son ransa sannan yayi shiru yasa Maimunatu gaba suka fita,bayan yaga tafiyarta sannan ya dawo,ya shigo parlor da tunanin samunta a nan ya k'arasa zazzage mata rashin mutunci ya tarar bata nan,cije lips yayi ya wuce yana fad'in
"Me yasa baki jira ba kika

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login