Showing 165001 words to 168000 words out of 220972 words
Binitta dake tsaye ta biyo bayansu tana yi musu sallama,Abbah ya wuce gaba while Nusrah suka taho tare da Binitta,har bakin mota ta rakata suna zuwa driver yasa kayansu a booth,suka shiga back seat,driver ya tada mota Binitta tana d'aga musu hannu,luf Nusrah tayi tana karanto addu'o'i from wanda idan mutum ya dai²ta a cikin abun hawa har zuwa na tafiya,ana bud'e get motarsu ta fara tafiya a hankali,lokacin da suka dai²ta a bisan titi driver ya d'age glasses sama here suka fara gudu.
Nusrah sighs as she sends her text to Nuraz tana sanar masa sun tafi,tana turawa ta kashe network d'in wayar had'e da turawa a handbag,she slowly turned ta kalli Abbah and smiles,kafin tayi magana Abbah yace "Labarin ki kike son tuna min ko?" Ta kad'a kai,yace "ban manta ba nima" she smiled again,Abbah ya gyara babbar rigarsa ta gefe d'aya yace "Hajiya Karima! As u heard about her since then asalin sani na da ita she was coming to plaza tana kawo abinci" Nusrah tace "dama Abbah a nan ka santa?" Yace "Yeah! u know i'm not really going to plaza until weekend,so lokacin da na fara ganinta was on the weekend,ranar wani Saturday da yamma na bar gida na nufi plaza a lokacin it was exactly three months of ur mother's death,zuwan mu ke da wuya za mu shiga cikin plaza ita kuma za ta shiga da packages a hanunta,cikin mamaki kasancewar ban tab'a sanin akwai masu kawo abinci ba,and a lokacin banyi tunanin abinci ta kawo ba,nasa driver ya tsaya nace yayi min magana da ita,driver ya sauke glasses yace "Hajiya ana magana" ta waiwayo ta kalleshi tace "Waye yake magana?" Glasses d'in side nasa ya sauke na kalleta nace "Sannu ko?" Ta amsa tana kallona da mamaki,nace "Me kika shigo yi nan?" Wani irin kallo tayi min bud'ar bakinta tace "ban gane me nazo yi ba? Kayan sana'a na kawo mana,or do u think i might steal here?" Kalamanta sun ba ni mamaki but ba hayaniya nake so muyi da ita ba,na kad'a kai nacewa driver muje,muka wuce muka barta a nan,mun shigo ciki here we found more than half of the shopkeepers sitting on the floor kan tabarmin da aka shimfid'a suka yi sallah,muka gaisa da su kamar ko wane lokaci suna yi min barka da zuwa,Karima ta k'araso cikin mamakin yadda taga ana girmama ni ta bada abinci ga wad'anda suka yi order,na duba abunda ya kaini na fito na ji suna magana da wani matashi da take tambayarsa shin wane ne wannan mutumin da taga ana girmamawa? Here Farouk ya shaida mata cewa "Ai shi ne mai wannan plaza d'in,dukanmu nan a k'ark'ashinsa muke" Karima cikin mamaki tace "Tabbb' d'i jan,babbar magana!" Matashin da suke magana ganin ta yi shiru and to then furucin da tayi yace "Lafiya dai ko Hajiya?" Bud'e bakin da za tayi tace "Wollahi Farouk ba lafiya ba" yace "Me ya faru Hajiya?" Tace "Yanzun nan muka had'u da shi zan shigo ya tambayeni ina zanje? Na gwab'a masa magana" ya kad'a kai yace "Babbar magana,Allah yasa kada ki jawowa kanki matsala,even though na san Alhaji ba shi da matsala,but ya kamata kije ki bashi hak'uri gaskiya,tunda kinga mu duka a k'asansa muke,babu dad'i ace sannadiyyar mu wani abu mara dad'i ya faru da shi" tace "Dan Allah ta ina kake ganin zanje na ba shi hak'uri? Nima kaina na ji ban kyauta ba yanzun,kuma ko ba wannan ba kada yace na daina kawo abinci nan,ka ga dai wannan sana'ar fiye da rabin ku ne customers d'inmu" yace "Gaskiya ne ya kamata kiyi hakan,but ba ki da matsala duk lokacin da kika shirya zan raka ki in Allah ya yarda,sai dai gaskiya ba kullum yake zuwa ba,sai weekend wani lokacin ma sau d'aya yake shigowa a weekend" Karima replied with a certainty koma yaushe ne za ta kasance cikin shiri,what happened after that time as they had arranged with Farouk to come and apologize Allah shi ne masani,because i didn't know her heart,da wani week d'in ya zagayo ina zaune office a plaza kasancewar ranar daga wajen d'aurin aure na wuce na isa da wuri,ya akayi² ban sani ba,ina zaune aka yi sallama na amsa na bada izinin shigowa,Farouk ya shigo muka gaisa,har zuciyata na manta wancan abu da ya faru,da naga Farouk ya tsaya na kalleshi da tambayar "Lafiya dai ko Malam Farouk!" Yace "Ehh lafiya k'alau Alhaji,sai dai akwai wata y'ar matsala ne" nace "toh ina saurarenka" yace "Dama Alhaji akwai wata mata ce da take kawo mana abinci,wancan week d'in da ya wuce mun yi magana da ita ta fad'a min kun d'an samu sab'ani har ta fad'a maka magana,to shi ne tace tana so ta baka hak'uri kasancewar daga baya ta ji bata kyauta ba" nace "To Farouk banda abunka,ai wannan ba abune da za'a damu akansa ba,na tabbatar da ta san ko ni waye ba za ta yi min abunda tayi ba,but ka fad'a mata na hak'ura kuma na gode" Farouk yace "Ai Alhaji tare muke da ita,dama cewa tayi na nema mata izinin zuwa kuyi magana" Allah ya sani ba don son raina na amince nace Farouk yace ta shigo ba,yana fita ya sanar da ita ta shigo tana sunkuyar da kai shyly,muka gaisa ta ba ni hak'uri ta yi min gaisuwar Momman ki,i was very surprised but i didn't asked her where she knew an yi min rasuwa na sallameta ta tafi,tun daga wannan ranar ya kasance duk weekend ta mayar da plaza gurin zuwanta,wani lokacin har mamaki al'amuranta a cikin plaza suke ba ni,lokacin da na fara fahimtar inda manufarta yake,na yi k'ok'arin nuna mata tayi hak'uri because at this time i was not ready to get married,but i was committed to helping her whenever buk'atar hakan ya taso,but she didn't seem to care,ita dai kawai buk'atarta na aureta,nace "Ta yi hak'uri ta nemi miji ni kuma in Allah ya amince zan yi mata komai na kayan d'aki" ranta ya b'aci ta tashi ta kalleni bud'ar bakinta tace "Wollahi Alhaji duk yadda zan yi sai na yi ka aure ni" nace "Allah shi yake k'addara faruwar komai,duk abunda za kiyi ba zan hana ki ba,but aure tsakaninmu babu shi" ta kalleni tayi k'wafa tace "Well,let's see it",daga haka she didn't say anything ta fice daga office,tun daga ranar ban sake ganinta ba sai da aka d'auki tsayin wata guda,ranar ta shigo plaza cikin ado ta shigo office,i can't remember what really happened after this time,abunda kawai na sani shi ne lokacin da ta shigo bata yi sallama ba,na d'ago zanyi magana jin an shigo muna had'a ido na tsinci kaina in a state of kasa furta abunda nayi niyya,daga nan naji duk duniya ita kad'ai nake da burin aura,naje Gombe na sanarwa Malam yak'i amincewa,da na dawo bayan mun yi magana da Karima because lokacin ba na iya b'oye mata komai na sirrina tace "Ai ba dole sai ya amince ba,za mu iya zuwa a d'aura mana aure" na amince da shawararta daga nan muka sami limamin unguwarsu ya d'aura mana aure,,,wannan shi ne abunda ya faru a tak'aitace,abunda ya faru bayan haka tabbas ba na cikin nutsuwar da zan iya ganewa,but ki yi hak'uri da duk halin da kika shiga a dalilina,haka Allah ya k'addara and bayan nan komai ya zama tarihi tunda ga shi Allah ya sauya miki da mafi alkhairi.. "
Murmushi tayi tana kad'a kai tace "Haka ne Abbah,Allah yasa hakan shi ne alkhairi a gare mu baki d'aya",ya amsa "ameen",hira suka ci gaba da yi cikin farin ciki,yayin da driver yake ta sharara gudu,tafiyar awanni biyar da wasu mintuna ta kawo su cikin k'auyen *KUMO* that located in AKKO Local government area,Gombe state,dai² k'ofar gidan su Abbah driver yayi parking lokacin ana fitowa daga sallar azahar,gidan gininzamani ne har da bene sai dai ba get bane wani irin babban zaure ne mai d'auke da k'atuwar k'ofa,as their car parked a k'ofar gidan suka fito,Nusrah was quietly looking at her legs da zama yasa su kumbura ta yamutsa fuska saboda jin suna yi mata wani iri,ta lumshe idanunta ta bud'e and continued to walk slowly,kafin su shiga cikin zauren gidan muryar dattijon dake fitowa daga masallaci ya daki kunnensu *"ABUBAKAR!"* ya kira sunan Abbah cikin tsananin mamaki,a tare suka juya suka kalli inda suka jiyo maganarsa,Abbah ya sunkuyar da kai ganin mahaifinsa tsaye yana k'are masa kallo yace "Malam barka da fitowa" dattijon ya kad'a kai yace "Idonka kenan?" Abbah ya d'an waiwaya ya kalli inda suke ya sake sunkuyar da kai yace "Ayi hak'uri Malam,yanzu ne Allah yayi nufin mu zo" Malam ya jinjina kai yace "Mu shiga ciki",babu musu suka wuce,sun fara tafiya Malam yaga Nusrah yace "Tare kuke ne?" Abbah yace "Ehh! Malam baka gane ta ba?" Malam yayi murmushi yace "Ina kuwa zan kasa shaidata,duk da ba kwa zuwa ai ba zan manta da jik'ata ba." Abbah ya kad'a kai yace "Ayi hak'uri Malam" He did not say anything at all suka shiga cikin gida,a parlor'n k'asa wanda kusan a nan Malam yake ganin bak'i suka zauna,Nusrah ta nemi guri ta zauna tana sauke numfashi,Malam ya kallesu bayan sun gaisa yace "ABUBAKAR! Ina labarin matar da ka aura?" Abbah bowed his head yace "Malam mun rabu da ita watanni hud'u da suka wuce" Malam yace "Mene ne musabbabin rabuwarku?" Abbah yayi shiru ya kasa magana,Malam ya kad'a kai yace "shaid'aniya! Tun farko da ka zo min da labarin aurenka sai da na nuna maka ka fara yin bincike,idan halayenta masu kyaune shi kenan,amma k'arshe me ya faru? Ka rabu da mu saboda ita,baka sake waiwayar mu ba,shin wani ya fad'a maka tun da ka tafi bama sanin halin da kake ciki?" Abbah ya sake sunkuyar da kai,Malam ya kalle shi yayi murmushi yace "duk abunda ya danganci rayuwarku muna sani,na zuba maka ido ne kawai,amma a kullum ina bincikawa kuma ina yi muku addu'ah akan al'amuranku" waiwayawa Malam yayi gefen Nusrah yace "ko abunda ya faru da ita wannan yarinyar Allah ya taimaka na yi bincike a lokacin amma abunda aka so ya sameta Allah kad'ai ya sani" Abbah yayi saurin d'ago kansa zai yi magana,Malam yace "An so a jefa rayuwarta a cikin matsanancin hali,bayan an rabata da gidan mahaifinta,an had'a ta da shaid'anun aljanu wanda a wannan fitar da tayi so aka yi ta bar nahiyar nan gaba d'aya,sannan idan ta tafi ta fad'a hannun mutanen da basu san taimako ba,cikin hukuncin Allah,ubangiji ya nufe ni da yin bincike akan halin da kuke ciki,a nan na gano wasu daga cikin k'ulle²n da ake yi,,to kasancewar mun yi nisa ba zan iya samun damar ganinta ba bare nayi mata ruk'yah,na yi mata rok'on Allah ta tsaya nan cikin gari,Ubangiji kuma ya had'a ta da mutanen kirki,duk da anso a b'ata rayuwarta ta bibiyi maza,Allah ya kareta ya had'a ta da mutum mai tsoron Allah,mai tsayawa akan addini,wannan ma abun farin ciki ne.." Nusrah dake zaune gefe tayi shiru tana tunanin labarin da Nuraz ya bata lokacin da ya ganta,taji hawaye sun cika mata ido,her thoughts return to a life of mental illness da tayi,briefly idan har ta fahimci bayanin Malam yanzun da kuma wancan labarin da Nuraz ya fad'a mata a baya so aka yi lokacin da take bibiyarsa duk inda yayi,idan ba mai tsoron Allah bane sai ya keta mata haddi,ta sunkuyar da kanta hawaye suna zubo mata,yayin da a zuciyarta tayi rauni a nan ta sake yiwa Allah godiya bisa canjin da yayi mata,after rescuing her from the evils of his servants ya had'a ta da mutumin da ya zame mata garkuwa and was always proud to find him,Abbah looked at her sympathetically yace "Alhamdulillah alaa kulli halin.." Malam yace "Allah shi ne abun godiya,duk abunda ya faru haka Allah ya k'addara,fatan Allah ya gafarta mana ta dalilin k'addarorin da suka rataya a wuyanmu" suka amsa da ameen,daga nan nasiha sosai Malam ya yiwa Abbah,yayin da duk tunanin Abbah ya gama bashi Malam zai d'auki zafi akan abunda yayi but sai yaga sab'anin haka,har hira yake jansu da shi,Abbah ya kasa daurewa yace "Allah ya gafarta shin baka yi fushi da abunda na aikata ba?" Malam yayi murmushi yace "shin mene ne ribar yin fushi? Mene amfanin yin jayayya akan abunda Allah ya hukunta faruwarsa??" Abbah ya kad'a kai cikin gamsuwa,again thanking Allah for giving him such a father who was gentle and quick to understand how things were going.
Ranar tunda suka zo after they received a warm welcome wanda basu tab'a tunanin samu ba,Abbah ya sake sakewa sosai da Malam,they were sitting in a well-furnished parlor suna hira Malam yasa aka damo fura mai kyau aka kawo,Nusrah dai gaba d'aya ta kasa samun sukuni saboda al'amuran da Malam ya warware musu duk sun haddasa mata shiga damuwa,Malam da ya kula da halin da take ciki yasa a rakata masaukinta yace taje ta huta,jikinta a sanyaye ta tashi tabi bayan yarinyar da Malam yasa ta rakata y'ar gidan wani k'anin su Abbah da yake zaune a cikin garin Gombe,suna zuwa Nusrah thanked her ta karb'i jakarta ta shige da sauri jin mararta tana d'an yi mata ciwo kad'an².
Bayan tafiyar Nusrah Abbah were conversing with Malam yace "Malam ina labarin Yaya?" Malam yayi murmushi yace "Duk da yake ka jima baka zo ba,amma shi kam yana zuwa,iyalinsa ne dai basa zuwa" Abbah yayi murmushi yace "Na jima ban ganshi ba,tun rasuwar *KHADIJAH"* Malam yace "Allah sarki,Allah ya yi mata rahama" nan yayi ta yabon halayenta na k'warai,Abbah ya amsa,Malam yace "shi d'an uwan naka da jimawa ya bar k'asar Amuruka" Abbah yayi saurin cewa "Malam yaushe ya bar US?" Malam yayi murmushi yace "Da jimawa sosai wani zuwa da yayi ya sanar da ni" Abbah yace "Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi,amma wace k'asa ya koma bayan nan?" Malam yace "Yana nan a ingila (England)" Abbah cikin mamaki yace "Ai kuwa Nusrah ma a can take aure" Malam yace "Ta yi aure amma ba mu sani ba?" Abbah ya sunkuyar da kai yace "Ayi hak'uri Malam,al'amarin ne ya zo da gaggawa" a nan ya warwarewa Malam duk yadda al'amarin ya faru,Malam yayi ajiyar zuciya,here ya sake yiwa Abbah nasiha sosai,even though ya samu labarin wanda Nusran take aure was the man who helped her and he was very happy but ya yi masa fad'a duk lokacin da wani al'amari ya tashi ya sanar masa.
As Nusrah was lying on the bed after ta idar da sallah al'amuran rayuwarsu became worse for her,she slowly burst into tears as she feels wani sabon tsanar Hajiya Karima yana mamayeta bisa abunda ta aikata musu,cikin kuka tace "Yah Allah ka yiwa wannan baiwar ta ka hukunci dai² da laifin da ta aikata." Tana gama fad'in haka tayi whipping tears and ta d'auki wayarta trying to call Nuraz cike da saka rai akan damuwar da take ciki zai ragu,but she made three calls for him ba'a d'auka ba,yayin da bugun tafiyar wayar yake tafiya dai² da bugawar zuciyarta,kira na uku yana katsewa she close her painful eyes,kafin wani lokaci ciwon da take ji kad'an² ya fara k'aruwa,ta koma baya a hankali ta sake kwantawa tana sauke numfashi hardly.
*OXFORD...*
He wakes up from his worst nightmare and pick up his phone idanunsa suka ci karo da miss calls d'inta,gabansa yana fad'uwa ya fara kiran line nata,kusan sau biyar yana jera kiranta but ba'a d'auka ba,hankalinsa a tashe ya manta ya kira line Abbah ya fito parlor yana kiran Lolly,hankalinta ita kanta a tashe ta fito daga bedroom saboda yanayin kiran ta san was not normal,ta kalleshi lokacin da yake k'arasowa tace "Lafiya kake min irin kiran nan?" He moved close to her,ya rik'eta quickly yace "Mom i was calling Nusrah but ba na samunta" Tayi ajiyar zuciya tace "Shi ne ka tayar da hankali?" Ya marairaice yace "Ba haka bane Mom,kawai ina jin kamar ba lafiya ba" here he began to tell her about his dream of seeing her die,Lolly tana kallonsa tace "Kai kam wani lokaci ka iya shiririta,shi kenan daga yin mafarki sai ka yarda abu ya faru da gaske?" Yace "Ni dai Mom ki kira ki tambaya" ta kad'a kai tace "Ta ina zan kira tunda kaima baka samu ba?" Sai lokacin ya tuna yace "Let me call Abbah" tace "hurry up" ya juya zai koma arean bedroom d'insu Lolly's phone rang,da sauri ya waiwayo Lolly da ta bishi da kallo tayi ajiyar zuciya tace "ka tafi mana wayata aka kira" ya juya a hankali yana yin ajiyar zuciya,while ita kuma ta d'aga wayar tayi sallama *"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..."* da ta ambata ya sa Nuraz fasa shiga bedroom d'in da sauri ya dawo fuskarsa kamar zai fasa ihu,Lolly stared at him da phone d'in a kunne tace "When did that happen?" Tayi jim,a hankali tace "if Allah (S.W.T) approved we would come tomorrow" he did not wait her to end the statement,ya fara tambayar abunda yake faruwa,Lolly was silent and said nothing,da taga ya damu ta fara yi masa nasiha,ya sake hargitsewa idanunsa sun canja color yace "Please Mom tell me,ina son sani if there's something da yake faruwa da ita" she closed her eyes sympathetically tana cewa "calm down my son" mik'ewa yayi saurin yi yace "since ba za ki fad'a min ba,i have to go now" quickly ta rik'o hannunsa and looked at him with affection bakinta yana rawa tace.....
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
*Allahumma ballighna ramadhana bil iimaan..👏*
*I extend my deepest sympathies to u and ur family (Fatima Muhammad Dodo),may Allah (S.W.T) forgive and accept his soul into the garden of eden,near the one whom he seeks