Showing 33001 words to 36000 words out of 220972 words
shi suka dawo parlor,ta zauna a kasa saman rug ta d'orashi kan cinyarta,hannunsa ya fara turawa cikin rigarta tana kallonsa ta cire hannun tana had'e rai saboda duk tana jin babu dad'i,ya sake mayarwa ta cire,yana shirin sake mayarwa ta rik'e hannunsa tana masa kallon k'asan ido,kuka ya fara mata yana kai mata duka da d'ayan hannun cikin gwaranci saboda ba sosai ake gane me yake cewa ba yana mata magana,tausayinsa ya kamata tayi saurin fito masa da nonon ta bashi,ya kama yana sha yana ajiyar zuciya duk da ba wani sosai yayi kukan ba,a hankali ta zuba masa ido tana kallonsa hawaye suka gangaro mata,tayi saurin d'auke kanta gefe,a hankali tayi kukanta mara sauti yana gama sha ta mayar ta d'auko bowl d'in data rufe ta fara sha tana bashi,bata wani sha da yawa ba taji ya fita a kanta taci gaba da bashi,shima bai sha sosai ba ya kautar da kansa gefe,data sake bashi ya girgiza mata kai alamun ya k'oshi,ya mika mata hannu yana k'ok'arin karb'ar spoon d'in a hannunta,sake masa tayi a hankali taga ya karkata spoon d'in ya deb'o ba mai yawa ba yana k'ok'arin kai mata bakinta,k'ura masa ido tayi tana kallo,shi kuma sai magana yake mata yana so ta bud'e bakinta ya bata,bata san lokacin data fashe da kuka mai k'arfi,ta rungume shi tana jin babu dad'i,,ta dakata da kukan ta barshi a nan parlor taje kitchen ta wanke kayan ta dawo ta d'auke shi ta wuce d'aki bayan ta kashe electronics,tunda ta shiga d'akin dashi ta sauya masa kaya itama ta canja zuwa nighty ta zauna shiru tana tunani,bai yi bacci ba har wajen eleven,da yayi bacci ma nan ya barta ita kam bata samu ta runtsa ba saboda tsoron dare da kad'aici daya cika mata zuciya,har wajen asubah bata iya yin bacci ba sai da gari ya waye,lokacin bacci ya fara fizgarta Nuraz ya tashi,nan ya dasa rigima,yana ta laluben abincinsa,da kyar ta daure tayi feeding d'insa ta shirya shi ta d'an kwanta lamo tana ta kallonsa,tana son yin bacci saboda a lokacin har kanta ya fara ciwo amma babu dama,a tak'aice dai haka rainonka ya kasance ga mahaifiyarka da dare baka bacci da wuri,tsoro da tunane² dake d'awainiya da ita kuma suka sa ko ta kwanta bata iya bacci,da safe hidimar ka and baka bari ta kwanta bare ta samu baccin ko yaya ne,kullum ya kasance mata da matsanancin ciwon kai take rayuwa,tun yana mata kad'an² yana damunta har ta saba ya daina damunta,ta rasa yadda zata yi ga tunanin gida da yak'i barinta ta huta,but tsoron abunda zata tarar yasa ta kasa samun sukunin zuwa,ranar da ta cika sati da komawa gidan,ta gaji ta yanke shawaran zuwa ta sake zuwa ta rok'i Baba gafara duk da ta san bata aikata abunda ake zaginta da shi ba,idan ya yarda shi kenan sai tayi masa bayanin komai da yadda ya faru idan kuma yak'i saurarenta zata ci gaba da hak'uri har zuwa lokacin da Allah zai sa ya sakko ya yarda ta koma gidan,,ta gama shiryawa ta fito ta kulle gidan ta samu napep da zui kaita k'ofar Na'isa,misalin 12pm ta sauka ta sallami mai napep,ta kama hanyar da zata sada ta da gidan mahaifinta,tunda ta tsinci kanta a k'ofar gidan mahaifinta take jin k'irjinta yana sake tsananta bugawa.....
*#😢😢 Yah Allah ga baiwarka nan,kasa ko mene ne zai faru ya zo mata da sauk'i...*
#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
*I just finished typing the page,,but don't know how wollahi na yi deleting,be patient with how the page comes to u my people.😢*
Pᴀɢᴇ 11.
#Uɴᴇᴀꜱʏ
Gefe guda ta samu ta tsaya da tunanin yadda za tayi ta samu damar yin magana da ni,ta jima sosai tsaye tana kalle² da tunanin wanda zata aika ya kira ni,tana nan tsaye ta rasa mafita k'arshe taga tana b'ata lokaci,ta yanke shawaran zuwa da kanta,,ta nufo k'ofar gida tana tunanin idan ta samy Baba a gida kuma fa.!? suka kusa bugar juna,yana k'ok'arin fita zuwa wajen taron su na siyasa,tayi saurin komawa baya muryarta na rawa tace "Kayi hak'uri Baba,ban san kana hanya ba"
Ya kalleta ya d'aure fuska cikin hayaniya yace "Wa kika zo nema a nan.!?"
Tayi shiru tana sunkuyar da kanta k'asa,a bakin hanya ya kafe ya kama waist ya k'i matsawa,ta d'ago a hankali tana gaida shi,bai amsa ba sai tambayar daya sake jefo mata "waye tazo nema a gidansa.!?"
Ta daure tana jin fad'uwar gaba sosai tace "Baba na zo naga Yaya Maryam ne"
Ya kalleta kamar zai yi magana ya fasa,cikin gidan ya wuce ya barta a tsaye,zuciyarta a lokacin har ta fara saka mata Baba ya tafi ya kira mata ni,kamar yadda tayi zato haka ce ta faru sai dai sab'anin da aka samu,ko da Baba ya sako ni a gaba muna fitowa ya kalleta yace "Ita ce wannan.!?"
Hauwa ta gyad'a kai tana kallonsa idanunta cike da hawaue,Baba ya juyo ya kalkeni yace "Maryam kin san wannan.!?"
Jikina yana b'ari na amsa na santa,yace "Wace ce ita kuma mene ne alak'ar ku.!?"
Nayi shiru ina tunanin tambayar da amsar daya dace na ba shi,ya daka min tsawa,cikin hargari yace "Ba da ke nake magana ba dan uwarki"
Ban iya kallonsa ba nace "Na santa" yace "A ina.!?"
Nace "A nan gidan"
Ya girgiza kai "ita wace ce d'inki.!?" Na d'ago kaina na kalli Hauwa a sanyaye nace "Y'ar uwata ce."
Wani irin girgiza kai naga babanmu yana yi,kafin ya juyo kaina yace "Maryam.!" Na amsa "Na'am" yace daga yau "ita ba y'ar uwarki bace"
Na d'ago zanyi magana baba yace "Kul! Kika ce min wani abu,yanzun nan zan sallamaku duka" nayi shiru ban ce komai ba,ya kalle ni yace "kin ji me nace!?"
Na girgiza kai" yace "Daga yau na haramta miki zama ahalinta,na raba ku rabuwa ta har abada,idan ta sake zuwa ta aika a kira ki,kika kuskura kika tsaya magana da ita Allah ya isa ban yafe miki ba,kuma wollahi thumma billahi,kinji rantsuwa ko.!?" Na girgiza kai da sauri cikin tsoro yace "Sai kin bar min gidana,daga ranar ina so ki d'auka ni ba mahaifinki bane,tunda kin zama mara jin maganata"
Ina kuka ina kallon Hauwa da tausayawa,baba ya wuce ya barmu tsaye a nan kamar wad'anda aka sassak'a,kusan zan iya cewa gara ni na samu hawaye sun zubo min,amma ita Hauwa tunda ta kafe a nan Allah kad'ai ya barwa kansa sanin abunda ya faru da ita,tana raye,suma ta yi ko ta mutu Allah shi ne masani,,bayan tafiyar Babah da jimawa yayi tunanin ya aiko yaro ya duba masa na shiga gida ko ina nan,yaro yazo ya koma ya fad'a masa ban tafi ba,sai ganin Baba nayi ya dawo da kansa cikin fushi,ina ganinsa na matso da sauri ina kuka zanyi magana tun kafin na bud'e baki cikin fad'a kamar zai dake ni ya korani gida,ina tafiya ina waiwayen y'ar uwata kamar ba zan tafi ba haka har na shiga gida,baba ya koma kan Hauwa da fad'a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,sai daya tabbatar ko zuwa unguwar ba lallai ne ta sake yi ba,sannan ya juya ya barta,,cikin tsananin tashin hankali bayan dogon lokacin da ta d'auka cikin halin da bata san a wace duniyar take ba ta ja k'afafunta da kyar ta shiga shop d'in dake a nan line mu ta siya Biro da takarda,doguwar wasik'a ta rubuto min mai d'auke da duk wani abu daya faru da ita a zaman da tayi da Rafeek da ahalinsa,a k'arshe ta rok'i alfarmar na nema mata yafiyar Baba,,bayan ta tabbatar sak'onta ya iso gare ni ta juya ta bar unguwar zuciyarta cike da k'unci.
Ina cikin gida bak'in cikin abunda ya faru ya same ni,d'an sak'on data aiko ya kawo min wasik'a,na warware bayan na keb'e kaina na fara karantawa,tun ban yi nisa karantawa ba hawaye sun wanke min fuska,na daure na karanta,lokacin da Baba ya dawo na je masa da wasik'a,dana fad'a masa duk abunda yake faruwa ya nuna bai yarda ba,na karanta masa takardar da ta aiko min.
Baba ya kalle ni ya jinjina kai yace "Na ji wannan tatsuniyar,,sai dai abunda nake so ki gane Maryam ni ban amince haka ta faru ba,kuma ko na ce na yarda shin zancen ya wuce ko.?"
Na girgiza kai nace "Ehh.! Baba"
Ya kalle ni yace "To ban yarda ba.."
Na d'aga kaina nace "Saboda me ba zaka yarda ba Baba.!? Kai nefa ka haifemu dukan mu,ka san halin kowa a cikin mu,duk abunda za mu iya aikatawa ka san shi haka ma wanda ba za mu iya ba"
Baba yayi min kallon banza yace "Idan na yarda shin sauran mutanen gari za su yarda.!? Ko kuwa su d'inma za ki bisu da takarda ki karanta musu ne.!?"
Na girgiza kai cike da bak'in ciki,baba yace "Though tunda kin san da haka,ko da wasa kada ki sake nufo ni da irin wannan shirmen,na riga na yi muku shamaki da juna,idan har kin d'auke ni mahaifi ki bi maganata,idan kuma y'ar uwarki kike son bi,k'ofa a bud'e take dan na cire y'ay'a biyu daga cikin ahalina ba abune da zai tada min hankali ba,zab'i ya rage naki ni ko ita.!"
Nayi shiru ban iya cewa komai ba,Baba yace "Za ki iya tafiya idan maganar da ta kawo ki kenan" jiki a sanyaye na juya ina ci gaba da kukan zuci har na koma d'aki,babban abunda yafi damuna ya tayarmin da hankali a lokacin ba komai bane,illa rashin sanin address na inda Hauwa take,tunda ta kama hanya ta tafi kuma ko a labari banji wani mutum d'aya da ya zo yace ya san inda take ba,a haka kwanaki suka yita zuwa suna wucewa ba tare da na samu wani gamsashen labarin inda kuka nufa ba,,na ci gaba da rayuwa a gida amma fa tamkar mutum-mutumi na zamewa y'an gidanmu,idan aka yi min magana daga Umm sai um'um,na daina shiga maganar kowa,idan hayaniyar su ta tashi can suke yin abunsu su kad'ai,,kullum cikin jiran tsammani da tunani nake naji ko da wucewarta ne wani ya zo yace min ya gani,amma shiru tamkar an shuka dusa har muka cinye sama da sati biyu.
3 Month later...
Laying and rising is loss of living,haka nan a gurin ubangiji a year is like a day,cikin hukuncin ubangiji tun daga wannan tafiyar da Hauwa tayi sai ya zama bata sake tunanin waiwayar gida ba saboda abunda ya faru tsakaninta da Baba,bayan tafiyarta babu jimawa damuwa tayi mata yawa,har ya zama ciwo ya fara k'ok'arin kayar da ita,tun tana yi a tsaitsaye taba jurewa har lamarin ya so fin k'arfinta,damuwa da fargabar abunda zai iya faruwa da rayuwarta yak'i barin zuciyarta ta samu nutsuwar sake dawowa,ta ga al'amarin still ba mai k'arewa bane,duk da tsoron dake tare da ita ta sake yanke shawaran dawowa ko da zai kasance skasance wannan shi ne zuwanta na k'arshe,but ta gwammace zuwan da ace ciwo ya yi ajalinta ita kad'ai a gurin da babu wani cikin ahalinta,cikin y'an watannin ta yi wani irin ramewa ta yi duhu kamar ba ita ba,duk wanda ya santa idan ya ganta a wannan tak'aitaccen lokacin na tabbata zai yi wahala lokaci d'aya yayi saurin ganeta,ta kamo hanyar K'ofar Na'isa a karo na biyu cike da fargaba,but data tashi zuwa wannan lokacin sai bata yi k'ok'arin shiga gida ba ko nema na,ta sake aiko min wasik'a,ina zaune cikin d'aki jigum sak'on ta ya riske ni,na karanta naga fiye da rabin maganarta akan na nema mata yafiya ne a gurin Baba,sai sauran mutanen da nasan wani mu'amala ya tab'a had'a su,ina kuka ina karamtawa har na zo inda take barmin wasiyya tana sanar min ta jima ba ta da lafiya na taimaketa na nema mata alfarma gurin Baba na zo na ganta ko da sau d'aya ne kafin ta Allah ta kasance mata,a wannan wasik'ar nayi gamo da tsananin tashin hankalin da ya wuce tunani na
_"Kiyi hak'uri y'ar uwata.! Babu yadda zanyi,ya zame min wajibi na sanar miki,duk da na san kema ba laifinki bane da kika kasa zuwa inda muke,,a halin da nake ciki,bayan dawiwa ta ciwo ya ci k'arfina,ina jin kamar ba zan rayu ba,idan haka ya kasance ina rok'on za ki nema min alfarma a gurin Baba,idan ya barki ko da a shek'ara sau d'aya ne zan yi alfahari da hakan,kema ina fatan za ki je ki duba min yarona,ban san yadda rayuwa ta zata kasance ba,shi yasa na yanke shawaran sanar da ke tun yanzun,zan kai Nuraz orphanage,idan kin samu dama dan Allah Yaya ina rok'on ki kije ki ganshi,na san Yarona ba zai yi maraici ba idan kina raye,na san yana da wata mahaifiyar kamar ki kuma za ki kula da shi fiye da yadda zanyi masa,ni dai tawa ta zo k'arshe sai dai ina yi mana fatan mu kasance tare har a aljannah,idan na yi miki wani laifi ina neman afuwar tun daga yarinta har zuwa girma na,ki yafe min y'ar uwata... Allah ya k'addara saduwarmu.. BISSALAAM.!"_
Daga k'anwar ki mai k'aunar k'i har abada *HAUWA BABA MUHAMMAD...*
Tsananin firgici da tsoro na shiga lokacin dana gama karanta sak'on ta,ba tare da na jira neman izinin fita a gurin Baba ba na fito daga gida kamar zararriya nabi hanya ko zan ganta,ina tafiya ina tambayar mutanen unguwa ko sun ganta.!? Sai ace min yanzun babu jimawa ta wuce,da sauri nake wucewa na bar wajen na yi gaba,ina tafe ina sake tambaya,amma abun takaici har na fito titi na gama dubawa ko mai kama da ita ban samu ba,na koma gida cikin firgici na tarar Baba ya dawo,ina kuka na sake zuwa gurinsa da wasik'a ko zai tausaya min ya bari naje,still Baba ya sawa idanunsa toka kamar waccan ranar,ya nuna min sam baya ko son yin maganar,dana takura akan ya barni naje yace idan na sake na fita bada izinin sa ba Allah ya isa bai yafe min ba.
Tsoro da tashin hankali suka sake shigata,rashin sanin matsayin Allah ya isa da Baba yayi min,da tsoron halin da y'ar uwata take ciki suka sa na kasa ko magana,ina ji ina gani ga address d'in inda take amma zuwa na dubata ya gagare ni,ban san mene ne zai faru ba idan na fita ba da izininsa Bana ba,sannan mene ne makomata idan na sab'awa umarninsa,,sati guda da zuwanta kullum da ciwon kai nake yini saboda damuwa ga yawan mafarkai da nake yi marasa dad'i,zuciyata kullum cikin yi min khud'ubar naje na duba ku take,na daure na ci gaba da zama ina jiran tsammani,,a cikin satin wani abu daya faru ya sake sawa jiki na yayi sanyi,ko wane lokaci na kwanta bacci da rana ko dare mafarkin Hauwa nake yi,a ko wane lokaci da zan ganta tana kuka tana sake rok'ona kada na manta da kai na kula mata da kai,,kwana biyu tsakani na sake yin mafarki da Innarmu,tun bayan rasuwarta da nayi ta mafarkai da ita,na jima sosai ban sake ganinta ba,ranar na kwanta bacci kenan tazo min cikin wani irin fuska mai ban tsoro,ina murna na nufi inda take zaune da niyyar na rik'e ta sai na ga ta yi tafiyarta,na dunga binta ina rok'on ta tsaya amma bata sake waiwayowa ba,sai dana gaji na fad'i a k'asa,ina kuka ina kiranta da rok'on ta tsaya,sannan naga ta juyo tana kallona tana kuka,hankali na a tashe nace "Inna mene ne ya saki kuka.??" Bud'ar bakinta tace "Ban san haka za kuyi min ba Maryam.. Ke da mahaifinki kun tozarta ni,kun wulakanta ni.. Laifin me nayi muku haka.!?"
Nace "Inna laifin me muka yi miki ne.!? Ban gane abunda kike magana ba.!"
Ta share hawaye tace "Saboda kunga bana raye kuka wulakanta min y'ata.! Me yasa sai da kuka bari na tafi sannan za ku wofantar da ita.!?"
Ina kuka ina bawa Inna hak'uri,bata saurare ni ba ta juya ta ci gaba da tafiya tana cewa "Idan har baki nemi inda y'ar uwarki take kin zauna tare da ita ba,kada ki sake kira na mahaifiyarki,ni ba mahaifiyarki bace,a kullum ina jin bak'in ciki na haifi y'a irin ki.."
Nace "Inna ki yi hak'uri dan Allah,nima fa duka ba laifi na bane,ki yarda dani,babanmu ya hana ni zuwa na dubasu."
Ta juyo ta kalle ni tana goge hawaye tace "Shi kenan,tunda kin yarda ya raba muku zumunci ki zauna tare da mahaifinki,in sha Allah ubangijin daya hallice mu ba zai tab'a barin Hauwa'u tayi maraici ba.. Daga yau ba zaki sake gani na ba,ki je ki zauna da mahaifinki.."
Tana gama fad'ar haka ta juya da sauri,ina kuka ina kiranta amma bata sake waiwayowa ba,jan jiki naci gaba da yi ina son bin hanyar da ta bi,saboda lokacin dana fad'i na ji ciwo sosai a k'afata,na kasa tashi na bita ina nan kwance ina kuka da kiranta har ta b'acewa ganina,cikin k'araji na kwalla kiran Inna,,a firgice na tashi ina dube²,na bud'e ido naga y'an uwanmu mata zagaye da ni sai kallona suke yi suna jiran su ji abunda ya faru na ke zabgaga ihu a farkon dare,na daure na juya ban yiwa kowa magana ba duk tarin tambayoyin da suke min,da suka ga ba ni da niyyar amsa musu kowacce ta juya ta kwanta,,a wannan daren ni dai ban samu damar komawa bacci ba har gari ya waye.
Misalin k'arfe 10am lokacin babanmu ya fita na shirya cikin damuwa,ba tare da sanin kowa ba