Showing 42001 words to 45000 words out of 220972 words
da ita fa.!?"
Annie ta jinjina kai tace "Ka yi tunani mai kyau,in sha Allah babu damuwa sai ta zauna tare da mu zuwa lokacin da zata samu lafiya,,ubangiji yayi maka kyakykyawan jagoranci akan niyyar ka ta alkhairi"
Yace "Ameen Annie,bari na barta a nan ko,zanyi wanka but zan dawo"
Ta amsa masa da "toh" ya tashi ya fita,tana ganin ya fita ya fara tafiya ta bishi,kai tsaye ya wuce bedroom d'insa bai san tana binsa ba sai daya shiga yana k'ok'arin rage kayan jikinsa da niyyar shiga ya watsa ruwa,ya ganta tsaye a wajen study table d'insa,mamakin lokacin data biyo shi bai sani ba yasa shi tsayawa yana ta kallonta,ya sake had'e rai ya cire kayan bai kulata ba,ya wuce bathroom ya barta nan tsaye,tana juyowa taga zai shige tayi tunanin fita zai sake yi tayi sauri ta biyo shi,ya juyo zai rufe k'ofar ya ganta a gabansa ya tsaya yana kallonta fuskatsa a matuk'ar d'aure yace "why are u still following me.!?"
Ta kalleshi tayi shiru,a fusace ya daka mata tsawa yace "ba dake nake magana ba kin kafe ni da ido.!? Za ki daina bina duk inda nayi ko sai na faffalla miki mari.!?"
Nanma tayi shiru tana ta kallonsa,ya fito daga toilet d'in ya kama hannunta ya shiga janta,sai daya kaita gefen bed d'insa ya zaunar da ita idanunsa cike da tsoratarwa yace "Nan za ki zauna,idan kika sake bina sai na zane ki"
Ya k'arasa yana zare mata ido,jikinta ya hau b'ari,tana ta kallonsa bata ce komai ba ya juya ya tafi,sai daya kai bakin k'ofa kamar ance masa turn,ya sake ganinta biye da shi sau da k'afa,ransa a b'ace fiye da karon farko ya tsaya ya rik'e waist,itama ta tsaya a inda take tana ta kallonsa like ta ga sabuwar halitta,ya jinjina kai cike da b'acin rai yace "wato baza ki daina bina ba kenan.!? Ke haukar naki haka ya nuna miki ki yi,toilet d'inma sai kin bini.!?"
Tayi shiru tana kallon bakinsa da yake motsawa,ya daka mata tsawa yace "koma can ki zauna ki jira ni nace"
Annie data shigo d'akin a time d'in tace "A'ah A'ah.! Habibiiy,ya zaka na mata tsawa,ka bita a hankali mana"
Ya d'ago kai ya kalli Annie kamar zai fashe da kuka yace "To Annie fisabilillah sai kawai ta dunga wani bina duk inda nayi,nace ta zauna na fito,har fa mayar da ita nayi ta sake biyo ni"
Annie tayi murmushi tace "To yi hak'uri je kayi wankan bari na tafi da ita"
Ya juya ya banka mata harara ya wuce bathroom ya kulle,ta tsaya a bakin k'ofar tana ta kallo,Annie ta matso inda take ta kama hannunta,ta juya ta kalleta Annie ta sake yi mata murmushi tace "Muje ko daughter.!"
Tayi shiru ta k'ura mata ido,Annie ta fara tafiya tace "muje maza kiyi wanka kema" ta fara binta kamar ta gane abunda Annien take nufi,suna tafiya tana waiwaye har suka fita,Annie ta kaita bedroom d'inta ta zaunar gefen bed tace "maza zauna nan ki jira ni,bari na had'a miki ruwan wanka."
Tana fad'a ta wuce bathroom d'inta ta had'a mata ruwa mai d'umi ta fito,tana shirin yin magana taga wayam babu kowa a gurin ,da mamaki tace "Toh! Ina tayi kuma.!?"
Ta fito tayi following footstep d'inta,ta duba parlor bata sameta ba ta wuce bedroom d'insa,tsaye ta ganta a bakin entrance na bathroom tana waiting fitowarsa,Annie ta girgiza kai taje ta kama hannunta,saurin kallon Annie tayi ta kalli entrance d'in,Annie cikin sanyi ta shafa kanta tace "u don't worry ur self daughter,muje zai zo gurin ki idan ya fito"
Ta k'urawa Annie ido,Annie ta kama hannunta suka fita,har bathroom ta kaita ta rufe mata k'ofa ta waje,almost thirty minutes da shigar da ita wanka ya shigo cikin shirin bacci,Annie ta kalleshi tace "Yanzun ya zamu yi ne da k'anwar taka.!?"
Yayi saurin kallonta yana bud'e idonsa sosai yace "Annie.! K'ANWATA kuma.!?"
Tayi murmushi ta gyad'a masa kai,ya tab'e baki yace "Kiji Annie wai K'ANWATA,daga ganinta yau har ta zama relative d'inmu.!?"
Tayi y'ar dariya tace "sosai ma,tunda bata da kowa yanzun sai mu ai ta zama ahalinmu"
Ya sake tab'e baki yana k'arewa d'akin kallo yace "Annie where's she.!?"
Tace "Na sa mata ruwa tayi wanka"
Yayi murmushi da gefen baki yace "Annie! Wai ita ce za tayi wankan..?"
Tace "Ehh! Mana wani abu ne.!?"
Yace "A'ah! Nothing"
Ta kalle shi tace "ka fad'a dai idan da matsala"
Ya girgiza mata kai,ta kalleshi sosai ta d'auke kai,ya zauna saman couch yana jira ta fito,kusan mintuna ashirin yana ta zaune yaji shiru ya kalli Annie data fita ta sake shigowa d'akin yana squeezing face,Annie ta kalleshi ta kalli k'ofar bathroom dake rufe har lokacin da mamaki a fuskarta tace "Wai har yanzun bata gama ba.!?"
Ya girgiza kai yace "Ehh",wucewa tayi wajen k'ofar toilet tayi knocking,mintuna biyu sannan ta bud'e ta shiga,tsaye ta ganta sai raba idanu take bata yi wankan ba,ta dunga mamakinta though she knew something was wrong with her brain,lek'owa tayi ta ganshi yana kallon k'ofar kamar yana tunani tayi ajiyar zuciya tace "Habibiiy! Ka jira mu zan mata wanka"
Ya jinjina kai ya tab'e baki kad'an daya tuna abunda ta yi masa,Annie ta koma tayi mata wanka ta wanke mata kanta da yayi datti sannan suka fito tana rik'e da hannunta,ya d'ago kansa a hankali ya kallesu,akan santala² k'afafunta idonsa ya fara sauka,ya dunga d'agowa a hankali har ya kai kan gashinta da yake jik'e,gabansa yayi mugun fad'uwa da suka had'a ido,ya d'auke kansa daga kanta ya kalli Annie a rikice yana mik'ewa tsaye yace "Annie good night"
Ta kalleshi tace "toh Allah ya bamu alkhairi" ya fita yana amsawa,ta bishi da kallo ganin ya fita kamar zata bishi,Annie dake rik'e da hannunta ta kaita saman stool ta zaunar sannan taje ta rufe k'ofa,ita ta yi mata kwalliya ta gyara mata gashinta tayi masa tufka d'aya ya sauka saman shoulder d'inta,ta bud'e closet ta ciro mata wani sleeping gown mara nauyi data siya da jimawa yayi mata kad'an tana ta ajiyarsa,taje ta sake bud'e d'ayan bedroom da take ajiye wasu kayan idan order su yazo,ta zab'a mata inner wears masu kyau,ta dawo ta ganta a tsaye sai kalle² take saboda data fita rufe k'ofa tayi shi yasa bata samu damar fita ba,tayi murmushi sannan ta kamata ta saka mata kayan ta kama hannunta ta kaita saman bed d'inta ta zaunar da ita,abinci taje kitchen ta had'o mata ta dawo,tana bata tana ci tana kallonta har ta k'oshi,Annie tayi mata murmushi sannan ta fita da kayan ta dawo,still a tsaye ta ganta kamar wacce ta had'iye spears (mashi) kama ta tayi ta suka zauna shiru,har to 11 tana zaune,da Annie ta gama abunda za tayi lokacin tana ta hamma cos a time d'in Nuraz ya sake dawowa abunda yazo yi dama kenan ganin da ya yi mata yasa shi fita d'azun babu shiri ya yi mata allurai suka yi sallama da Annie,kamata tayi a hankali ta kwantar da ita ta rufe ta saboda sanyi,ta musu deactivating light ta yi musu addu'ah ta tofa duka edges na d'akin sannan ta kwanta itama.
Da safe Annie ta fita kitchen around 7am ganin tana bacci har lokacin sai bata kulle door ba ta barshi a bud'e,suna ta aiki a kitchen ita da Bareerah,wajen 9am sun gama abunda suke ta dawo da niyyar ta tasheta tayi mata wanka,tana shigowa ta iske gurin data kwanta babu kowa,Annie ta girgiza kai ta juya,bedroom d'insa da take tunanin tana can ta nufa,dai² zata shiga ta jiyo muryarsa cikin fad'a² yana mata masifar zuwa masa d'aki ta tsaya masa akai yana bacci,Annie ta k'arasa da sauri ta kamo hannunta ko magana bata yi masa ba ta wuce da ita bedroom d'inta ta mata wanka ta shiryata cikin wasu English wears riga da skirt,sosai tayi kyau kayan sun zauna mata dai²,ta bata abinci sai da ta k'oshi sannan ta kyale ta,,bayan Nuraz ya fito ya yi break ya dubata sosai,a nan ya tabbatar tana da damuwa sai dai kuma lamarin nata ya shige masa duhu bcos ba hauka take da Allah ya d'ora mata ba kamar na mahaifiyarsa.
Ya kalli Annie da damuwa a fuskarsa yace "Annie matsalar nan fa ina tunanin bana hospital bane"
Annie tayi shiru tana kallonsa har ya gama fad'a mata kan matsalar,ta juya ta kalli inda take kwance tana bacci tace "Yanzun yaya za muyi kenan.!?"
Yace "ina tunanin ko za mu gwada kaita gurin malaman addini maybe a dace a can ko.!?"
Annie tace "to shi kenan,zansa a tambaya mana a cikin gari,idan Allah ya sa an dace sai muje."
Ya jinjina kai yace "Allah sa a dace" tace "Ameen",kusan kwanakin ta goma a gidan Annie ta bada cigiyar a nema mata malaman da suke ruk'yah,a cikin sati na uku Allah yasa aka dace,aka turo mata address d'in malamin,a ranar da aka fad'a mata an samu malamin ta fad'awa Nuraz,yace washe gari zasu je in sha Allah gudun sake b'ata lokaci.
Da safe Annie tana kitchen kamar kullum,though tun washe garin zuwanta gidan data fita sakamakon barin k'ofa a bud'e, Annie take rufeta idan za ta fita,ranar sai aka samu akasi Annien ta manta bata yi locking door ba,tana can kitchen suna aikin had'a breakfast ita da Bareerah,,duka fitar Annie a d'akin babu jimawa ta farka tana ta kalle²,ta sauka daga saman bed ta tsaya,k'ofa ta hango a bud'e da sauri ta juya tayi hanyar fita,kai tsaye ta nufi hanyar bedroom d'insa cos bata manta ba,har ta kawo bakin entrance,yadda ta taho ba zaka tab'a tunanin akwai abunda zai dakatar da ita ba,amma sai ta ci burki a nan ta kasa k'arasawa tana rarraba idanu.
Muryarsa ce take tashi cikin daddad'an sautinsa yana karanta alk'ur'ani cikin suratul bak'rah,ya zo dai² kan ayah ta (102 wattaba'uu..) Bai san da zuwanta ba,saboda ya tattara nutsuwarsa akan karatun da yake,wani irin gurnani ta fara a low tune numfashinta ya fara sama² ta ci gaba da fizgarsa da kyar,tana daga tsaye k'afafunta suka fara rawa kafin ayi taking time jikinta duka ya d'auka,yana ci gaba da karatunsa daga inda yake zaune saman pray mat ya jiyo sautin kamar fad'uwar abu kusa da entrance d'in d'akin,sai da ya kai ayah sannan ya waiwayo,ganin babu komai a gurin ya tab'e baki ya ci gaba,ko ayah d'aya bai sake kaiwa ba ta kurma wani irin gigitaccen k'arar da yasa dole ya dakata ya mik'e tsaye da sauri gabansa yana fad'uwa......
#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
Pᴀɢᴇ 14.
#Dᴇᴍᴏɴ ʙᴜʀɴ
Dai² yana fitowa Annie da Bareerah suna k'arasowa gurin cikin sauri,kwance take a k'asa ta mimmik'e idanunta sun k'afe baka ganin bakin ciki sai zallar farin,ga wani irin gurnani da take kamar dabbar jeji,suka yi tsaye kanta duk sun kasa tab'ata bare su iya d'aukarta su fita da ita,Annie tayi k'arfin hali tace
"Habibiiy.! Ina ganin ya kamata mu tafi da ita gurin malamin nan yanzun"
Ya kalli Annie fuskarsa da damuwa yace "Annie yanzu.!?"
Tace "Ehh yanzu mana,maza taimaka ka kaita mota"
Ya kalleta ya kalli Annie yace "Ni kuma.!?"
Tayi saurin d'agowa ta kalleshi tace "Kai d'in mana,ba kaine namiji ba,kuma dai ai ka san ka fimu k'wari ko.!?"
Ya sake kallon yadda take yi ya d'ago ya kalli Annie yana marairaicewa yace "please Annie ku dai kamata ku kaita"
Ta b'ata rai ta hararesa tana barin gurin tace "idan ba zaka yi ba ka barta nan idan na fito sai ka goya min ita a bayana"
Yana jin tace haka ya san magana ta fad'a masa,babu shiri ya koma cikin room d'insa da sauri ya d'auko car keys ya fito,Annie ta dawo tana sanye da hijab,ya sunkuya ya d'auketa suka fita Annie tana bada Bareerah sak'o ta kula da gidan da Hauwa dake d'aki though ta san har su dawo ba lallai ta farka ba,suma in sha Allah za su dawo yanzun babu jimawa,ta amsa tana biye da su har ta rakasu bakin mota,ya bud'e back seat ya kwantar da ita,Annie da shi suka shiga front seat yaja mota suka fita,suna tafiya Annie taga bai tambayeta inda zasu ba,ta juya tana kallonsa tace "Dama ka san gurin ne.!?"
Ya d'an kallota kad'an ta cikin mirror ya ci gaba da driven yace "Ehh!" Mota tayi remaining silence baka jin komai sai sautin groaning d'inta,har suka shiga unguwar Yakasai babu wanda ya sake yin magana,yana ta bin kwatancen,suka tsaya a bakin line ya gyara parking,da yake gidan malamin babu nisa daga inda suka tsaya,suka fita ya d'auketa har suka k'araso k'ofar gidan malamin,sun d'an tarar da mutane zaune a k'atuwar rumfar gidan,suka tsaya kad'an yana rik'e da ita har lokacin,suna ta jira har mutane suka ragu,aka yi musu iso gurinsa suka shiga,ya kallesu yana musu barka da zuwa ya nunawa Nuraz gefe yace ya ajiye ta,suka gaisa da shi cikin mutunci,bai tambayesu abunda yake tafe da su ba ko dan ganin yanayin da take ciki ma kad'ai yasa shi fahimtar inda matsalar take,ya kalleta yayi murmushi kad'an ya kalli Annie yace "tana da tsarki.!?"
Annie tace masa "Ehh.!" Yace "Alwala fa.!?"
Annie tace "A'ah.!"
Ya kalleta yace "Ku shiga da ita cikin gida ayi mata alwala"
Annie ta amsa tana kallon Nuraz "D'auke ta muje.!"
Babu musu ya d'auke ta suka shiga cikin gidan,aka basu ruwa a buta yana rik'e da ita a jikinsa Annie tayi mata alwala,sannan suka dawo gurin Malam,har lokacin bata daina wannan gurnanin ba,Malam yace "Ajiyeta ta kalli gabas" ya sauketa daga jikinsa ta kalli gabas,malam yasa aka kira masa d'ansa guda d'aya yace "zauna ka rik'e min manyan yatsunta na k'afa" ya rik'e su da kyau kamar yadda malam yace,Nuraz da Annie suna gefe suna kallon ikon Allah,Malam ya rik'o forehead d'inta ya fara karanto ta'awizi yayi basmala after then ya fara karanto ayatur-ruk'yah,wani irin gigitaccen k'ara tayi ta runtse idonta hawaye suka fara bin fuskarta,Nuraz yaji gabansa yana ta fad'uwa,tunda tayi ihun yaji yana neman rasa nutsuwarsa,Annie dake gefensa ta dunga shafa kansa da jikinsa har ya d'an samu k'awrin guiwar ci gaba da zama amma duk a tsorace yake,malamin bai saurara da karatu ba har sanda Aljanun dake jikinta suka ce za su yi magana,yana ta karatu sai daya tabbatar ya galabaitar da su sannan ya dakata suka yi magana da su,duk abunda ya faru sai da suka bashi labarin suma ba laifinsu bane turo su aka yi su shiga jikinta
Yace "wane ne ya aiko ku.!?"
Suka amsa masa "Shugabanmu ne ya aiko mu.!"
Yayi murmushi yace "K'arya kuke.. Za ku fad'a min gaskiya ko saina k'one ku.!?"
Suka yi shiru basu ce komai ba,ya sake maimaitawa nan ma shiru,ya kalli d'ansa dake rik'e da k'afafunta yace "Rik'e sosai mu ci gaba" yana fad'a yaci gaba da karatu,tana ta kuka da iface² bai dakata ba sai daya sake galaibatar dasu,sannan ya maimaita tambayar wane ne ya aiko su.!? Babu gardama ko taurin kai suka ce "Shugabanmu ne."
Yace "me tayi masa zai aiko ku shiga jikinta.!?"
Aljanin dake magana a jikintan yace "Ba shi ta yiwa ba."
Malam yace "Wane ne to.!?"
Yace "Matar Babanta ce"
Malam yayi murmushi yace "Kada kuyi min k'arya,kun san zan k'ona ku ko.!?"
Aljanin yace "Ba karya muke yi ba,itace tasa shi yayi mata aiki,shi ne ya aiko mu muka shiga jikinta"
Yace "Saboda me.!?"
Aljanin yace "saboda soyayyar da mahaifinta yake mata ta yi yawa.."
Malam ya jinjina kai yace "A matsayin me aka aiko ku kuyi a jikinta.!?"
"Suka ce "Mu haukatar da ita ta fita ta bar gida.."
Malam ya sake jinjina kai yace "Ku kuma sai kuka shiga jikinta ko.?"
Suka yi Shiru basu amsa ba,yace "da ku ake amfani ana cutar bayin Allah,bayan kuma bayinsa ne kuma zaku je zaku tarar da shi,shin bakwa tsoron had'uwa da shi ne.!?"
Suka ce "Muna ji.!"
Yace "K'arya kuke yi,da kuna jin tsoronsa da wani abun baku yi shi ba,,yanzun zaku fita daga jikin baiwar Allah ko kuma kuna so mu ci gaba da fafatawa ni da ku.!?"
Suka yi shiru basu amsa ba,ya sake maimaitawa nan ma shiru,Malam ya jinjina kai yana kallon su Annie yace "Baza su tafi ta dad'in rai ba,dole sai na k'ona su"
Yana fad'a ya ci gaba da karatu,ihu taci gaba da yi,can da suka ji azaba suka amsa "Zzzzzzzz... Zzz... Za mu fita..! Kayi hahaha.. Hahak'uri.. Zzz zza mu tafi.."
Malam ya dakata yace "zaku fita.!?"
Suka ce "Ehh.! Za mu fita"
Yace "maza ku fita,ta ina za ku tafi.!?"
A gaggauce suka ce "Ta k'afa"
Ya girgiza kai yace "Ban amince ba"
Suka ce "ta baki" nan ma yace "A'ah.! ku dai zab'i wani gurin"
Suka ce "To to ta hanci"