Showing 51001 words to 54000 words out of 220972 words

Chapter 18 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1185

lalata ba.!? Abun dai da mamaki,kuma dai a gaban idonka kalli yadda ya rik'e ta,mutumin da ba muharramin ta ba,ba mijinta ba ya rik'e ta babu damuwar komai a tare da su,kenan sun saba shigewa juna,kai wollahi gara daka kore su,suje can su ci gaba da lalatar."
   Nuraz ya ji ciwon maganar sosai,afusace har wani huci yake shi kad'ansa yana k'ok'arin juyawa Nusrah tayi saurin sake damk'e hannunsa,ya kalleta with his coloured eyes zai yi magana tayi saurin girgiza masa kai,ba don ya so ba yayi k'wafa suka fice daga gidan.
    
     Bayan sun baro gidan su Nusrah,zuciyoyinsu duka babu dad'i Nusrah har lokacin kuka take,mamaki da damuwar yadda Abba'nta mahaifi yayi furucin shi ba y'arsa bace ita ya hana zuciyarta samun sukuni,,Nuraz ya kalleta yace "U should be sorry for that,and u have to stop shedding ur tears,one day a history will repeat it self,what ever happened,will happen long before we were created and that already written in the book of destiny,,ki godewa Allah da irin ta ki k'addarar,u have a mother,father and other relatives,someone who sits next to u after his mother and a mother's sister,he has no one apart of relatives,,bai san dad'in kasancewa tare da mahaifi ba ko wasu dangi,even da za ki tambaye shi wani abu daga mahaifinsa.!? Zai ce miki ne he don't know,bcos bai sani d'in ba.. But he is always grateful da irin k'addarar da ubangiji ya zana masa,,ki daina kuka ubangiji ya tsara abunda zai faru and komai na rayuwa mai wucewa ne in sha Allah.."
   Wani irin sanyi taji kalamansa sun saukar mata,a hankali ta goge hawayen dake sauka saman fuskarta uncontrollable,silently bata yi tunanin zai ji ba tace "Thank u" ya jinjina kai yace "Babu komai,,but kici gaba da addu'ah in sha Allah zan yi miki nima.."
    Ta d'an juya kanta ta kalleshi kad'an,tausayinsa taji ya kamata da taji ya fad'a mata shi bai san mahaifinsa ba,sun yi tafiya mai d'an tsayi shiru babu wanda ya sake magana,tayi breaking silence d'in da tambayarsa "To amma ina mahaifinkan yake.!?"
   
      Yayi murmushi mai ciwo idanunsa suna tara hawaye yace "I don't know.!"
   
       Tayi saurin kallonsa tace "Kamar yaya.!?"
   
       Yace "Ehh! Haka na taso na ganni ina rayuwa,kin ga gidanmu bamu da yawa,daga ni sai Annie,Mamma na,then get man and maidservant,mu kenan muke rayuwa,ba mu da wasu dangi,babu wanda yake zuwa gidanmu sai abokan kasuwancin mu,muma kuma babu gidan wanda muke zuwa da sunan ziyara.."

        Tana kallonsa tace "To amma ai kace baka da mahaifi,ta yaya mutum zai kasance haka.!?"
       Yace "Haka tawa k'addarar take,dole ne idan har ina son kasancewa cikin bayin Allah na gari,na zama mai karb'ar duk wani kaddarar da zai zo min,mai dad'i ko akasin sa"
       Tayi shiru tana tunani can ta d'ago ta kalle shi,tana son yi masa tambaya amma tana tunanin yadda zai d'auki zancen ta,yana driven shima ya waiwayo ya kalleta,a hankali yace "speak ur mind" tayi saurin girgiza masa kai,yayi tak'aitaccen murmushi yace "Me yasa.!?"
    Tace "Ai babu abunda zan fad'a" ya kalleta sosai yace "Akwai" tace "A'ah! Babu" yayi ajiyar zuciya yace "Na fad'a miki abunda kike son cewa.!?"
    Tayi shiru tana kallonsa,ya waiwayo ya kalleta ya d'aga mata gira yace "Can i.!?" Ta girgiza masa kai alamar ehh,yace "To amma ai ina ji ana cewa duk mutumin da aka haifa ba shi da baba,mutane suna cewa shege ne,,kai kuma fa mene ne.!?"
        Ta zaro kumburarrun idanunta tana toshe baki,she was so excited da taji ya fad'i haka tace "Wollahi ba haka nake nufi ba" yayi murmushi yace "Dole ne ko waye ya ji tarihi na ya kira ni da wannan sunan,duk da na kasance ina da mahaifi,na zo ta hanya tsarkakakkiya,na kasance d'an sunnah kamar ko wane d'a da aka samar bayan biyan sadaki,had'uwar al-waliys,d'aurin aure tare da shaidawar al'ummah a matsayin halatacce.."
       Tayi saurin kallonsa tace "to kuma amma kace baka san mahaifinka ba.!?" Yace "Haka ne ban san shi ba.!" Nusrah tace "to saboda me.!?" Yace "Saboda yace baya so na a matsayin d'an da ya haifa.!"
   Ta yi shiru tana jinjina kalamansa,bata sake magana ba taga ya d'auke hanya,a bakin wani photo studio suka tsaya,bayan yayi parking ya juyo yana kallonta yace "get down" bata kalleshi ba tana wasa da ring d'inta ta d'aga ido ta kalli gurin tace "Me za muyi.!?" Yace "Muje za ki gani",suka shiga yasa ayi mata passports,tana kallonsa ta matso kusa da shi saboda bata so masu aikin su ji tace "Me za'ayi da su.!?" Ya kalleta kad'an yace "K'onawa" ta marairaice tace "Please.! Ba da wani nufin na tambaya ba" ya sake kallonta jin yadda tayi magana a yangance yace "Je suyi miki mu tafi,kada Annie tayi fad'an mun jima" tace "To amma fa idona..!"
    Sai tayi shiru tana sunkuyar da kai,yace "What happen to ur eye.!?" Silently tace "Sun kumbura ne,kuma photon ko anyi ba kyau za suyi ba" ya tab'e baki yace "Go idan anyi naga ba suyi ba sai mu dawo a canja wasu" ta girgiza masa kai a hankali ta wuce,bayan anyi mata an wanke suka karb'a suka fito,sake d'aukan hanya suka yi,tana ta tunanin abunda zaiyi da passports da school documents d'inta,kanta a k'asa tana ta wasa da ring d'inta har suka shigo cikin gida,a parlor suka iske Annie ta fito daga room d'in da Hauwa take,tana kallonsu tace "Wlcm home" suka gaisheta a tare,ta amsa tace "Wai ina kuka je kuka zauna daga cewa yanzun za ku dawo.!?"
     Nusrah tayi shiru tana sunkuyar da kanta k'asa,yana nuna Nusrah yace "Annie gidan su muka je" ta zaro ido tace "Kuka je kuka yi me.!?"
    Yace "School document d'inta muka karb'o" tayi ajiyar zuciya tace "Ina fatan babu abunda ya faru.?"
    Ya kalleta yana tab'e baki yace "Babu",Annie ta kalleshi sosai tace "Ka san ba zan yarda ba ko..!?" Yayi murmushi ya shafa k'eyarsa yace "Ki yarda Annie babu.!" Ta girgiza kai tace "Zan so ace haka ne,amma na tabbata tunda kayi saurin amsawa akwai abunda ya faru" yayi blinking eyes d'insa yana kallon Nusrah da tayi shiru ya bawa Annie amsa "Annie da gaske fa.!" Tace "da gaske me.!?" Yace "Mun d'an samu matsala" ta girgiza kai tace "I knew dole za'ayi haka" har yayi gaba yayi saurin juyowa yace "Annie bafa yadda kike tunani bane" ta harare shi tace "Kai tafi can,,ni zaka fad'awa wannan maganar na yarda.!?"
    Yayi murmushi ya wuce bedroom yana fad'in "Zan fad'a miki abunda ya faru Annie,,bari na fito.."
        Ta girgiza kai bata ce komai ba ta kalli Nusrah da take cikin damuwa tace "Daughter wuce ki ci abinci kiyi shirin bacci",ta d'ago a hankali ta amsa sannan ta wuce dining.
   
     Tana zaune tana cin jellop spaghetti da yaji kayan lambu ya shigo cikin parlor'n,Annie tana zaune a parlor'n tana kallon Nusrah dake cin abinci kamar bata so,ya k'araso inda Annie take ya kwanta a jikinta,Nusrah ta d'ago idonta ta ganshi kwance a jikin Annie,ta d'auke kanta da sauri ganin yana kallonta,haka nan taji gabanta yana fad'uwa,ta sake d'agowa taga still ita yake kallo,ko kwakwkwaran mintuna goma bata k'ara ba bayan fitowarsa ta mike a gurin ta tattara komai dake wajen ta nufi kitchen,ta fito bayan ta wanke kayan da ta shiga dasu ta wuce su tana yi musu sai da safe,Annie ta amsa mata,shi kuma ya bita da ido,Annie ta shafi kansa tace "Habibiiy.! Me ya faru da kuka je can d'in.!?"
   Yayi saurin juyowa ya kalleta daga kwancen da yake yace "Annie d'an sab'ani ne fa kad'ai" nan ya kwashe komai ya fad'a mata,Annie tayi shiru idonta yana tara k'walla tunawa da nasu tarihin da tausayin Nusrah daya cika mata zuciya tace "Me yasa y'ay'a mata a ko wace lokaci muke kasancewa a damuwa.!?" Nuraz yayi saurin mik'ewa ya zauna fuskarsa tana rikid'ewa yace "Annie please.! Kiyi hak'uri dan Allah kada ki ce za ki bawa hawaye damar zuba daga idanunki,yanzun ba lokacin da za'a ce kina sa damuwa a ranki bane,u know the best kin san matsalar da damuwa take haifarwa,ke shaida ce akan hakan,ko wani kika gani yana shiga damuwa ke mai bashi shawaran kada yayi ne,,duk abunda ya faru rubutacce ne daga ubangiji,addu'ah ya kamata muyi ubangiji yasa muna da rabon cin duk wasu jarabawarsa akanmu."
    Kallonsa Annie ta ci gaba da yi yana magana cikin sanyi,shi kansa da zai samu dama tana fara kuka zai saki nasa hawayen,but a yanzun yana tunanin lokacin kuka a gurinsu ya gama wucewa,a hankali tayi ajiyar zuciya tana maida hawayenta tace "Shukhraan'kthiir habibiiy."
    Ya girgiza mata kai yana yin ajiyar zuciya,basu wani jima ba sosai bayan da ya gama kwantar mata da hankali,ya tabbatar bata tare da wani sauran damuwa ya yi mata sallama ya kama hanyar room d'insa.

     Nusrah tana shiga bedroom ta fara cire kayanta,ta d'aura towel a hankali ta wuce bathroom cikin rashin kuzari.....

   
#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*


*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2


Pᴀɢᴇ 17.
#Vɪᴄɪɴɪᴛʏ

Wanka ta fara yi bata tsaya shafa komai ba,ta saka kayan bacci ta kwanta,tunda d'akin yayi remaining silence taji zuciyarta tayi mata rauni,a hankali ta fara tunanin yadda rayuwarta ta baya ta kasance mai cike da soyayyar iyayenta har ta kai shekaru sha biyar bata san wani abu damuwa ba,bcos a lokacin tana tare da farin cikinta,sai ga shi within 2 years gaba d'aya al'amura sun canja mata,bayan k'addara ta raba ta da mahaifiyarta,duk wani farin cikinta ya fara rushewa,again yau rana a tsaka an sake wayar gari mahaifin da take tak'ama da shi shima yayi mata nisa,wasu irin hawayen k'unci ne suka ci gaba da zirarowa ta fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciya,knocking aka yi tayi saurin goge hawayen kafin ta kwanta ta lullub'e jikinta ya shigo,ya kalleta yace "Annie fa.!?"
Tayi ajiyar zuciya tace "bata shigo ba" har ya juya zai fita ya fasa ya dawo ya zauna kad'an daga gefen bed ya kalleta na wasu mintuna yace "Kuka ko.!?" Tayi saurin girgiza masa kai tana sauke idanunta k'asa,ya lumshe idonsa ya bud'e yace "D'azun na manta ban tambayeki wani abu ba!" Ta d'ago kad'an bata yi magana ba

Yace "where's ur mom.!?"

Taji hawaye sun sake gangaro mata tace "Allah ya yi mata rasuwa." Yace "Eyyaahh.! Allah yayi mata rahama." Tace "ameen" suka d'anyi shiru na wani lokaci,ya mik'e slowly yace "good night" tayi shiru bata amsa ba,ya juya yana tafiya ta bishi da kallo,har ya je bakin door d'in zai fita ya waiwayo zai yi magana yaga shi take kallo,tayi saurin d'auke kanta,ya girgiza kai yace "ko na dawo ne.!?" Tayi saurin kallonsa tana k'ik'k'ifta ido,haka nan ranar yau take jin ta zame mata wata daban,tun abunda ya faru a gidansu da yace tayi addu'ah take ta maimaita "Allahumma laa sahala illaa maa ja'altahu sahala wa'anta taj'alul-hazna izhaa shi'ita sahala.. Allaahumma inniiy a'uzhu bika minal-hammi walhazan,wal'ajazi walkasal,walbukhli waljubn,wa-dhala'id-daini wa-ghalabatir-rijaal.. Laa ilaaha illallaahul-azhiimul-haliim,laa ilaaha illallaahu rabbul-arshil-'azhiim,laa ilaaha illallaahu rabbus-samaawaati wa rabbul-ardhi wa-rabbul-arshil-kareem.."
Ta ji sanyi a zuciyarta,snapping yayi tayi saurin kallonsa yace "Uhn" ta tsaya kame²,ya tsaya a inda yake yana kallonta yace "What.!?" Ta girgiza masa kai alamar babu,yace "Allah yasa" tayi saurin kallonsa,ya juya yaci gaba da tafiya,yana fita babu jimawa Annie ta shigo,tana kallonta tace "Daughter ba kiyi bacci ba.!?" Ta gyad'a kai tace "Yanzun zan yi" tace "Ok! Allah ya bamu alkhairi"
Nusrah ta amsa sannan ta kwanta ta rufe jikinta bcos garin akwai sanyi sosai saboda ruwan da aka yi da safe,bayan kwanciyarta tunani still ta ci gaba da yi,tana tuno yadda komai ya faru a d'azun,damuwar daya gwada akan matsalarta da yadda suka yi hira yasa tayi luf a cikin spread,hiran da yayi mata da labarinsa taji inama lokaci yana komawa baya,da ta tambaye shi asalin labarinsa,wani irin tausayinsa taji data tuno maganarsa,a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace "Every being has his own problems,and a reason to live,,ya rabbi kai ka tsara mana yadda zamu rayu,ubangiji kasa duk k'addarar da zamu gamu da ita ta kasance mai sauk'i a gare mu.."
Ta jima sosai tana tunani kafin bacci ya d'auke ta,shima a b'angarensa lokacin da ya barta,d'akin da mahaifiyarsa take ya fara shiga ya duba ta,sannan ya wuce bedroom d'insa,daya kwanta kasa bacci yayi yana ta tunani sai da dare yayi nisa sosai.

Da safe lokacin ya fito ya samu Annie a parlor ya zauna kusa da ita kamar wani orphan,Annie ta kalleshi tana shafa kansa tace "What happen habibiiy.!?" Ya sake marairaicewa yace "Annie.! Tafiyar nan fa saura kwana uku,,ni ban san yaya za muyi ba.!"
Annie ta kalleshi sosai tace "Kamar yaya baka san ya za'ayi ba.!?" Yace "Annie gani nayi wai tunda tare za mu tafi da ita,waye zai zauna da ita a can d'in,kinga akwai buk'atar mu tafi da wani ko.!?"
Ta tab'e baki tace "Na san da haka,but ma'anar tambayar naka na kasa fahimta" yayi shiru na wani lokaci yana tunani can ya d'ago yace "Annie kawai fa na tambaya ne nima" tayi tsaki tace "Shirme kawai" yana kallonta yace "Annie" tace "Mene ne.!?"
Yayi shiru bai ce komai ba,ta kalleshi ta d'auke kai,ya d'ago a d'an tsorace cos bai san yaya zata d'auki lamarin ba yace "Annie.!" Tayi saurin juyowa ta kalleshi,ya sauke idanunsa k'asa yace "Dama fa ina son fad'a miki ne,ko za mu tafi da ita.!?"
kai. Tayi saurin tarar numfashinsa "Ku tafi da wa.!? Ku biyu kake nufin kace min za ku tafi ko me.!?" Yayi saurin girgiza kai,tace "To kai da waye.!?" Yace "Da ita" tace "ita wa.!?" Ya kalleta yace "Waccan yarinyar" ta tsaya kallonsa da mamaki tace "Wace yarinyar.!?" Yayi jim a hankali ya furta "NUSRAH.!"
Tana kallonsa tace "Saboda me.!?" Bai iya d'ago kansa ba yayi shiru ya kasa amsawa,tayi tsaki tace "Saboda ni bani da amfani ko dan mene ne kake son tafiya da ita.!? A hakan ma ka rasa wacce zaka ce min sai yarinya k'arama da bata gama sanin kanta ba bare ta iya sanin yadda zata jurewa wahalar jinya. Ni mene ne amfani na kenan.!?" Yayi shiru bai ce komai ba,tace "Tambayarka nake,ka bani amsa." Ya d'ago a hankali yace "I'm sorry Annie,but ba da wata manufa nace haka ba" ta harare shi tace "Fad'a mini manufar da tasa kace hakan" ya sake yin shiru,tayi tsaki tace "Zancen banza zancen wofi,idan banda yarinta da shiririta ina raye da lafiyata kana ganin akwai wanda yafi cancanta ya kula da Hauwa.!?" Ya girgiza mata kai yace "Babu" tace "Ka san da haka kake son tafiya da wata kenan.!? Idan kunje amfanin me za tayi maka kenan.!?" Ya gyara zama a hankali yana sunkuyar da kansa k'asa yace "Dan Allah Annie kiyi hak'uri,i swear to God abunda kike tunani ba shi bane,duka manufar bai wuce na son nisanta ta da k'asar nan ba,I've already told u abunda ya faru jiya,wannan dalilin yasa na yanke shawaran sanar dake ko za'a nema mata admission a can itama cos hakan zai taimaka mata sosai,ina tsoron abunda ya faru da mahaifiyata ya faru da wani,yarinya ce ita k'arama,besides ba lallai ta iya jurewa ba saboda shekarunta"

Annie tayi shiru tana saurarensa har ya dasa aya taja ajiyar zuciya a hankali,cikin sanyi tace "Kana ganin tafiya da itan zai bata kariya.!?"

Ya gyad'a kai yace "Haka dai nake tunani,kamar idan bata k'asar abun bazai yi affecting tunaninta ba sosai" ta gyad'a kai a sanyaye tace "Shi kenan zanyi tunani,amma ka san babu yadda za'ayi ko na amince na barku tafiya da ita,dole tunda ka kawo maganar neman admission akwai buk'atar wanda zai zauna da ku duka,kuma ni a nawa tunanin idan haka ne gara mu tafi gaba d'aya,zuwa lokacin da Allah ya nufi zamanmu a can" yayi ajiyar zuciya yace "Hakan ma ina tunanin zaifi mu tafi taren" Annie ta sake sauke ajiyar zuciya tace "Shi kenan,Allah ya iya mana" yace "Ameen".

Kwanaki biyu tsakanin zuwansu gidan su Nusrah shirin tafiyarsu ya kankama,duk abunda ake buk'ata Annie da Bareerah sun shirya musu,Nuraz ya je ya nema musu Visa tafiya U.K,washe gari da safe jirginsu ya bar k'asar,su biyar ne duka har mahaifiyarsan,Nusrah tana gefen window tayi shiru tana tunanin rayuwarta,ita da Nuraz seat d'insu yana kusa,Annie,Bareerah da Hauwa kuma suna bayansu,har suka sauka babu wani kwakwkwaran kalmomi goma da suka had'a su,daga airport suna sauka charter cab suka d'auka zuwa Albert street,babban apartment suka kama haya tunda ba zama duka suka dawo yi k'asar ba,suna sauka suka tarar komai a gyare a muhallinsa,gidan ta ko ina ya tsaru babu abunda za ace bai yi ba,sallolin da ake binsu suka fara yi,suka sake gyara gidan Nuraz zai fita ya kalli Nusrah da tayi shiru alamar tana duniyar tunani yace "will u go with me.!?" D'agowa tayi ta kalleshi da manyan idanunta,a hankali ta juya ta saci kallon Annie,har ranta ta ji tana son zuwa amma bata san me zata ce Annie ta barta ba,Annie bata kalli inda suke ba amma duk abunda suke yi tana sauraren su,tab'e baki yayi ya wuce zai tafi yana fad'in "Annie.! I'll be back soon" tace "Allah ya tsare",Nusrah ta sunkuyar da kai tana wasa da middle finger d'inta,Annie ta kalleta tayi murmushi ta san tana son fitar,har ya fita sannan Annie ta kirata "Daughter.!" Da sauri ta d'ago kanta,Annie tayi mata murmushi tace "Would u like to go out.!?" Murmushi ne

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login