Showing 186001 words to 189000 words out of 220972 words
ya rufe bakinsa her brain had already calculated what to say,tana kallon sauran jama'ar da suka yi shiru suna saurarensu tace "Ehhh! Gaskiya bamu kyauta ba,sai dai yaya za mu yi,tafiya ta same mu da sassafe,sai muka ga bai kyautu a irin wannan lokacin mu kwankwasa muku k'ofa ba kuna bacci" saurin tarar numfashinta yayi "Amma Hajiya ko da sak'on waya kuka tura ai za mu san abun da yake faruwa" shiru ta d'anyi cikin kame-kamen abunda za ta fad'a,da sauri ta furta "To sai dai muce kuyi hak'uri,wayoyin babu chaji muka fita da su,sannan bamu dawo da wuri ba sai wajen 2:00am,kaga dai wannan lokacin shima bai dace mu kwankwasa muku gida ba" duka jama'ar gurin were pleased with her statement,it was there suka fara fashewa,masu Allah ya tsare suna yi,wanda suka zo d'aukan labari suka fita suna jin haushi. Bayan tafiyar mutanen Hajiya Karima tayi bayyanannen ajiyar zuciya tana fad'in "Waii Hajiya! Allah ya so ba ni kad'ai nake zama gidan nan ba,yau ai da ban san me zan fad'a ba idan mutanen nan suka tambayeni" Hajiya Mariya tayi makirin murmushi as she passes zuwa cikin parlor da wani takun tafiya irin nasu da suka san ta kan duniya,tun daga hakan basu yarda sun bari anji kan yadda al'amarin ya faru ba,a cewarsu za ayi musu dariya.
Two weeks after the incident,duk inda suke tunanin samun mafita sun buga sai dai rashin nasara,and at this time duka abunda yayi saura hannunsu ko half na fili bazai siya musu ba bare gida,tun lokacin yau idan suka samu labarin wani malami da aikinsa yake ci a gari kaza,a goben za su tattara su tafi,idan sun tarar da ba yadda suke buk'ata ba,goben suka samu labarin wani,without thinking of abunda zai je ya dawo za su sake d'iban jiki su tafi,cikin wannan yanayin duk abunda suke tak'amar suna da ya fara janyewa,lokaci kuma yana ci gaba da tafiya.
Two weeks later,which is two months da mutuwar aurenta,it was during this time suka samo wani bokan da aka ce idan yayi musu aikin tabbas zai yi za su yi mamaki,but cikin ayyukansa akwai sharud'a,suka ce sunji aun amince,yadda aka ba su labarinsa duk haka suka tarar,bayan zuwansu kafin suyi masa bayani ya dakatar da su,ya zayyana musu duk abunda yake tafe da su,Hajiya Karima ta amsa shi da haka ne duk abunda ya fad'a babu musu,boka ya kece da dariya,bayan ya dakata yace "Za'ayi muku aiki,sai dai akwai sharud'a" Hajiya Mariya ta cafe zance da fad'in "Ka sanar da mu kowane irin sharadi ne,za mu bi duk abunda kasa mu aikatawa,matuk'ar buk'atarmu zai biya" Boka yace "buk'atar ku zai biya sai dai sharud'a" jikinsu yana rawa suka ce ya fad'a,it was there b'ataccen ya fara shirya musu zancen "Da fari duk wani aikin da za muyi ba zai yi ba har sai Hajiya Karima kin koma gidan Alh Abubakar kin nemo kusanci da wani cikin na jikinsa like mata/y'a/mahaifi/k'ani/hadiminsa" Hajiya Mariya cikin kid'imewa tace "Aiki ga mai k'are ka,yanzun ta ina za ta samu wannan damar bayan lokacin da ya wuce munyi k'ok'ari mun raba shi da kowa,shin ta ina ne za ta samu damar shiga gidan har akai ga yin haka?" Bokan ya sake kecewa da dariya "Wannan duk ba damuwa bane,idan har tana son cikar burinta,dole sai ta shiga gidan nan,ita da kanta za tayi wannan aikin,amma akwai taimakawar shaid'anu!" Calmly Hajiya Mariya ta washe baki "Aikin sun ma ai zai fi sauk'i fiye da mu da sai mun faki idanu,me zai sa baza mu biya ba,sai su aiwatar da aikin kawai" Boka yana kallon Hajiya Mariya da wani irin muryarsa mai ban tsoro yace "Ba ita za tayi ba,su za mu sa su aiwatar!" Kan Hajiya Mariya ya kulle jin abunda ya fad'a tace "Ta yaya kenan uban shaid'anu?" Ya sake kecewa da dariya,bayan ya d'auki lokaci ya dakata yace "Wannan ba huruminki bane,kada ku shiga abunda ba ku da ruwa cikinsa!" Hajiya Mariya cikin gamsuwa tace "An gama shu'umi uban la'anannu!" Hajiya Karima was sitting on the side tana tunanin yadda aikin zai kasance,da farko bokan yace aljanu ne za su yi ba ita ba,and yace she had to look for closeness with someone cikin family'n Alh Abubakar Kumo,how can she get this chance? Duk ba ma wannan ba,ita yadda za ta shiga gidan shi ne abunda ya d'aure mata kai,a bayan auren sun ta raba shi da kowa nasa shin ta yaya ne wani d'an uwansa zai bari ta rab'e shi a yanzun? "Where's Umar Farouk?" Zuciyarta ta tambaye ta dai² lokacin da take neman mafita,wani irin cafka ta kaiwa wayarta,da sauri ta d'auka ta fara lalube,in less than three minutes ta hango lambarsa da tun wancan lokacin bayan ta samu damar had'a connection da shi zuwa ga Abbah har ya aureta take ajiye da ita,bata jira gama yanke shawaran abunda ya kamata tayi ba ta danna masa kiraa,wayar tana shiga Farouk ya d'auka had'e da fara zuba mata kirari,Hajiya Karima ta furzar da iska mai zafi maimakon abun ya burgeta kamar ko wane lokaci sai taji wani irin k'unci ya lullub'e zuciyarta,har a lokacin suna zaune gaban bokan nasu da gaggawa ta furta "Farouk kana ina ne?" Daga gefen Farouk ya amsa "Hajajju wani abu ne kike nemana da gaggawa?" Hajiya Karima tace "Idan babu damuwa ina son ganinka" Farouk yana jin ta ce haka yace "Tabbb' d'i jan! Ai wollahi Hajiya ba na kusa,maganar da muke yi da ke yanzun haka ma ina shirin barin k'asar ne" Hankalin Hajiya Karima a tashe ta tari numfashinsa "Zuwa ina?" Farouk yace "Wollahi daga gida aka yi min waya mahaifiyata ba ta da lafiya jikinta yayi tsanani" Hajiya Karima cikin tsananin tashin hankali tace "Idan ka tafi sai yaushe za ka dawo kenan?" Farouk yace "Gaskiya babu lokaci,dawowa na sai lokacin da Allah yayi kawai" Hajiya Mariya ta tab'a Hajiya Karima tana tambaya "Me yake faruwa ne?" Hajiya Karima ta kalleta idanunta sun k'ank'ance tace "Shi kenan Farouk,sai ka dawo d'in za muyi magana",har suka gama maganar suna shirin ajiye waya Farouk yaji bata tambayi mai jiki ba,har zuciyarsa sai yaji babu dad'i,za ta kashe wayar kenan Farouk yace "Hajiya wai kuwa kina da labarin Yallab'ai ya yi aure?" Hajiya Karima tana yamutse fuska tace "Wane ne yayi aure?" Farouk yana sakin murmushin mugunta a ransa yace "Bari nayi miki abunda ba za ki ji dad'i ba tunda tsayin rayuwarki baki san mai miki mutunci ba" a fili yace "I'm talking to ur ex-husband Alh Abubakar Kumoo!" Wani irin zabura tayi tana zunduma ashar,Hajiya Mariya tayi saurin rik'o ta,a fusace ta fizge hannunta tana fad'in "Kan uba! When did he get married?" Farouk yace "Ina tunanin wata d'aya kenan yanzun" hankalinta a mugun tashe take girgiza kai jikinta duk sai rawa yake,kallo d'aya za kayi mata ka tabbatar da tsananin tashin hankalin da take ciki,ko gama sauraren Farouk bata yi ba,da taji ya ce bari ya turo mata I.V d'in dan ta tabbatar ta yanke kiran sai huci take idanunta sun sake k'ank'ancewa,duk abunda yake faruwa a gaban Bokan sun aka yi aka gama,lokaci d'aya fuskarta ta yi jaa because she never thought Abbah would get married this soon shi yasa ta sakankance,bata kai ga ajiye wayar ba sak'on Farouk ya shigo,tana bud'ewa idanunta suka sauka kan sunan Abbah,hankalinta ya sake tashi fiye da farko,ta d'ago idanunta da suka k'ank'ance sunyi wani irin jaa mai ban tsoro tana kallon witch d'in ta furta "Duk abunda zai faru sai dai ya faru amma ko zan yi yawo tsirara sai na raba auren nan,Abubakar baka isa ka rabu da ni sannan kayi tunanin zan bari ka zauna da wata mace daban ba!" Boka yana jin furucin da tayi ya kece da dariya,ta zuba masa ido tana kallonsa zuciyarta tana sake tunzurota da mugayen k'uduri,cike da fusatuwa tace "ina so a raba auren sun nan!" Boka yana ci gaba da dariya yake nunata da hannu,sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita da watso mata tambaya "Me kike so ayi musu?" Tace "Ni dai komai ma ayi,amma kada su zauna k'ark'ashin inuwa d'aya!" Wasu irin d'alasiman tsafi ya fara furtawa idanunsa a rufe,bayan wani lokaci yayi saurin bud'e idanunsa,yana kallonta da wasu irin jajayen idanunsa yace "Canza wani buk'atar wannan bazai yi ba" a razane ta kalleshi tace "Kamar ya bazai yi ba?" Yace "Abunda na gani kenan,su duka suna tare da tsari daga ubangijinsu,raba su abu ne mai matuk'ar wahala" Hajiya Karima ta runtse idanunta felt like a chilli powder was poured on tace "Ni dai kawai ayi duk yadda za ayi a raba su" sake rufe idanu yayi yana ci gaba da sambatu,ba'a d'auki lokaci ba ya bud'e idanunsa ya sauke kan Hajiya Karima da fad'in "Akwai hanya d'aya idan kin amince,sai dai akwai had'ari!" Bai k'arasa fad'a ba ta amsa da fad'in "Whatever a danger na amince!" Bokan ya jinjina kai ya juya gefensa dama da hagu sannan ya kalleta yace.....
#Ku k'ara hak'uri da ni please,all these days wayana take ba ni matsala.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
🎉 *U stood with me every time i snapped,u made my every childhood experience a memorable one,u are my best friends since all these years,and u are the reason i believe in myself. Thank u for all the awesome times we shared 😍,wish u a very happy birthday habibtiiys.♥*
*NI'IMATULLAH (Aunty Hassy) & RAHMATULLAH (Aunty Hussy).🎂*
Pᴀɢᴇ 50.
#A ɴᴇᴡ ʙɪʀᴛʜ
Yace "Sharad'in aikinki shi ne duk abunda muka yi idan bai yi tasiri akan su ba zai dawo gareki!" Idanun Hajiya Karima's were closed and she saw nothing except d'aukar fansa,ba tare da tunani ba tace ta ji ta amince,sun yi hakan da shi ya fi a lissafa tace ita dai ta amince,Boka yace "d'aga hannunki na hagu sama!" Tayi kamar yadda yace,sai ga abu kamar tandun kwalli na k'arfe da wasu irin layu da aka rufe da jar fata,a tsorace ta d'aga kai tana dubawa,taga babu kowa a kusa da ita,lamarin ya girgiza su sosai har ita Hajiya Mariya,Boka yayi dariya kafin ya d'ora mata bayani "lallai ki tabbatar kin adana wad'annan kayan,idan kin yi wasa da su shaid'anu za su dawo mana da su,ranar da za kije can gidan,za ki tafi da su duka,shi kwallin idan kika je shiga za ki saka a idonki na hagu kad'ai,kina shiga ki kira sunanta sau uku amma ba yadda za ta ji ba,dakarun shaid'anu da za mu wakilta suyi aiki,za su k'arasa sauran aikin,yayin da za musa taji kamar ana kiranta,a wannan lokacin ki tabbatar kina cikin gidan,da zaran ta ji za ta waiwayo,amfanin kasancewarki cikin gidan shi ne tana ganinki za ta rasa nutsuwarta,za tayi tunanin ke kika kirata,za ta amsa kiran,da zaran ta amsa,shi kenan buk'atar ki ta biya,sai ki binne layun a cikin gidan ki fito,aikinki ya kammala sai jiran sakamako!" Hajiya Mariya dake gefe ta washe baki "Wannan ai duk babu mai wahala a ciki,ko ni zan iya aiwatarwa indai shi kenan abunda za ayin" Boka dai bai sake cewa komai ba bayan nan ya salleamrsu da fad'in "za ku iya tafiya sai dai daga nan zuwa kwanaki biyu ina jiran zuwanku,shi kuma sakamakon aiki sai nan da wata guda!" suka amsashi sannan suka kama hanyar tafiya,har suka baro cikin surk'uk'in dajin babu wacce ta sake magana. Tafiyar awanni biyu da mintuna ta dawo da su cikin gari,tun da suka dawo Hajiya Mariya take zuga Hajiya Karima kan lallai kada tayi sanya,ta hanzarta a gobe taje ta aiwatar da aikin zuwa jibin su koma,Hajiya Karima tayi na'am da batun Gwaggonta,bcus ita kanta ta damu gari ya waye taje ta gabatar da aikinta kamar yadda bokan yace.
At about 11:05am Hajiya Karima sun gama shiryawa,Hajiya Mariya tana kallonta fuskarta d'auke da makirin murmushi take yi mata kirari,literally duk mai hankali yaji ana yi masa irin wannan kirarin he most knows there's no love cikin yabon da ake yi masan,tare suka fito bayan sun yiwa Hajiya Amina sallama suka wuce gidan Abban,11:40am a bakin get d'in gidan yayi musu,tun daga nan suka fara rigima da get man saboda ya sanar da su Abbah ba ya k'asar,Hajiya Mariya ta d'age kai tace "da waye yace maka wajensa muka zo? Idan za ka bud'e get ka bud'e mu wuce,ina ce aikinka kenan gadi?" Da suka takura sai sun shiga tunda yaji suna cewa they would call Abbah and tell him ya hanasu shiga,sai bai yi tunanin komai ba ya bud'e musu get suka shige suna zaginsa uwa da uba,shi dai bai sake kula su ba har suka yi nisa da get.
Suna tsayawa a varenda dai² bakin entrance,Hajiya Mariya ta waiwaya taga babu kowa tayi ma Hajiya Karima alama,da sauri suna waiwaye irin na mutumin da ba shi da gaskiya ta d'auko kwallin tasa then ta mayar jaka suka yi knocking,suna jin tafiya kafin azo bud'ewa Hajiya Karima ta kira sunan Annie as their witch says and ta gani jikin Invitation card,suna jin takun takalmi a kusa sosai suka kalli juna,they smile together and gazing into the parlor lokacin da ake bud'e k'ofar,idanu hud'u suka yi da Binitta,ran Hajiya Mariya ya d'an sosu,but ta yi k'ok'ari ta danne tana kallon Binitta tace "To azagwai har yanzun ashe ana nan? Ba mu hanya mu wuce ko?!" Binitta tayi murmushi tana kallonsu duka bata tanka maganar Hajiya Mariya na farko ba tace "Aunty sannu de zuwa" Hajiya Karima bata ce komai ba sai d'aure fuskar da ta sake yi,Binitta ta basu hanya suka wuce and walked up behind them,suka zauna cikin parlor d'in sai kallon yadda aka sake gyara gidan suke yi,suna jinjina uban dukiyar dake cikinsa,suka wani tab'e baki a tare had'e da yin tsaki,Binitta bata tsaya ba taje ta kawo musu drink da snacks,ta ajiye musu sai murmushi take yi da gani ka san tana cikin farin ciki yanzun,Hajiya Mariya ta kalleta tana yatsina fuska tace "Ina masu gidan?" Binitta tayi y'ar dariyar da ta bayyana hak'oranta tana nuna musu entrance,suka waiwaya a tare because they all thought su d'in ne a wajen,sai da suka ga wayam suka yi tsaki,cikin hayaniya Hajiya Mariya ta waiwayo kan Binitta "What kind of stupidity is this? Ana tambayarki kin mayar da mutane sa'annin ki?" Binitta bata ji haushi ba ta sake yin murmushi tace "Ai Hajiya baya k'asar,sun yi tafi da boss!" A tare suka zaro ido suna tambaya "Ehhh!?" Ta kad'a musu kai tace "Tunda akayi musu aure sunka yi tafi har yanzun basu dewo ba" a rud'e Hajiya Mariya ta kalli Hajiya Karima,saboda rud'ani da tashin hankali Hajiya Karima doesn't know when ta d'ora hannu akai tana fad'in "Na shiga uku!" Hajiya Mariya ta yi shiru duk ta rasa abunda za tace sai kallon yadda Hajiya Karima tayi take,da sauri tayi mata alama da ido,ta had'iye saliva's da kyar,k'ok'arinta ta saita nutsuwarta a gaban Binitta but abu ya fi k'arfin ta,sai wani irin abu take yi ita ba wacce ta samu matsalar kwakwalwa ba ita ba mai lafiya ba,haka suka tashi jiki babu k'wari ko sallama nasu yiwa Binitta ba,instead of da suka fito su hak'urewa k'arasa aikin,here Hajiya Karima ta dage lallai sai su binne layun,Hajiya Mariya tace a'a su yi waya su tambayi bokan,Hajiya Karima ta kafe lallai sai anyi saboda haka Boka yace su yi,ganin yadda take wasu irin attitude ba cikin nutsuwarta ba dole Hajiya Mariya barinta tayi yadda take so,tana gamawa suka fita daga gidan,but hankalin Hajiya Mariya ya kasa kwanciya saboda abunda take ganin Hajiya Karima na yi like she had a problem,da suka koma gida taji ta kasa nutsuwa so she calls the witch over the phone take sanar da shi what is about to happen,here ya bud'e musu wutar masifa akan me yasa suka binne layun? Da suka je basa nan da sun kira sun fad'a masa kafin su aikata hakan ai,Hajiya Mariya tace "Yanzun yaya za ayi?" Yace "Yanzun kam sai abunda kuka gani,tun farko na sanar da ku sharad'in aikin,kuka ce kun amince,so yanzun babu abunda zan iya yi muku" hankalin Hajiya Mariya ya tashi tayi shiru tana kallon Hajiya Karima tace to "uban shaid'anu yanzun kai babu abunda za ka iya yi mana ne na taimako?" Yace "babu! Sai dai ku jira sakamakon abunda zai faru nan da zuwan kwanaki talatin" Hajiya Mariya tace "me zai faru boka?" Strictly yace "duk abunda ya faru tsayin lokaci da duk wasu mugun k'ullin da kuka yi da hannunku,za ta tona muku asiri.." Bai k'arasa ba Hajiya Mariya ta kurma ihu tana fad'in "mun shiga uku,uban shaid'anu ka taimake mu,wollahi idan asirin mu ya tonu mun bushe" wata mahaukaciyar dariya ya fashe da shi har sai da Hajiya Mariya taji haushinsa,a fusace tace "dole mu bar garin nan,mu gudu kawai mu nemi wani wajen mu k'arasa rayuwarmu zai fiye mana sauk'i" Boka ya sake shek'ewa da dariya yace "hakan ba mai yiwuwa bane,saboda duk inda kuke wata rana dole asirin nan da kuke b'oyewa zai bayyana,dole wanda aka yiwa su sani,sai dai kuma idan mutuwa.." Bai k'arasa ba Hajiya Mariya ta zabgaga masa uban ashar ta kashe wayar had'e da jifa da ita,ta daki bango ta tarwatse.
(A raina nace kin huta,da kin rik'e kya raka sauran rayuwarki da ita)
Since that day incidence d'in ya faru kullum sai Karima ta fito da wasu sabbin attitude,abun nata tun baiyi k'arfi ba har al'amarin tan ya fara bawa Hajiya Mariya tsoro ta d'auke mata wuta ta daina shiga al'amuranta,da al'amarin tan yaci gaba da lalacewa ta fara surutai marasa kan gado,abun yana damun Hajiya Mariya sai take rufe ta a d'akin,duk neman da Hajiya Amina mak'ociyar su ke zuwa yi sai Hajiya Mariya tace bata garin ta yi tafiya,a hakan kwanaki suka fara juyawa zuwa sati abu kamar wasa har aka fara neman shafe kwanaki 20. The days are long gone,yayin da zuwa wannan lokacin komai ya gama k'azanta,al'amarin Hajiya Karima sam ba'a cewa komai,a ranar da