Showing 183001 words to 186000 words out of 220972 words

Chapter 62 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1189

giving right? Why Hayat za ka tada hankalinka akai?" Yayi k'asa da idanunsa yana kallonta da wani irin fuskar damuwa "Roohii! u know i love children,and this is what i was waiting for" quickly tayi nodding masa kai cikin damuwa "I know Hayat! But ba kai d'aya bane,duka muna buk'atar yara da za su d'auke mana kewar rashin y'an uwa,idan muka dage da yin addu'ah in sha Allah za mu samu" jikinsa ya d'an yi sanyi da kalamanta,a hankali ya lumshe idanunsa yana furta "Allah ya amsa!" Tace "Ameen",daga hakan bai sake cewa komai ba ya saketa,har ta juya za ta tafi,ganin bai saki fuskarsa ba ta rik'e hannunsa ta shagwab'e fuska tana fad'in "To ka yi min murmushi please" ya kalleta kad'an but he couldn't saboda damuwar da ke ransa,tayi wearing fuskar tausayi tace "Please! Ka sani ma ko mun samu da daren" tana mannuwa a jikinsa,wani wawan ajiyar zuciya yayi looking at her with a wide smiling face,because har ransa ya ji dad'in furucin tan,a ransa yana yin addu'ar Allah yasa abunda ta fad'a ya tabbata,sai da ta fara mayar masa da murmushin then suka wuce tare suka yi wanka,bayan sun fito daga wanka sun shirya juna cike da so da nuna kulawa kamar ba sune cikin damuwa ba yanzun,parlor suka fara fitowa da yaji kayan more rayuwa,after sun yi breakfast they began to look around kamar yadda Daddy'nsu Rafeek yace idan akwai abunda bai yi musu ba sai a canja,sai da suka shiga ko ina sannan suka dawo bedroom d'inta da basu shiga ba tun lek'awan da suka yi da dare,suna shiga ya wuce saman bed ya kwanta yana fad'in "Washhh! I'm tired Roohii!" While yana sake kallon d'akin da mamakin adadin dukiyar da aka narkar,Nusrah kam tun shigowarsu ganin ya wuce ya barta sai ta tsaya ta k'i yarda ta zauna,yaji shiru bata k'araso kusa da shi ba,a hankali ya d'ago kansa yana kallonta,da ido yayi mata tambayar me yake faruwa? Ta kwab'e fuska tana cewa "Ba kai ne ka barni a tsayen ba" yana rage girman idanunsa ya mik'a mata hannunsa yana sakin mata makirin murmushinsa nan,a yangance ta fara tahowa ta kama hannunsan ta haura saman jikinsa,ya rungumeta sosai yana shak'ar k'amshinta da shafa jikinta,tayi luf a jikinsan tana jin yadda yake bin sassan jikinta da shafa,ba'a jima ba ya fara lalubenta da sauri ta d'ago kanta tana kallonsa,ya d'age mata gira yana tambayarta mene ne kuma? Ta shagwab'e fuska tace "Mun fasa zuwa ne?" Ya fara licking lips d'inta then yace "where?" Tace "Side d'in su Aunty!" Ya girgiza kai idanunsa akan lips d'inta yana sake nufarsu k'asa² yace "Sai an jima za muje" daga hakan bai sake bata chance na yin magana ba ya rufe mata baki da nasa yana laluben harshenta,da saurin tura masa tana lumshe idanu,here wasan sun ya canja salo,bayan tsayin lokacin da suka d'auka suna aikin faranta ran juna,suka sake yin wanka,suna fitowa Nusrah ta wuce arean closet kasancewar ta san baza ta rasa wasu kayan da za su saka ba "Hayat!" Tayi kiransa in panic and surprise,yana tsaye in front of magnifying mirror yayi saurin waiwayawa without yace wani abu,idanunsa akanta ganin tana dawowa inda yake kafin yayi magana ta rik'e hannunsa ta fara jansa zuwa arean closet d'in,babu musu ya bita har a time d'in bai yi magana ba sai da suka tsaya ciki his eyes began to drift towards the closet yadda aka jera akwatuna masu 7 har set hud'u ya sake d'aure masa jijiyoyin jikinsa,ya ci gaba da bin ko ina da kallo,yadda aka cika gurin da kaya kamar za'a bud'e wani super market ya mugun basu mamaki,Nusrah ta bud'e baki za tayi masa tambayar na mene ne? Ya kad'a kai har lokacin yana cikin mamaki,ya d'age shoulders ya furta "Don't ask me nima ban san na mene ne ba" tayi shiru ta bishi da kallo,ganin ya wuce ya fara tafiya ta biyo bayansa da sauri tace "To ka tambaya mana" yayi shiru bai ce komai ba har suka gama shiryawa,bayan wani lokaci like someone who had remembered something ya rik'e hannunta da sauri yace "get up" babu musu ta biyo shi suka nufi hanyar fita daga apartment d'in,duk inda suka wuce girmamasu kad'ai security ke yi,sun fara zuwa apartment d'in Hajiya sun gaisheta,suka tab'a hira da barkwanci sannan daga can suka shiga family apartment d'insu,a nan aka dunga fito da mahaukatan gifts da suka samu on the night of the show suna dubawa suna hira,a nan ne suka ji bayanin akwatunan lefenta ne daga Daddy'nsu Rafeek who had set the target for a while but was afraid of how to deal with it,yanzun da ya samu kansu a cewarsa shi ne yayi biyan bashi,sun yi farin ciki sosai and sun yi masa godiya da addu'o'i wad'anda yaji dad'in su sosai,har ya rasa bakin yin magana,sun dad'e sosai a nan d'in sannan suka yiwa iyayen sallama suka tafi apartment d'insu su basu lokaci su mori zamanin su.

***

Rayuwa ta ci gaba da tafiya yayin da al'amura suke sake zuwa suna wucewa,wasu masu dad'i wasun kuma kishiyar haka,yayin da a b'angaren family d'in Rafeek sosai rayuwarsu ta daidaita,yanzun they have no problems at all sai dai damuwar da ba'a rasa kowane bawa da ita,zuwa yanzun an samu kimanin watanni uku da auren Annie da Abbah,and har a time d'in they had been living in London,sam sun k'i yarda su koma 9ja tun bayan auren su,da Abbah yaji bazai iya ci gaba da aikin banki bama yayi resigned and to say that his business da abunda ya mallaka ya ishesu rayuwa,and it was during this period Nusrah ta samu hutu,after their holiday da kwanaki uku,a nan duka suka fara shirin zuwa Nigeria har family d'in Baffanta Mr Sajid saboda yanzun haka closeness da suka yi sharing tsakaninsu tun zuwan su Annie k'asar da rashin nuna mata komai after knowing Aatif as their son,and how Annie and Lolly are often suke yin hirar family d'insu yasa Mom fahimtar mutum ba komai bane idan ya rasa wasu makusantansa,so there she regains the importance of fellowship da falalarsa,and that is why she must decide ta k'arfafa zumunci da danginta da ta watsar a baya.

*****

*Ina labarin Hajiya Karima?*

On the side of Hajia Karima kam,since the day asirinta ya tonu bayan Binnita ta k'ona black magic da ta gani a d'akinta,wannan dalilin yayi sanadin tsafin da ta yiwa Abban ya warware and to break through,after she gathered all her belongings kafin ta tafi ta yi making promise to not let them live in peace,a ranar ko da ta bar gidan kai tsaye unguwar da suke zama ta nufa,da yake her parent has long passed away,tsayin rayuwarta tana zaune tare da k'anwar mahaifinta Gwaggo Mari,a hannunta ta girma duk aure² da tayi da biye²n bokaye gurinta tayi degree d'insa,duk gidan da ta shiga if wasn't the kinda house suke so ne Gwaggon nata ita ke sawa ta kashe auren ta fito,lokacin da al'amura suka yi tsanani da rashin abun b'atarwa kafin aurenta da Abbah sai ya kasance sun tattara abunda yake hannunsu suka fara sana'ar abincin siyarwa,a bayan aurenta da Abbah kuma ko da suka ga sun samu irin gidan da suke muradi a nan suka shimfid'a mulki that were full of cruelty and greed,everything Hajiya Karima does na azabtarwa da cutarwa ga Nusrah za ka tarar da sa hannun Gwaggon,wacce lokaci guda da suka samu duniya a hannunsu ta fashe ta koma Hajiya Mariya,irin mugunta da k'eta da suka dunga gwadawa dukiyar Abba'n na ganin sun talauta shi,duk Allah bai yi nufin hakan zai faru ba,but they developed a desire suka raba shi da gudan jininsan ta hanyar tura mata bak'ak'en aljanun da they stay in her body for a long time until they finally got her out of the house,likkafa ya dad'a gaba suka d'ora daga inda suka tsaya,har ya zama duk wani abu na Abbah mai muhimmanci idan suka d'ora idanunsu akai sai sun san yadda suka yi suka raba shi da abun,lokacin da al'amarin yaci gaba da tafiya a hakan sai ya zama all his valuable assets da abubuwansa masu muhimmanci da suka yi saura basu samu damar farautarsa ba ya tattara su lokaci guda yayi storing d'insu a bank.


Bayan mutuwar auren Hajiya Karima ko da ta dawo gida,yanayin sauyawar da tayi da yadda take mu'amala da manyan Hajiyoyi a bayan duk sai ta raina k'urar data kwaso sauran al'umma na cikin unguwar,ba ta mutunci da kowa sai wata mak'ociyar su Hajiya Amina,itama d'in da yake basu jima da tarewa sosai a unguwar ba,and gidanta da maigidan sun fi k'arfin a kalla a wulak'anta,which is why Hajiya Karima ta k'ulla k'awance da ita kad'ai,a bayanta kam babu wani gida ko matar da suke mutunci,tsakaninta da sauran mutanen unguwa kallon k'ask'anci da wulak'anci,tun wasu na jin haushinta har suka bari saboda sun fahimci giyar dukiyar data shiga ne,though ta fito waje yanzun but bai gama sakinta ba,and their house was not in its original form,wancan ya kasance ginin laka,wannan kuwa na zamani mai d'auke da makeken get da babbar haraba,a tak'aice dai they had forced Abbah to buy some houses nearby aka rusa,and to renovating zuwa yadda suka tsara.


*A month later...*

About a month da mutuwar auren Hajiya Karima but to that point nothing has changed cikin rayuwarsu,da daren ranar suna zaune suna hira cikin parlor at about 12:30pm,ita da Hajiya Mariya suna sake tsara yadda za su koma rayuwar Abbah,so saboda dare gari duka was silent at that moment,and hirar nasu ma duka k'asa² suke yinsa,sai suka ji kamar k'arar fad'owar abu cikin gidan,Hajiya Karima ta waiwaya ta kalli Gwaggonta Hajiya Mariya tana fad'in "Hajiya kamar abu ya fad'o ko?" Hajiya Mariya ta girgiza kai tana tab'e baki cikin izza tace "Nima kamar na so jin hakan,amma bari na duba na gani" tana yin maganar ta dafa ta mik'e ta nufi hanyar k'ofa,kamar wacce aka hankad'o ta dawo da baya tim kake ji ta fad'i k'asa,Hajiya Karima da komai ya faru kan idonta ta zaro ido tana dafe baki,da sauri ta tashi za ta nufo ta,suka ji an buga tsawa daga bakin k'ofar da fad'in "Nemi guri ki zauna kafin na fasa miki kai!" A firgice su duka suka d'aga kai suka kalli inda suka jiyo maganar,manyan zaratan samari ne su biyar suke shigowa,kowanne fuskarsa sanye da bak'in face mask,banda k'wayar idanu da zagayen baki there's nothing da ake gani a fuskokinsu,mutum biyu ciki suna rik'e da guns k'irar ak74,while ogan sun dake gaba yana rik'e da wani shegen pistol black one k'irar TAURUS 9MM,sai biyu dake rik'e da WASR-2,idanun Hajiya suka k'ara girma cikinta ya bada sautin "K'uuuu!" A ranta fad'i take "shi kenan,ta faru ta k'are!" Wanda shi ne a kan gaban ya d'aga kai yana k'arewa parlor d'in kallo,then he turned to look at Hajiya Mariya da ta kafeshi da idanu,yana zare jajayen idanunsa da wani irin fasashshen murya yace "Ke! Me kike kallo ne?" Tayi saurin girgiza kai ganin yana saita ta da bindiga and narrowed her eyes,yadda duk suka yi tsumu² ita da Hajiya Karima sauran suka fashe da wani irin mahaukaciyar dariya banda shi,yana ci gaba da muzurai ya juya ya kalli Hajiya Karima da take k'ifi² da idanu yace "Munji labari akwai k'udi a gidan nan,so we do not want to waste any time here aje a fito mana da su" Hajiya Mariya dai bata iya sake d'agowa ba bare tayi magana,sai Hajiya Karima itama d'in cikin rawar baki,jikinta ko ina kyarma yake and was swearing profusely babu kud'i,ya kalleta a fusace "Kada ki rainawa kanki hankali Hajiya maza kije ki fito da su ko yanzun mu harbeku har lahira" jikinta yana b'ari tace "Billahillaziiy laa ilaaha illaa huwaa ba-mu da kud'i,sai dai ko kayan kud'in!" Har ya turb'une fuska jin ta ce akwai kayan kud'i da sauri ya kalli yaransa yace "Maza aje a bincika,kada a b'ata lokaci" suka amsa suna tisa k'eyarta zuwa ciki,duk wasu sark'ok'in da suka mallaka ta dalilin Abbah da y'an canjin kud'i da suka yi saura cikin gidan basu yarda sun bari ba,sai da suka raba su da komai,duk da hakan basu barsu haka nan ba sai da suka turmushe su har ita tsohuwar najadun (Hajiya Mariya) sannan suka fita suka barsu da warning d'in idan suka yi musu ihu bayan fitarsu duk sai sun kashe su,bakin kowacce a b'ame hawaye masu k'una na irin wulak'ancin da suka fuskanta suna kwaranya daga idanunsu,a haka daren ya wuce suna nan zaune inda suka barsu,har garin Allah ya gama wayewa ba tare da sun samu damar runtsawa ba ko wani ciki ya danni zuciyarsa ya baiwa d'an uwansa hak'uri.


They've spent the whole day there in this situation babu wacce ta motsa daga gurin bare tayi tunanin sanya wani abu wa cikinta,da dare Hajiya Amina mak'ociyarsu taji shirun yayi yawa ta lek'o,bayan ta jima tana knocking ba'a bud'e ba,har ta tafi ta sake dawowa tare da mijinta,suna tsaye bakin get d'in gidan shiru ya kalleta yace "Anya gidan nan akwai mutane cikinsa kuwa Hajjo?" She was silent and thought for a moment tace "Gaskiya ina kyautata zaton suna nan,da ba sa nan Hajiya Karima za ta fad'a min,ko baza su jima ba idan sun fita tana k'ok'arin sanar da ni" ya jinjina kai yace "well maybe something happened shi yasa muka ji su shiru har yanzun!?" Yayi emphasising maganar,Hajiya Amina tayi jim kafin cikin sarewa tace "Komai ma zai iya kasancewa,fatan dai Allah yasa lafiya" yace "Ameen!" Suka ci gaba da jira,atleast sai da suka spending an hour da wasu minutes suna knocking ko za'a bud'e but shiru,haka layukan wayoyinsu sai kira suke yi suma d'in amsa d'aya suke samu a rufe duka wayoyin suke,da suka ga babu mafita nan suka kama hanyar komawa,sai dai sun ajiye shawaran zuwa gobe idan basu samu wani gamsashen bayani akan lamarin su Hajiya Karima d'in ba za suje gidan mai unguwa,idan yaso ko bude gidan ne sai ayi a duba.

Wasa² daga awa d'aya,biyu abu har wani daren,suna zaune kowacce da damuwar dake damun ranta,bayan tsayin awanni suna nan zaune kamar ginannun duwatsu,Hajiya Mariya tayi wani irin jan zuciyar da ya bata damar d'aga hannu ta goge hawayen da suka sauko saman fuskarta,in a kind of calm tone da wannan dasashshiyar muryar tan,bata yarda sun had'a ido da Hajiya Karima ba ta fara magana "Kuka ba zai tab'a zama mafita ba,ya kamata mu tashi tsaye mu san abun yi kafin lokaci ya k'ure mana!" Furucinta ya bawa Hajiya Karima damar dawowa daga duniyar rud'anin abunda ya faru da su,tana yin ajiyar zuciya and to blink her swollen red eyes,muryarta ba ta fita sosai har gara ta Hajiya Mariya tace "Yanzun Hajiya mene ne kike ganin za mu iya yi?" Hajiya Mariya tace "Komawa cikin rayuwar Alhaji Abubakar shi ne abunda ya dace,ko da babu aure dole muyi masa rik'on da babu abunda zai sa ya kufce daga gare mu!" Hajiya Karima was silent and listened to her speeches,while k'asan zuciyarta yake cike with different emotions,jin ta yi shiru Hajiya Mariya tace "Kina sauraren abunda nake fad'a Karima?" Hajiya Karima ta d'ago ta zuba mata idanu ba tare da ta yi magana ba,Hajiya Mariya ta ci gaba da yi mata khud'uba bisa busa da zugar shaid'an. A wannan daren duk wani mafitar da suke nema,sai da suka tabbatar sun nemo,sannan suka kwantar da hak'ark'arinsu,ba wai dan baccin yana musu dad'i ba,but solution to their problems da suka finding ya basu nutsuwa.

Washe gari tun da asubah bayan an fito masjeed,suna kwance suna ramuwar baccin da basu samu yi ba,hayaniyar dake tashi kofar gidan ya farkar da Hajiya Mariya,cikin tsananin mamaki ta bud'e idanunta ta saka slippers ta kama hanyar fitowa daga bedroom d'inta,a hanya suka had'u da Hajiya Karima tana fitowa parlor,Hajiya Karima tana murza ido take tambaya "Hajiya me yake faruwa cikin unguwar nan nake jin hayaniya?" Hajiya Mariya tayi shiru tana bud'e k'ofar parlor,kafin ta fita ta waiwaya ta kalli Hajiya Karima "Kamar ma a k'ofar get nake jin hayaniyar" Hajiya Karima ta kad'a mata kai,kafin ta yi magana aka diro cikin gidan,da gudu har suna bige juna suka shige cikin parlor kowacce na neman wajen b'oyewa,matashin da ya diro ciki bai kula da su ba ya bud'e get,mutanen dake waje suka fara shigowa,mijin Hajiya Amina ne kan gaba da mai unguwa,sai sauran mutane y'an son d'orar da labari,Hajiya Mariya jin hayaniyar ta k'i tsagaitawa ta d'aga kanta a hankali daga bayan armchair da ta b'uya,ko ina jikinta sai kyarma yake ta sad'ad'a ta lek'a window,taron jama'ar da ta gano ya bata damar yin ajiyar zuciya and then ta fito daga mab'oyarta tana kiran Karima,Hajiya Karima ta lek'o daga bayan armchair as if ana cewa kyat za ta fita a guje duk ta had'a gumi,Hajiya Mariya tace "zo ki gane min nan" a sad'ad'e cikin tsoro Hajiya Karima ta fara tahowa inda Gwaggon nata take rik'e da curtains na window ta d'an lek'a,sai da tayi ajiyar zuciya sannan ta kalli Hajiya Mariya tace "Ina tunanin Hajiya Amina ta neme mu bata samu labari ba!" Hajiya Karima ta kad'a kai bata yi magana ba taji ana k'ok'arin b'alle k'ofar parlor da sauri taje ta fara k'ok'arin bud'ewa,daga can wajen lokacin ko da suke kan k'ok'arin bud'ewa jin daga ciki ana bud'ewa abun yayi mugun basu mamaki,but they keep an eye out for what is about to happen,Hajiya Mariya tana bud'e k'ofa idanun jama'a yayi yuuu! Kansu,duk hayaniyar da ake yi lokaci d'aya duka sai aka yi shiru kamar ruwa ya cinye wajen,mijin Hajiya Amina yayi saurin matsowa cikin hard'ewar baki yana kallonsu da jefo musu tambaya "Hajiya! Kuna lafiya? Babu abunda ya faru da ku?" Hajiya Mariya tayi murmushin yak'e ta girgiza masa kai "Babu komai,lafiyar mu k'alau" a rud'e ya furta "Amma Hajiya ina kuka shiga haka babu sanarwa,Hajjo ta tayar da hankali sai an duba ku?" Kafin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login