Showing 15001 words to 18000 words out of 220972 words
da dariya da Maimunatu kanwarsa,duk da a bayan kafin zuwan wannan lokacin idan ta ganshi tana gaisheshi da bashi girma a matsayin yayan k'awarta,daya bayyanar mata a matsayin mijin aurenta hakan bai sa ta canja daga yadda take ba,sai k'arawa ma da tayi,cikin hukuncin ubangiji a hankali tun bata sake da shi ba,yanayin mu'amalarsa da barkwancinsa yasa ta fara sakewa da shi,kafin a d'auki lokaci shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakaninsu,har ya kasance idan yana gari,ya zo hutu duk inda zata je shi yake mata rakiya,ya zame mata kamar wani bodyguard,mutanen unguwa kuma duk lokacin da suka gansu tare nan zaka ji yan gulamammaki suna ci gaba da yad'uwa,but da yake Rafeek ba mutum ne shi mai yawan magana akan abunda babu ruwansa baya tab'a kulawa.
Alhaji ya maida Hauwa makaranta mai kyau tare da Maimunatu,aka ajiye su class d'aya,gurin zaman su da komai tare suke yinsa a gida ko a makaranta,their closeness to each other continued to grow as they were blood relatives before.
Laying and rising is kinda loss of living,haka nan a wajen ubangiji shekara is like a day,su Hauwa sun gama secondary school bayan wucewar shekaru uku masu kyau,yayin da Rafeek ya kammala degree d'insa har ya nemi wucewa masters but ba'a Nigeria ya nema ba,ya nema ne a k'asar Ghana,though har zuwa lokacin basu tura masa sun bashi admission ba,Alhaji zakar yayi deciding tunda Allah yasa duk suna zaune a gida,mai zai hana ayi bikinsu,zuwa lokacin da can k'asar za su kirashi sai ya d'auki matarsa ko ya barta a nan gurinsu,da ace suna ta zaune basu san matsayin auren nasu ba,da ya sanar musu hukuncin daya zartar sun yi farin ciki sosai,bayan y'an kwanaki aka tashi hidima,Alhaji zakar ya yiwa Hauwa akwatunan lefe guda bakwai kowanne cike taf da kaya na gani a yaba,aka tsaida ranar biki sati guda,,anyi hidima sosai a bikin auren su,yadda ya kashe dukiya babu wanda ba zai yi tunanin y'ar cikinsa yake aurar wa ba,tsayin kwanaki uku akayi biki bisa al'ada da tsari aka gama,aka kai amarya gidanta dake nan a cikin unguwar K'ofar Na'isan itama,tsakanin mu duka babu nisa sosai,tun da muka rakata muka dawo ake ta labarin gidanta,yadda aka kashe mata dukiya a d'akunanta,ko wata y'ar gatan ba zata nuna mata komai ba,a haka dai aka baro amarya a gidanta cikin rufin asirin Allah,,,a kowane dare kamar yadda ko wane ango da amarya suke kasancewa bayan sun kad'aita,a tarihin aure da ma'aurata suma gare su haka ce ta faru tsakanin su,lokacin da komai ya lafa sun samu nutsuwa cike da k'aunar juna da nuna kulawarsu ga juna Rafeek ya lallab'ata tayi bacci,but a gurinsa shi kuma baccin ya k'i zuwa masa,saboda tsananin farin cikin daya tsinci kansa a ciki,a haka ya ga wayewar gari lafiya wacce ta kasance musu mafari.
Kamar yadda na sanar da kai Rafeek ya nemi admission amma basu kirashi ba har time d'in,cikin hukuncin ubangiji duk kwanakin da aka d'iba a baya basu neme shi ba,sai ga shi kwatsam rana a sama,kimanin kwanaki uku da tarewarsu sun aiko masa sak'on sun bashi gurbin karatu,duk lokacin daya shirya daga nan zuwa sati guda yana iya tuntub'ar su,,a lokacin da Rafeek ya samu sak'on sai da yaji kamar yace ya fasa tafiyar dan yana ganin kamar zai cutu idan ya bar Hauwa a 9ja,can k'asar da zai je kuma shi ga shi ba sanin yaya take ya yi ba bare yace kai tsaye zai tafi da ita,wannan dalilin yasa yayi shawaran fara yin magana da iyayensa tukun kafin ya san abun yi,da yaje gida ya sanar da mahaifansa,suma dai basu bashi goyon bayan ya fara tafiya da ita ba,sun k'arfafa masa guiwa akan tunda karatu ne kuma na shekara d'aya yana iya zuwa ya dawo,lokacin da yaso yana iya zuwa ya ganta,but batun tafiya da ita tunda su ba gida ne dasu a can ba bare wasu dangi,gwara ya barta a nan d'in yaje abunsa,,Rafeek dai ba haka ya so ba,though he respects the words of his parents dole ya sawa zuciyarsa hak'urin tafiya da ita.
Cikin satin ya kammala shirin tafiya,cike da kewar matarsa da yake tsananin so,bayan ya maida ita gidansu wajen mahaifiyarsa ya bar k'asarsa ta haihuwa,,saukar sa a k'asar Ghana ya fad'a harkar makaranta ba da wasa ba,,kamar yadda a Nigeria suma su Hauwa Alhaji yasa aka nema musu gurbin karatu a School of nursing ita da Maimunatu a b'angaren *Midwifery* suka fara attending class,this time too is like their secondary life d'insu ne komai tare suke yinsa,basu da wasu k'awaye sune abokan juna kuma aminin junan,sun fara karatu cikin nasara,,once again Hauwa becomes a star among her relatives,ta sake zama itace mace ta farko da aka samu a tarihin gidanmu ta tsallake matakin karatun secondary,,a kullum tunda Rafeek ya bar kasar idan ya fito daga skul ko ya samu intervals haka yake b'ata lokaci kiranta a waya,su shafe tsayin yini mak'ale da juna,shak'uwarsu yana sake k'aruwa,soyayyar su tana sake bayyana,tafiyarsa da y'an watanni Hauwa ta fara laulayi,lamarin daya zamewa ahalin gidan Alhaji Zakar babban abun farin ciki da suka jima basu gani ba,kowa ka kalli fuskarsa da yanayin kulawar da yake bata ya isa ya tabbar da tsantsar d'aukin da suke ga cikin nata,but still a time d'inma babu wanda ya fad'awa Rafeek halin da ake ciki (this is the first mistake the family has made),kowa yaja bakinsa yayi shiru ba tare da tunanin za'a samu matsala ba,sai jiran zuwansa da kowa yakee yi daga iyayen har maids kowa jiran ganin lokacin dawowarsa suke,ko ita kanta Hauwa a lokacin the folly she did was bata sanar masa ba,a duk lokacin da zai kirata sai dai tayi k'ok'arin sake hidden,idan suna waya tana iya k'ok'arinta ta amsa shi kamar babu wani abu dake damunta,duk da yanayin cikin yazo mata da laulayi mai wahalarwa,ko yaya yaga canji a tare da ita yana tambayarta yace "tana lafiya.?" Takan ce masa "ehh! Tana lafiya" Idan ya tambaya babu matsala nanma takan ce masa babu,every day within 12 hours they spend countless hours suna aikin abu guda,yanzun zai kirata after a few minutes he will just make a call again badon komai ba sai dan ya tabbatar da lafiyarta,video call kuwa yadda suka maida shi kamar cin abinci yafi musu wuya,though duk kusan lokacin da suke wayan takan yi covering jikinta da enamors hijab,shi yasa har zuwa lokacin da cikintan ya fara bayyana bai kula ba,sau da yawa sukan yi fad'a akan hijab d'in da take sawa,suyi fushin su shirya duka within few minutes,yakan ce mata "he don't know what's come over her take wani rurrufe masa jikinta al'halin tasan halal d'insa ne idan ya gani",sometimes yakan ce yana so ta nuna masa some private parts of her,sai dai tayi dariya ko tace "u know fa babu kyau kallonsu,suna b'ata ido" mostly yana jin ta fad'i haka yasan bazata nuna masa ba,kuma duk wayon da zai mata,har ya nuna mata yayi kewarta ne shi yasa yake buk'atar ganinsun,bata yarda ta nuna masa,a haka ya shafe tsayin watanni biyar da tafiya,har a lokacin duk k'ok'arin da yayi na son zuwa ya ganta,but al'amura sun sha kansa dole yake zaune cikin hak'uri tunda bai samu damar zuwan ba,watanni uku ya k'ara har da kwanaki wanda yayi dai² da watannin sa takwas da y'an kwanaki duk da a daddafe yayi su,yaga yayi hakur'in har ya koma takura rayuwarsa and ba komai yake fahimta ba,wannan dalilin makes him decides to ya taho 9ja ko zai samu peace of mind daya rasa tsayin watanni,,ya iso Nigeria a ranar wata Sunday ba tare daya sanarma kowa yana zuwa ba bcos he wants to surprise them,yayin da suma a gurinsu sun b'oye batun cikinsa da Hauwa take d'auke da shi a k'ok'arin su na son su masa surprise,kowa burinsa shi ne yana son ganin yadda Rafeek zai yi idan ya ji labarin and ya gani da idanunsa,within few hours jirginsu ya sauka a Kano,daga nan ya nemi charter taxi da zai kai shi gida,tafiya suke a hanya but Rafeek gani yake kamar ba yi suke ba,burinsa su isa ya damu ya ganshi kusa da matarsa,cikin hakan suka samu damar isowa dai² katafaren get d'in gidan su dake unguwar k'ofar Na'isa,ya sallami mai taxi daya sauke shi ya juya yana kallon gidan yana murmusawa,ajiyar zuciya yayi lokacin daya sawo kai cikin harabar gidan daga shi sai halinsa ya tunkari ainihin entrance d'in main gidan yana tafiya yana sake sakin kyakykyawan murmushinsa masu k'ara masa kyau da kwarjini,kda yake bai tarar da mai gadin nasu ba har ya iso entrance d'in parlor'nsu bai had'u da kowa ba,a bakin door d'in ya d'an tsaya kad'an jiyo sautin muryarta tana magana,ya dakata yana sauraren hirar da suke yi ita da Maimunatu k'afin yayi alerting nasu zuwan sa,murmushi ya sake yi ya saki sanyayyan ajiyar zuciya slowly ya janye curtains d'in da suka zagaye parlor'n ya shigo ciki da sallama a bakinsa cikin takunsa na had'ad'd'e kuma wayayyen namiji mai ji da ilimi,lokacin daya shigo Maimunatu kawai ya iske zaune,nan ya fara waiwayen hanya yana nemanta,amma babu alamunta a gurin bcos dai² lokacin da yake shigowa kafin ya bayyana itan ta bar wajen,itanma kuma bata san da zuwansa ba,ihu Maimunatu ta saki lokacin data ganshi da d'an gudun murna ta mak'ale shi tana masa sannu da dawowa,ya amsa da kulawa yana ci gaba da kalle² yace
"Where's she.!?" Maimunatu dake dariya tana kula da shi ta fahimci matarsa yake tambaya but a wayo tace
"Hajiya.!? Ai tana side d'in Abba.."
Murmushi yayi mata yayi shiru suka k'arasa cikin parlor suka zauna,daya gaji da jira ganin shiru bata fito ba har sannan ya kalli Maimunatu dake ta hidima da shi yace
"Wai ba yanzun kafin na shigo naji maganarta ba.!?"
Still tayi kamar bata gane ba tace "Yah Rafeek wai Hajiya.? Bafa ita bace,i think kamar kusan one hour kenan data tafi gurin Abba.."
Ido ya bud'e yana kallonta cikin takaici cos ya fahimci zolayarsa take yace
"Waye yace miki wai Hajiya nake ta tambaya ne.?? I thought na tambayi inda take first so mene ne kuma zai sa na sake tambayar inda take bayan na samu amsa.?"
Cikin shagwab'a Maimunatu ta marairaice fuska tace
"Yah Rafeek to ai nima thought akanta ne kake maganar,shi yasa na baka amsa iri d'aya",kansa ya girgiza kad'an yace "ba ita nake nufi ba to.."
Murmushi tayi masa,ya had'e fuska slowly ta masa nuni da hanyar bedroom d'insa before ya bar gidan,mik'ewa yayi da sauri yabi bayanta,yana tafiya yana murmusawa dan Allah kad'ai yasan irin kewarta da yayi,,bai bawa kansa wahala wajen yin knocking door d'in ba ya bud'e kai tsaye ya shiga,da bayanta ya fara arba tana kwance ta juyawa entrance d'in d'akin baya,yadda tayi d'ai² da alamun gajiya a tattare da ita yasa a sad'ad'e ya maida k'ofar ya rufe yana ta sakin murmushi har ya iso daf da bayanta,saman gadon ya hauro a hankali yana matsawa har ya had'e jikinsu guri guda,a tare suka sauke wani irin munafikin ajiyar zuciya,pleasantly take shak'o sanyayyun scent's d'insa da suka bada goyon baya wajen nakasa mata every joint dake jikinta ta kasa motsawa,cikin kunnenta kasa² da wani irin yanayin kashe jiki yace
"Hi.!"
Saurin bud'e ido tayi tana k'ok'arin tashi ta zauna,ya hanata yin hakan,d'an juyowa tayi kad'an tana kallonsa da mamaki tace
"Yaushe ka taho ne.!?"
Murmushi ya sakar mata yana dad'a kusanta fuskokinsu muryarsa a shak'e yayi sucking lips d'inta passionately yace
"Yanzun na zo..?!"
Jinjina kai tayi a hankali idanunta suna kallon hannayensa da yake k'ok'arin tura su jikinta ta rausayar da kai gefe tace
"Ka fad'awa Hajiya kana zuwa dama.!?"
Da idanunsa yayi mata alamar A'a, had'e rai tayi ta fara k'ok'arin tashi yana hanawa,can da ta gaji ga zafin da take ji a jikinta bcos data shigo da hijab d'in a jinta ta kwanta sai ta d'an narke masa tace
"Please.! Ka bari na cire hijab d'in ya dame ni."
Tab'e baki yayi yace "dama ai ni tuni nasan yana damunki,kawai dai dan anga bana nan shi yasa ake yi min rowa,sai wani b'ob'b'oye min abubuwa na.."
Bata jira ya gama fad'ar abunda yake niyya ba cikin damuwa tana ta kallonsa tace "bafa haka bane.!?" Bai kalleta ba shima yana k'ok'arin rabata da hijab d'in yace "Da yaya ne.!?" Tace "to ba kaine daka tafi kak'i zuwa ka gansu ba.. Sai kayi ta cewa na nuna maka.!" Tayi furucin cike da shagwab'a mai tafiya da nutsuwa,idanunsa ya d'aga ya kalleta kad'an ya sake tab'e baki yace "Uhn! Nayi laifi ko da nace haka.!?"
Ta gyad'a masa kai bata ce komai ba,idanunsa ya kawar gefe yace
"Yanzun ma nayi laifi.!?" Tace "da aka yi mene ne.!?" Yace "da nake son ganinsu a fili.!" Kai ta kad'a masa alamun A'a,a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana nufo bakinta dake ta glittering ya d'ora nasa akai ya fara sarrafasu,saurin kulle idanunta tayi tana murmushi da sake rik'e shi,a hankali cikin dabara ya cire mata hijab d'in,sunyi nisa sosai bai kula ba,dai² lokacin daya bud'e birkitattun idanunsa da nufin ya kalli muradin zuciyarsa idanunsa suka sauka akan k'aton cikinta,lokaci guda idanunsa suka yo waje har bai san lokacin da bakinsa ya kub'uce ya furta
"Whaaaatttt..!??"
#Turkashi..!! Yanzu wasan zai fara... Lemme run. 🏃🏻♀
#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
*Right from the very first time we held u in our arms,we knew u were special... Today we find ourselves really happy to see u grown up so beautifully.. Happy Birthday to our little princess Maryam Abubakar Sa'ad (Khausar).🎊*
Pᴀɢᴇ 6.
#Uᴘꜱʜᴏᴛ
Murmushi tayi ta sake matsawa jikinsa ta rik'o hannayensa duka tace "Mene ne ya faru ne.!?"
Ta nuna kamar bata san abunda yake nufi ba,fuskarsa d'auke da wani irin expressions da baka tab'a rarrabewa yake ci gaba da kallonta,muryarsa tana wani irin trembling yace
"Mene ne wannan d'in.!?" Ya nuna k'aton cikinta,hannunsa d'aya dake rik'e a nata ta kai kan cikin ta dafe,suna kallon juna fuskar kowannensu da irin sak'on da take bayyanarwa ta fara masa magana in a calmness way
"It's a gift from Allah (S.W.T),he has blessed us with it.."
Da mamaki shimfid'e a fuskarsa ya gwalo ido yace "what.!?" Tace masa "yeah.!" Girgiza kansa yayi ya lumshe ido ya bud'e yace "how and when..!?" Tace "bayan tafiyarka babu jimawa ne na fara rashin lafiya,da Hajiya tasa likita ya duba ni shi ne yace ina da juna biyu.."
Kallon mamaki still yake mata yace "Bayan tafiya na..!?" Da wani irin muryan dake nuna rashin gamsuwa da amsarta,tace "Ehhh.!" Still yake sake kallonta sai yayi shiru ya kasa cewa komai,ya d'auki tsayin lokaci cikin halin mamaki da tunani,jikinsa ta shige da damuwa tace "ain't u happy with it.!?",kallonta kad'ai yayi ya tureta daga jikinsa cikin b'acin rai,bai sake yin magana ba ya fita daga d'akin,fad'uwa gabanta ya dunga yi cikin tsananin tashin hankali ta sakko ta biyo bayansa,parlor Rafeek ya fito gaba d'aya ya kasa fahimtar yadda akayi ta samu juna biyu
"When did that happen.!?" Ya tambayi kansa a fili da muguwar damuwa,zuwan Maimunatu yasa shi saurin kallonta yana tambaya
"Ke tun yaushe ne waccan bata da lafiya.!?"
Maimunatu da murnanta tace "Yah ai tun bayan tafiyar ka ne" jinjina kai yayi yana shirin yin magana Hauwa ta rik'e masa hannu,a fusace ya juya yana kallonta ya fizge hannunsa,sake kai hannunta tayi zata rik'e shi ya buga mata tsawan da sai da ta firgita,hak'oransa suna datsewa da wani irin traction mai fidda sauti,muryarsa cike da warning yace "don't u dare touch me.. I warned u"
Cikin tsananin firgita muryarta na kyarma tace "to wai mene ne ya faru ne.!? Ni mene ne nayi maka kake fushi,ban san laifina ba,ya kamata ka fad'a min.."
Harararta yayi yace "Really.!?" Ta gyad'a masa kai kamar za tayi kuka,jinjina kai yayi kafin yayi magana Hajiya da Abba'nsa sun iso,har Maimunatu ta kai rahoton su zo ba lafiya,shi ne fa da sauri suka fito daga site d'in Abba'n sunyi tunanin ma ko wani abu ya samu Hauwa,suna shigowa cikin parlor'n Hajiya taga Rafeek tsaye ya kasa zama ta fiddo ido da mamaki tana tambaya "kai kuma fa.!? Saukar yaushe.!?"
Bai iya kallon mahaifiyar tasa ba yace "Yanzun.. Nazo" zuciyarsa duk babu dad'i
"Amma shi ne baka ce za ka zo ba,sai dai mu ganka kawai.!?"
Bai iya tankawa ba,yana ci gaba da kallon ta har lokacin da b'acin rai yace "Hajiya! When did she got pregnancy..!?"
Murmushi Hajiya tayi dake nuna tsantsar jin dad'i ta tace "Bayan tafiyarka ne babu jimawa,so sai muka yi deciding mu b'oye maka saboda muna son maka surprise,yanzun kam ko shakka babu naga alamun ka ji mamaki da ganinta d'auke da juna biyun.." Ta k'arasa fad'a so excited,jinjina kai yake babu k'ak'k'autawa yace "K'warai kam naji mamaki Hajiya da na ganta d'auke da k'aton ciki,but still noe i don't even know cikin na wane ne..!?"
Kallon mamaki Hajiya suke binsa da shi yayin da shi kuma yake watsawa Hauwa wani irin lafiyayyen kallo mai kama da na tsana,Hajiya cikin rashin fahimta tace "Ban gane abunda kake nufi ba Rafeek,,ya kamata ka fito kai tsaye ka mana bayani,maganganun ka sun fara sa ni shiga rud'ani."
Yace "Nifa Hajiya ba wani abu nake nufi ba,kawai dai i was confused about her pregnancy.."
Idanun su duka a waje suna had'a baki suka ce "Meh.!?"
Yace "Ehh! Hajiya gaskiya i didn't agree with..."
Tsawa Hajiya tayi masa tun bai k'arasa ba tace "kai Rafeek kada ka mai damu wasu marasa tunani mana,cikin ne baka yarda da shi ba.? Kasan duk inda za'a je a dawo kai ne mammallakin cikin nan ko..? Idan ka ce ba naka bane yanzun ka yi min bayani na uban waye.?"