Showing 174001 words to 177000 words out of 220972 words

Chapter 59 - DAN MACE COMPLETE Hausa Novel

23 Aug 2025

1206

tafiya duka da yake dama ba wasu mutane ne na daban ba,y'an uwane kawai,gida ya rage lolly,Nusrah sai Bareerah kasancewarta y'ar amana,sannan a yanzun su duka suna yi mata kallon wata ta jikinsu saboda halacci,duk inda suke suna tare da ita ba-sa barin wani abu ya sameta ko ta wulak'anta,suna zaune lokacin kafin su tafi Annie ta kallesu ta yi shiru,because har lokacin bata gama yarda wai ita ce tayi aure ba,ta fi ganin abunda yake faruwa irin a mafarki d'in nan,Lolly da suke hira jin shirun na ta ya yi yawa ta kalleta fuskarta da fara'a sosai tace "Adda tunanin me kike yi?" A hankali Annie ta kalleta hawaye suna taruwa a idonta tace "Ina tunanin rayuwar mu ne a baya,yanzun da komai ya zama tarihi sai nake ganin kamar duk wad'annan abubuwan sun faru ne a mafarki!" Lolly tayi murmushi mai cike da nutsuwa tace "Haka ne Annien mu,amfanin bawa ya kasance mai hak'uri,juriya da addu'ah kenan,duk abunda ya same shi idan lokacin ya wuce sai ya dunga ganin kamar ba'ayi ba",Nusrah tayi dariya tace "Laaahh! Aunty kema Annien kika ce?" Duka suka yi murmushi,Annie ma ta yi murmushi mai tafe da hawaye,Lolly tana rik'e da hannunta tana kallonta take bawa Nusrah amsa "Tabbas Angel! Adda maryam ta cancanci na kirata da sunan mahaifiya,kasancewar tun ban gama wayo ba mahaifiyarmu ta rasu,daga wannan lokacin ta sakance ita take yi min komai,bayan ita ban san kowa ba,kasancewarta mutum ta farko da tunda na zo duniya bata tab'a gwada min k'iyayya ba,ta so ni da dukkan zuciyarta,ta zauna da ni a lokacin da na rasa hankali,ta kasance mai sadaukar da farin cikinta akaina,shin idan ban kira wannan matar mahaifiya ba da wane suna ya kamata na kirata?? Matsayinta a gurina ya wuce y'ar uwa kawai,idan har akwai wata mahaifiyar a bayan wacce ta kawo ni izuwa wannan duniyar tabbas zai kasance ita ce,tarbiyyana da komai itace,idan na yi kuka ba ta samun nutsuwa har sai ta ga na yi dariya,idan ina farin ciki tana yin sama da nawa,for nothing other than ban yi kuka ba,itan y'ar baiwa ce kuma abun alfahari a gurin kowane ahali,tabbas da ace ana iya tambayar mutum lokacin da za'a raba shi da wanda yake so,a lokacin da mutuwa ta kusanci d'aya ko a bashi damar musanyawa da wani abu,hak'ik'a da na rok'i a barmin ita,na musanyata da sauran dangina,duk da mun kasance bamu tashi mun san dangin mahaifiyarmu ba a kullum suna nan a cikin zuk'atanmu,muna marmari da begen ganinsu ko da sau d'aya ne a rayuwa kafin mutuwa ta riske mu ko su d'in,sai dai har zuwa yanzun muna k'aunarsa ne kawai amma su d'in babu wanda ya damu da rayuwarmu bare su neme mu,ko su san halin da muke ciki,har yanzun bamu samu wani mutum d'aya wanda a tarihi za mu nuna muce ya fito daga dangin mahaifiyarmu ba,shin a wannan zamanin da muka kasance muna rayuwa mu kad'ai idan bamu so juna ba waye za mu so? Dangin mu basu damu da mu ba,basu san inda muke ba,babu wanda yake kulawa da mu,suna nan a raye ko sun mutu bamu sani ba,amma kasancewata tare da ita yasa a kullum na kasance ina yiwa Allah godiya tare da jin cewa ban rasa ahali ba,ba don komai ba sai saboda itan ta kasance d'aya daga cikin ahalina,tabbas ina alfahari da samunta!" Hawaye su duka suka share saboda yadda maganarta ta tab'a musu zuciya,Annie kuwa gaba d'aya ta kasa samun bakin magana banda hawaye babu abunda take sharewa,Lolly tayi murmushi tace "Saboda haka nake jin idan na kira ta da sunan Mahaifiya ban yi ba dai² ba.." Sun jima sosai a gidan yayin da duka hirar ta su ya kasance kalmomin yabo ga Annie da labarin rashin sanin inda ahalin mahaifiyarsu suke,a nan itama Nusrah zuciyarta ta cika taf da begen nata ahalin mahaifiyar har ta sake k'udurcewa a ranta lallai za ta sake yiwa Abbah magana ko da ace ba zai kaita ba lallai tana buk'atar ya ba ta address,ita da kanta sau ta neme su,wajen misalin k'arfe 9:00pm suna kan yin hiran Nuraz ya kira ta,tana d'auka bayan ta yi sallama,maganarsa a low tone yace "Madam kin manta da ni gaba d'ayan" tayi murmushi da sauri ta tashi ta haura sama,tana cewa "ta yaya zan mantawa da rayuwata? Idan na manta da kai ashe zan manta da kaina" yayi murmushi yace "kawai kince haka ne Madam,but na san hidima yasa an manta da ni,tunda ga shi daga zuwa rakiya ank'i a dawo" tana kwanciya a saman bed d'inta na gidan tace "No! Ba haka bane fa,kawai dai babu dad'i mu taho mu barta ita kad'ai ne,su Abbah muke jira har yanzun su zo,uhn! Sai nake jin ma kamar na kwana a nan" yayi murmushi yana cewa "to ko za ki gwada?" Tana dariya tace "Idan ka fad'a ba zan k'i ba" ya jinjina kai yace "Wai sai yaushe za ku taho?" Tace "Muna jiran su Abbah su zo" ya tab'e baki yana adjusting kwanciyarsa yace "Ni dai a dawo da wuri a san yadda za'ayi da ni" murmushi tayi muryarta a low tone tace "Me zan yi?" Yace "Ohooo! Kin fi kowa sani" ta shagwab'e tace "well,kawai ka zo mu tafi" yace "Ke kina wasa ko? A hakan zan wani biyo ki? Ko so kike na yi miki ciki a gabansu?" Kyalkyalewa tayi da dariya tana rufe baki tace "Allah yasa ban ji abunda kace ba" shi kansa sai da ta fad'i hakan ya tuna me yace,yayi dariya yace "idan kuma kina so nazo shi kenan dama ai muna da d'aki a nan right?" Ta kad'a kai tace "Ehh muna da shi" yace "Shi kenan ga ni nan,yau a nan za mu kwana",tayi sauri ta katse shi "wai da gaske kake yi?" Yayi dariya yace "absolutely sure" tace "Ka rufa min asiri kayi zamanka,yanzun za mu dawo" cikin zolaya yace "A'aahh! Dama ai asirinka a rufe yake" Tace "Pleasee!" Tana shagwab'ewa,da kyar yace mata ya yarda but tayi sauri,idan ba haka ba zai biyo sahunta,ta amsa tana dariya,tana gama wayar ta fito tana murmushi ta jiyo maganar Father In-law d'inta yana tsokanar Lolly,tayi dariya a fili tace "hali zanen dutse!" Ta sauko k'asa lokacin ta tarar da su har sun mik'e za su tafi,ta kalli lokaci taga 10pm yayi,here tayi realizing sun b'ata almost one hour suna magana,a gurguje taje ta d'auki kayanta suka yiwa su Annie fatan alkhairi had'e da sallama,kamar kada su tafi haka suka dunga ji sai da Rafeek yayi da gaske yasa su gaba yana zolayarsu sannan suka fita suna waiwayen Annie kamar wanda ba za su sake had'uwa ba,a mota suna tafiya kasancewar Lolly ce a front seat kusa da Yallab'ai dake jin tuk'i da kansa,Nusrah ta zauna kusa da Bareerah a back seat,da yake mota d'aya suka zo da shi babu security,Rafeek sai tsokanar Lollyn yake yi ganin tunda suka taho tayi shiru ta kasa cewa komai,fuskarta duk ta nuna damuwa,lokacin kuyinas their car parked tun da bikin ya matso yadda take shige da fice ya sake mata suna yake kiranta da *KIN FI AMARYA*,duk lokacin da yaji tsokana da hakan yake kiranta,basu yi nisa ba ta biye masa lamari ya canja salo,kunyar tafiyar nasu tare yasa gaba d'aya Nusrah ta kasa motsawa tana jin kamar ta shige cikin seat d'in,har suka iso gida tunda ta rufe idanunta sai da taji sunyi parking sannan ta bud'esu a hankali ta kalli harabar gidan,as their car parked guards suka bud'e ta fito da sauri cikin jin kunya,duk gaisuwar da suke yi mata bata tsaya amsawa ba ta shige ciki da sauri,tana shigowa bata jita ba direct ta nufi bedroom d'in da suka sauka,a nan ta tarar da Nuraz kwance daga shi sai nickers yana waya,tana shigowa yayi mata alamar barka da zuwa,ta kalleshi tana yin murmushi da sauri ta ajiye jakarta ta wuce bathroom,lokacin da ta fito ya gama wayar yana dai kwance har lokacin,yana ganin ta fito ya sakko daga saman bed d'in yana yi mata wani irin kallon dake narkar mata da zuciya,tayi baya a hankali tana sakin murmushi,yace "ina za ki je kuma?" Ta kad'a masa kai,abunda ya faru a mota ya dawo mata a rai ita kad'ai ta kyalkyale da dariya,ya rik'o ta yana cewa "What are u laughing?" She nodded again tana b'oye d'uriyarta,ya rik'o waist d'inta yana cusa kansa tsakanin neck d'inta yace "Ba ni labarin naji" Tayi ajiyar zuciya tana sake yin murmushi tace "nothing" yace "anya zan yarda babu komai?" Tace "why not?" Because da kunya ta iya fad'a masa abunda ta gani,daga nan ya d'aga ta yace "ok! Muje a ba ni kulawa" tayi dariya tana kai hannunta saman beard d'insa.

*****

Tun da suka bar gidan Annie take zaune a gurin tak'i yarda ta tashi,Abbah dake shigowa lokacin ya yi musu rakiya bayan ya yi addu'o'in neman tsari da kariya ya kulle k'ofofin gidan duka,ya dawo inda take fuskarsa d'auke da murmushi mai tattare da nutsuwa,yana fara tahowa inda Annien take ta sake sunkuyar da kanta k'asa tana yin duk addu'ar da yazo bakinta saboda yadda take ganin abubuwan suna faruwa kamar ba gaske ba,Abbah ya k'araso cikin rantsatstsen parlor'nsu da yaji wasu irin royals na musamman masu kama da anyi musu feshin gold,ya zauna yana fad'in "Rabbigfirliiy watuub alayya innaka antat'tawwabul gafuur",sun zauna shiru na wani lokaci kafin Abbah yayi gyaran murya,a hankali yana kallonta yayi ajiyar zuciya ya fara magana
"Arhm! Ina son cewa wani abu,but i just don't know idan nace zan fad'i abunda yake raina yanzun maybe ko zan takura ki?" Annie dake tunanin yadda rayuwar ta nan gaba zai kasance tayi ajiyar zuciya a hankali ta d'ago tace "Babu komai" yayi murmushi yace "Na gode" shiru parlor'n yayi na wani lokaci kafin Abbah ya numfasa,a hankali ya fara da fad'in "Alal hak'ik'a even though na san dukan mu babu yaro,and then yanayin mu'amalar ki ya tabbatar kina da sani,ina da tabbacin ba za ki tab'a yin abunda yake ba dai² ba in Allah ya amince" sai da yayi shiru kafin ya d'ora da fad'in "A gaskiya na yi matuk'ar farin ciki,kuma ina yiwa Allah godiya da wannan baiwar da yayi min,though a bayan na yi aure sau biyu,na san kina da labari wani kuma kin san abunda ya faru,but duk dai ina son sake sanar da ke ne ba don komai ba sai domin ina tsammanin samun zaman lafiya,nutsuwa da kwanciyar hankali daga gare ki,a zamanin aure na farko bayan shekarun da muka d'auka tare da ita KHADIJAH,duk da Allah yayi mata rasuwa,alhamdulillah tun da muke zaune da KHADIJAH ban fuskanci wani matsala gareta ba har Allah ya karb'i rayuwarta,sai dai wacce na aura a karo na biyun a zaman da muka yi duk da shekarun ba su da yawa na fuskanci matsaloli masu tarin yawa,wanda har kullum na tuna ina jin bak'in cikin kasancewa da irin wannan matar,sai dai ita rayuwa duka kana yin naka tsarin ubangiji yana nasa,sannan rayuwar kanta tana tafiya ne bisa doro na k'addara,abunda Allah ya nufa shi yake kasancewa,wanda bai so ba kuma ba ya kasancewa,sai dai ina fatan zaman da zamu yi yanzun zai kasance zama na amana,duk abunda kika gani zan yi ba dai² ba za ki tallafeni ki yimin jagoranci zuwa kyakykyawan hanya,kamar yadda idan na ga za kiyi zan nuna miki hanyar da ya dace" Annie dake sauraron jawabin Abbah ta kad'a kai a hankali tace "In sha Allah ina fatan hakan,ina rok'on Allah ya ba ni ikon yi maka biyayya tare da sauke hak'k'ok'in da suka rataya a wuyana" Abbah yayi murmushin jin dad'i ya amsa da "Ameen",daga nan yayi mata jagoranci zuwa bedroom d'insu,here na basu guri kun san soyayyar manya yafi k'arfin idanuwan mu.

*Asubah ta gari (A²)...*

*****

Rayuwar gidan Annie ya kasance wani irin rayuwa ne mai cike da tsafta da girmama juna,kasancewar su duka ba yara bane,but tsarin zaman sun abun burgewa ne ga kowa,tun daga kan yanayin soyayya,kulawar da suke gwadawa juna idan ka shiga gidan za su sa kayi tunanin auren sun tun na saurayi da budurwa ne,yayin da a b'angaren Abbah ya kasance tun da ya samu Annie matsayin matar aure yake jin wani irin nutsuwar da bai tab'a samun irin ta ba a duka rayuwarsa ta baya,haka itama Annie a nata gefen sai take jin kamar da can ba aure tayi ba yanzun ne tayi shi a inda ya dace,even though mijin tan na baya da ya rasu yana sonta sosai but soyayyar Abbah gareta ya zame mata tamkar wani babban *KUNDIN* da bata tab'a bud'e shafin sa ba bare tayi karatu a cikinsa.

Cikin sati biyu da su Lolly suka sake yi a Nigeria tare da su bayan sun huta gajiyar biki,a nan Nusrah ta yi tunanin yiwa Abbah maganar zuwa dangin Mamma'nta,saboda rabonta da su baza ta iya tunawa ba,lokacin da ta yiwa Abbah maganar yayi shiru bai ce komai ba,da ta takura masa yace ta bari idan sun samu lokaci zai kaita,tayi shiru tana tunani because an d'auki tsayin lokaci take cewa tana so ya kaita ko ya barta taje yana hanawa,a gefen Abbah kuwa duk wannan hanya² da yake mata ba don komai bane sai don tsoron abunda zai iya faruwa,kasancewar bai manta irin rabuwar da suka yi da dangin Khadijah ba a lokacin da ta rasu,k'aramin yak'in da aka yi akan sun nuna suna so ya basu Nusrah su tafi da ita duk da ba yarinya bace k'arama da za ace idan tayi wayo za'a dawo masa da ita,Abbah yace ba zai iya ba ita kad'ai yake da,suyi hak'uri su bar masa y'arsa,an kai ruwa rana sosai lokacin har daga baya dai aka rabu dutse a hannun riga,daga nan ne tunda suka yi fushi basu sake zuwa ba saboda mangaganu da akayi musayarsu,shima kuma Abba'n sai bai kaita ba saboda sun nuna basa buk'atarta ya rik'e y'arsa,suna cikin wannan rigimar da Abban ta dage akan lallai ita ko address d'in ya bata taje da kanta,cikin satin ayyuka suka tasowa Rafeek,dole yasa suka tattara har su Annie suka nufi UK,unlike su Hajiya da su tun a satin da aka yi biki suka koma,a cewar Rafeek ko da suka yi magana da Abbah yana tambayarsa me za suje yi Uk? Rafeek yace yana da kyau suje honeymoon ne,Abbah dai yayi dariya but a zahiri ya fahimci dalilin aminin nasa na yin hakan,kasancewar ba ya iya b'oye masa komai haka shima,ko da suka sauka a k'asar lokacin da aka zo d'aukansu a airport har suka zo gida babu wani maganar da suka ji daga garesa,sai da suka shigo cikin mansion,a nan idanunsu suka tarar da abun mamakin da basu tab'a zato ba,kasancewar sati uku kenan basa k'asar,sannan a saninsu apartment biyu ne a gidan daga nasu sai na Hajiya,yanzun kuma sai lsuka tarar da k'arin guda ma'ana apartment d'in sun koma uku,duka suka tsaya kallon Rafeek because sun san aikinsa ne,yayi murmushi yana kallonsu kamar yadda suke yi sai yak'i cewa komai,Lolly tace "Yallab'ai! Wannan ginin fa?" Ya kalli su Nuraz yana yin murmushi yace "Na yara na ne",ta kalleshi da mamaki tace "wane yaran na ka?" Murmushi ya sake yi yana wucewa cikin apartment d'in Hajiya yace "kin fi kowa sanin wane yara nake nufi" quickly ta biyo bayansa tana cewa "Please Yallab'ai ka yi min bayani!" He didn't stop yana ci gaba da tafiya yace "u will soon understand" Su kansu su Nusran da suke tsaye ganin tafiyarsu da abunda suka ji yana fad'a ya ba su mamaki,sai dai babu wanda yayi tunanin wani abu,duka suka biyo bayansu,kafin su k'arasa shigowa Hajiya ta taho tarbarsu,ganinsu duka sunaa shigowa yasa cike da farin ciki ta bud'e baki,duk sai ta rasa wanda za ta fara tarba a cikinsu saboda yanayin da suke ciki ya tabbatar mata suna cikin kwanciyar hankali. Tarba na musamman da ta shirya saboda ta san da zuwan sun ya k'ayatar da su,bayan sun anci an sha aka zauna hira a parlor'n tsohuwar,ana tsokanar juna da wasa da dariya abun gwanin burgewa,yanayin ranar ya fi komai yiwa Hajiya dad'i,cikin tsananin farin cikin yadda family'n suka had'e kai tayi murmushi tana sake yiwa Allah godiya bisa wannan ni'imar da yayi a garesu.

Da dare a time d'in kowa yayi shirin bacci bayan sun gama hira,Nusrah ta shigo bedroom bata yi sallama ba sai b'ata rai take,ya d'ago kansa daga aikin da yake yi a computer ya kalleta bai ce komai ba,tana zuwa za ta wuce ta gabansa yayi saurin rik'o ta ya dawo da ita,ta kalleshi bata ce komai ba,yayi ajiyar zuciya yana k'ureta da kallo yace "what happen?" Ta girgiza kai bata ce komai ba sai k'ifta ido da take yi,a hankali ya janyota ya zaunar a jikinsa ya rik'o fuskarta,muryarsa k'asa² yace "Ba za ki fad'a min ba?" Kuka ta fashe masa da shi,ya lumshe idonsa yayi shiru sai da yaga ba ta da niyyar dainawa ya bud'e idonsa yana kallonta da kyar yayi ta maza yace "Shhhh! Be quite please" ya rungumeta yana shafa bayanta,da kyar ya samu tayi shiru tana yin ajiyar zuciya yace "Mene ne aka yi miki?" Sheshshek'ar kuka ta fara,za ta ci gaba yayi saurin cewa "u know ba na son kuka,yana tayarmin da hankali duk lokacin da naji ana yinsa kusa da ni,sau nawa kike so na fad'a miki ba na son kina yin kuka?" Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya,a hankali ya sauketa daga jikinsa ya fita,ta bishi da kallo har ya dawo tana inda ya barta,yana zuwa ya mik'a ruwa,ta karb'a ta sha ya sake zaunawa a gefenta,sai da ya bari ta samu nutsuwa then yace "Za ki iya fad'a min abunda aka yi miki?" Ta lumshe ido fuskarta tana bayyana damuwarta cikin shagwab'a tace "ba Abbah ne saboda nace ya kaini family'n Mamana.." Bata k'arasa ba yace "Me za kiyi musu ne kike son zuwa?" Tayi saurin kallonsa,ya kalleta yace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login