Showing 21001 words to 24000 words out of 130249 words
na neman halaka shi ya samu da'kyar ya kwace daga rikon dayai masa yana tsalle ya koma saman macijiyar da matukar gudu macijiyar ta tashi sama a hanzarce Asad ya harbo macijiyar da bindiga tayo kasa kara harbinta yai itama saita zama ruwa kafin ya saitin mutumin a satin Zuciyar shi ya harbeshi shi shima kara yai sai kuma ya kama da wuta faaaa kamar an zuba masa fetur wanda yaji falon ya kaure suna cewa "Asad lafiya me kakeyi haka"?.
Da sauri Asad ya dawo cikin nutsuwar yana kallon su cikin alamar tambaya yace "me nayi"? Hararar sa Ajeeb yai yana cewa "ban sani ba tsabar rashin mutunci kagani fa yadda ka harbi TV gashi nan ta fashe me kake kallo kodan kaiba ma'abocin son wasan kwallo bane maimakon kace mu canza channel shine ka lalata TV gabadaya wato mu daina kallon kenan"? Kasa cewa komai Asad yai sai Khimiyyah daya zubawa ido gira ta dage masa tana murmushi ba tare datai magana ba Ajeeb yaci gaba "wai Asad meke damunka ne sai anyi magana kai banza da mutum ko ka kure shi da kallo kamar Wanda ya warke daga ciwon makaranta" shidai Asad rasa ta cewa yai sai kallon Khimiyyah kadai yana mamakin abubuwan daya gani yanzu kenan Khimiyyah me take nufi wannan abun da ya gani hakan na nufin tana da ala'ka da kungiyar da yake nema? Jiyai tace "prince Asad kada ka damu da abinda ka gani wannan mafari ne ba'a nuna maka komai ba saidai ana farkar dakai ana maka gargadin cewa ka fita daga sahun masu son gano wannan abar kayi shawara" harararta Ameer yai yana cewa "ke kuma me kike cewa sai wani magana kike a juye me kike nufi"? Dariya tai tana mikewa tace "babu komai prince Ameer kawai dai na fad'a ne shi yasan me nake nufi" tana fadin haka ta mike tana fita a parlon "wai ita wannan meke damunta ne? Yawancin lokuta zakaji tana magana wata kala da batai kama data masu hankali" Annur ya fad'a shima yana mikewa ya cigaba "Khimiyyah a kaf cikin mu na fahimta itace ta fita daban take wasu irin abubuwa masu wuyar fassara yarinyar nan tana da matsala a kwakwalwarta".
"Ai Annur ba kai kadai ne ka fahimci hakan ba nima na gani sau tarin wasu abubuwan ta akwai abun duba da tambaya amma koma maye mu sa mata ido matsayin mu na yan uwanta muna da hakkin kula da duk wani motsin ta mu dawo da ita kan hanya" Ajeeb yai maganar yana mikewa shima zai fita har yakai kofar palon ya juyo yana kallon Asad yace "Asad kai kasan me Khimiyyah take nufi tunda dakai take sai ka fara tunani kayi nazarin ta mu hada gwiwa muna kula da komai nata" yana gama fadin haka yai waje tsaki Ameer yai yana cewa "waye zai tsaya bata lokacin sa akanta Khimiyyah ta fara zarce inda ake zaton ta a iya sani na banda makaranta daya zama dole babu inda ake barinsu su fita amma idan tayi wani abu zaka rantse irin wadannan tantiran yan matan club din nan ne" "eh kaima kace wani abu anan amma ai ni banga hujjar da zamu zauna muna binciken ta da sa mata ido ba kawai su Abba zamu sanarwa" kai Ameer ya girgiza "a'a Annur idan su Abba suka sani akwai matsala zamu lalata zaman jin dad'i na wani lokaci kawai ka 'kyale mu samo hujjoji da kanmu kafin mu sanar musu" "ok shikenan hakan ya kamata muyi" Asad ya kalla yana cewa "Babyn Mami muje lokacin sallah yayi" mikewa Asad yai yana rufe laptop din da sauri Makiyyah tace "prince Asad kawo na aje kuje masallacin" "no thanks I don't want" ya fad'a yana ficewa dariya Shaukiyyah tai tana cewa "kai gaskiya iska tana wahalar da mai kayan kara ina son shi yana zamewa" a fusace Makiyyah tace "ki dakata malama fatan ba dani kike ba"? Zaro ido Shaukiyyah tai tana shirin sakin wata dariyar tace "da nace miki me? Yau nake ganin isa da mallaka sharri zaki min Makiyyah"? Hararar ta Makiyyah tai cikin takaici tace "jarrabawa ce kema baki fi karfin a jarrabe kiba so haka yake fad'i da babbar murya ki 'kara ina matukar son Asad so mai tsanani ma kuwa" cikin tsokana Shaukiyyah tace "au haba so fa mai tsanani kika ce? Tab lallai kina da aiki wallahi prince Asad babu yan mata a gaban shi balle soyayya karma ki nemi dorawa kanki hawan jini" caraf Khaldiyyah tace "haka kike gani amma tunda taji tana son sa zata iya daukar duk wata damuwa mukan namu ido ne tunda mutum ya fad'a ruwa sai muga da yadda zai fito" nuna ta Makiyyah tai da yatsa tana cewa "ki dakata haka ki daina yi dani tun farko soyayya Asad a jini na take ta riga da ta zama kwalliya ta kuma bazan daina ba ko ku taya ni son abinda nake so ko ku zuba min ido nai gwagwarmaya ta da kaina na nemi soyayya ta" "to shikenan Mrs prince Asad Allah ya baki shi musha biki" Shaukiyyah tai maganar tana kau dakai dan kada Makiyyah taga dariya take mata mikewa Makiyyah tai tana cewa "amin inda gaske kike" fuuuu ta fice ta bar iya su biyu sauke ajiyar zuciya Khaldiyyah tai tana cewa "wallahi ina tausaya mana nida Makiyyah dukka hankalin zaratan namu ba'a kan mu yake ba" tabe baki Shaukiyyah tai tace "nikam shiyasa tun farko ban dorawa kaina wahala ba farko na harbu dason Ameer da naga kawai zan bata lokaci na kawai na share abun kuma da haka kukai ina tunanin zaifi domin ni gashi na zauna lafiya" kai Khaldiyyah tai girgiza cikin damuwa tace "bazan iya Shaukeey kawai zanci gaba da hakuri har ranar da prince Annur zai ce yana sona" kai Shaukiyyah ta kad'a "shikenan Allah ya kaimu wannan ranar" "Amin ya kamata muje muyi sallah kinga har lokaci ya fita" mikewa sukai Shaukiyyah na cewa "oh haka ne fa to sai muyi sauri".
Lokacin da Asad ya dawo daga tunanin kallon Isham yai tare da jinjina kai yace "Isham I believe what you said tabbas Khimiyyah tasan wani abu akan kungiyar nan domin ta ta'ba nuna min alama a bayyane" "oho ka gani ko dama na fad'a maka sai ka tsaya kayi nazari zaka sake gano komai, yanzu wanne irin mataki zaka dauka"? Shiru Asad yai zuwa lokaci mai tsawo kafin yace "sai nayi nazari" kai Isham ya d'aga "ok shikenan buddy amma ka taso muje ka kwanta dan Allah ka samu nutsuwa ka saba zama ka kwana ido biyu kana tunani da ayyuka bakai komai ba please let go" mi'kewa yai batare daya sake magana suka shiga bedroom.
Mrs al'ameen Ahmad ce π.
Yau ba dogon bayani kawai Allah ya tashe mu lafiya mu d'ora inda muka tsaya yau kaina na min ciwoπ.
11~AL-KHALIQU
The creator
12~AL-BARI
The Designer
6~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Taibina.
πππππππ
πππππ
πππ
ππ
π
π REVENGE ND WREAKπ
Episode 11&12
*'KAUYE*
Asubar fari tun ba'a shiga masallaci ba Asabe ta fito daga d'akin ta jin yadda ake kad'a iska mai sanyi yasa ta koma d'aki tana dauko hijab sannan ta fito ta bud'e randa ta soma kamfatar ruwa tana zubawa a bokati Saida ta cika ta kinkima ta shiga d'akin su Indo kwance ta ganta tana bacci can dayan 'bangaren Bahijjah ce itama a tata shimfidar cike da mugunta Asabe ta d'aga bokitin ruwan sanyin ta kwarewa Indo a kanta a firgice Indo ta farka tare da fasa 'kara jikin ta na ma'kyarkyata tsawa Asabe ta daka mata tana cewa.
"Ke dallacan munafika mitsiyaciya ki rufe min baki dama yanzu lokacin hutu ne tashi ki fito ki tafi debo min ruwa me nace miki jiya ban ce kika bari na sake zuwa tashin ki saina fasa miki baki ba"? Shiru ido tai ta kasa magana sakamakon kakkarwa da bakinta yake wani irin duka Asabe ta sauke mata tana finciko ta kiiiii ta wurga ta waje tana daukar ice ta soma jinka mata tana cewa "ke dan uwarki nice zanyi miki magana ki tsaya kina kallo na da idonki kamar na mayu tsinanniya makira mai halin mujiya zaki tashi ki debo min ko saina farfasa miki jiki"?.
Da'kyar Indo ta mike tana jan kafa ta dau bokiti hawaye masu zafi suna zuba a idonta tai hanyar fita Bahijjah dake tsaye a kofar d'akinsu tasa kuka tana cewa "gaskiya ni kun cuce ni gashi nan kun tada ni a bacci na kawai kin ji'ka min jiki" juyawa Asabe tai tana kallon Bahijjah zatai kiyi hakuri Bahijjah jeki ci gaba da baccin ki" tura baki tai tana juyawa ta koma cikin d'aki daidai Balarabe ya fito zaiyi alwala Asabe tace "gaskiya malam bakai sa'ar haihuwa ba ehe dole na fad'a wannan Indo ba yar mutunci bace tasha a nono wai ni zata zaga"? "Zagi dai"? Balarabe ya tambaya yana zaro ido hararar sa Asabe tai "oh nayi karya kenan naga ka zaro ido waje kamar wanda ka hadiyi 'kayar kifi to wallahi ta dawo kaja mata kunne karya kuskure ta sake zubawa Bahijjah ruwan sanyi a jikin ta wannan mugun halin har ina bazai yiwu ba bazan dauka ba" cikin lallami Balarabe yace "dan Allah Asabe kiyi hakuri ki shiru kinga fa ma'kota naji gari bai waye ba" "au gari bai waye ba shine abinda zaka ce? To bari na jira garin ya waye saina sauke maka buhun bala'in zakai bayani" tana kai nan ta shige d'aki gasa'ke Balarabe yai yana kallon kofar d'akin nata kafin ya dauki buta ya daura alwala ya tafi masallaci.
Misalin 'karfe sha biyu da rabi na rana su Amatu na zaune a tsakar gida suka ji an rafka sallama mace ta shigo A'i ce tayo wuf ta bakad'o labule ta fito tana cewa "a'a Kande kece shigo man kika tsaya anan ga kujera" "ba zama ya kawo niba ina Saude"? Dariya A'i tai "tofa yau ake yinta kema garin nema neman bashin ta taje ta yaudare ki da maganganu kin bata kaya tayo gwarama ko? Tab aiko baza ki samu ko nera biyar ba Saude bata biyan bashi tafi son na lahira................
"Allah ya tsinewa munafiki Allah ya d'ed'eta shi ya hana shi jin dad'in zaman duniya" Saude tai maganar cikin 'bacin rai ta karaso gurin ta'be baki A'i tai tana cewa "oh ji borin kunya harda tsine tsine dad'in abun ma ba karya naiba kowa yasan kina da taurin bashi" a fusace Saude tace "ai shiyasa nace Allah ya tsinewa munafiki Allah ya talauta shi" juyawa A'i tai zata bar gurin tace "ba Amin ba dan kina jin haushi na fiki kud'i da hanyar samu shine kike neman arziki na yai kasa to bakin ki ya fad'i a kasa".
Cikin takaici Amatu tace "Aisha ku tashi mu koma d'aki" mi'kewa sukai suna shiga Saude dake mamakin zuwan Kande tace "Kande lafiya dai na ganki a haka ki karaso ciki man".
Kai Kande ta girgiza "a'a ba wannan nazo yiba kuma ba zama ya kawo ni ba nazo ne nayi miki gargadi keda 'yarki Saude ki jawa Asma'u kunne ta fita hanyar d'ana Buba yafi karfin ta yafi karfin auren ta bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane me zaiyi da ita na riga nayi masa mace acan kauyen mu ki fad'a mata kada ta kuskura ta sake zuwa inda yake idan kuma ba haka ba sai kinga matakin dazan dauka a kanku sai nasa an wulakanta 'yar taki" tana kaiwa nan tai waje" tsaye tabar Saude ta rasa meyake mata dad'i cikin duniya babu wanda ya ta'ba zuwa ya tsaya yace a kira masa wace ba sai Buba sun fara murna kuma yanzu ga uwansa tazo ta yi musu diban albarka.
"Ahayye nanaye yau take gobe sai labari nisa tazo kusa wato dama Buba ne yazo gurin Asma'u kuna ta farin ciki sai gashi uwar tazo tayi muku wankin babban bargo murna ta koma ciki cabdijan gaskiya Kande ta iya wulakanci" A'i tai maganar tana sakin dariya Saude na tsaye shiru duk zufa ta rike mata jiki ta rasa meke mata dad'i ba maganganun A'i ne damuwar taba na Kande ne suka sosa mata rai.
Bata kula A'i dake ta magana ba ta shareta ta tura mata aniyarta da'kyar ta d'aga kafafunta ta koma d'aki suma su Amatu dake d'aki sunji komai kuka Asma'u keyi ba 'kakkautawa harda shid'ewa cikin jin zafin kukan nata da tausayawa Amatu tace.
"Dan Allah Asma'u kiyi hakuri ki daina kukan nan haka kada ki dorawa kanki zazzabi ki dauka hakan da tayi shine mafificin alkairi kiyi adduar Allah ya kawo miki miji na gari wanda yafi Buba nagarta" cikin kuka Asma'u tace "amma Amatu ina son Buba meyasa zatai min haka ta raba ni dashi kowa ya tsane mu a kauyen nan wai me muka yiwa mutane ne da basa so su gam mu cikin walwala"?.
Kai Amatu ta girgiza "babu abinda mukai musu kuma ba tsanar mu sukai ba a haka rayuwar tazo mana da 'kalubale ni nasan meye matsalar rashin wadatuwa da mahaifin mu baida shi ne yasa kowa baya damuwa damu amma dan Allah kiyi hakuri insha Allahu zaki samu miji na gari wanda ya take Buba nagarta kinji" kai Asma'u ta d'aga tana goge hawayen fuskarta tare da yin murmushi tace "Amatu na gode gaskiya ke 'yar uwa ce ta gari mai kawar da damuwa da kwantarwa mutum hankali ya dawo cikin nutsuwar sa Allah ya biya ki" dariya Amatu tai tana cewa "kai wallahi kema dai Asma'u ji kamar wanda na baki wani abu" sauke ajiyar zuciya Asma'u tai tana kallon Jamila da kawai ta zuba musu ido tace "wani abu ne mana ai Asma'u a rayuwa d'an uwanka yafi komai shiyasa koda yaushe nake son na ganku cikin farin ciki" kai ta jinjina "mun gode sosai Amatu Allah ya barmu tare" "Amin kawai Amatu tace tana mayar da hankalin ta kan littafin dake hannunta Aisha data kasa hakuri tace "wai nikam Amatu littafin nan na meye ne kullum yana hannunki" d'agowa Amatu "oh littafin karatu ne" "wanne irin karatu"? Jamila tai tambaya tana le'ka littafin amsa Amatu ta bata "karatu dai wanda kika sani akwai wani bambanci ne"? "Eh akwai man watakila littafin soyayya akwai na ya'ki akwai na karatu 'karin ilimi wannene daga ciki"? Dariya Amatu tai "to ba daya kodan kin canka littafin karatun karin ilimi ne daga Dutse na taho dashi lokacin da naje gurin baba Bashir" "a karanta mana a fili muji" Asma'u tai maganar tana kwanciya akan shimfidar su kallon ta Aisha tai "ai dama na sani ko fara karatun baza ai ba zaki bacci dan nasan d'an halin" hararar ta Asma'u tai "ke kuma wa yasako dake to ba baccin zanyi ba saina ji komai kuma zaki gani" dariya ce ta kama Aisha Amma ta dake tace "ni kuma indai aka gama karanta littafin nan baki bacci ba nasa raina d'ari" "aiko yarinya zanci kuma duk inda d'ari take saikin 'kwakulo kin bani" "shikenan kuna jin mu dai ko to ku zama sheda Amatu karato mana" fara karanta musu tai suna sauraron ta sunji dad'in karatun ko ba komai zai d'an debe musu kewa kafin lokacin tafiya tallar abinci.
Gidan Balarabe Indo wuni tai a rana babu ko karyawar safe sai uban wanki da take yi tayi matukar gajiya duk zufa ta ji'ke mata jiki sai haki take Dalah ce ta fito daga d'aki cikin takaici ta karaso tana cewa "ke Indo tashi haka tsaya da wankin nan kici abinci kada olsa ta kama ki tun dazu na kawo miki na dauka ma kinci yanzu harya huce" numfashi mai zafi Indo ta fitar tana mi'kewa tsaye tare da rike bayan ta cikin yamutsa fuska alamar bayan ya rike ciwo yake mata ta fita cikin kayan wankin tana zama kan kujera ta bud'e kwanon ta fara cin abincin.
Fitowar Asabe kenan ganin abinda dake faruwa yasa ta karaso gurin da sauri tana zuwa tasa 'kafa tai bol da kwanon abincin ya tarwatse a kasa tabi da takalmi ta murmushe shi a kasa kafin ta juyo ta dauke Indo da mari wanda sai data kifa daga kan kujerar da take.
A masife ta soma magana "amma lallai Indo kin raina min hankali har nice zan kafa miki doka wannan bulkumar uwar taki mai kama da icen dogon yaro da ba'kin ido ta sa kika sabawa umarni na? Aiko yau sai kinci 'kashin ubarki" ta karasa maganar tana rufeta da doka ta ko'ina.
Wani irin d'aci ne yazo ya tokarewa Dalah a makoshi tana kallon yadda Asabe ke dukan Indo wanda ta rantse da Allah ko jaki baza a yiwa wannan dukan ba jin ihun da Indo take abin tausayi ga jini yana fita a hancin ta yasa zuciya tazowa Dalah wuya a fusace taje ta fincike Asabe a kan Indo tai wurgi da ita tana d'aga Indon dake kwance tana kiran wayyo ciki wayyo ciki.
Yunkurawa Asabe tai da'kyar ta mike domin ta bugu a kafa ta karaso tare da cukumar Dalah itama Dalah da ta riga ta hauro ranta a mugun 'bace ta sha'ki asaben wanda asabe taji shakar cikin bala'i ta soma magana "ki sake min wuya Dalah wallahi kin kira masifa da kanki zaki ga bala'in dayafi karfin tunanin ki saina sauya miki kamanni ki saki ni nace".
'Kara sha'ke ta Dalah tai tana cewa "ke din banza baki isa kimin komai ba bari kiji wata magana 'kyale kin da nake kike min cin mutunci kike yi duk abinda kikai niyya kinga na zuba miki ido ba yana nufin bazan iya daukar fansar abinda kike min bane amma yau kin gama yawo Asabe zaki yabawa aya za'kin ta".
Da gudu Bahijjah ta fito daga d'aki tana cewa "ai wallahi Dalah baki isa ba kika kashe min uwa kema saina kashe ki dallacan sake mata wuya" ta karasa maganar tana jan hannun Dalah wanda Dalah cikin kunar rai tasa d'ayan hannunta ta saukewa Bahijjah mari kara Bahijjah ta saki a gigice tai baya tana kuka kokawar kwacewa Asabe ta soma tana cewa "kinsan Allah Dalah kin shiga uku kin gama yawo kwanan ki ya 'kare kuma zaki gani" "naga alkairi baki isa kimin abinda Allah baiyi min ba" Dalah