Showing 90001 words to 93000 words out of 130249 words

Chapter 31 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17635

tare dasu Isham suna bincike.

๐Ÿ•š๐Ÿ˜ƒ๐Ÿค—
Asad na zaune a wata babbar kafaffiyar rumfa dake cikin 'katon barrack d'in da laptop๐Ÿ’ป a gaban shi yana aiki Yusairat da Clarah suka shigo suna zama bai d'ago ba da sukai masa sallama amma ya amsa kallonsa Yusairat tayi tana cewa.

"Asad an ta'ba ce maka kai kyakkyawa ne"?.

Ba Asad ba hatta Clarah saida ta kalleta da mamaki da kuma kishi cikin alamun tambaya yace.

"Kamar ya"?.

Murmushi Yusairat tai "kamar ina nufin wani ya ta'ba ce maka kana da kyau"?๐Ÿ™….

Kai ya jinjina "eh ba mutum d'aya ko biyu ba mahaifana ne farko sun fi kowa yabo na".

Gyara zama Yusairat tai tana cewa "nima ina son ka saka ni a cikin su Asad kai kyakkyawa ne kuma na fad'i abinda yake 'karkashin zuciya ta sannan ina so idan ka samu lokaci zamuyi magana".

"Ok ina jinki"?.

Kallon Clarah Yusairat tai da kulawa tace "please Clarina dan Allah ki d'an bamu wuri kamar minti biyar" wani irin razanannan kallo Clarah ta mata jin abinda take cewa cikin takaici ta mi'ke tana jin zuciyarta na suya fuuu zatai gaba dakatar da ita Yusairat tai ganin kamar yanayin ta ya sauya tace.

"Am Clarah kiyi hakuri fatan hakan bai 'bata miki rai ba"?.

Jin tambayar data sake jefo mata yasa a fusace ta juyo tana huci ji take kamar ta rufeta da duka muryarta cikin fushi tace.

"Eh".

Tana fad'in haka tayi gaba da kallo Yusairat ta bita kafin ta sauke numfashi tasan Clarah da rashin fahimta maybe yanzu har taji haushin ta share batun tai tana maida hankalin ta kan Asad tace.

"Asad idan baza ka damu ba zance ina sonka"?.

Daina abinda yake yi yayi yana d'agowa ya zuba mata ido na wani lokaci baice komai ba daga baya ya mayar da hankalin sa kan laptop shiru Yusairat tai a ranta tana ayyana Allah yasa ba 'bata masa rai tayi ba saidai ba yadda ta iya dole ta kasa ha'kuri gara ta fad'a masa ta hutar da zuciyarta muryarta da damuwa tace "kayi hakuri nasan zakaji mamaki taya na iya furta maka saidai bazan yi maka 'karya ba na dad'e da kamuwa da ciwon son ka tun ranar dana fara ganinka nayi kokarin dannewa amma na gaza kayi hakuri zuciyata tayi nisa a halin yanzu tana gaf da fashewa bazan iya jurewa ba" tana kaiwa nan ta mi'ke zata bar gurin jiki a sanyaye taji saukar muryarsa.

"Yusairat Bikirah (Abbakar) meyasa kika bari zuciyarki tayi rauni ta kamu da soyayya alhalin kamata yai ace kin ri'ke aikin ki why"?.

Ji tayi hawaye yana zuba mata dama ta sani bazai amince mata ba amma dai duk da haka gara data fad'a masa ya sani.

"Me kike tunani"?.

Kai ta girgiza "babu komai kayi hakuri".

"Ok yayi zaki iya tafiya ki tabbata kin mayar da hankalinki kan aikin ki kada ki sare akwai nasara a gaba".

"Shikenan Asad na gode sai an jima" tana fad'in haka tayi gaba a harabar part dinsu ta samu Clarah zaune ta zuba tagumi zuwa tai tana zama a kusa da ita d'agowa Clarah tai idonta yayi ja kallo d'aya taiwa Yusairat ganin alamar kuka tai yasa tace.

"Meya faru kuka ki kai"?.

Kai Yusairat ta girgiza tana sake goge hawayen fuskarta tace "nayi kuka ne saboda zuciya ta batai min adalci ba taya zata kamu da soyayya bayan ni kuma aiki nazo ba shirme ba".

Zaro ido Clarah tai jin abinda take cewa har 'kwaruwa take wajen cewa "soyayyar wa"๐Ÿ˜ฒ?.

"Clarah soyayyar Asad ina cikin matsala na shiga rud'u tabbas na mayar da hankalina kan aikina amma yanzu Asad nake so nake mafarkin samu Clarah ke kanki kin sani Asad na dabam ne taya bazan haukace akansa ba in masa son da ban ta'ba yiwa wani mahalu'ki ba kuma aurensa zanyi shine burina".

Tab Yusairat na rufe baki Clarah ta zabura tai cikin tashin hankali tace "what kina sonshi kuma aurensa zaki"?.

Kai Yusairat ta d'aga "eh haka nace masa kuma ina matukar sonsa koda ace shi baya sona indai ya amince zai aure ni a haka zai zauna dani a shirye nake".

Wani ba'kin fitinannan kallo mai ma'anar kin samu ta'bin 'kwa'kwalwata ne? Clarah tai mata tana cewa "amma wallahi Yusairat kin bani mamaki ban ta'ba zaton haka daga gareki ba shin dama soyayya zatai tasiri a kanki ai na dauka jarumtarki bazata bari ba karki manta abinda kika ce shekarun baya aiki ne ya kawo ki ba shirmen soyayya ba mune muka zo soyayya damu ta dace dan haka me zai hana kici gaba da zama a hakan".

Girgiza kai Yusairat tai cikin gazawa tace "bazan iya ba Clarah ina son Asad da dukkan zuciya ta nayi nisa a cikinsa please ke bakya gani ne ki kokari ki fahimce ni man"๐Ÿค” had'e rai Clarah tai cikin takaici tace "na fahimce ki shikenan abar maganar ta isa haka" kallonta Yusairat tai kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa kawai ta 'kyale aje a hakan saidai tasha mamaki ganin kamar Clarah ta nuna kishinta a lokacin datace mata ga wanda take so kuma tana fatan Allah yasa Clarah bata fad'a cikin son shi ba inko haka ta faru zata iya bar mata komai batare data damu ba amma banda Asad.

Bayan wani lokaci iya 'kokari Yusairat tayi na ganin ta shawo kan Asad domin ya sota amma abun yaci tura karshe ya bata za'bi ya kuma fad'a mata gaskiya shi baiji sonta a ransa ba idan kuma tana ganin zata iya aurensa a haka ya bata dama ranar tayi farin ciki ta 'kara ta kuma amince koda bazai ta'ba son nata ba zata aure shin jin wannan batu ba 'karamin kad'uwa Clarah tayi saidai ta sami wani wuri ta 'boya tasha kukan ba'kin ciki gabadaya tabi ta lalace ta rasa me yake mata dad'i har ciwon zuciya ya sameta kullum tana hanyar asibiti a haka tafiya taci gaba da mi'kawa har lokacin da Yusairat ta bukaci a d'an bata kwanaki ta jima rabonta da gida zataje bayan ta gama shiri saida taje sukai sallama da Asad kamar ta fasa tafiya saboda dashi haka taji da'kyar tabar gurin sa yana zaune yana aiki ta shiga 'bangaren Clarah amma neman duniya bata ganta ba ta kira wayarta ba'a d'agawa ha'kura tai ta koma tana sanarwa Asad cewa idan Clarah ta dawo ya fad'a mata tafi sati uku zatai ta dawo bata dau wasu kaya masu yawa ba kawai tahau motar dazai kaita airport ta wuce.

Clarah dake gefen titi zaune a cikin mota ganin Yusairat ta fito tana mi'kawa d'an taxi din kud'in sa yasa tayi wani irin murmushi tana jinjina kai tare da kunna motar da mugun gudu ta figeta tayi kan Yusairat data juya ta fara tafiya gadan-gadan ta nufeta cikin tsana da kishi tana zuwa gaf da ita ta sake d'iban motar da gudun gaske ji kake gammmmmm ta sureta ta tafka da kasa tabi ta kanta ta wuce a d'ari tabar gurin tunda dama abunda ta 'kudura kenan kuma burinta ya cika sai datai nisa da gari ta tsaya tana fita a motar ganin yadda jini ya 'bata tayoyin yasa da sauri ta d'auko fetur ta bulbule motar dashi ta 'kyasta ashana faaaa ta kama da wuta cikin azama tabar gurin tana wata irin dariya ta farin ciki ji take kamar ta sauke wani 'katon dutse dake kanta.

A halin data bar Yusairat kuwa cikin jini faca-faca abun babu kyan gani mutane sun taru a kanta babu wanda ya santa a ciki amma anyi dace da akwai wani soja dayazo giftawa ya gani shima da'kyar ya ganeta saboda yadda Clarah ta sauya mata halitta a gigice ya d'aga waya ya kira Isham ya fad'a masa wanda Isham tsabar rud'ewa bayan ya sanar da Asad ko mota basuyi tunanin hawa ba a kafa suka zo an cika guri yayi ma'kil ta tsakanin mutane Asad ya samu ya shiga tana kwance cikin jini sai juya kai take cike da azaba da sauri yayi kneel down a gabanta ya ma kasa magana sai kallonta yake cikin tashin hankali Isham ne yai 'karfin halin cewa.

"Asad meka tsaya kallo ya kamata mu kaita asibiti๐Ÿฅ๐Ÿš‘ yana rufe baki sukaji jiniyar motar asibiti ta karaso gurin shikam ba maharraminta bane shiyasa koda wasa bai ta'ba taba haka aka dauketa zuwa asibiti likitoci sun rufu a kanta sai aiki suke amma basu iya ceto ranta ba ta rasu lokacin da suka sanar da Asad baisan a wanne yanayi yake ba magana ma aiki ta zame masa kawai iya abinda yake gani a idon zuciyar shi shine abinda ya faru a baya rayuwar su irin yadda take da jarumtaka lokaci guda yau an wayi gari rana ta fito babu ita iyacinta kenan Shikenan.

Da Clarah ake komai harda kukan ta na munafirci babu wanda yayi zaton itace silar mutuwar Yusairat haka ta fitittike har Bangkok taje saida aka gama komai suka dawo Marshall islands harda zama wata so silent๐Ÿ˜” ta daina wargi duk dan kar a zargeta daga baya irin wai abun nan ya zama jiki sai tazo ta ware ta kama harkokinta kullum ta dage ta kara azama dan Asad ya yabeta kamar yadda yake yabon Yusairat yace ita jaruma ce shishshigi iri iri har ta samu suka 'kulla abota amma baya baya ita kuma abin nata harda za'kewa ta nuna soyayya fili 'karara baiji mamakin ta ba dan yasan dama za'a rina yaga take taken ta tun a wancan lokacin bai nuna bane kawai ya share ta.

Shekara d'aya tsakani da mutuwar Yusairat Asad yaje gida a lokacin khimiyyah tayi nisa sosai ta samu yanki babba cikin wannan mummunar 'kungiyar kwatsam ta fahimci asirin su yana gaf da tonuwa a daren ta cikin mirron tsafi ta kira Hudayyah ta sanar da ita abinda yake faruwa ita kuma a take tace tazo su had'u a samo mafita taje suka had'a meeting da shugabannin cewa su bazasu shigo masarautar ba akwai tsaro za'a iya samun matsala amma ita tunda anan take itace zatai musu aikin lallai ta dakatar dashi kar asirin su ya tonu tunda ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye tayi la"be tayi le'ke a ranar Asad yayi waya da Isham cewa gobe zai taso sannan ya kusa gano abinda yake nema da shirinsa cikin kayan sojoji hula ce kad'ai da takalmansu bai saba kwana yai curr yana aiki sai asuba ya fita sallah masallaci tayi amfani da wannan damar ta shiga masa d'akin sirrin sa tayi masa 'barna dalilin samunta dayai a d'akin shine hujjar dayai mata dukan hallaka sannan ya shirya batare da sanin kowa ba yabar masarautar a ranar ya koma Marshall islands.


๐Ÿ’‹MRS AL-AMEEN AHMAD CE๐Ÿ˜˜.

See you next time, tanks for ur support I really appreciate it ๐ŸŒน๐Ÿ’“๐Ÿ’ฏ nagode 'kwarai da gaske masoya ha'ki'ka kuna raina har bansan yadda zan kwatanta a gane ba baki bazai iya fad'a ba kalmomi bazasu tsaru ba kawai abinda zan iya cewa saidai nace ina son ku da dukkan zuciya ta ๐Ÿ’‹๐ŸคŸ๐Ÿ’”๐Ÿ’—.


YรšSRรƒH Mร›Sรƒ ร€BรšBร…Kร‚R
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

5608ร‘G๐Ÿ“ฒ F4D, J7ร‘/ร€ร‘/Bร–BD 67แบž4ร€H M7แบžร€ ร€B7BรƒKฤ€4๐Ÿ’ป๐ŸŽค ku fito nazo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿค—.


๐Ÿ’Ž Mร‰ KรƒMรƒR SรRKร ๐Ÿ’Ž


WhatsApp no:234 905 527 3614
๐Ÿค™โœ๏ธ YUSRAH MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒน.
Ba maraya๐Ÿ˜ฃ___sai rago๐Ÿ˜ช
Ba nakasashe๐Ÿคจ___sai kasashshe๐Ÿ˜ž
Ba mai raina kad'an๐Ÿ™„___sai 'barawo
Ba makaho๐Ÿšถ____sai ma'ki gaskiya๐Ÿคฅ
Ba munafiki๐Ÿ˜ณ____sai wanda ya'ki gaskiya, idan kaga abinda ba daidai ana aikatawa please yan uwa mu gyara shi๐Ÿ‘ whoever sees a wrong thing should correct it๐Ÿ™.NONE OF YOU WILL HAVE FAITH UNTIL HE WISHES FOR HIS BROTHER WHAT HE LIKE FOR HIM SELF. Removing harmful object from the road is charity.

ร€ร‘ร‘ร™RรŒ WRรŒTร‰R'S รƒSSร•ร‡รŒร…Tรร”ร‘๐Ÿ’ซ
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_________________
______________________________
__________________

๐Ÿ’ซA*W*A๐Ÿ’ซ
MRS รƒL'ร…Mร‰ร‰ร‘ รHMรƒD ร‡ร‹๐Ÿ˜˜
_________________________

Mai tambarin yma dutse Jigawa state new world ๐ŸŒน new life and new style sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa.

๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ
May Allah bless u may Allah protect you and your household frm all calamities ๐Ÿคฒ๐Ÿ‘๐Ÿ™.
HรƒPPY JรšMรƒ'ร‚T MรœBร…Rร„K
๐Ÿ‡๐Ÿ‰๐ŸŽ๐Ÿฅฅ๐Ÿ“๐ŸŒ๐ŸŠ๐Ÿ’๐Ÿ๐Ÿฅ๐Ÿฅ•๐Ÿ.


๐ŸŽˆY๐ŸŽ‰U๐ŸŽˆS๐ŸŽ‰R๐ŸŽˆA๐ŸŽ‰H๐ŸŽˆ๐ŸŽ‰๐ŸŽˆ๐ŸŽ‰
โœจ๐ŸŽ€Mโœจ๐ŸŽ€Uโœจ๐ŸŽ€Sโœจ๐ŸŽ€A
๐ŸŽŠA๐ŸŽB๐ŸŽŠU๐ŸŽB๐ŸŽŠA๐ŸŽ
๐ŸŽ†K๐ŸŽ‘A๐ŸŽ‡R๐ŸŽ‘
๐ŸŽ„Y๐ŸŽ‹M๐ŸŽ„
๐ŸŽˆA๐ŸŽ‰
๐ŸŽˆ

LITTLE ZARAN AUNTY ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
๐Ÿ’ฎ๐ŸŒธ๐ŸŒผ๐Ÿต๏ธ๐Ÿ’ฎ๐ŸŒธ๐ŸŒผ๐Ÿต๏ธ๐Ÿ’ฎ๐ŸŒธ๐ŸŒผ๐Ÿต๏ธ

41~AL-JALIL
The majestic
42~AL-KARIM
The bountiful

20~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Akilinah.

๐ŸŒ„AVENGE ND REASSURE๐ŸŒ„
Episode 41&42
Asabe bata gida kwananta biyar kuma koda wasa bata fad'awa Balarabe inda taje ba amma sakamakon ta gama dashi ta shanye shi yasa baya da kata'bus bazai iya cewa ina taje ba, tana can ta sake sabo shiri ta d'ingumo masa wani asirin na cin mutumci gabadaya a duniya ya rasa dawa yake son kasancewa sai 'yarsa Indo kullum yana ha'kon ta yana neman d'an dalilin da zai fitar da Dalah anguwa ya samu abinda yake so Asabe bata auri Balarabe dan ta samu wani abu daga bangaren dukiya ba kawai wannan d'auke mata kan da yayi lokacin da taiwa Indo kyautar 'kosai da sanda ta shigo gidansa ya wulakanta ta wannan hujjar yasa ta aure shi da niyyar tarwatsa masa iyalinsa da hana shi farin ciki daga burinta ya gama cika koya saketa ko karya saketa zata tattare kayanta ta 'kara gaba ta koma Lagos tare da 'yarta Bahijjah.

Kamar yadda Balarabe yai fata hakan ne ya faru Asabe bata dawo ba Dalah ta tafi gidansu yana shigowa tana zaune tana wanke-wanke d'an gyara murya yai a firgice ta waigo domin yanzu masifar tsoron sa take ji murya na rawa tace.

"sannu baba" ta karasa maganar a d'ari-d'ari a mamakin sai taga ba kamar kullum ba ya saki fuska harda murmushi yace "yauwa me kike anan"? 'kara d'agowa tai tana kallon sa jin me yake cewa anya babanta ne mutumin da baya kulata ya tsaneta rabon da tai masa magana ya amsa mata a sake harta manta jin ya sake cewa "Indo ba dake nake ba nace meye kikeyi anan"?.

A zabure tace "ina wanke kwanuka ne" kallon kofar d'akin Dalah yai ganin ba takalminta yace "ina Dalah"? Cikin sanyi Indo tace "taje gidan babah Aliyah tace zata biyo ta gida su gaisa da Innah" kai ya jinjina "to to shikenan zonan yanzu" yana fad'in haka wuff ya fad'a d'aki mi'kewa Indo tai jikinta na rawa ta bishi d'aki tana shiga ya banko kofa๐Ÿ™Š.

Shigowar Dalah ganin ba Indo a gurin wanke wanken kuma ga takalmanta dana Balarabe a kofar d'akinsa yasa da sauri taje tura kofar tayi sa'a baisa sakata ba abinda ta gani ne yasa hankalin ta yai mugun tashi zuciyarta na bugawa ta rafka wani uban salati dafe 'kirji tace "na shiga uku na lalace malam mezan gani haka? Wacce irin ba'kar rana ce wannan"? Jin maganar Dalah yasa a firgice Balarabe ya saki Indo dake kuka tana ta kokawar 'kwacewa daga jikinsa jin ya saketa da sauri ta mi'ke da gudu ta fita daga d'akin tana kuka dan ma Allah ya rufa asiri babu abinda yai mata binta Dalah itama tayi da sauri dan batasan inda zata nufa ba shima Balaraben biyo bayansu yayi sai muzurai yake cikin takaici Dalah tace "Malam wacce masifa ce ta sameka ace 'yar daka haifa kake kokarin lalata da ita meya sameka haka ya akai ka canza rayuwa"? Daidai Asabe zata shigo taji abinda Dalah ke cewa dan haka a hankali cikin sand'a ta koma da baya ta la'be tana murmushi wato ha'konta ya cimma ruwa.

Tsawa Balarabe ya daka mata cikin borin kunya yace "ke dalla gafara matsa min anan danai me mekike nufi dan kawai nace ta shiga d'akina tamin shara shine ke kuma saboda gidahuma ce har kika fassara hakan da wata tsiyar" kai jimin mutum kallon sa Dalah tai hawaye na taruwa mata a ido ta ce " yanzu tsakanin ka da Allah Malam ko kunya bakaji ba kake kokarin lalata mata rayuwa gaskiya nagaji bazan iya ba wallahi kawai ka canza hali" a masife yace "bazan canza d'in ba da nace bazan canza d'in ba kinga Dalah ki kiyaye zanci mutunci fa mekike nufi da zan lalata mata rayuwa iye? Saboda ga 'kwarto jikan 'kwarata ko? To nayi maza kisa lasafika garin nan da kewayensa kowa ya sani na nemi Indo wallahi duk ranar da tsautsayi yasa kika tona min asiri naji wannan labarin ya fita waje sai kinga yadda zanyi dake shashashar banza mahaukaciyar wofi" yana kaiwa nan yayi waje yana surutai iri iri na borin kunya da gudu Asabe ta fice a gidan dan karya ganta sauri take kamar zata tashi sama daidai anyi kiran sallar magriba suka had'u da 'kawarta Markah da sauri ta tareta.

"Ke Markah ina zuwa haka? gurin ki fa na taho".

"Tofa 'kawar arziki ince dai lafiya ko asirin ne ya karye muku fito rana bankad'a ta same mu"?.

Kai Asabe ta girgiza "ke a'a waya fad'a miki ai kinsan nace miki na tafi gurin boka ko? To zuwa nai aka sake bani sabon sihiri nasa boka ya cusawa Balarabe son kasancewa da Indo aiko sai gashi d'azu gida ba kowa sai ita kad'ai Dalah bata nan ya lallameta yasata a d'akinsa humm naso yayi 'barna ya aikata abun kunyar dazai bar abin fad'a har jikokinsa amma shegiyar Dalah ta dawo ta katse min hanzari yauwa kuma sannan ya gargad'eta kada ta kuskura wannan labarin wani ya sani basu san ina ra'be ina jiba shiyasa na garzayo na fad'a miki dan kema in kinyi gaba ki yad'a so nake zancen ya bazu ko'ina".

Dariya Markah tai "kai amma wallahi 'kawata baki da mutunci kin iya tsiya ya kamata ki barshi haka ai kin rama yanzu saiki 'kyale shi ki fita rayuwar sa ki barshi ya huta".

"Ta'be baki Asabe tai "humm naki wasa ne tabd'ijan waya fad'a miki na gama ramawa ina dai kan hanya har yanzu nasan komai ya lafa bari na koma gidan naje nayi 'kirmishishi kamar bansan komai ba sai anjima kawata" "to shikenan 'kawar dama gulma ce ta kawo ki kuma kin fad'a min hankalinki ya kwanta nima bari na koma gidana, toni dama ina zanje ne mema na fito yi a waje? Dan tsaki taja tuna had'uwar da sukai da Asaben yasa ta manta kawai ta juya gida, duk abinda suke tattaunawa Malam Habu yana zaune 'kar'kashin wata bishiya yana jinsu ya danji mamakin Balarabe daya nemi 'yarsa Indo subahanallahi kai jama'a Allah ya kiyaye 'bacin rana.

Tafiya sannu sannu kwana nesa lokaci ya mi'ka shekarun da aka d'ebawa Tanko na zaman gidan yari sun cika ya dawo gida Hummm!!!๐Ÿคช Me kuke tunani Tanko ya dawo bayan wadannan shekaru da wani irin turnu'kakken ba'kin dafin d'acin 'bacin rai na daukar fansa da mugun nufi musamman daya tarar babu iyayen sa ko daya sun

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login