Showing 81001 words to 84000 words out of 130249 words
wayon 'kauyen naku gaskiya ku barmu mu sarara ko kuma ku fita a bedroom d'in akan me muna zaune lafiya zaku hana mu jin dad'i gashi abinda haushin wanda kuke fad'an akansa baisan kunayi ba bai damu daku ba bakwa gaban sa na tabbata duk tsiya ko yana ra'ayin ku saidai ya auri d'aya kunsan bazei auri ku duka ba amma kuka tsaya kuna wahalar da kanku kun manta matar mutum kabarin sa maybe babu mai rabo a cikin ku saikun gama haukan ku yaje ya auro wata daga waje gashi kun girgiza junanku da fad'a da 'kiyayya meyasa ku bakwa tunani ne? Haba kamar wasu ma'kiyan juna gaskiya nake fad'a muku koda bai shafeni ba kuna abinda bai dace ba ku gyara ku mayar da hankali".
Wani banzan kallo duk su biyun suka watsa mata Khimiyyah tace "d'an maimaita abinda kikace banji sosai ba"?.
Had'e rai Shaukiyyah tai "bazan maimaita ba kada Allah yasa ki gane duk ranar da kika bud'e ido kikaga Asad da matarsa maybe ranar kyayi surrender ki gane kinyi kuskure".
"Ai wallahi Shaukiyyah babu ranar da zata zo wacce zanji wata nadama ta kamani har abada kuma zan iya yin komai dan cikar burina dan na samu abinda nake so kin gane? Dan haka bar 'bata bakinki a kaina ba fahimtarki zanyi ba".
Kai Shaukiyyah ta jinjina tana cewa "shikenan Allah yasa ki gane nikam shine fatana da ban nuna inason kowa ba a cikin su gashi na zauna lafiya sannan ban wahalar da zuciyata ba nasa mata rai akan abinda nasan bazata samu ba".
A banza Shaukiyyah take magana babu wanda ya fahimce ta a cikin su gani suke ba'kin ciki take musu ko dai akwai abinda take boyewa a ranta ita kuwa a zahirin gaskiya tana nuna musu abinda zai fishe su ne kar zuwa gaba wani mummunan abu ya faru wanda baza aji dad'i ba.
Khaldiyyah dake kwance da littafi a hannunta tana karatu batai musu magana ba tunda suka fara abinsu sai yanzu ta tashi zaune tana rufe littafin ta aje tare da kallon su har yanzu suna aikawa juna kallan kallo murmushi tai tana sake kai kallonta kan Shaukiyyah data d'auke kai daga saitinsu domin tayi iya yinta sun 'ki fahimtar ta kai ta girgiza tana cewa.
"Haba ku kuwa ladies👯 meye matsalar kune zaku li'kewa mutum daya? Ku bari na sasanta na raba muku fad'an inace mu hud'u ne kuma suma su hud'u ne? Ni a nawa ganin kawai kowa ta kama d'aya zaifi koba haka ba"?.
Kallonta Khimiyyah tai fuska ba rahma tace "me kike nufi su waye su hud'u"?.
Gyara zama Khaldiyyah tai "ina nufin mu hud'u suma su hud'u ne an raba kowa saita kama d'aya nikam dama na za'bi nawa tun tuni amma kunga da ban nuna ba ai na zauna lafiya lokaci nake jira wanda da kansa zai fahimta basai na furta masa ba domin neman kima da daraja a idonsa".
"Waye kike so a cikin su amma badai Asad ba"? Khimiyyah tai maganar tana kallon Khaldiyyah datai murmushi tace "a'a rufa min asiri ni kaza 🐔 abinci na dusa waneni Asad yafi 'karfina 😊 saidai manyan mata irinku" ta karasa maganar tana dariya.
'Kara had'e rai Khimiyyah tai "ai ba dogon bayani na nemi kimin ba cewa nai waye kike so a cikin su"?.
"Humm wannan kuma bai shafeki ba Khimiyyah dama an fad'a miki ni gariyace dazan fad'a miki wanda nake so wato kije ki fad'a masa batare dana bi a hankali ya soni ta sassaukar hanya ba ki ri'ke naki na ri'ke nawa".
Numfasawa Shaukiyyah tai tana cewa "nikam zan fad'i wanda nake so ba kuma bana jin shakkar a fad'a masa ban sani ba ko shima ya kamu da sona lokacin da banyi zato ba".
Dariya Khaldiyyah tai "ke wa kike so Allah yasa ba wanda nake so bane dan nima yanzu zamu hau sama mu fad'o".
Kafad'a Shaukiyyah ta d'aga tana cewa "to muhau man tunda yayin fad'an ake nikam wanda nake so "Ameer ne Allah yasa ke bashi bane"?.
Cikin tsokana Khaldiyyah tace "kika ce Ameer kike so? Kai Shaukiyyah ta d'aga Khaldiyyah taci gaba "innalillahi ai nima shine za'bin nawa"😲 zaro ido Shaukiyyah tai kamar zai fito waje tace "dan Allah da gaske kike Ameer kike so? Nashiga uku yanzu ya zanyi bazan iya fad'a dake ba koda hakan zai zama cutarwa ga rayuwata zan bar miki shi na dau dangana Allah ya bani wanda ya fisa".
Dariya Khaldiyyah tai cikin yabawa da saukin hali irin na Shaukiyyah tace "ke da wasa nake dan naga yadda zaki ne ni Annur nake so" wani numfashi Shaukiyyah ta sauke harda jan ajiyar zuciya tace "kai har naji dad'i wallahi" ta karasa maganar tana dafe kirji tace "kiji yadda zuciya ta take harbawa kai gaskiya so bala'i ne" wata uwar harara Khimiyyah ta mako mata tana cewa "au haba dai kinsan so bala'i ne kike ce min na ha'kura da wanda zuciya ta keson kasancewa dashi? Humm Asad gwarzon namiji ne yana da 'kira ga kyan halitta bana gajiya da kallonsa bana son abinda zai zo ya gifta tsakanin mu a yayin da nake kallon wannan haskakakkiyar sharararriyar kyakkyawar fuskartasa mai cike da manyan idanuwa farare tas dogon hanci pink lips kwantaccen gashin kai ba'ki wuluk mai she'ki da daukar hankali ga tsararran saje na kwatance mai burge wanda ya shagala wajen kallonsa saima kinzo ma'kura 'karshen magana wato halittarsa jikinsa ko'ina a murd'e yake ga gashi kullum zuciya ta tana kwad'aita min na kalleshi batare da riga a jikinsa ba naga 'kira inaga wannan rana bansan irin farin cikin dazan tsinci kaina a ciki ba" d'an shiru Khimiyyah tai tana murmushi tare da ri'ko hannun Shaukiyyah tace "dan Allah Shauki ki fad'a min waye zai 'kyale jajurtaccen namiji ingarma sadauki irin Asad ya had'u yana da kyau har bansan yadda zan tsara miki ki fahimce ni ba kema shaida ce tunda kin sanshi" kai Shaukiyyah ta daga.
" 'kwarai Khimiyyah na sani kuma matukar mace zatai ido da ido da Asad duk kyanta da mulkinta saita kalleshi ta 'kara sai taji ya burgeta ta aje 'kasaitarta tayi mafarkin samunsa ya tafi da jinta da ganinta zata rud'e ta gigice ta rasa nutsuwar ta ne a yayin da tai tozali dashi".
Zabura Khimiyyah tai cike da shauki tana jin yadda son Asad ke kara zurfi da fad'ad'a da yalwa yana sake samun guri a zuciyarta tace "to dan Allah kin gani ko taya zanyi sake na 'kyale Asad zan jure komai dan na sameshi zan 'batar da komai harsai mafarki na da burina na zamowa matarsa ya cika inaso na jini a cikin jikinsa in kwanta a lallausn jikinsa nasani ranar ne zanyi barci cikin 'yanci da dad'i please Shaukiyyah nasan kina sona kina son abinda nake so dan Allah ki taya ni addu'ar na sameshi matsayin mijina😕😏.
Kai Shaukiyyah ta jinjina "shikenan sis na fahimce ki gaskiya Asad ya gama tafiya da komai naki to ina miki fatan karki sha wahalar banza shima yasoki koda bakai wanda kike masa ba ki zama matarsa musha biki" rungumeta Khimiyyah tai tana cewa "nagode sosai na gode Shaukiyyah ke yar uwa ta 'kwarai ce tunda har kika fahimci halin da nake ciki a yayin da wannan bagidajiyar take neman rusa min tunani na" ta karasa maganar tana kallon inda Makiyyah ke tsaye babu ita babu alamar ta tsaki taja tana cewa "can ta matse miki wallahi mu zuba mu gani" mi'kewa tai tana sauka a gadon ta fita "nayi gurin mom d'ina" tace tana yin waje gyara kwanciya Khaldiyyah tai tana cewa "uhmm inji mai ciwon baki mukam bamu da ta cewa Allah ya rufa asiri" tashi Shaukiyyah tai tana dariya tace "to Amin dai bari nima naje bangaren mu na dawo" itama fita tai suka bar iya Khaldiyyah wacce taja bargo tana lullu'be jikinta gabadaya tare da fara tunani da nazarin yan uwan nata da abinda yake faruwa to meke damunsu ace ubansu d'aya suna son mutum d'aya akansa suna neman jefa fitana fad'a da 'kiyayya a zuciyarsu wanda ta tabbata Asad zata iya rantsuwa da Allah tayi masa farin sani basa gabansa babu wacce zaiso a cikonsu bawai tanai musu fata bane amma bata ji a jikinta cewa akwai matar Asad a tsakanin Khimiyyah da Makiyyah kawai haukan su suke sauke numfashi tai tana sake jan bargo ta rufe har kanta tayi shiru tun tana tunani har barci ya d'auketa.
MRS AL-AMEEN AHMAD CE 😘🤩.
Thanks for ur support💓💯💓💯🤗 I really appreciate it 🌹💓💗💞 Allah yabar 'kauna yan uwa insha Allahu gobe xakuji ta yadda aka samo asalin tushe ta wannan 'kungiya da farkon wanda ya samar da ita da had'arin da take dashi👹👿☠️💀.
Typing📲 sun jun 9/24 yr Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty 💃🧚🧜🙋🤷.
Mai tambarin yma dutse Jigawa new world 🌹🤙 new life and new style sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa 😜 garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa ⛰️🏞️🗻.
Ranar muce masoya maza karda muyi sanya muyu rausaya yan uwa mu taho da baya baya mune muke shagali💃💃 ranar mu tayi haske 🌃.
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY GIDAN KAR'BAR MUTANE HANNU BIYU DA ZAMAN LAFIYA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI YAYANTA HAKA TAKEN MU YAKE 🌹✌️.
STORY AND WRITTEN
✍️YUSRAHMS ABUBAKAR 🌹🤙 MRS SIR👌 YALLA'BAI🙇 MAI GIRMA🙅 MAI NASARA🤙 MAI D'AUKAKA🤞 BABBA🤛 KAFIN ALLAH ALHAJI👋 KAINE GATANA🤗 AL'AMEEN NA YUSRAH KAKE MALAMINA😍 OGANA🙈 MAI GIDANA🤷 LIMAMINA🤷 SUPERSTAR⭐🌠🌟 D'INA SIR AL-AMEEN AHMAD😘😘😘🙇🙅.
Wannan page din naka ne dan uwa rabin jiki NURA SANI ABBAN MUHAMMAD AND SHUKHRAH FATAN ALKAIRIN ALLAH YAKAI MAKA DUK INDA KAKE BROS💯 NA YABA DA KYAWUN HALAYENKA👌👍💓💯.
#Vote
#share
#fallow.
yusrahmusa65@gmail.com 🙅.
__________________________________
37~AL-KABIR
The Great
38~AL-HAFIZ
The preserver.
18~Allahumma salli wa ala sayyidina muhammadin sayyidil Hafizinah.
🌄WITCHERY ND SUDDENLY🌄
Episode 37&38.
A cikin wani 'bakin kumburarran mummunan fusataccen daji na tsafi masu duhuwa ababen tsoro da mugayen manya bishiyoyi a tsaye d'ima d'ima kamar tsaunuka masu wasu irin ganyaye da rassa abin tsoro kallon su kad'ai zai iya tashar maka da hankali lokaci guda ka fita hayyacinka musamman in suna kad'awa maimakon subada iska mai dad'i saidai su hankad'o wani turnu'kakken ba'kin zafi kamar ana watso tafashasshan ruwan zafi babu wanda yasan da zaman dajin balle har a samu wani mai 'kwarin gwiwar iya zuwa har yace zai binciki wani abu da kuwa ranar za'ai babu shi saidai uwarsa ta haifi 'kaninsa dan zai tafi lahira kai tsaye babu wani jinkiri ko kwano-kwano dajin ya kasance dajine na tsafi ba kowa yake ganinsa ba asalinsa na wasu baka'ken munanan aljanu 👹👹👻 ne horarru wajen iya tsari da sarrafa mugunta babu d'igon imani a tattare dasu basu da tausayi basa d'aga 'kafa basa uziri ko a jariri ne mutum mai gaskiya kuwa basu da ma'kiyin daya kaishi zasuyi fad'a dashi su ya'ke shi akan yabar hanyar 'kwarai d'ai dai ne masu tsallewa tarkonsu ta wannan hanyar suke bi suka halaka mutane da yawa suka rijayo mutane da yawa sukai musu mubaya'a sun kasance anan tsahon shekaru suna rayuwa a ciki tare da wata had'ararriyar shahararriyar bokanya matsafiya abar tsoro mai tsoratarwa asalinta mutum ce kuma ta kasance a cikin mutane daga baya ta za'bi ba'kar rayuwa ta za'bi ta zama masifa da fitina a cikin mutane ta hana su zaman lafiya.👹👹.
Shiru dajin yake tsit baka jin komai sai dariyarta zaune take a wani ba'kin kogo ta tan'kwashe kafafunta da manya manyan wasu darukan tsafi a gabanta sai sautikan kuka ne ke fita a ciki abubuwa ne 'kanana saika lura zaka gane mutane ne tayi musu tsafi suka zama wadannan yan kananun kamar teddyn roba ta wasan yara ta d'aga kanta sama sai dariya take hannuwanta a bud'e ha'koranta na tsiyayar jini idanuwanta ma haka kayan jikinta duk jini ne a jiki ga takubba🗡️⚔️🏹 da wu'ka'ke a gefenta da yawa.
Daina dariyar tai tare da sauke kanta kasa tana kallon darukan muryarta kamar zai fashe tace "kuma ku zama jini domin baku da amfani" ta karasa maganar tana zuba musu wani ruwan tsafi akan a take suka narke jini ya balle ya fara bubbuga nan da nan ya cika gurin tanjan kamar kogi tashi tsaye tai ta fara zagawa da wani sandar tsafi a hannunta ta nuna jinin tana cewa.
"Wannan jinin kaine zaka zama jigon wannan 'kungiya kaine masifa da fitana saika zama bala'i ga duk wanda yaso gano asirin mu saiya hallaka dakai zamuyi amfani wajen kare kanmu da kungiyarmu kaine asirin mu kaine tanadinmu nayi alkawarin saina hallakar da mutane masu tarin yawa dakai" ta karasa maganar tana busa wani abu a take jinin ya 'bace ya zama gurin ya gyaru kamar dai babu abinda ya faru kira ta fara da wasu irin sunaye marasa dad'in ji nan take wasu 'bakaken aljanu 👹👻 suka fara dira a gabanta masu siffa abin tsora.
Cikin bada umarni tace "ku zama mutane ku bazu kubar dajinnan ku shiga gari gari kasa kasa ku fara aikin dana saku babu tausayi har jariri tsohuwa ko bazata iya tashi ba ku had'o da ita ina so naga na hana kowa jin dad'i da sukuni ina so na tarwatsa farin ciki kuje na baku umarni" nan take suka fara baza fuka fukansu suna tashi suka tarwatse suka watsu ko'ina bayan sun fita daga asalin dajin tsafin suka fara sauka kasa suna zamowa mutane kallon kansu aljanun sukai bayan su komo mutanen sukace wannan siffar akwai kyau dole ne ma muyi aure da mutane muje zuwa kowa ya kama gabansa" nan take kowa yai inda yasa gaba suka bazu d'ai d'ai kamar wasu matunen arziki.
Zaune wani hamsha'kin mutum yake a office dinsa ya jingina bayansa da kujera yana juyawa a hankali idonsa a rufe AC na seseta shi saidai da alama baya cikin yanayin jin dad'i ba wata walwala akan fuskarsa yayi matukar zurfi a tunanin da yake knocking akai masa batare daya bud'e ido ba yace "yes waye? zaka iya shigowa".
Bud'e kofa yai yana shigowa kansa a sunkuye cikin sanyin jiki ya tsaya tare da gaidashi sai lokacin ya d'ago daga jingine a kujerar da yake tare da cewa "lafiya na ganka a haka miya faru"? Kasa magana Safyan yai saboda tunanin abinda zai faru idan ya masa bayanin mutanen da suka bar nan yanzu domin basu bukaci had'uwa dashi ko su samu tattaunawa ba basa bukatar jin komai daga bakinsa saidai ya girbi abinda ya dad'e yana shukawa.....................
"Kai Safyanu magana fa nake maka da akwai wani abu ne"?.
Kai Safyan ya d'aga yana mi'ka masa takardar hannunsa yace "eh yalla'bai gashi sa'ko daga commissioner daga can sama yace a kawo maka" jiki na 'bari yasa hannu ya kar'ba da sauri ya bud'e yana karantawa ganin abinda ke ciki an dakatar dashi aiki sam ba suspect ba balle yasa ran dawowa ba wani abu dazai samu nan gaba takardarsa bazata sake masa wani amfani ba saidai yai kasuwanci yasa ya mi'ke tsaye gumi na tsatstsafo masa yana kallon takardar idonsa yayi ja ransa a mugun'bace yana huci yace.
"What!!!? Ni commissioner zaiwa haka ni zai wulakanta Safyan kaine silar komai kai kaja min asarar rasa aikina wai shin ranar gidan uban wa kaje kabar bakin office d'in nan har wannan tsinannan commissioner ya shigo min office batare da izini naba"?.
Sunkuyar dakai Safyan yai yana cewa "yalla'bai kayi hakuri bada sona bane".
Cikin tsawa ya d'aga masa hannu "zancen banza kenan hakurin uwar wa? Ya zanyi bayan ka jamin masifa ai duk silarka ne komai ya faru munafiki mai ba'kin ido🙊 yanzu me zakace min shashashan banza shashashan wofi da nace ka tsaya a kofar da baka bar gurin ba taya commissioner zai shigo ya kama ni da wannan yarinyar saboda cin mutumci maimakon ya rufa min asiri mu rufe maganar a office d'ina amma dan ya muzanta ni ya nuna ni 'kwarto ne a gaban yarana ya tozartani ya nuna ni ba mutumin arziki bane eh me zakace akan haka"?.
Shi dai Safyan shiru yai yana sauraron sa dama yasan irin wannan ranar zata zo kullum mutum ka girma amma kana da budurwar zuciya da son lalata yaran mutane kawai ka basu kud'i da motoci dan jin dad'i kamar kai baka haifa ba.
"Safyan tunanin uban me kake ne? Wato ina magana ka mayar dani majnun ko? Yanzun ina commissionern yake"?.
"Ai yalla'bai ba shine yazo ba wani drivern sa ya baiwa shine kawo kuma bai zauna ba tafiya yai".
Komawa yai da baya takwash ya zauna akan kujerar yana sake kallon takardar dasa hannun Governor shikenan ya shiga uku ya fito rana gashi wasu ma'kudan miliyoyin kud'ad'e da yake jiran shigowar su 'karshen wannan watan ne ga bala'in daya same shi tonan asiri biyu babu wanda yasan yayi danniyar kud'in na al-umma ne da gwamna ya bayar ayi musu aiki ya 'boye amma yasan dole yanzu kowa ya sani har gidajen TV za'a yad'ashi dafe kai yayi ransa na 'kuna kansa ya d'au zafi yace.
"Zaka iya tafiya".
"To yalla'bai a huta lafiya" Safyan ya fad'a yana fita "uban na huta ina cikin masifar taya zan samu lokacin hutu" ya karasa maganar yana huci shiru yai yana tunani zuwa wani lokaci ya rasa abinda yake masa dad'i jin ana kiransa a waya yasa ya d'auka jikinsa har rawa yake ya d'aga yana cewa.
"Hello haba commissioner ya zakai min haka wannan wanne irin cin mutumci ne da cin fuska ka nuna min"?.
Daga can 'bangaren commissioner yace "Prof ya kake"? Haushi maganar ta bashi kamar zaice ban sani ba sai kuma yace "ina lafiya amma yanzu abinda kai min ka kyauta kenan commissioner"? Cikin basarwa commissioner yace "oh sa'kon ya iso gareka kenan? Jin yai shiru yaci gaba "idan ka duba zakaga from Governor ne bani ba nima dan aike ne kawai aka bani kuma na isar dan haka yace a fad'a maka babu kai babu 'kara yin aikin gomnati har abada bayan haka yace sisi bazaka samu ba sannan wannan miliyoyin kud'ad'e da kace sunyi 'batan dabo watan daya wuce yanzu yace a fad'a maka ya samesu ta asusun jarinka da yake Australia na kamfanin ka ta hannun Mr wiliyam Emmanuel ka gane gobe zai aika ayi masa 'kwakkwaran bincike acan da abubuwanka saiya tabbatar wannan kamfanin iya kud'in kane Babu na gwamnati a ciki".
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Prof Jibril