Showing 30001 words to 33000 words out of 130249 words
saba" bata fasa ba tace "wallahi malam saina je saina tabbatar musu na amayar abinda ke cin raina tunda kai bazaka iya ba" tana fadin haka fuuuuu tai waje kai malam ya girgiza batare daya kalli sauran matan nasa ya shiga d'aki cikin tausayawa suka bishi da kallo domin a zahirance Ramatu tana matukar wahalar dashi da halinta.
Mayafi a kafad'a Ramatu ta shiga gidan ganin yaran ta 'yan mata su biyu kawai ta fad'a musu da duka babu neman dalili ko tsayawa tambaya tana masifa "ina tsinannun gidan nan ku fito naci uwar ku dan dambun ubanku jahilci akai ya Jummai da Mamman matsiyata 'ya'yan Allah bani mu huta gori kina ina ba'kar munafika fito nace".
Fitowa Jummai tai cikin mamaki take kallon Ramatu dake ta jibgar 'ya'yan ta kamar ta samu kayan wanki sai ihu suke rai bace tazo tana rufe Ramatu da duka ita nan fad'a ya kaure hayaniya ta cika gida mutanen ma'kota sai shigowa suke tuni akai caaa aka rabasu kowa na tambayar mai ya faru.
"Jummai na huci tace "ina nasan abinda ke faruwa kawai ji nai yara suna ihu ina lekowa naga ta danne su sai dukan su take komai sukai mata oho matsiyaciyar mata kawai" han'kurowa Ramatu tai zata kawowa Jummai cafka mutane suka tare tana cewa "dama taya zaki san abinda sukai min tsinanniyar kanta munafika mai ba'kin hali wallahi bazan yarda ko kijawa yaranki kunne ko jiki yai tsami ina d'an dalili zasu tisa min 'ya a gaba sai ramar ta suke bata da sukuni kamar wata mujiya kullum tana ra'be a gefen dandali bata da wargi hakan bai ishe suba sai sunce mata jahila to ku sani ba itace jahila ba Jummai ce" ta karasa maganar tana sake kai hannu zata cafko yarinyar dake gefe tana kuka tace "zo nan dan uwar ki mai siffar aljanu har nice zanyi magana ki zuro min ido kina kallona.
Mamakin 'karfin halin Ramatu kowa keyi Jummai takai matukar jin d'acin maganganun da Ramatun keyi amma ta dake tana kallon yaran nata tace "meyasa zaku ce wa 'yarta jahila ina ruwanku da ita" cikin kuka Hanne tace "wallahi babah bansan da wannan zancen ba ni a yau ma ban had'u da Lami ba" kallon dayar 'yar Jummai tai cikin fad'a tace "dan ubanki kece ko? ina ruwan ki da ita"? Itama cikin kuka tace "ni fa bani bace wallahi bance mata komai ba" a hangule t Ramatu tace "kuna nufin sharri zatai muku dan darar ubanku"? Haushi ya kama Jummai tace "Ramatu wulakancin ya isa haka sunce basu bane dole saikin tilasta musu sun karbi laifin da ba nasu ba na rantse da Allah bazan yarda ba sai munje gaban me gari yai mana iyaka bani bake ba 'yarki ba 'ya'yana karar ki zankai".
Shewa Ramatu tai tana cewa "kin dad'e baki kaini ba mai garin banza da wofi ai ni kare ya fishi a wajena in kinga dama ki kaini ramin gyare karewar kara aikin banza kawai ina jiranki idan kin fasa kaini uwarki cikin shegen ki tayi ta haife idan kin fasa kaina ba'a haifeki da jini ba idan kin fasa kaini ke ba yar halak bace goyon bola da juji ce ke" tana gama fadin ta sa'bi gyalen ta dake 'kar tai waje kamar wacce ta samu ta'bi sai hararrami take.
Kowa mamaki yake duk da dama sun san Ramatu sani na ha'ki'ka ba mace mai kirki bace wata mata dake kusa da Jummai ce ta kalle ta tana cewa "ke kwa Jummai wanne tsautsayin ne ya had'o ki fad'a da rahma"? 'kwafa Jummai tai cikin takaici tace "taya zan sani Ladi ina d'aki fa naji kukan yaran nan kawai tazo ta rufe su da duka wai sunce wa Lami jahila kiji fa dan Allah gashi yaran da bakin sun ce basu bane".
"Aiko wallahi Jummai karki yarda ki kai kararta gurin mai gari ko ki biya kud'i ki hau mashin kije ki d'ebo mata 'yan sanda domin wannan cin fuskar yayi yawa azo har gidan a zageka a d'aki yayanka" Ladi ta fad'a ranta a'bace "ai basai kince komai ba Ladi dole na kaita kara idan na bari ni banza tasha gaba ma wata tsiyar zata sake tsirowa tazo ta sauke min idan taga ban dau mataki a wannan ba" "a tabbas karki ta'ba yarda Jummai ki kaita kara a yau din nan kice baki yarda ba a bi miki kadin zuwa miki gar gida datai ta dakar miki 'ya'ya" hijab Jummai ta dauka tana cewa "yanzu ma kuwa zanje" fita sukai tare da sauran mutanen da suka zo ceto Jummai ta nufi gidan mai gari.
Ramatu na shiga gida ta aje gyale tare da bud'e randa ta kamfato ruwa tasha ta sake debowa tana jan kujera tace "haba kai sai yanzu naji sanyi a raina da naje na idar musu hankali na ya kwanta mu zuba idan basu gaji da ce wa Lami jahila ba nima bazan gaji da jibgar su ba haba mutum matsoraci ma bai had'u malam kowa ya d'ebo bolarsa kai zai zubawa tunda yaga baka da kata'bus amma idan ka iya masifa zakaga kowa yana tsoron ka" tana rufe baki yaro yai sallama yana cewa "wai malam yana nan"? Lekowa daga d'aki Baffah yai yana cewa "eh ina nan meya faru"? Yaro na kallon yadda Ramatu ke hararar sa yace "malam isubu ne yace wai kaje inji me gari" wani kallo Baffah yaiwa Ramatu kafin yace "jeka ina zuwa" yaro na fita Baffah ya kalli Ramatu yana cewa "sai ki tashi kije aina fad'a miki idan kinsan farkon fitina bakisan karshen taba babu ruwa na a cikin wannan al'amarin duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka indai bazan fad'a miki magana kiji ba nima na zare hannu na daga safgarki" yana fadin haka ya koma daki.
Mi'kewa Ramatu tai tana cewa "bari nidin naje rigima ba uban wanda ta kashe kowa yaci tuwo dani miya yasha ba'ai d'an dazai taka ni na barshi ya huta ba saina 'kaddamar masa da daukar fansa" sa'ba gyale ta kuma yi tai waje matar Baffah Salamatu ta bita da kallo ta gaza gane wacce Ramatu takamaimai mutum ce ko aljan.
Fal ta samu gaban mai gari ya cika da mutane ana jiran zuwan ta ga Jummai a gefe tana zaune da yaranta itama zama tai tana harararsu can ta hango Lami tafi bayanta Iluh ne yaron mai gari da alama a dandali yaje ya kirata bayan sun 'karaso mai gari yace "Ramatu kinsan dalilin kiran ki nan"? Kamar bazatai magana ba sai kuma tace "eh na sani tunda naga wannan ba'kar munafikar tare da yaran ta nasan karata ta kawo" a fusace Jummai tace "kece babbar ba'kar munafika annamimiya mai hana zaman lafiy............................
Katse su mai gari yayi da cewa "ba hayaniya na ce kumin ba sannan bance kuyi zagi na zaga a gaba ba ke Jummai ba ke na tambaya ba ki bari nazo kanki" "kayi hakuri mai gari amma ka hana ta zagina" Jummai na rufe baki Ramatu tace "an zageki tsinanniyar tashaπ²" tsawa Bukar ya daka musu cikin fad'a yace "gaban mai gari kuke hatta ko yanzu nan a kira muku hukuma" ta'be baki Ramatu "kai kuma asuwa baka da wannan matsayin ka bari wanda ya isa yai magana zaka kancaro mana jajayen ha'kora wani kai kai gaban mai gari kukeπ ai mun sani tunda ba makafi bane mu" "ya ishe ki haka Ramatu" Bukar ya fad'a yana nuna ta da yatsa zatai magana taji mai gari yace "wai wannan wanne irin iskanci ne zaku saurare ni ko harkar gaban naku zakuyi shin kun dauke ni mutumin banza ne"? Shiru sukai sai isubu da yace "Allah ya huci zuciyar ka kayi hakuri ayi musu afuwa sunyi kuskure" caraf Ramatu tace "amma dai Isubu na kayan miya kake nema wanda yai lefi baibada hakuri ba sai d'an kallo" "karki 'kara domin ni ba sa'an yinki bane" dariya Ramatu tai kamar zararriya tace "a lallai Isubu wannan ai borin kunya ne idan na kara me zaka iya yi"? Kai tsaye isubu da ransa ya gama 'baci yace "zan kai ki gaban hukuma ne" nan ma dariya ta kuma yi tana cewa "anzo inda nake son ji kaga idan ka turo yan sanda suka kamani 'kalau dani gaba ta kaini dama ina son zuwa garin sarin kayan miya saina saro abina ko ya kace tunani me kyau" kowa kallon mamaki yai mata wato wannan matar ta zama annuba ba mai iyawa da ita.
Zuba musu ido kawai mai gari yai saida gama da akai sa'a Isubu bai sake kulata ba ya kalli me gari yana cewa "kayi hakuri ranka ya dad'e" d'an tsaki mai gari yayi kamar zai daddannawa Ramatu zagi dan ta gama 'kular dashi cikin kaiwa zuciyarsa nesa ya kalli Lami dake gefe yana cewa.
"Ke Lami me ya had'a ki da wadannan yaran har suke ce miki jahila"? Kallon su Hanne dake gefe Lami tayi tare da girgiza kai tace "basu bane Balkin gidan me layo ce ita da Razi'kah ta gidan su baba Abuh "kina nufin ba su Hanne bane suka fad'a miki"? "Eh me gari basu bane" kai ya jinjina yana cewa "kinji da kunnenki Ramatu basu bane amma kikaje har gida kika dake su kika ci zarafin uwar su" Mamman mijin Jummai dake gefe yace "nikam me gari koda ma ace sune bazan yarda da dukan datai musu ba balle yanzu da gaskiya ta bayyana a gaban kowa dan haka ina so amin adalci abi min kadin shiga min gida datai ba neman izni ta dakar min yara harda fasa baki ta ciwa mata ta mutunci ko na kaita gaba gurin yan sanda" "gun yan kokara zaka kaini wallahi baka isa ba sisi bazan bayar ba 'ya'yan kane idan kaga dama ka sai musu magani idan kaga hagu ka barsu da ciwon jiki ba matsala ta bace ba ruwa na da hakan" kai Mamman ya jinjina zaiyi magana me gari ya katse shi da cewa "kaga karka ce komai Mamman ka 'kyale zan biya kudin kaje ka sai musu maganin zuwa gobe zan kira azo a tafi da ita inda wuya zata sa tayi ladabi tunda taga nan kafad'a ta daidai take da tata zaku iya tafiya zan kira ka gobe da safe" godiya Mamman yai yana mikewa shida Jummai da yaransa sukai gida.
Me gari na kallon Ramatu data mi'ke yace "ke kuma gobe ki kwana cikin shiri da zuwan sammaci domin na gaji da kashe shari'arki gara na kaiki gaba inda za'a saita miki zama" shewa da gud'a ta saki tana cewa "ai kayi ta banza meyasa zaka bari sai gobe ka kaini a yau mana me gemun wofi" tana fadin haka ta karkad'e masa 'kura tai gaba tana yiwa Lami masifa "kema dan ubanki meyasa baki fad'a min wanda yace miki jahilar ba kika 'kyale gashi kin jawo min zuwa gurin yan sanda" muryar Lami da damuwa tace "kiyi hakuri dan Allah bada sona bane" "shikenan koma gurin tallar ki bari nabi ta gidan su Balkin itama naci uwarta ta fad'a tana kama hanyar anguwar da kallo Lami tabi bayanta tare da sauke ajiyar zuciya ta share hawayen daya zubo mata ko kadan bata farin ciki da kasancewar Ramatu uwa a gareta kowanne d'a zaiyi tunkaho ya nuna uwarsa a ko'ina amma banda ita juyawa tai ta nufi dandali tun daga nesa taga yadda ake nunata ana 'kus 'kus amma ba yadda ta iya haka ta daure ta karasa ta samu guri kawai ta zauna tare da sunkuyar dakai kasa ta rafka tagumi kunyar kowa take ji abinda Ramatu take aikatawa a garin indai yaro ya d'ago yakai shekara hud'u zuwa biyar to yasan Ramatu saboda bala'in ta.
βοΈMRS AL'AMEEN AHMAD CE ππ.
Sai Allah ya kaimu gobe zamu d'ora maman little Zaran aunty.
Kai jama'a Ramatu mai zamani Ramatu Ramatu tuwaiye Ramatu Ramatu me kike dafawa kan awakai kiyi ki dafa ki bani nawa zani ba takai ba ko kano ne kije ki dawo ai na Sara miki Ramatu dole na wake ki tab muje zuwa readers yanzu aka fara.
IN ANA BATUN JIRGI ME AKE DA MOTA AHMAD BIN MUHAMMAD DA GA NANA BINTA A CIKIN WALIYYAI KAINE KAKE SARAUTA JIKAN MA'AIKI INA MI'KO GAISUWA TA.
Rayuwar da ba annabi ba rayuwa ba dakai naffake rasulullah ban fake da kowa ba na kirayi sunan Allah mamallaki mai mulkin dukkan halittu marashin mataimaki auwalu akiru zahiru badinu ya madaukaki ka karar dubun basira badan halina baπΉπ.
YUSRAH πΉ MUSA ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY π.
TYPING π² πME KAMAR SARKI ππ EMPIRE DAULA.
ποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈ
π«ANNURI WRITER'S ASSOCIATION π«
ποΈ Home of π€ hospitality and πΉπππ harmony gidan karba hannu biyu da zaman lafiya.
π»βοΈ Yusrah yar Musa jikar Abubakar Muhammad ta kowa ce π ku fito mu warwasa yau zamu shiga duniyar nishadi mu Debi nishadi yadda ya kamataπ§ ga ayu ma yazo taya mu.
17~AR-RAZZAK
The provider
18~AL-FATTAHU
The victory giver
9~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Salihina.
π REMEMBER ND ABSENT MINDEDπ
Episode 17&18
Washe gari tun asuba Baffah vya tashi 'ya'yan sa sukai sallah zasu tafi gona kowa da fartanya a hannun sa suna shirin fita gani su biyu ne yace "ah kai Sabi'u ina Ilyah ba nace ka tashe shiba"? Amsa ya bashi "eh Baffah na tashe shi yaje masallaci sallah tare muka dawo yana d'aki" "au yana d'aki yai shiru? Kai Iliyasu kana ina"? Jin ba'a amsa ba yasa Baffah aje ledar buhun dake hannunsa ya je kofar d'akin su ya d'aga labule cikin mamaki yagan shi kwance idonsa tar cikin nashi.
Da fad'a Baffah yace "dama kana jina ina magana kayi shiru kaifa muke jira zamu tafi gona kaso ka sake sabon kwanciya" banza Ilyah yai kamar da dutse Baffah ke magana ba mutum ba, "dakai fa nake Iliyasu"? Tsaki Ilyah yai yana juyawa Baffah baya yace "bazanje ba ko dole ne"? "Baza kaje ba Ilyasu"? "Eh Baffah haka nace bazan je ba na gaji" "meke damunka Iliyasu yau ni kake cewa baza kaje ba kamar kana magana da abokin ka"? Maimakon ya tashi saiya kuma jan bargo yana rufe jikinsa.
Abu Baffah yaji ya tsirga masa har saida ya dafe saitin Zuciyar shi yana bin Ilyah dake lullu'be cikin bargo da kallo kafin muryarsa a sar'ke yace "Iliyasu ni mahaifin ka yau kake cewa wai baza kaje ba har abin nake yakai haka? Allah ya shirye ba bazan maka baki domin kai d'ana ne bana so ka shiga wani hali amma indai kaci gaba da fand'are min zamu raba hanya dakai".
Baffah na rufe baki yaji ance "to saime dan kun raba hanya dama wani abun arziki kake bashi saidai shi idan ya samu ka ri'ka zizzilla ido kamar 'bera a ragaya kana jiran a baka kullum hannun ka a bud'e kamar ganyen rogo bari kaji maganar gaskiya Iliyasu daga yau ya daina yi maka wahala wadannan din dai suje su karata inma kashe su zakai amma banda d'ana" sosai Baffah ke kallon Ramatu ya ma kasa magana ga juyawa da kansa keyi duhu ya fara gani da sauri ya dafe bango jin zai fad'i ya soma karanto addu'a zuwa wani lokaci daya ji sauki ya kalli sauran yaran nasa yana cewa "Sabi'u kuma ku zauna ku huta yau gobe sai kuje kaji" kai Sabi'u ya girgiza cikin damuwa da jin zafin abinda Ramatu tayi da rashin biyayyar Ilyah ga Baffah yana jin tsoron kada wata Rana a wayi gari sun kashe shi da ba'kin cikin da suke kunsa masa tunda a yanzu ma hawan jini ya kama shi ance ya daina yawan tunani da tuna abinda ya bata masa rai.
Yace "a'a Baffah zamuje nida Habubakar mu karasa noman ka zauna a gida basai kaje ba zamuji da komai" ya fad'a yana rike Baffan ya mayar shi d'aki ya dauki maganin shi ya bashi kafin ya fito suka wuce.
Kwana biyu a tsakani Baffah na zaune a kofar d'akinsa yana rubutun allo yaji sallama yana d'aga kai yayi murmushi saboda ganin wanda ya shigo fuskarsa da fara'a yace "Musbahu sannu da zuwa yanzu kake tafe 'karaso shimfida maza ka zauna kee Salamatu munyi ba'ko kawo masa ruwa" zama Musbahu yai cikin farin cikin zuwansa da ganin Baffah domin rabonsu da juna harya manta gaida shi yayi daidai Salamatu ta aje kofin ruwa a gaban sa ya gaishe da ita amsawa tayi tana tambaya sa "Musbahu mutanen birni ya iyalin suke"? "Wallahi suna lafiya Innah ina Sabi'u habu da Ilyah"? "Ayya suna gona amma kila yanzu zaka sun dawo yau ne ma naga sun danyi jinkiri ko maye ya tsayar dasu"? Ta fad'a tana mikewa ta tafi d'ebo masa abinci daidai fitowar Lami daga d'aki zata fita talle ganin sa yasa ta karaso har kasa ta durkusa ta gaida shi amsawa yai cikin mamaki bayan ta fita ya dubi Baffah dake faman rubutu yace.
"Baffah wai wannan yarinyar naka ce har tayi girma haka? Lallai abun da mamaki gaskiya na dad'e rabona da wajajen nan haka tun batafi shekara biyar ba fa ko Baffah"? Murmushi Baffah yai "eh haka ne Musbahu yanzu kuma shekarar ta sha biyar kaga kai kuma shekara goma kenan baka zo ba" kai Musbahu ya jinjina yana cewa "amma Baffah badan talla al'adarku bace yarinyar nan da kun sata a makaranta ilimi shine gaba da komai" kai Baffah ya girgiza "Musbahu matsalar ba'a ni bane ko yarinyar a uwarta ne bazata barta tayi karatun ba amma da yanzu ta dau wani matsayi ni kaina abun na damu na dashi nake kwana nake tashi balle ita yarinyar duk komai nata da 'kwallafa ranta akan karatu amma har yau burinta bai cika ina ba'kin ciki matsayi na na uba gareta ace na kasa biya mata hakkinta da ina da gurin dazan kai Lami tayi karatu da yanzu na kaita na dauketa daga wannan damuwar".
Shiru Musbahu yayi yana tunani zuwa wani lokaci yace "to Baffah da zaka amince sai na tafi da ita ta zauna a hannun matata tayi karatu rayuwar ta tayi inganci" da sauri Baffah ya d'ago yana kallon Musbahu yace "da gaske zaka rike min ita tayi karatu ta cika burinta"? "Eh Baffah alkawari ne bazan ci amana ba duba da irin zaman arzikin da kukai da mahaifina gashi sai ala'kar ta zama alkairi nima har yanzu ban yada ba"