Showing 123001 words to 126000 words out of 130249 words
ruwa a kasa tasha dan dad'i haka nan akai komai jikin Balarabe a mace kamar mara laka yace a fad'owa Dalah mahaifiyar tace tana da alhakin sani haka Asabe ta hana babu yadda ya iya taya labari ya jewa Dauda a tsegumin gari suna zaune ana tattaunawa sai ganinsa sukai shida Dalah sun shigo gidan zaro ido Asabe tai a ranta tace "to shi kuma wannan yaron uban waye ya fad'a masa har yazo".
"Dawa kikai shawara kike shirin yi mata auren dole saidai kiba da 'yarki Bahijjah domin itace kike da iko a kanta" Dauda ya fad'a yana zaro mata girman idonsa kallon Balarabe Asabe tai wanda ya girgiza kai yana cewa.
"Ahh ya kike kallona? ba nine wanda na gayyatosu ba".
Kai Dalah ta d'aga tana murmushi tace "eh mana babu wanda ya gayyato mu nan".
Sa'kwa'kwa Asabe tai tana kallon ta tace "mene babu wanda ya gayyato ku"?.
"eh a bisa ra'ayin kanmu muka zo".
"Me kenan"?.
"Au ke mekike inace kar'bar auren 'yata kika bararraje kinayi to muma shi mukazo yi saidai kin makara ki sani baki isa ba wallahi lokacin dana d'au cikin ta da wahalhalu baki sani ba na raineta dan haka baki da wani iko a kanta ganin dama tace nace ga wanda zata aura dan haka bari kiji ban amince da wannan za'bin naki ba".
Dariya Asabe tai tana cewa "dama kinji nace ki amince da za'bi na ai na riga na gama magana na basu aurenta nasa rana karshen watan nan maganar na isa ko ina da iko ya wuce aure kuma dole".
Kai Dalah ta jinjina tana cewa "au haba auren Bahijjah zaki ashe to Allah ya bada zaman lafiya idan ankai mana minti zamu zo musha biki mu shari taushe" sannan ta mayar da hankalinta kan Balarabe tana kallon sa shima ita yake kallo zatai magana a bazata taji yace.
"Dalah na dawo dake😲".
Zaro ido Dalah tai tana sake kallonsa da mamaki tace "me kace Balarabe"?.
Da gefen ido Balarabe ya kalli Asabe cikin tsoro da raunin murya yace "na dawo dake d'akin ki kizo kiyi bikin 'yarki da kanki".
A zabure Asabe tace "meee maimaita abinda kace Balarabe dan banji sosai ba ka dawo da ita ina"?.
Dariya Dalah tai tana cewa "ai dama bazaki fahimta ba amma idan kika ganni a cikin gidan na dawo zaki fahimta" maida hankalin ta kan iyayen Iluh tai tana cigaba "ku kuma kunga gaskiya dai ba 'yarta bace zura ku tai a kwalba dan taci kud'inku nice mahaifiyar yarinya bata shawarce niba bansan da wata maganar aure ba asali ma bansan d'anku ba saifa yanzu dana ganshi ni 'yata nayi mata miji dan Allah kuyi ha'kuri fatan ranku bai 'baci ba".
Murmushin ya'ke innar Iluh tai tana kallon Dalah cikin girmamawa tace "ayya karki damu mun fahimce ki wallahi babu komai ai d'a na kowa ne Allah ya bada zaman lafiya yasa gidan zama ne shi kuma Allah ya bashi wata".
Amin Dalah tace tana mayar da hankalinta kan Balarabe tace "to na gode amma kasan nayi iddah fa dole sabon aure za'ai da sadaki na da kayan lefe duk zakai ko kuwa a'a"?.
Kai Balarabe ya d'aga "eh duk zanyi nan da sati zan had'a komai sannan maganar Dauda da Indo d'in ki turo min Malam Balah muyi maganar".
Kai Dalah ta d'aga "to malam nagode Allah ya saka da alkairi ni zan koma ba'ki ku gaida gida Asabe a huta lafiya" tana fad'in haka ta juya suka fita itada Dauda wata ba'kar d'anyar ashar Asabe ta saki tana kallon Balarabe tace.
"Me zan gani haka Balarabe wacce irin asara ce ta sameka ka dawo da Dalah gidan nan naji kana cewa? Tabbb heyyyy jama'a kuzo ku tayani figa uwar kishiya ta zama kaza😲😁 wallahi baka isa ka dawo da itaba ko zaka mutu harda wani li'ke hanci na dawo dake d'akin ki kizo kiyi bikin 'yarki da kanki to kar naji karna gani ka gane? Aikin banza aikin wofi uban meye abinso a jikin Dalah mace kimmm haka babu fasali ku kuma sai ku d'ebi tsummokan ku kuyi gaba tunda wannan matsiyatan suka sani baza ai auren ba" mikewa tai tana shiga d'aki sai bala'i take.
Shiru Balarabe yai ba um ba um um ya rasa abinda ke masa dad'i kallonsa baffan Iluh yai yana cewa "to mun gode da karramawa malam mu zamu koma Allah ya 'kaddara saduwarmu".
Harsun mi'ke Innah tace "amma wani anzari ba gudu dan Allah Malam Balarabe naga ai kamar da akwai wata budurwar a gidan nan bayan ita yarinyar da mukaxo neman auren ta ko za'a bashi itan dan Allah"🙊😳.
TAB INNAH KIN 'DEBO DA ZAFI☕ ANYA ASABE ZATA BAIWA 'DANKI ILUH AUREN BAHIJJAH KUWA???🤔🤔🤔 HHUMM GABA-GABA DAI MUJE ZUWA ME HANKALI YA HAU KURA🐆🐵.
Tun Balarabe baiyi magana ba Asabe ta fito daga d'aki da gudu tana cewa "me kike cewa na baiwa Iluh auren Bahijjah? Dama am fad'a miki daga turu aka kunto ni ko mazan duniya sun kare me Bahijjah zatai da wannan duguzunzumin 'kazamin d'an naki wanda baya wanka balle wanki kalli fa kayan jikinsa da sumar kansa fatarsa har mai'ko take da kirci tsabar daud'a amma tsabar kanki ya kwance kike had'a Bahijjah dashi tabdijan Allah ya suturi bu'kwi inji kishiyar 'konanna tafi 'karfin auren irinsa gaba da baya wallahi kuje can da tsiyarku yaje ya nemi irinsa kucaka ya aura".
Duk su ukun da kallo suka bita banda Balarabe wanda shi dama already yana da tabbacin zatai fin haka ma tsananin mamaki ne ya kama su har suna kallon juna jiki ba 'kwari Innah tace "haba ke kuwa baiwar Allah idan ma bazaki bashi 'yarki ba ai magana mai dad'i ma sadaka ce amma irin wannan cin mutumci haka koba komai ance ka girmama ba'konka ke a ganinki kinyi daidai kena................
Bata karasa ba a tsawace Asabe ta d'aga mata hannu tana cewa "Kee dalla gafara can rufa min baki ke harkin isa nai tsari dake 'karama 'yace nace bazan bayar ba dan haka ku tattara ya naku ya naku ku 'kara gaba domin marabarku babu ita anan sannan bugu da 'kari akanka ne kai Iluh zan ja maka kunne da gargad'i daf da duk wallahi tun garin nan gurin zamanka ne kada tsautsayi yasa naji labari yazo min kayiwa Bahijjah magana saidai hukuma ta rabamu domin ba sa'ar aurenka bace ka gane kaje ka nemi jaka 'karama marar aji irinka ka aura zaku iya tashi ku 'bace min dan na gaji da ganin wad'annan munanan fuskokin naku🙊 aikin banza kawai" tana gama fad'in haka ta sa'bi gyale a kafad'a dan ko aka bata d'ora shiba tai waje tana tsine tsine.
Sukam sak sukai kamar ruwan 'kan'kara ya ji'kesu suna bin hanyar da Asabe ta fita da kallo suna kuma jinjinawa rashin mutunci da daraja d'an Adam irin nata Iluh da jikinsa ke tsuma saboda 'bacin rai dama mafarauci ne mi'kewa yai a fusace yana cewa .
"Innah baffah ku tashi mu tafi na rantse da Allah tayi da d'an halak saina d'au fansa zatasan waye Iluh ba'a ta'ba ni a kwana lafiya nine gagara gasa naci dubu sai ceto ni fasa taro na zama gar'kami wandon 'karfe sanya ka saida dabara harni zatai wa shigo shigo ba zurfi ta d'auka bansan me nake ba hummm wuya ai nan wuya ai can wuya....................🙊tofa Asabe kin d'ebo ruwan dama kanki😣.
Katse shi baffah yai yana mi'kewa yace "kaga! kaga!! Saurara dan Allah yi shiru haka mu tafi wacce kakeyi don ita bata nan muje kawai".
Jikin Iluh na tsuma yace "ni bazanje ko'ina ba saita dawo ta sameni wallahi bazan ha'kura ba wulakancin datai min zan nuna mata tayi karya badai tace 'yarta tafi karfin auren irina ba? Zan bata mamaki saina sata kuka da idanuwanta😭 saita gwammaci mutuwa da rayuw............................
Rufe masa baki baffah yai bai bari ya karasa ba ya kalli Balarabe Wanda da alama ba lallai hankalin sa yana kansu ba yace "to mu zamu koma mun gode sai wata rana" shiru Balarabe yai domin baya tare dasu hankalinsa yana can tunani da mamaki suke kallon sa tabd'ijan gaskiya wannan mutumin da alama wannan matar tana gana masa azaba ji yadda yayi zurfi a tunani har ayi magana kamar haka baiji ba da d'an 'karfi baffah yace.
"Malam Balarabe zamu koma sai wata rana".
A firgice Balarabe yace "na'am me kace"? Ya karasa maganar da 'karfi sosai kamar irin bebe d'in nan yana kallon su murmushi baffah yai yana cewa "nace mun tafi sai wata rana Allah ya kaddara saduwarmu" Amin Balarabe yace yana mi'kewa sukai musabaha da baffah sannan ya fita musu rakiya ganin tsumin Iluh ya riga ya tashi baya cikin hayyacinsa sosai sun sani matukar suka barshi anan akwai matsala ba karama ba domin yakan yi kwana uku bai dawo daidai ba dole suka tafi dashi gida.
Bayan fitar Dalah da Dauda kai tsaye gidan malam Balah suka wuce taje ta sanarwa da yayarta Aliyah duk yadda sukai har komenta da Balarabe ya bukata domin tayi bikin 'yarta da kanta kamar yadda ya ambata.
Sauke numfashi Aliyah tai tana cewa "to nikam bazan hanaki komawa d'akin kiba tunda kina so amma fa gaskiya duk da haka Indo bazata koma wannan gidan ba sai ana gobe d'aurin aurenta zataci gaba da zama anan saboda tsaro kinga dai gashi sharrin da taso 'kulla mata da wannan yaron Iluh d'an garuwa Allah ya ku'butar da ita tunda Indo bata da alhakinta insha Allahu Asabe saita girbi abinda ta shuka zata gani a 'ko'konta babu komai Allah ya tsare gaba" Amin Dalah tace daga haka babu wanda ya sake magana a cikin kowa da abinda yake sa'kawa.
MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD CÊ😘.
See 👀 you tomorrow morning 😝 tanks for ur support I luv u all my fans MUCH APPRECIATED🤗 💋💃💃💓.
TYPING 📲 YUSRAH MUSA ABUBAKAR MUHAMMAD CE 😘.
💖Më kâmâr särkï💖
💫 ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ÃSSÕÇÌÅTÍÔÑ💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya🙅.
ÀÑÑÙRÌ haske💡 le'ka gidan kowa💙 koda ma'kiya na kallon ka ramin kura🐆 sai 'ya'yanta haka muke👌.
WhatsApp no:234 816 098 3083.
DEDICATED TO👇
🌹MR HÂUSÅ ËBÔÔKS📚
📔📕📗📘📙📓📖📕📒📔📙
SHURAIHU USMÁN CÈÔ FÂUNDÉR ÖF TÁSKÃR NÖVÉLS🙅💃.
STORY WRITTEN ND EDITING
YÚSRÃH MÛSÃ ÃBÚBĀKÅR
✍️Mrs ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD cë😘.
Kuzo mu shiga duniyar nishad'i🤣 mu d'ebi nishad'i yadda ya kamata🤩.
Nifa i have no girman kai🙅 if you are fushi dani😠 to wallahi you are just 'batawa kan k lokaci🕦 haka nake bani da haushin kowa🤗😃.
Wannan page din naku ne 'yan uwana fatan alkhairin Allah ya riske ku duk inda kuke.
🏵️Usman Ibrahim Usman
🌺Sulaiman Ibrahim Usman
💮Abubakar Ibrahim Usman
🌸Khalid Ibrahim Usman
🌼Husnah Ibrahim Usman.
Assamu alaikum yan uwana musulmai ina mai helar sanar daku cewa na sake dogon nazari kamar yadda na saba kawo muku had'dd'un littattafai masu aji dasa nishad'i to yauma kamar haka nazo muku da wani kyakkyawan zankad'ed'an littafi mai suna👇
✍️📚 🏘️A GIDAN TALAKA yana nan tafe insha Allahu bayan na kammala wannan cikin yardar ubangiji.
55~AL-WALIYYU
The friend, patron and helper
56~AL-HAMIDU
The all praiseworthy.
27~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Alamina.
🌄NASTY ND DISCONTENT🌄
Episode 55&56
_______Ilyah ne tsaye a kofar d'akin su Hassan ya bud'e murya sai 'kwala musu kira yake yana buga kofar da karfi suna jinsa amma kowa yai kunnen uwar shegu dashi sai gyara kwanciya sukai suna jan barguna jin ya sake bugowa yasa Hassan bankad'e bargon yana tashi ya jan tsaki yana le'kowa ta window🙊 ya kalli Ilyah daketa faman buga kofa yana Kiran sunayen su yace.
"Wai dan Allah baba meye hakan ne kai yanzu da dad'i kana barci aje a dameka da buga kofa shin zakaji dad'i? haba Dan Allah wannan wacce irin rayuwa ce mufa munxo yin hutu neba takurar kaba mutsss" yana gama fad'in haka ya koma yana rufo windon.
Zama Ilyah yai akan kujera yana huci a fusace ba tazo yaji karar abu a kunnen sa kamar irin karar homa a firgice ya zabura yana gocewa daga kan kujerar ji kake timm ya fad'o kasa dariya Hussaini yai yana nuna Ilyah wanda yake baje a kasa yace "tab Hassan fito kaga baba a yadda yake dan Allah a haka dawa yaima kama?.
Da sauri Hassan ya fito yana Kallon Ilyah kafin ya fashe da dariya yana cewa "wallahi Hussaini baba kama yake da wannan mahaukacin nan na wancan 'kauyen kusa damu meye ma sunansa ranar da yazo garin nan naji yara suna fad'a shi kuma yana rawa"?.
Kallon juna sukai suna d'aga kai sama alamar tunani sannan a tare suka ce 'kwalisa😝 wallahi dashi yake kama a haka Hussaini d'auko wayata a d'aki kai masa hoto kodan tunawa kaga gaba saimu nunawa 'ya'yanmu muce ga kakanku lokacin da yake jin kansa🙊" SUBAHANALLAHI🤔😲
Shidai Ilyah bakin ciki ya hanashi tashi sai kallonsu da ido yake yana jin kamar ya zubar da hawaye wai 'ya'yan daya haifa ne suke masa haka? OH HUMYIM BA DAD'I KAI KAYIWA BAFFAH😔😖.
A fusace Bara'atu taxo tana cewa wai ku kuna da hankali kuwa"? Ace baku da abin tozartawa sai uban daya haifeku wai me kuke son mayar da kanku a garin nan ne mahaukata wadanda kansu ya fara kwancewa kome"? Ta karasa maganar tana d'ora yatsarta a gefen kai alamar kwakwalwar su kalau take?.
Kai Hassan ya d'aga yana cewa "Umma rassss muke sai nishad'i ai ba mune muka kayar dashi ba da kansa ya fad'i kawai kinji abinda nai masa" yana rufe baki ya hura mata itama a garin matsawa baya a tsorace sai gata takwash😭 ta fad'i 'kasa dafe kai maimuna tai cikin takaici saidai tari da bai kama taba batai musu ba sunfi kusa harshe da ha'kori dan yanzun tana magana sai su had'a da ita.
Fitowa Nafisa tai daga d'akinsu tana cewa "wai dan Allah yaya Hassan me kuke yi haka? Tun ranar da kuka dawo kun hargitsa mana gida gaskiya bazai yiwa ba idan ku bakwa sonsu ni inason kayana ehe🙄".
Tana rufe baki taji saukar wani zazzafan dundu a bayanta cikin tsawa Hassan yace "dan ubanki me kama da gyare ke kuma ubanwa ya sako dake"? Ya fad'a yana murd'e mata kunne da karfi cike da mugunta Hussaini kuma ya bata ran'kwashi mai zafi aka😳 yana cewa.
"Hassan barni da shegiya mara kunya yau sai naga wanda ya tsaya miki".
Dariya Hassan yai yana cewa "yo Ina wanda suka tsaya matan suma mun zaunar dasu🤥" ya karasa maganar yana sake murd'e mata kunnen.
Kuka Nafisa ta saki jin zasu kasheta shizai cire mata kunne Hussaini kuma zai fasa mata 'ko'kon kai rai 'bace Bara'atu tace "Hassan ka sakarwa yarinyar nan kunne idan wani abu ya sameta wallahi tallahi kaji na rantse ko? Bazan yafe maka ba".
Ta'be baki Hassan yai yana sakin kunnen Nafisa yace "dama ni bance ki yafeni ba ko kinji lokacin dana fad'a? Inada uwar kud'i na nasan yanzu a rayuwa shine maganin wulakanci kuma shi kuka ri'ke kuke tozarta kawun mu Habubakar dan shi talaka ne kuma ni bana neman yafiyar kowanne so'ko'ko a gidan nan🙊" kallon Hussaini yai yana cewa "Hussaini kai kaji nace su yafeni"?.
Kaiya girgiza "a'a inafa naji kaga share umma muje zan nuna maka wani abu domin mu munada aikin yi😲 bama zaman kashe wando kullum bamuda aiki sai zancen 'yarmu zata auri dan birni kwanan nan😞 muje kawai" fita sukai a gidan yayin da Nafisa tahau yi musu Allah ya isa da kukanta ta koma d'aki Salmah dake kallonta tari da bai kama taba batai ba haka nan Bara'atu da Ilyah kowa gurun yai suna bin hanyar fita da kallo cikin takaici ilyah ya goge hawayen daya zubo masa bai iya cewa komai ba ya tashi daga qasan dayake ya koma kan kujera.😔
Ba yadda Balarabe baiyi ba Dalah ta dawo Asabe tai tsayin daka ta hana sai fitina take iri iri dan haka Aliyah ta hana Dalan dawowa tace ta bari sai bayan bikin Indo da Dauda wanda a yanzu haka 'yan kwanaki ne suka rage komai an gama tanada ranar suke jira dan hutun da Indo ta samu a kwanakin ba takura ba tsinuwa da aiyuka ko fargaba tayi 'kiba abinta ta ciko har wasu 'yan kumatuttuka tayi😁😂.
Kamar yadda Iluh ya furta haka ne ya faru bayan ya dawo tun a ranar ya fara zuwa kofar gidan Balarabe ana yo masa sallama da Bahijjah sai kud'i yake kashe mata kamar hauka tun Bahijjah bata kulashi har tazo yanzu ya zama duniya babu wanda taji tana so sama da Iluh hankalin Asabe yai mugun tashi tayi fad'an tayi dukan akan dole sai Bahijjah ta rabu dashi itama taja tunga tayi tsayin daka tace wallahi mutuwa ce zata rabata da Iluh har gurin bokanta Asabe taje akan wannan al'amarin ya bata magunguna tayi dan ta rabusu amma kamar wanda ta sake d'ora musu dan'kon soyayya haka kullum suna manne har shagon da yake kwana take binsa idan yai jinkiri baizo gurin ta da wuri ba daga nan su juyo su dawo kofar gidan Balarabe har kusan raba dare suke suna hira🙊 gari kwa nan ya d'auka ko'ina gulmarsu ake daba-daba mafi yawa saidai sucewa Asabe Allah ya 'kara alhakin Indo ne da Balarabe ya fara binta tun daga yanzu ta fara ganin sakayya ba'a shuka gyad'a dawa ta fito.
Yauma kamar kullum yadda suka saba suna zaune manne gaf da juna wai a hakan hira suke bakajin tashin muryar su Asabe ce ta fito daga cikin gida a fusace ko mayafi babu balle takalmi tana zuwa ta d'auke Bahijjah da mari cikin ba'kin ciki take nuna ta da yatsa muryarta na rawa tace.
"Bahijjah idan na isa dake ki shiga gida kafin naci uban daya kawoki duniya".
Juyawa tai kan Iluh tana cewa "kai kuma tsinanne la'ananne indai ka lalata min 'ya wallahi bazan yarda ba saikayi zaman gidan yari sau nawa zan fad'a maka bakai ba ita tafi karfin auren talaka matsiyaci irinka saboda kai maye ne d'an mayu jikan mayu ka nace sai naga da yadda zaka aureta da 'karfin da kake nunawa dan ko kai uwa yata maye bazan d'au Bahijjah na baka ba domin mahaukacin kare bai cije ni ba ko Bahijjah zata kare rayuwar ta babu aure wallahi tallahi baka isa ka aureta ba kaji na fad'a ma shege matsiyaci mara zuciya ana korarka kana mannewa".
Dariya Iluh yai yana mata kallon mahaukaciya yace "wai da gaske kike ban isa na aure taba tab kan bala'i lallai zaki azumin kaffara