Showing 3001 words to 6000 words out of 130249 words
bata daina share hawaye ba Wanda saida ta sake shan matsa a d'aki A'i tana mata gargadin karta sake ta dawo mata da kwashen abinci.
Da sallama Binta ta shiga d'akin malam Habu Wanda yake kwance akan wata gajiyayyiyar 'yar katifa mai yanayi da tabarma ya rufe ido kamar mai bacci jin sallama yasa shi budewa tare da tashi zaune yai shiru kana ganinsa kasan cewa yana cikin matsananciyar damuwa ko ba'a fad'a maka ba aje kwanon hannunta Binta tai tana zama a gefensa tace "malam ga abinci" ganin yai shiru bai amsa mata ba tace "malam dan Allah kayi hakuri ka daina sa damuwa a ranka kada hawan jini ya kama ka arziki da talauci duka na Allah ba wanda aka haife shi da kud'i kowa a duniya ya samu a duniya zai barshi mai rai baya fidda rai da rabo".
Ganin jiya iyau bai tanka ba yasa tadan dafa kafadar shi tana cewa "malam lafiya"? Sauke ajiyar zuciya yai "eh lafiya Binta kada ki damu kalau nake" cikin tausayawa tace "to amma malam dan Allah ka rage yawan tunanin nan idan jari ne zan baka aron dubu goma ka saro koda mangoro ne kana saidawa" kai ya girgiza "Binta matsalar ba'a ni bane na kasa gane meke damu na kamar me rariyar hannu ko me na ta'ba bazai albarka ba sai kace mai bakin iyaye kuma kinsan wani abu Binta wallahi harna rabu da mahaifana babu ranar da zata fito ta fad'i basu ce Allah yamin albarka ba na d'ago ina matashi nayi tashen kud'i da manya manyan kasuwanci amma lokaci guda kud'i ya narke min a ka ba iya nawa ba harda na mutane dole filayen Dana mallaka da gonaki haka na rika d'agawa ina Saida su dan dole ina biyan mutane kudaden su tun daga wannan lokaci rayuwa ta juya min baya ban kuma samun kwanciyar hankali ba harwa yau Binta" ya karasa maganar yana dafe kanshi dake sara masa.
Goge hawayen fuskarta Binta tai tana cewa "kayi hakuri malam hakan ma jarrabawa ce kayi kokarin ciyewa sai Allah ya maida maka mafi alkairin sa" kai ya jinjina "na gode Binta hakan yasa naji dama dama ki kaimin ruwa bayi zan fito wanka yanzu" mikewa tai tana cewa "to malam kaci abincin kafin nan bari na dafa ma ruwan saboda naji kamar garin da dan sanyi sanyi" ta fad'a tana bud'e labule ta fita ganin Amatu tai zaune a kofar d'akinsu ta zuba tagumi naban tausayin tana kallon guri daya har zatai mata magana kuma saita fasa ta wuce aikin ta tana tausayawa ahlin gidan nan.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE๐
Yusrah Musa Abubakar maman Fatima ilham )(little Zaran aunty)(
To reader's anan zan tsaya insha Allahu sai wanda yake damu ya bamu aron rai zuwa gobe idan naga comment naku shine zai tabbatar min da kuna bina ko a'a sai mu d'ora fata na a koda yaushe ku kasance cikin farin ciki.
Sannan ina son saidawa masoyana cewa Yusrah Musa Abubakar ta kowa ce ga mai bukatar magana dani๐
+234-816-098-3083
Chat with me, be with me at always my lovers, we will me again till we meet.
#โ
OTE
#COMMENTS
#SHARE
#FALLOW.
Ina gaisuwa gareki gudan jini na 'yar uwata Naja'at Musa Abubakar banda tankar ki Allah ya kara hada kan zumuncin mu ya tsare min ke daga dukkan sharrin mutum da aljan Amin ๐.
๐๐ฟManzon Allah s a w๐ฟ๐
Ya mai nasiha ga alumma muso juna mu rike gaskiya amana dan gudun kuna mu raya zuminci hanya ne na aljannah makiyin zumunci baya kusanci ceto ba, azimu domin muntahal mukami a kara hau Dani makurar mukami a karfafa mini a dade ni kaimi na bayayyanar da sirri na zuciya ta sallim ala abban su nana Binta mafi cika da girma a duk halitta ai nuru babullah mafi nagarta dashi halittu suka samu gata, kofar shiga da fita nana Fadima ce rahmar halitta zahra'u arziki ce kai Fadima tsikar jikin jiki ce na mustaphal arabi sannu nana Binta, ya wanda halinsa ne tayar damai rauni d'abi'ar kace taimako ya Nasuruddini a kujerar ka auwalun ne kai marar sani ya Wanda bai ta'ba hanawa masu nema ba, nabiyul huda da kaine aka bud'e kullalle rahmarka ta isarwa wahallalle da makalalle ka sada bayi da Allah zuwanka shalele badon dakai ba ba'a san azumi da zakka ba, ka saita bayi akan hanya ta Islama a koyarwar ka harda ladabin sanya takalma abinci kwa kar aci shi sai ansa hannun dama Bismillah ayi baza'a ci harda shed'an ba.
03~ AL-MALIK
The king
04~ AL-QUDDUS
The holy.
๐จ Think before you do ๐จ
๐๐๐๐
๐๏ธ ''yar Musa jikar Abubakar Muhammad ta kowa ce๐.
Till we meet masoya sai naji comment dinku koda ma ace zanci gaba gobe ngd.
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
Mrs Al'ameen Ahmad ce.
Barkan mu da kwana masoya yan uwa makaranta da marubuta inaiwa kowa da kowa fatan alkairi da samun rahmar ubangiji.
Yusrah Musa Abubakar maman Fatima ilham little Zaran aunty little Zaran Abba.
๐ซANNURI WRITER'S ASSOCIATION ๐ซ HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY GIDAN KARBAR MUTANE HANNU BIYU DA ZAMAN LAFIYA MAI DOREWA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI 'YA'YAN TA.
๐ME KAMAR SARKI ๐
Dedicated to
MR HAUSA EBOOKS๐
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Daga โ๏ธalkamin YUSRAHMS marubuciyar๐
Yarima Abdulmalik
Rayuwa biyu
Safriyyah
Husnah ko Badiyat
'Dan millionaire
Haskena sauban
Dama kece
Kowacce 'kwarya
Mina-umer
Royalty
A gidan talaka
Zuciyar Aliyu and now๐.........
๐๐น๐Me kamar sarki๐๐น๐
2-Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mujahidina.
YUSRAHMS#
๐ SESSION ND REACTION ๐
Episode 03 nd 04
Bayan sallar la'asar rana tayi lis ta tafi faduwa almurun magriba ya fara bayyana malam Habu ya fito daga d'aki zai fita waje da sauri A'i ta tare shi tana cewa "malam kud'i na fa da nake binka gaskiya ka bani nima kwanakin nan na shiga talauci" kallon yadda take jijjiga malam Habu yai kamar wacce ke shirin dambe dashi kafin ya budi baki yace "bani dashi" zai sa kai ya fita ta kuma shan gaban sa "malam gaskiya nifa na gajiya kullum da anyi magana kace baka dashi sai kace kai talauci ya wasa ka tashi ka nema ka'ki nidai bazan iya ci gaba da irin wannan rayuwar ba ehe" "bani hanya A'i" malam Habu ya fad'a cikin tsawa da nuna fushi wanda da sauri ta matsa gefe tsakin takaici yai yana ficewa yayin da A'i ta rakashi da harara tana cewa "haka dai ka iya mutum yai magana aga zafin sa wannan bakin talauci haka wallahi bazan iya ba malam ka dawo ko me za'ai ayi ko hatsin daka noma ne saika warar mun na kud'i na" ta fad'a tana komawa ta zauna.
Malam Habu majalisar zaman su ta manyan gari ya nufa tun daga nesa yake jiyo dariyar su da hayaniya wanda idan da sabo ya saba suna zolayar sa yana karasawa wani tsakatsakin mutum yace "a'a malam alhaji sir Habubakar mai arziki kamar da bakin kwarya kaga na baba mai ruwan nairori taka sannu d'an uwan malam Sabi'u na attajiri Ilyasu kaga d'an Baffah masu hannu da maiko sai kayi" nan kowa ya fara 'babbaka dariyar rainin wayo da mugunta sunsan ba'a malam Tanko yake masa.
Ran malam Habu ya baci amma saiya danne bai nuna ba ya zaune yana basu hannu suka gaisa caraf malam Mudi yace "ai na wuce ta gefen gonar ka dazu naga kuna ta aiki kaida yan matan ka yanzu kai malam Habu tsabar son kud'i maimakon ka dauki yan aiki mutum biyu maza kaje kana wahalar da yayanka gaskiya ba tsari abinda kake ka daina ko hakan ne zaisa kayi arziki"? Nan dariya suka washe da ita cikin bacin rai malam Habu yace "eh kuyi dariyar ku nikam lokacin dariya na ya wuce tunda har mahaifa na suka mutu suna tsine min kuma ban roki yafiyar suba shiyasa naga yanzu arziki har bina yake" ya fad'a yana kawar dakai a fuakace Tanko yace "nasan Dani kake malam Habu bada kowa ba duk gurin nan kowa yasan haka" kallon sa malam Habu yai yana cewa "au abinda ciwo ashe aina dauka baza kaji zafi ba? Kuma ni ai ban fad'i suna ba zarguwa kawai kayi, gara ni ina da arzikin 'ya'ya matan kuma alhamdulillah na godewa Allah yaya mata sun min komai wani kwa bazai iya rikar mace ko daya ba balle har ya samu 'ya'yan kaga babu wanda ya kai shi talauci ko akwai"? Ya karasa maganar yana kallon malam malam Tanko.
A zabure Mudi yace "wannan kuma dani kake malam Habu eh ban rike mace dayan ba amma ai ina da abinda me mata da yawan baida shi kud'i gonaki da yawa da kuma filaye ba abinda wani shege zai fad'a min" kai malam Habu ya jinjina yana cewa "kayi kokari Mudi kuma ka tabbata mai fad'a da cikawa ni kaina naga haka amma saidai duk kud'i na da wadatar da nake dashi bai amfane niba domin kuwa nasan d'ai d'ai ne a majalisar nan wanda bai bina kud'i kuma bazan biya ba naci na lahira haka nake ni haram din ma nemanta nake" duk zaro ido sukai suna bin malam Habu da kallon mamaki kafin Balarabe yace "amma dai malam Habu gaskiya kana da idon akuya uban Isyaku ne fa amma a idon sa kake ci masa mutunci" kai malam Habu ya girgiza bai kalli saitin da Isyaku yake ba saiya kalli idanun Balarabe yana cewa "ka fad'i gaskiya Balarabe idon akuya gare ni, kuma kowa ya shaida haka tunda kwanan baya har kama ni akai zanyi kwartanci da 'yata kaga ina kunya anan"? Dafa kirji Balarabe yai idon sa kamar zai fito waje na mamakin a ina malam Habu yasan wannan maganar bayan a iya gidan sa abin ya faru daga shi sai matarsa sai kuma yarsa ya kashe mata warning karta fad'awa kowa ya akai malam Habu ya San.........
Katse mata tunani malam Habu yai ta hanyar cewa "ko kana tantama ne naga kamar ka shiga shakkun magana ta" dawo da kallon sa Balarabe yai kan malam Habu kafin ya kalli kowa da yake gurin gashi sun subo masa ido alamar neman karin bayani yasa cikin takaici da borin kunya yace "wanne tsinannan ne ya fad'a maka"? Hade rai malam Habu yai yana cewa "kana mamaki ne"? A fusace Balarabe yace "Allah ya kwashewa wanda ya fad'a maka Allah ya tsine masa ya hada shi da masifu iri iri" amin Amin duka guri ya kaure gyara zama malam Habu yai yana cewa "ai Balarabe duk gurin ba wanda bai san haka ba kawai suna boye maka ne suna nuna basu sani ba amma a zahirin gaskiya ta hannun sha'ki'kin ka muka samu labarin" "waye wani sha'ki'ki na"? "Ai bani zaka tambaya ba malam Balarabe ka tambayi yan gurin mana na dai fi tunanin ba ni kadai ne mai ruhi anan ba" mikewa Balarabe yai yana cewa "to duk Wanda ya fad'a ma Allah ya tsine masa albarka ya d'ora masa mugun ba'kin talauci" yana gama fadin haka ya karkade rigarsa yai gaba yana tafe ya na masifa a layi.
Tanko ne yace "gaskiya malam Habu baka kyauta ba dan me zaka ce masa haka kuskure aka samu" wani kallo malam Habu yai masa yasa cewa " ka jira ni kaima ban gama dakai ba akwai tsakin mu da tsakuwa dakai dan wallahi nafi karfin wulakancin kowa a cikin ku" Mudi cikin haushin gorin da malam Habu yai masa dazu yace "ah kafi karfin wulakancin kowa Kam tunda ka samu shiga yayan matarka yana binni shine yake turo maka kud'i shiyasa kakewa kowa kallon hadarin kaji" kai malam Habu ya d'aga "ai hakan ma arziki ne wani ya samu yayan matar tasa ya ri'ka turo masa kamar ni din idan zai iya na isa ne" "ka isa kuma"? Tanko yai maganar cikin 'kulewa malam Habu bai damu da tunzurar da Tanko yai ba yaci gaba "eh na isa ne harna wuce inda ake tunani kuma a gabaki dayan majalisar nan babu wanda ya isa kamo kafa ta arziki badan ruwa da yaiwa babban zakara duka ya dawo d'an tsiyako ba" cikin ba'a Mudi yace "au au ba wani ruwa daya daki babban zakara ka dawo da arzikin naka mana watakila tunkaho da gadara daka fara nuna mana ne Allah ya jarrabe ka da talauci da rariyar hannu ya kwace kudin" "wa ya fad'a maka jahili"? Malam Habu ya tambaye shi yana kallon yadda Mudi ya zuro masa ido "rai bace Mudi yace "ka fad'i komai malam Habu lokacin kane dan banyi karatu ba kake goranta min kaima ba wayon Kane ya baka ba" caraf Sadi dake gefe tun dasu yana son yai magana sai yanzu yace "wai ku dan Allah meyasa kuke haka? Matukar malam Habu yazo gurin nan baza kubar shi ya huta ba waye ne keba da talauci ko arziki?" Ganin sunyi shiru yaci gaba "gaskiya yan majalisar nan ku gyara malam Habu fa ba karamin mutum bane ba abin rainawa bane ya kamata kusa hankalinku guri daya lokacin da yake da abin hannu kullum kuna li'ke dashi kuna yan'kare masa hakori da wayon 'kauye shi kuma ba rowa yana baku kud'i kuna bushasha amma yanzu dan karaya ta same shi kuke masa dariya gaskiya kun zama bulutu masu manta kyautar jiya ku sake tunani".
Tsam Tanko ya tsomo baki "to kai Sadi indai ba munafirci da shishshigi ba meye naka a ciki waye baisan bakin talaucin malam Habu ba saifa ba'ko wanda mota ta sauke amma indai d'an gari ne haifaffan kauyen nan yasan malam Habu fa'kiri ne a fa'kiran ma shine ogon yan rashin wadatuwa da komai" dariya Mudi yai yana cewa "haka nefa Tanko kila yanzu inka latsa shi bashi da biyar tasa rabon da yaga kud'i harya manta saidai ya hango su daga nesa a hannun wani yayi fatar ina ma shine kila biyar tasa bazai kuma mallaka ba" dariya suka bushe da ita harda masu rike ciki wanda malam Habu yaji zafin dariyar amma ya danne kamar bai damu ba yace "ba dani kuke ba da wanda ya jarrabe ni kuke" "waye ya jarrabe ka" Mudi yai maganar yana kuma shekewa da dariya "ban sani ba ๐ " malam Habu yace yana daure fuska.
Sadi dai da baya jin dad'in abinda ke faruwa yace "dan Allah malam Habu kayi hakuri" cikin nuna rashin damuwa malam Habu yace "ba abinda ya bata min rai kasan su ba komai suke ganewa ba" "maye bama ganewa"? Tanko ya fad'a yana dauko sigari akan farantin gaban Mudi zai kunna wuta da sauri malam Habu ya tashi tsaye zai tafi yace "kune abin tausayin amma kun kasa ganewa Allah ya ganar daku" da sauri Tanko da Mudi suka ce "Amin inda gaske kake idan kuma ka fada ne dan ace kai malami ne na Allah Zuciyar ka a wanke take nan kuwa ba'ki 'kirim take aniyarka ta bika" malam Habu dai bai kuma sauraron suba yai gaba domin sun kore shi sakamakon wannan sigari da Tanko ya kunno.
Sadi daya bi malam Habu da kallo harya 'bacewa ganin sa yace "kai jama'a rayuwa a gaskiya ina tausayawa mutumin ace kullum rayuwar ka ba sauyi kome a ta'ba kamar me bakin iyaye saiya narke" tsaki Mudi yai yana cewa "kai dallacan wa ya fad'a maka malam Habu abin tausayi ne? Ai talauci da rariyar hannu yanzu ya fara gani ba ya nace saiya iya rike gidan saba muje zuwa waye mai nasara" cikin mamaki Sadi yace "ban gane meye abinda kake cewa ba kamar akwai abinda ka sani game dashi"? Murmushi Mudi yai mai ma'ana yana sake kure Sadi da kallo yace "karka damu haka malam Habu zai Kare rayuwar sa kamar 'beran masallaci bazai ta'ba samun wadata ba" "wai me kake cewa ne Mudi lafazin ka ya nuna da akwai wani abu da kake shiryawa" dariya Tanko yai yana cewa "malam Sadi karka damu wannan ba shafin ka bane mu tsaya iya haka kada ka sake neman binciken wani abu gare mu" shiru Sadi yai duk hankalinsa bai kwanta ba yace "amma da akwai wani abu da kuke boye min"? Har hada baki sukai wajen cewa "karka damu damu" sauke numfashi Sadi yai yana cewa "to meyasa bakwa so na sani"? A zafafe Mudi yace "to kai munafikin banza me kake so ka sani bayan wanda ka sani"? Sadi bai damu da zagin mudi ba ya kalli Tanko yana cewa "to me kuke boyewa" kafada Tanko ya d'aga "babu abinda muke boyewa kaga abu sa'banin hankali ne a tattare damu"? Kai Sadi ya jinjina yana cewa "kwarai ba abu daya ba da yawa kuke boyewa kuji tsoron Allah idan da hannun ku akan bawan Allahn nan ku kyale shi yaji dad'in rayuwar sa dan Allah" harararsa Tanko yai yana fadin "ka damu da kanka kaima ka kashe wutar dake gabanka kafin kai kokarin kashe ta wani" mikewa Sadi yai yana cewa "indai kune silar durkushewar malam Habu gaskiya kun cika azzalumai makiya a garesa amma ba damuwa akwai Allah zai saka masa" Sadi zaibar wajen caraf Tanko ya rike masa riga yana cewa "to ba kaji sirrin mu ba kada ka fad'awa kowa idan tsautsayi yasa ka fitar da zancen nan zakaga yadda ake wasan tsutsa a rana" cikin takaici Sadi ya fisge daga rikon da Tanko yai masa yana jan tsaki yabar gurin aka barsu iya su kadai sai zu'kar hayaki suke kallo d'aya zakai musu kasan su 'kware a wannan fannin.
Balarabe na zuwa cikin gidan shi ya bankad'a labule yana cewa "munafika ina kike fito yau asirin ya tonu kin gama yawa mitsiyaciya mai farar 'kafar dama zaman hakuri nake dake komai nawa a sace hakan bai ishe kiba harsai kin fad'awa duniya hali na bankadaddiya mai hana zaman lafiya da ke nake mai idon d'inya kina ina ko saina shigo d'akin na cillo waje dake zakifi fahimtar abinda nake fad'a".
Shiru yaji ba'a amsa ba a hargitse yace "Dalah ke Dalah kina jina kikai banza saboda ga d'an iska yazo yana magana ko"? Da sauri Asabe ta fito daga dayan dakin cikin munafirci tace "ayya malami na ango na uban yayana meya faru ne bansanka da fushi ba" Balarabe na jijjiga kamar mace yana huci yace "ina Dalah take"? Dad'i fal ran Asabe tace "ai bata taje anguwa ba" "anguwa uban wa ta tambaya har ta samu damar fita"?