Showing 57001 words to 60000 words out of 130249 words

Chapter 20 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17608

ya barsu da kewarsa.

Kasa basu baki Dr Usman yai sai fita dayai yana sanar da cewa a kira masu motan daukar gawa zuwa kauyen su.

Dama haka rayuwa take yau mune gobe ba mune ba Allah ka bamu cikawa da imani Amin.

Sabi'u ko Habu babu mai karfin gwiwar iya tafiya da 'kafunshi ma balle ya iya wani abu saka Baffah a mota da komai su Dr Lukman ne har lokacin suma basu daina sharar hawaye ba haka suka dauko hanyar kauyen su cikin dagulewar lissafi har kofar gida.

Nan gari ya kaure da salati da koke koke mutane sai tittid'owa suke cikin gida ya cika kofar gida ma har akai masa sutura aka fito waje cikin makara aka sallace shi tare da daukarsa zuwa ma'kabarta.

Hankalin Habu bai sake mugun tashi ba sai lokacin daya d'aga hannu suka fara zubawa Baffah 'kasa wasu zafafan hawaye ne masu tsananin 'kuna suke zuba a idanun sa kansa na juyawa yana ganin duhu da'kyar suka kammala akai masa addu'a suka baro ma'kabartar sun d'an fara tafiya Sabi'u ya farga baiga Habu ba a tare dasu da sauri ya waiga baya can ya gano shi dur'kushe gaban 'kabarin Baffah bai taso ba, da sauri ya koma yana d'ago shi tare da share masa hawayen dake zuba baice komai ba ya ri'ko hannun sa suka fito suna bin bayan sauran mutanen gari har aka dawo kofar gidan tare da shimfida manyan tabarma na zaman kar'bar gaisuwa amma abun mamaki duk abin nan da ake Ilyah kamar bai damu ba haka yake harkokinsa.

A ranar Musbahu da matarsa suka zo suma sunyi kuka sun jinjina mutuwar sun kara saida akai kwana uku suka koma gida yayin da aka bar yan tsirarun mutane wadanda zasu zauna sai anyi bakwai.

Abinda ya baiwa kowa mamaki tun ranar sadakar uku Ramatu ta soma maganar rabon gado da farko kowa yayi tunanin ko mutuwar Baffah ce tasa mata ta'bin kwakwalwa ta zare sai aka barta a haka amma me ranar sadakar bakwai ma Saida tai batun a gaban liman cewa a raba gado tunda yanzu babu Baffah idan ba'a raba kowa yasan matsayin sa ba baza ai zaman lafiya ba dole tasa Saida liman ya amsa mata dan haka ta dameshi zuwanta gidansa uku cikin wata daya da rasuwar Baffah cewa har yanzu taji shiru dan haka yace ta jira zai magana da manyan gari da shedu zasu zo sannan fa ya samu ta 'kyale shi liman kuma akwai abinda yake dubawa musamman 'ya'yansa Sabi'u da Habu yana jin kunyar tararasu daga rasuwar ubansu ko zafin mutuwar bai gama barin jikin su ba a tsiro musu da zancen wani rabon gado.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE๐Ÿ˜˜.

MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY ๐Ÿ’ƒ๐ŸŽถ๐ŸŽต๐ŸŽป.

Sai mun sake had'uwa gobe masoya idan me duka ya kaimu da nisan kwana godiya ๐Ÿ’– nake sosai da nuna kaunarku gareni Allah ya kara barin mu tare Amin.


YUSRAHMS ABUBAKAR TA KOWA CE๐Ÿค—๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน.


TYPING ๐Ÿ“ฒ {Tue, Apr2/24 8:00} ยฅusrah Musa Abubakar.

๐Ÿ’ŽME KAMAR SARKI ๐Ÿ’Ž


Story and written by
โœ๏ธYUSRAH MUSA ABUBAKAR Mrs Al'ameen Ahmad ce.


Wannan page din naku ne iyaye masu girma daraja da kima Allah ya kara tsawon rai da shekaru irin dad'ewar dabino๐Ÿ‘๐ŸŒด.
Maman mu
Maman Huzaif
Umman Basiru
Umman Suraj
Umman Fati
Umman Usman
Maman baby
Maman Fadilah
Maman Maryam
Maman Hafeezah
Maman Feedow
Maman Shamsuddeen.


๐Ÿฅ€ Always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your life always.

13~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Qaiminah.

25~AL-MUDHILL
The giver of dishonour
26~AS-SAMII
The All hearing

๐ŸŒ„BEWITCH ND BADLY๐ŸŒ„
No 25_26.
Yau da gobe a kwana a tashi babu wuya rasuwar Baffah har yayi wata uku gashi abubuwan kadarorin Baffah da yawa an rasa su wai sun 'bata harda dabbobi da kud'ad'e.

Haka lokaci yaja rayuwa tana ta tafiya har Baffah yakai wata takwas da rasuwa sannan tabi jiki Ramatu ta tada 'kayar baya sai an raba gado kowa yasan matsayin sa a baiwa kowa hakkin sa yaci gashin kansa ba iya ahlin gidan ba hatta na waje da sukaji wannan maganar saida sukai tirrrr da Ramatu domin ta nuna 'kiri 'kiri gado ne damuwarta hartayi wa manyan gari maganar azo a raba kowa ya kama gaban sa.

Jin haka yasa Salamatu samunta tace "Ramatu naji kina maganar a raba gado a bawa kowa kason sa ko"? "Eh haka nace nan da gobe kowa zai san matsayin sa" kai Salamatu ta jinjina taci gaba "ina fata kinsan cewa gonaki biyun nan da malam yake nomawa na d'ana Sabi'u ne ko? Domin a gaban ki a gaba na da Hauwa duk muna gurin tare da yaran ya tara mu yace kada muji ance ya sayi gona ba tasa bace ta Sabi'u ce kar bai fad'a ba tarai ta kasance a samu sa'bani yace lokacin da aka kai su Sabi'u makaranta yake baiwa malaminsu ajiyar kud'i shi kuma dayaga kud'in ya taru da yawa da Baffah yaje saiyai masa bayani ya bashi yace ko gona ce ya saya masa kafin ya d'ago yai hankali.......................


Katse ta Ramatu tai "saurara da Allah Salamatu na gaji da wannan dogon bayanin naki aina sani nace ko" mi'kewa Salamatu tai tana cewa "a'a ba maganar kin sani bane sake tuna miki nai kada abu yazo ya cakud'e" tana gama fadin haka tai waje da harara Ramatu ta rakata daidai Ilyah zai shigo d'akin ganin Salamatu na shirin fitowa bai matsa mata ba itace tai 'ko'karin bashi hanya tare da matsawa gefe amma duk da haka Ilyah saida ya bangaje ta ya wuce mamakin tsaurin idonsa Salamatu tai saidai wannan mafari ne kadan ne daga cikin halayensa marasa tsari daya koya daga Ramatu wanda bazai kaishi ko'ina ba.

Yana shiga d'akin yaga Ramatu sai kaiwa da komowa take ganinsa yasa har tana 'kwarewa tace "yauwa Ilyah dama kai nake nema muna cikin bala'i mun shiga uku yau ranar tonon asiri tazo dole mu tashi tsaye mu kauda matsiyaciyar tsohuwar nan".

Zama Ilyah yai yana cewa "su waye meya faru"? Ramatu na huci kamar wacce tai gudu tace "Salamatu man yanzu baku had'u da ita ba tazo tayi so'ko'ko aka wai tana tuna min cewa manyan gonaki biyun da malam yake nomawa na d'anta Sabi'u ne taji ina zancen rabon gado kar nace za'a raba harda su" "to sai me dan ma yana da gonaki da yawa nasan da an raba mana zan zama me arziki ki had'a min da tumuninki na fara kasuwanci shiga da fitar kaya ina sayar da manyan hajoji masu tsada" washe baki Ramatu tai "kuma fa haka ne kaima ka iya kawo shawara yanzu dai shikenan bari a raba gadon muga iya kason mu na rantse da Allah Salamatu bata bina bashin rantsuwa idan ta kuma 'bata min rai akan maganar gonakin nan sai na shafe tarihin ta saidai ayi ba ita".

Ilyah dai na kallon Ramatu sai surfa bala'i take tana bushewa bai saike tanka mata ba ya tashi ya fice a kofar gida yaga Sabi'u da Habu sun shimfida tabarma suna zaune gabansu kwanuka tsaki yai baiko kallesu ba yazo zai wuce Sabi'u ya dakatar dashi "Ilyah tun dazu fa kai muke jira abincin har yayi sanyi bakazo ba" wata irin ba'kar harara Ilyah ya sakar masa yana cewa "dawa zakuci abincin? Amma dai bada niba na wuce ajin cin abinci da irinku" gaba yai bai saurari Sabi'u dake faman masa magana ba Habu da ransa ya gama 'baci yace "dan Allah yaya Sabi'u kaima ka 'kyale shi ai Allah ya gani mun fita hakkinsa duk wanda ya zagemu mun barshi da fitowar rana da fad'uwarta shiru Sabi'u yai cikin damuwa yace "ni bana so ne ace kanmu ba'a hade yake ba mutane a gari zasuga kamar mun ware shine amma babu komai muci kawai" sun kasance sun matukar damuwa da rashin d'a'ar da ilya yake nunawa saida ya zasuyi babu yadda suka iya.

Kamar yadda Ramatu ta bukata haka tai tsayin daka saida aka raba gadon nan kowa ya san matsayin sa nan da nan suka fara kasuwanci kamar abun gasa kudade suka fara shigowa wadata ta samu amma Sabi'u duk ya fisu samun bud'i da Ramatu ta bud'e ido taga Ilyah bai tara na kansa nan hassada ta shiga zuciyar ta da ba'kin ciki ta kasa zaune ta kasa tsaye afujajan taje gurin 'kawarta neman shawara ta kuwa samu ta kaita gurin boka wai ya baiwa Ilyah sa'a da kasuwa a sawa wadancan bakin 'kyalle da farko aikin yaci sosai daga baya yazo ya karye sun koma basuyi sa'a ba dan boka ya tashi daga dajin kuma basu san inda ya koma ba.

Hankali tashe ta samu ilyah "kai Ilyasu nifa ban gane ba anyi gabas da kare wai meya haka ne kwanan baya naga kasuwanci wada wada amma yanzu kace a sati baka rike dubu goma taka? Gaskiya ne Salamatu kwai muguwar mace wai asiri tai maka ko Sabi'u gashi nan har ya sayo shanu ya had'a amalanke amma kai ko kaza baka saya ba gashi tun daga zancen auren sa da Rakiya yar gidan na'ibi har anyi auren harda 'ya'ya biyu me kake kallo Habu ma daka girmeshi gashi nan da yake shi kasuwancin yana kai masa lokaci guda ya auro mata biyu Saude da Binta gashi shima a gidansa an samu 'karuwa Sauden ta haihu mace ansa sunan kakarku Asma'u naji Sadi ma abokinsa yayi kai kuma saboda mutuwar zuciya tun daga Bara'atu shekara kusa uku bata haihu ba kuma baka kara wani auren ba banji kace komai ba ina naka zancen da Maimuna ya kwana"? Ta'be baki Ilyah yai "yana nan man jira nake na karasa gini na kema na fitar dake daga wannan gidan ki koma guna" zaro ido tai cikin murna tace "Allah kace kwanan nan zamu fara shan romo" "umh zaki sha kam dan bijimi zan ri'ka yanka mana" rasa inda zata sa kanta Ramatu tai saboda jin dad'in abinda Ilyah yace har haskowa take tayi dumu dumu cikin mai'ko๐Ÿ˜‚.

Tace "yauwa d'an albarka kace yanzu zamuyi rayuwa me yanci da muna zaune a bushe a 'kai'kashe kamar kilishi kullum murna nake fata nake ina jiran wannan lokaci na bayan ran malam domin samu dukiyar gado dan haka maza ka shirya yanzun nan akwai wani guri da nake son muje idan mun samu abinda muke so matsalar mu ta zamo she'kak'kiya".

"Ina ne wanne wurin ne me zamuyo"?.

Ramatu na kokarin daukar gyale tace "kai dai tazo man ka gani ko bayan raina ka rike wannan ka huta yace sai dare ya raba zamuje yana cikin daji" "daji kuma amma mutumin arziki ne zaiyi rayuwa a daji"? "Yo Ilyah taya dama wanda yasan me yake zai bar zaman cikin jama'a ya koma daji boka ne fa".

"Boka kuma amma me ye had'i na da boka mezai bani"?.

"Me zai baka kake tambaya? Tab lallai Ilyah bansan asirin da sukai maka ka lalace haka ba har boka kake cewa wai me zai baka"? Zama Ilyah yayi yana jan wani kwano dake rufe ya bud'e ganin shinkafa yasa ya fara ci wani kallo Ramatu ta masa tana cewa "yau nake ganin sakarai sauna Iliyasu anya Habu da Sabi'u basu je gurin yan bori sun kashe maka zuciya ba gaskiya bazan yarda ba saina je gurin boka na naji komai" Ilyah bai sake ce mata 'kala ba haushi ne ya kama Ramatu ta soma balbale shi da masifa amma yai banza Saida ya gama ya mike yana kallon ta yace "karki damu nan da sati biyu zaki bud'e ido kiga surukar ki nima biyun zan aura Bara'atu da Maimuna domin ina matukar kishi da habu har bansan yadda zan kwatanta miki ba" cikin farin ciki Ramatu tace "yauwa d'an albarka haka nake son ji sai yanzu naji zuciya ta tayi sanyi na fasa zuwa gurin bokan yau sai wani lokacin" Ilyah na shirin fita yace "in an jima zansa a kawo miki nama" zaro ido Ramatu tai baki washe tace "kai kai kai kace yau zanyi bacci da mafarki ina jiranka dan albarka" sa kai Ilyah yai ya fita a gidan yayin da yabar Ramatu sai rawa take a d'aki tana shewa.

Alpha tunda ya fara jinyar rasuwar Lami ake fama dashi lafiya ta'ki samuwa saidai yanzun ba kamar da ba ya samu sauki jikinsa ya warware amma har lokacin nutsuwar sa bata dawo ba saidai da sauki tunda yana magana zaune yake a parlon gidan su Naja'atu wanda yanzu zuwa gurin ta na d'ebo masa kewa tsawon lokaci baiyi magana ba dan Naja'atu har ta fidda rai da zaice wani abu sai kuma taji yace.

"Naja'atu wai dan Allah da gaske shikenan Lami ta rasu bazan sake ganin taba har abada taya zan manta da ita"? Sauke ajiyar zuciya Naja'atu tayi tare da dan rufe ido tana tuno rayuwar da sukai a baya cikin son boye hawayen ta tace "Alpha kayi hakuri dan Allah tabbas Lami ta rasu bata duniya ta tafi ta barmu da kewarta babu yadda muka iya sai addu'a abinda ya rage tsakanin mu da ita bansan ta yadda zan fara kwatanta maka yadda na damu da Lami da halin dana shiga a kanta ba Alpha na sani kana tsananin son ta nice mutum ta farko dazan bada sheda akan haka dan Allah kayi hakuri ka dauka rayuwar da kukai a baya kamar mafarki ne" kai Alpha ya jinjina "lallai kowanne lokaci da irin nasa salon dole ya nemi taimako dan tunanin ta na gaf da rusa masa rayuwa Zuciyar sa ta kusa bugawa kallon Naja'atu yai kafin ya mi'ke yana cewa "shikenan Najat na gode zan tafi ki gaida min mama" mi'kewa Najat tayi suna fita tare tayi masa rakiya ya tafi bayan rasuwar Lami tana so ta fad'a masa tana son sa ta kasa kawai tana matukar tausaya masa ne daga haka abu ya zarce kullum idan suna waya tana shawarar fad'a masa ta kasa balle su had'u face to face saidai tana adda'ar Allah yasa shima yaji wani abu a kanta.

Zaune Balarabe yana shan fura yake gefensa Dalah tana tankad'en garin masara d'agowa yayi yana cewa "nikam ina Indo ne har yanzu ban ganta ba tunda na shigo gidan nan"? 'Dan murmushi Dalah tayi tana cewa "ai tun d'azu ta fita nidai tace min gurin Adama zataje kuma ban sani ba ko ta biyo ta wani gun" kallon ta Balarabe yai "amma me nace miki bance ki daina barinta tana fita koda yaushe saboda ina ji da ita bani da wata 'yar ita kadai ce jini na gashi ba wani girma tai ba ina tsoron kada wadannan yan iskan da suke lalata yara cin zalin nasu ya biyo ta kaina" sauke ajiyar zuciya Dalah tayi daidai ta mi'ke zata je gaban murhu tace "insha Allahu malam babu abinda zai same ta" shiru Balarabe yai hankalin sa jin bai kwanta ba mi'kewa yai yana cewa "bari na bi bayanta gaskiya na taho da 'yata" yana fadin haka yai waje da kallo Dalah ta bishi cikin jin dad'in nuna kulawarsa ga 'yar tasu guda tal kamar rai da yake.

Lokacin da yaje gidan Adama tace masa ta bar gidan tun d'azu nan fa yaji ya susuce da sauri cikin azama ya juyo yana kalle kallen inda zai ganta can ya hangota tana cikin yaran anguwa suna wasa karasawa yai yana cewa "Indo na me kike yi anan zo mu tafi gida" d'agowa Indo tayi ganin ubanta yasa da gudu ta mi'ke tana zuwa ta d'afe shi tana cewa "baba" daukarta Balarabe yayi yana cewa "me kika zo yi nan"? Tana washe baki tace "wasa" "wasan kuma har nan? Indo na muje gida kinji" to tace tana rike hannunsa yana tafe tana masa zance suka zo wucewa ta gefen wata mace dake zaune tana sakin 'kosai a wani kofar gida kana ganinta kaga 'yar duniya dan hatta bakinta yayi bakin busa haya'ki taje tayi rayuwa a gurare daban daban tasan harka har ta had'u da wani mutum alhaji me kud'i ya aureta ta haifi yarinyar gud'a d'aya Bahijjah kamar gaske suna zama cikin lumana rana daya ta aika shi lahira ta washe dukiyarsa tayo awon gaba da ita da yake ta haram ce tuni tasa tagaba ta 'kurmushe kamar yadda wuta ke cin audiga ta wajen inda take sana'arta Balarabe ya biyo daidai zai wuce cikin shishshigi ta d'ebi 'kosan a leda tana cewa.

" 'yan mata ga kosai".

"A'a ta gode kibar kayan ki" Balarabe ya fad'a batare daya kalli inda take ba kara matsowa tai tana cewa "haba kai kuwa ba kyau maida hannun kyauta baya dan Allah ka bari ta kar'ba" dakatawa Balarabe yai cikin jin haushin ta da sauri ta mi'kewa Indo ledar tana cewa "ki gaida mamanki" to Indo tace kafin ta sake magana fuuu Balarabe ya bar gurin da kallo ta bishi tana cewa wacce ke zaune kusa da ita.

"Ke Meroh kinsan wannan mutumin? A ina yake"?.

Dariya Meroh tayi tana gyara daurin kwalin kanta ta soke shi a gaban goshi tana cewa "meya faru kike tambaya"?.

Daidai Balarabe yasha kwana ya 'bacewa ganin ta tace "ba komai kawai kallo d'aya nayi masa naji ina son sa" zaro ido waje Meroh tayi "kai 'kawata kin d'ebo da zafi kinsan waye wannan har kikace kina son shi bazai ta'ba aurenki ba".

Jiki a sanyaye tace "meyasa kika ce haka"?.

Kai Meroh ta rausaya "saboda ba mata a gaban sa matar sa daya ce kamar rai sunanta Dalah yana matukar kaunar ta ita da wannan yarinyar da kika gani a hannunsa dan haka gara tun wuri ki saukewa kanki wahala".

Kai ta girgiza tana sake kallon hanyar daya bi tace "Meroh bazan iya ba ina son sa kuma dole saina aure shi ta dad'i kota akasin haka da yardarsa koda 'kinsa da amincewar sa ko da karfin hatsi nidai saina aure shi Meroh kiban shawara tun bayan rasuwar baban Bahijjah ban kara ganin Wanda ya kwanta min a rai ba sai shi yanzu ya zanyi"?.

Ta'be baki Meroh tayi "ya zakiyi kuwa Asabe bayan hakuri kece 'bakuwar zaman garin nan amma mu da bamuje ko'ina ba munsan waye balarabe ba mutum ne mai wargi ba baya daukar raini ki taka a sannu".

Shiru Asabe tai na d'an lokaci tana tunani kafin ta d'ago tana kallon Meroh tace "to amma kawata babu wata hanya da zanbi ya soni ko mu 'kulla mu'amala daga nan na samu kusanci dashi"?.

Zaro ido Meroh tai "ki samu kusanci da wa"? Lallai kam

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login