Showing 63001 words to 66000 words out of 130249 words
korarki kina mannewa saboda kinga kud'i ke kuma kandiya ya rage naki kiwa yarki fad'a ta rabu min da d'a idan ba haka ba sai munyi 'batacciya daku wallahi" tana fadin haka tai waje da ta'baryar ta a hannu kamar sabuwar kamu.
Mamaki ne ya kama kandiya tana kallon Bara'atu dake kuka tace "wai meya hada kune harda biyoki da ta'barya kuma"?.
Share hawaye Bara'atu tai tana cewa "babah kinsan halin matar nan ko ba'a fad'a miki dama da ya akai auren balle nayi shekara uku ban haihu ba akan haka tana goranta min da tsine min tace Ilyah ya karo aure wai ya auri Maimunan gidan san 'kira yar gidan malam Sa'idu to yau kuma sai ya shigo da kifi nasa a abinci ta kwace kifin ita kadai hakan bai isa ta zage ni ta hana na karasa dafa abincin ta goranta min sannan tace wai kina kaimin rubutu ina dafa musu abinci dashi ana haka Lawisa taje kawai dan taji muna zance shine tace wai kin aika a kar'bo miki abinci dan haka ta gaji sakin uwar miji ma saki ne naje ta sakeni".
Dafe kirji kandiya tai "kai jama'a mun shiga uku kinji wata masifar ko? Ni dama tun farko shiyasa ban goyi bayan auren nan naki da Ilyasu ba saboda nasan halin Ramatu koba dad'e koba jima sai wani tashin hankali ya shigo dacan ma maye balle yanzu kun dawo zama gida daya ni gara da haka ta faru ma ya sake ki yafi alkairi da wannan zaman damuwar da kike da mahaifiyarsa mu ri'ke talaucin mu bazaisa ki rasa wani mijin auren ba".
Tsaki Lawisa tai tana cewa "kinsan Allah innarmu da ace nice nake auren Ilyah wallahi Ramatu bata isa min haka ba koda taga Barah ba magana ce ta dameta ba da ace nice hummm da an d'ebi yan kallo".
Harararta kandiya tai "ke da Allah rufawa mutane baki sakarya kawai idan da ked'in cema me zaki iya yi wallahi a tsiwar ki yadda Ramatu bata da mutunci da yanzu ta dad'e da karya miki 'kafa tana daidai da zamaninki".
Ta'be baki Lawisa tai tana shigewa d'aki a ranta tana jin da fa ace itace bazata dauka d'in ba kamar yadda ta fada, kallon Bara'atu kandiya tai tana cewa "kinga Barah kiyi hakuri kinji shiga d'aki Allah yasa haka ne mafificin alkairi" Amin Bara'atu tace tana bin bayan Lawisa yayin da Kandiya tai zaman dirshan cikin jimami da damuwar tsiya da suka gayyatowa kansu na auren Bara'atun da Ilyah.
Har dare Ilyah bai dawo gida ba dan haka baisan me ake ba Ramatu kuwa tabarma ta dauko tana zama a waje ta kasa ta tsare tana jiran shigowar sa amma shiru har ta fara gyangyad'i sai dare sosai haka taji tafiyarsa da sauri ta bud'e ido ganin ya nufi kofar shiga d'aki tace.
"Ilyasu me zakai anan dama jiranka nake gidan uban wa ka tafi kayi dare haka baka dawo ba"?.
'Dan juyowa yai yana kallonta zuwa wani lokaci ya shige d'akin batare daya bata amsa ba dariya tai tana sake mi'ke 'kafa tace "zanji me zaka ce na karasa sauke ma damin bala'in dana dauko".
Wuf ta ganshi a kanta kamar wanda aka jefo shi cikin alamun tambaya yace "ina Bara'atu taje"?.
Wata uwar harara Ramatu ta zafga masa tana cewa "sannu ubana to matse ni saina fad'a maka inace duka na kazo yi dan irin wannan 'kerere da kayi a kaina duka kawai nake jira".
'Kara hade rai yai jin abinda tace shifa uwarsa ce amma harga Allah ta fara isar sa lamarin ta ya gama cika masa ciki...............
"Dan ubanka me kake kallo tunanin wa kake amma dai ba wannan tsinanniyar 'kai'kasashshiyar matar taka ba?.
"Wai dan Allah baba me kike yi haka ne"? Ilyah yai maganar ransa a mugun 'bace cikin fad'a Ramatu tace "dambun ubanka nake yi haka, wato dama akan shegiya matarka bankad'add'iya zaka gaya min magana? A lallai Ilyasu wuyanka ya isa yanka".
Takaici ne ya cika Ilyah shi ya rasa gane kan Ramatu kodai ta fara samu zarewa ne bai sani ba dan yaga abun nata yana neman wuce gona da iri amma bari ya bita a sannu tsuntsu me wayo ta wuya ake kamashi zama yai yana cewa "kiyi hakuri nifa dama ba akan wani abu na tambaye kiba mubar maganar d'azu bayan na fita alhaji Munniru yai Kira na akan zai sayar da wata gonar sa kozan saya saidai kafin mu gama ciniki kawai shegen nan Habubakar yaxo ya sayeta da filin kusa da gidan Buba haka mafa kwanan baya gidan me doki wanda ya rasu 'ya'yansa da suka d'aga zasu sayar shine ya saye ga gonar wajen gabar inda yake noman shinkafa kiga girman ta duk shekara saiya d'inke kusan buhu d'ari a bai samu da yawa ba ya samu buhu saba'in ko tanin komai aka d'aga a garin nan za'a sayar shi zai saya na rasa a ina yake samun kud'in sai kace me kud'in ganye ko matsafi kuma fa akwai haihuwa a gabansa amma tsabar had'ama alhaji Munniru ya kara masa kud'i shima da yake mitsiyaci ne ya sayar masa".
Zaro ido Ramatu tai tana cewa "kace da haihuwa a gabansa waye me ciki Saude ko Binta"?.
"Eh Binta ce harya tsufa kuma kwanan nan zai sake auren A'in gidan su me guga har ankai ro'kon arziki".
Dafe 'kirji Ramatu tai "au kuma shine tsabar hassada Salamatu bata zo ta gayyace niba aiko wallahi zan rama har ayi bikinka da Maimuna bazasu sani ba mitsiyatan mutane kawai duk sun asirceka ka'ki abun arziki amma na samo hanyar tarwatsa su kada ka damu Ilyah Bara'atu tayi gida nice na saketa domin bata haihuwa gara ka kara aure".
Kai ya d'aga cikin so kwantar mata da hankali yace "shikenan zan kara amma dan Allah ki bari na dawo da ita nifa ina son mata ta".
Shiru Ramatu tai tana kallon sa kamar me tunani zuwa wani lokaci tace "to shikenan ka dawo da ita amma ba yauba ba gobeba ba jibi ba sai an gama komai na maganar aurenka da Maimuna an tsayar da rana tukuna idan ma zan yarda ka dawo da itan kenan".
"A'a zaki yarda man na fad'a miki nifa ina son mata ta" hararar sa tai "sannu d'an masoya na gama magana matukar kana son sake bud'e ido kaga barakatu ko Bara'atu sunan nata? Indai kana son sake ganin ta matsayin matarka tofa saika kara aure".
Mi'kewa yai yana cewa "to shikenan zan 'kara saida safe" Ramatu data bishi da kallo tace "kowa ya kwana lafiya shi yaso๐" a'a kai jama'a wannan wacce irin uwace shidai tari da bai kama shiba bai sake yi ya shige d'aki.
Zunbur Ramatu ta mike tare da dauko maganin data kar'bo d'azu ta dauki bokiti da ruwa da sand'a tai waje tana yin hanyar daji ga ihun karnuka ya cika gari domin dare ya yi sosai yadda aka bata umarni haka ta aikata haka ta fara zuba magani cikin ruwan bokitin tayi wanka dashi kafin ta dauki gatarin da aka bata ta soma sara tana kiran Salamatu bayan ta tona tasa maganin ta rufe sannan ta dawo gida a bayan d'akinta nan ma tayi kamar yadda tai a dajin sai waige waige take kada Ilyah ya fito ta shiga uku tana gama tai wuf a guje ta fad'a d'aki tana gumi tare dayin dariya tace "haba malam sai yanzu naji daidai hankali na ya kwanta da wani ya kamani bansan me zai faru ba bari na kwanta mu jira wayewar gari muji me zai samu Salamatu"โน๏ธ๐ง ta karasa maganar tana kwanciya akan katifarta da Ilyah ya sayo mata.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE ๐
Maman little Zaran aunty sai Allah ya kaimu gobe da nisan kwana๐ฃ da rahmarsa garemu ina yiwa kowa da kowa fatan alkairi.
Yau typing d'in ba yawa sai hakuri.
๐จ GARGA'DI DA TUNATARWA๐จ
Ban yarda a juyi ko kwafin wani bangare daga cikin wannan littafin nawa ba domin hakki na ne mallaka ta da gumi na basira ta na 'kir'kira na rubuta kada mutum ya min satar koda kalma daya ce idan kuma ba haka ba mutum zaiga sakamako kada ace na yanke hukunci ba sanarwa shiyasa na fad'a sai a kiyaye idan kunne ๐๐ yaji?.....................๐ ๐ก.
๐'YAR MUSA JIKAR ABUBAKAR MUHAMMAD TA KOWA CE๐.
Nayi kewar ku kwana biyu yan uwa fatan kuna lafiya ku fito mu warwasa zamu shiga duniyar nishad'i๐คฃ๐๐
.
Bani da haushin kowa nifa i haven't girman kai if you are fushi dani to wallahi you are just 'batawa kan k lokaci ๐๐ค.
TYPING ๐ฒ {WEND 13/24 8:10AM}๐๐๐๐๐๐๐๐๐
๐Me kamar sarki ๐
๐ซAnnuri writer's association ๐ซ home of hospitality and harmony gidan karba hannu biyu da zaman lafiya.
Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty mai tambarin YMA dutse Jigawa new world new life and new style ๐. sabuwar duniya kuzo ku kallo dad'i yana Jigawa ๐ ga garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.
29~AL-ADAL
The utterly just
30~AL-LATIF
The Gentle
15~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mustagfirina.
๐ฆ๐๏ธYUSRAHMS ABUBAKAR
๐ฆyusrahmusa65@gmail.com.
๐ UNCARING ND TRAGEDY๐
Episode 29_30
Juyi Salamatu tayi cikin barci taji murya ana kiranta a firgice ta bud'e idonta ganin wani 'katon ba'kin abu tai a samanta yana yawo gashi bata ga alamar d'akin da take ciki a kwance ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda take maimaitawa 'kara matsowa abun yake taga yayi wani juyi wurrr ya rufo kanta da sauri ta tashi a guje ya sauka akan gadon sai kuma ya 'bace jitai kanta yana juyawa lokaci guda taji hajijiya na dibanta ko ganin gabanta batai ta kama hanyar fita daga gidan babu ko d'an kwali akanta.
Daidai Rakiya matar Sabi'u ta fito da buta a hannunta ganin inuwar mutum yana tafiya yasa a tsorace taja da baya tana cewa "a'uzubillahi minal shaidanur rajim" jikinta na 'bari ta haska da fitila cikin salati ganin wacce take shirin fita yasa tace "Babah ina zakije a wannan tsohon dare kanki fa ko d'an kwali babu"?.
Ganin tayi banza da ita yasa da sauri ta koma d'aki tana taso Sabi'u a gigice ya fito bai tsaya sa takalmi ba aguje ya fita waje can ya hango tayi nisa sai tafiya take ga karnuka na mata haushi cikin azama yaje yasha gabanta yana haki yace "Babah ina zakije"? Bata bashi amsa ba kuma bata kalleshi ba ganin haka yasa ya sake cewa "meya sameki ne ko baki da lafiya"?.
Namma shiru tayi masa kanta kuma yana kallon 'kasa ta'ki d'agowa mamaki ne ya kama shi sosai har ya kasa ce mata wani abu sai hannunta daya ri'ke yana janta don ya mayarta gida amma sai yaji ta tirje kamar yaja irin kafaffiyar bishiyar nan juyowa yai yana kallon ta tare da zaro ido waje jin 'karfi a jikinta kamar doki zaiyi magana kawai yaji ta kwashe da wata iriyar dariya da sauri ya saketa yana ja da baya dariya take sosai kamar zararriya d'ifff kuma yaji tayi shiru tare da dafe kanta ta kurma ihu tana yanke jiki ta fad'i 'kasa, da gudu Sabi'u yazo yana durkusawa a gabanta girgiza ta ya soma yi amma shiru mi'kewa yai cikin jarumta ya d'agata yana sa'bata a kafad'a yai gida da ita saida ya kaita har daki ya kwantar kafin ya fito yana mamakin ina Rakiya tayi ne nasu d'akin ya shiga can ya hangota saman gado ta lullu'ba sai kakkarwa take karasawa yai yana janye bargon yace.
"Rakiya meya sameki, baki da lafiya ne"?.
Jin muryar sa yasa ta bud'e ido tana cewa "a'a ina lafiya ihu naji da dariya daidai nasa hijab na fita zanbi bayanka shine tsoro ya kama ni na dawo gida ina Baban take ka ganta"?.
"Eh tana d'aki jira nake gari ya waye muje asibiti ni abun ne da tsoro kamar ciwon hauka ne ya kamata saboda ganin abunda takeyi itace fa me wannan ihun da dariyar kamar zata fasa gari" zaro ido Rakiya tai "itace kuma innalillahi wayyo Allah na meya samu Babah ne ban ta'ba ganin irin haka ba".
Zama yai yana sauke ajiyar zuciya yace "ni kaina Rakiya ban ta'ba gani ba sai yau Allah yasa dai ba aljanu ta had'u dasu ba" Amin Rakiya tace tana tashi zaune daga tashi tai tana le'ko kofar d'akin da Salamatu take ciki tana cewa "nifa ina jin tsoron karta 'kara fitowa bamu sani ba tayi waje ka taso muje gurin ta gara mu tsaya zuwa wayewar gari a gurin ta" mi'kewa yai yana cewa "shikenan muje" fita sukai suna shiga d'akinta a 'kan'kame suka sameta ta 'ka'k'kafe idanuwanta sun juye babu ko d'igon ba'ki sai fari tana wata irin jijjiga abin tsoro.
Rakiya dake kan gaba da sauri ta koma baya tana salati jikinta na rawa ganin abinda yafi 'karfin ta kuka ta kama cikin tashin hankali tana cewa "ta ya zamu bari sai gobe baban hajiya gaskiya musan yadda zamuyi a daren nan kalli fa abinda takeyi sai nad'ewa guri d'aya take kamar taya dan Allah kayi wani abu".
"To mezanyi wanda ya wuce addu'a ina zamuje dare ya riga ya raba mu ba asibiti ne damu a gari ba saidai muyi hakuri mu jira wayewar gari".
Goge hawaye Rakiya tai tana cewa "shikenan Allah ya kaimu Allah ya bata lafiya" amin yace tare da fara karanta mata addu'a haka suka kwana cur basuyi barci ba saida akai sallar asuba sannan ya samu wani d'an ma'koftansu mai mashin ya nemi alfarmar yakai su asibiti amma dayaje gida ba damar da zata iya hawa mashin dan tana nan a san'kare guri d'aya hatta yatsarta baya tan'kwasuwa balle ga'bo'bin jikinta rasa mafita Sabi'u yai dole karshe sai mashin d'in ya kar'bi aro yana fita wajen garinsu ya samo motar haya da'kyar suka fito da ita kamar itace haka suka sata a mota suka nufi asibiti.
Habu bai sani ba sakamakon baya gari ya tafi cikin Kano sarin kaya sai bayan ya dawo yaji labari ko hutawa baiyi ba ya tafi asibitin a zaune ya samu Sabi'u da Rakiya sunyi shiru cikin damuwa yace.
"Yaya Sabi'u dama Babah bata da lafiya? Wallahi ban sani ba dawowa ta kenan yanzu Binta take fad'a min ya jikin nata fatan da sauki"?.
Numfashi Sabi'u ya sauke tare da girgiza kai yace "Habubakar ban sani ba abun da tsoro tun safe muka zo amma har yanzu babu likitan daya fito balle muji wani labari da zaisa muji d'an dama dama".
"To meya sameta ne"?.
"Humm habu Habubakar to me zance na kasa ganewa 'kwa'kwalwata bazata dauka ba irin abubuwan da take da dare ya bani tsoro baka gani ba yadda take sandarewa kamar busashshen ice harda ihu".
Zaro ido Habu yai "innalillahi meya faru haka ko aljanu ne"?.
"Ban sani ba Habubakar Allah yasa dai ba wani mummunan abu ne ya sameta ba" Amin Habu yace yana samun guri ya zauna suna jiran tsamani kafin likitan daya kar'bi Salamatun ya fito.
GIDAN BALARABE
Dalah na zaune a kofar d'aki tana tajewa Indo gashi taji an rafka sallama tana d'aga kai taga mace ta shigo mamaki ne ya kama ta ganin Asabe a ranta tace ita kuma wannan lafiya ba dangin iya ba na baba katse mata tunani tai da cewa.
"Ke haka ake kar'bar ba'kuwa kin barni a tsaye kamar bishiya"?.
Da sabon mamaki Dalah ta kuma kallonta tana cewa "sannu da zuwa 'karaso bismilllah ga kujera ki zauna".
Zama Asabe tai tana 'karewa gidan kallo kamar wacce tazo duban tsafta zuwa wani lokaci tace humm tare da ta'be baki tana yiwa Dalah kallon uku saura sisi takaici ne ya gama cika Dalah ganin mace tazo mata har gida zata raina mata wayo tace.
"Wai meya faru ne kinzo bakice komai ba lafiya"?.
Gyara daurin kwalin kanta Asabe tai tana soke shi a gaban goshi tareda dauko cingum daga cikin Jakarta tasa a baki tana taunawa sannan ta soma magana "humm Hajiya Dalansi dama nasan zaki mamakin zuwa na saidai da baki wahalar da kanki ba domin ba wani abu ya kawo niba kawai nazo ne mu gaisa naji ya d'iya ta take".
Baki bud'e Dalah take duban Asabe jin abinda take cewa tace "kinzo ne mu gaisa kiji yadda lafiyar d'iyarki take"?.
Gira Asabe ta d'age "eh haka nace ranar baki ga tazo miki da 'kosai ba? Ai nice na bata har nake cewa idan tazo tace ina gaida ke ko bata fad'a miki ba"?.
"Eh bata fad'a min ba mun gode".
Karya kai Asabe tai cikin yanga zatai magana taji gyaran muryar Balarabe alamar ya shigo gidan cikin tane taji yana hautsinawa na shakku da tsoro tuna abinda 'kawarta Meroh tace mata akan Balaraben mi'kewa tai tana susa kamar me ciwon 'kazuwa tana rarraba ido tare da satar kallon Balarabe da yake tsaye ganin ta a gidansa muryarta na d'an rawa tace.
"Barka da gida ina yini"?.
Wani kallo ya mata yana d'auke kai bai amsa ba sai tambaya daya jefo mata "meya kawo ki gidana me kikazo yi shin kinyi ajiya ne"?.
Kallonsa Asabe keyi ganin yadda yai mugun had'e rai yasa jiki a sanyaye tace "kayi hakuri dan Allah yanzu zan tafi dama nazo ne mu gaisa".
Da yake mutum ne mai fad'a a hasale yai kanta yana cewa "da uban wa zaku gaisa dama kina zuwa min gida ne? Karki sake na sake ganin ki a gidannan idan ba haka ba zaki bayani saikin yabawa aya za'kin ta fita min a gida nacee" ya karasa maganar cikin tsawa yana nuna mata hanyar 'kofar fita jiki na 'bari Asabe tai waje kamar zata kifa tsabar sauri tana haki.
Juyawa yai cikin fad'a yana kallon Dalah yace "kece kika bud'e mata kofa kika bata lasisin shigowa gidana ko kuwa duniyanci ne ya kawo ta fad'a min naji"? Cikin shakku Dalah tace "kayi hakuri wallahi bansan komai ba kawai ganinta nai ta shigo wai tazo mu gaisa taga d'iyarta".
"Taga d'iyarta? A gidan uwar wa Indo na ta zama d'iyar yar duniya irinta kuma bari kiji daga yau na kafa doka kada ki kuskura na sake ganin wannan matar a gidan nan kin jini"? Kai Dalah ta d'aga "eh insha Allahu zan kiyaye kayi hakuri" tsaki yai yana yin hanyar ficewa daga gidan sai balbali yake d'an d'aga murya Dalah tai tana cewa "ga abincin ka" a fad'ace yace "bazan ci ba bana so" rike baki Dalah tai "oh ni Aminatu yau naga ta kaina Allah ka tsare ni da sharrin matar nan kada tai silar mutuwar aure na" ta karasa maganar tana kallon Indo tace "dauko min hijabi na a d'aki muje