Showing 54001 words to 57000 words out of 130249 words

Chapter 19 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17610

da da d'an ya'ke a fuskarta tace tace "wallhi nice ina kwana ya me jikin"?.

"Lafiya kalau gata nan jiki yayi sauki ya abinda ya faru"?.

Huuuuuuh Delu ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "hummm sai godiya ya zamuyi kaddara ce".

"To Allah ya 'kara rufa asiri".

Cikin takaici Delu tace "um Amin dai ai yaron nan ya cuce ni Tanko bansan ba mutumin arziki bane".

Jin zancen da suka soko yasa Jamila tabe baki cikin halin ko in kula tana shirin barin gurin da'kyar tace "ina kwana"?.

Kallonta Delu tai "lafiya Jamilatu zauna dan Allah magana nazo muyi".

Jitai kamar ta fashe da kuka tsabar takaici ta koma tana zama tare dayin 'kasa da kanta.

Cikin lallahi Delu ta soma magana "Jamila dan Allah kiyi hakuri abinda ya faru ki koma d'akin mijinki ki haihu acan na sani Tanko bai kyauta ba kada ki dubi halinsa ki tausaya min ki bini mu tafi".

Ba arziki Jamila ta d'ago tana kallon Delu muryarta cikin kuka tace "wallahi bazan koma gidan Tanko ba ni dashi har abada bazan ta'ba yafe masa ba sai Allah ya saka min dama yasan haka halayensa suke ya cuceni ya aureni tsabar mugunta harda ciki babu ni babu Tanko idan kin samu dama zuwa gurin sa kice ya sakeni kuma ko haihuwa nai a ranar dana haihu zan kawo muku dan'ku ko 'yarku bazan raineta ba" ta karasa maganar da kuka sosai na tsantsan tsanar tanko.

Ita kanta Delun kukan take ta kasa cewa komai sai kallon Jamila da take ganin ta mi'ke tabar gurin yasa tace "Gadoji dan girman Allah kiba Jamila hakuri tazo mu tafi wanda tai yajin dominsa baya nan a shekarun da aka yanke masa ko daya bai dauka ba gashi ta silarsa yaja mutuwar malam Balah ubansa zan iya rantse miki a cikin mu babu wanda yasan me Tanko yake aikatawa Saida asirin sa ya tonu akan yarinyar nan ashe duk fayd'en da akewa yan matan garin nan dana kewaye shine da Mudi har ran malam ya fita bai daina tsinewa Tanko ba".

Shiru itakam Gadoji tai domin itama a tana bangaren ta kudura cewa Jamila ta baro gidan Tanko har abada kuma tana fatan kada Allah yasa yaron da zata haifa yazo darai dan kada su samu ba'kin iri cikin danginsu babu wanda zaiyi alfahari da d'a mai mummunar d'abi'a irin tanko........................

Maganar da Deluh tai ne ya dawo da Gadoji daga duniyar tunanin data fad'a jin tace "Gadoji bakice komai kisa baki cikin maganar mu".

"Kai Gadoji ta girgiza "a'a bazan shiga ba Deluh bari na fad'a miki gaskiya Jamila nice nace bazata sake zaman aure da Tanko ba domin ni 'yata me tarbiyyace bazai bata min halayenta ba babu sauran ala'ka tsakanin Tanko da Jamila saki ne ya rage dan haka duk ranar da kikaje gano shi kice ya baki sakinta tunda ba mutumin arziki bane wa zaiso hada zuri'a dashi ya gama gur'bata rayuwar sa da banzayen d'abi'u marasa kyau gaskiya kawai kiyi hakuri".

Kuka sosai Delu keyi tana wa Gadoji magiya "dan Allah Gadoji ki taimaka kada ki duba halin Tanko ya dubeni ki bari mu tafi da Jamila".

Sauke ajiyar zuciya Gadoji tana cewa "gaskiya bazan iya ba taimako d'aya zan miki shine kawai kiyi hakuri ki dauki danga dan bazan bar Jamila taje ko'ina ba magiyar ya isa dan Allah ki fahimta".

Gadoji dan Allah kiyi hakur.................

Katse ta Gadoji "kinga Deluwa dan Allah karki sake ro'ko na na riga na fad'a miki gaskiyar lamari".

Goge hawaye Delu tai da gefen mayafinta tana mi'kewa zuciyarta na tafasa tace "shikenan nagode sai anjima".

Kai Gadoji ta d'aga "to Allah ya bamu alkairi".

Haka Delu ta koma gida hajijiya na dibanta ko gabanta bata gani haka zazzabi ya rufe harda amai gabadaya Tanko yasa rayuwarta a tsaka me wuya.


Baffah na zaune a kofar d'akinsa Sabi'u ya fito daga d'akin hatsi hankali tashe yana cewa "Baffah babu hatsi fa a d'akin nan".

Cikin mamaki Baffah ya dube shi "kamar ya ba hatsi kuma Sabi'u"?.

A rud'e Sabi'u yace "babu kusan rabi an sace".

"An sace kuma Sabi'u? Sake dubawa dai".

Shiru Sabi'u yai yana kallon Baffah cikin tausayawa kafin ya wuce yana duba sauran rumbunan amma dai labarin daya ne babu hatsi babu alamar sa fitowa yai ya had'a gumi da'kyar cikin jin nauyi yace.

"Baffah wallhi babu komai an debe duka".

Cika da tsananin mamaki Baffah yace "an d'ebe dai Sabi'u? Ikon Allah shikenan Allah ya rufa asiri".

"Dan Allah kayi hakuri Baffah".

"Babu komai Sabi'u karka damu Allah ya maka albarka".

"Amin Sabi'u yace yana cizon yatsa cikin takaici dan wallahi ya sani ko ba'a fad'a masa Ilyah da Ramatu ne suka d'ebe hatsin nan amma me sukai dashi ina suka kaishi d'an kwanakin da bai wuce 'kirge ba har sukai ta'addanci da 'barna haka....,.................


Dawo dashi daga duniyar tunani Baffah yai da cewa "Sabi'u bakomai jeka kaji kuma dan Allah kada ka fad'awa Habu kasanshi da zafin rai yanzu sai yazo hankali ya tashi tunda kowa yasan ba mai diban hatsin nan sai Ramatu da Ilyasu wadannan mutane suna 'bata min rai a rayuwa suna ba'kanta min bansan yadda zanyi da lamarinsu ba amma shikenan duniya ce gata nan suna ciki" Baffah ya karasa maganar yana dafe kirjinshi tare da runtse ido.

Sabi'u na tsaye yayi shiru yana kallon sa Zuciyar sa na tafasa ransa ya gama kai 'kololuwa wajen 'baci share hawaye yai yana ficewa daga gidan.

Kusan karo sukai da Habu zai shigo ganin yanayin sa kamar hankalin sa a tashe yasa Habu cewa "yaya lafiya na ganka haka"?.

Sauke ajiyar zuciya Sabi'u yai cikin sanyaya nazari da kuma tunanin me zaice masa wacce amsa ya kamata ya bashi tunda Baffah ya gargad'e shi kada ya fad'a mas....................................

Katse masa tunani Habu yai da cewa "yaya Sabi'u ya kayi shiru dan Allah ka fad'a min meyake faruwa?.

Kallonsa Sabi'u yai yana girgiza kai yace "bakomai muje gurin Baffah yana ciki".

Hankali tashe Habu yace "meya same shi ko ciwon ne"?.

Kai Sabi'u ya girgiza "a'a ba ciwon sane ya tashi ba kawai dai muje gurin sa yana kofar d'akinsa".

Tafiya Sabi'u ya fara jin shiru ya sashi waigowa ganin Habun na tsaye yasa ya dawo da baya yana rike hannunsa ya fara tafiya dashi yana cewa.

"Haba Habubakar ka taho man na fad'a maka ba komai bane Baffah na lafiya yanzu muka gama magana dash.....................................


Kasa 'karasa maganar Sabi'u yai ganin Baffah kwance akan tabarma yana ri'ke da kirji sai kiran sunan Allah yake a guje suka karasa suna kiran BAFFAH BAFFAH innalillahi wa inna ilaihi raji'un sannu Baffah".

Muryar Baffah da'kyar take fita cikin wahala da ciwo yace "ku kaini asibiti ku kaini gurin likita 'kirjina zai tsage zuciya ta ciwo take".

Tab jin furucin da Baffah yake yasa a rud'e suka cicci'be shi suna yin hanyar waje yayin da Salamatu ta biyo bayansu hannunta aka tana kuka ko takalmi babu a 'kafarta gashi babu mota a 'kauyen sai mashin haka suka d'ora shi akai Sabi'u ya hau bayan sa sukai gaba habu da Salamatu kowa yahau daya suma suka bisu.

Ko parking me mashin din baiyi ba Habu ya diro da gudu yana yin hanyar emergency dam ya samu guri cike da majinyata masu nemen taimako cikin gaggawa furmutsawa yai ya shige har gaba likita hawaye na zuba a idanun sa yace.

"Likita mun dawo da Baffah yana wani hali dan Allah ka saurare ni".

'Dagowa likata yai ganin sa yasa da sauri shima ya mi'ke yana cewa "Abbakar kaine subahanallahi ina Baffan yake"?.

"Yana tare da yaya Sabi'u likita Baffah mu jikinsa babu dad'i".

Da sauri likita yai gaba Habu na biye dashi daidai zasu sha kwana sukaga an turo Baffan sun shigo karasawa sukai likitan yai yana cewa.

"Sannu Baffah sannu" kallon wani doctor daya fito daga wani room yai yana cewa "Dr Usman 'karo mana kayan aiki yanzu".

"Kai Usman ya d'aga yana wucewa su kuma suka karasa shiga dashi sannan suka fito a zaune suka samu Salamatu tayi tagumi naban tausayi zama sukai kusa da ita ba wanda yace wani abu kowa zuciyarsa na bugawa suna wa Baffah addu'a da fatan alkairi.

Haka suka wuni a gurin babu alamar likita balle su samu wani d'an labari ko hankalin su ya kwanta sai kusan karfe tara na dare sannan suka ganshi ya fito bai bukaci suje office dinsa ba anan ya musu bayanin komai wanda abinda ya fad'a musu ya razana su ya burkita kwakwalwar su babu wanda baiyi kuka ba a cikin su haka suka kwana currr basuyi barci ba saida akai sallar asuba Salamatu ta tafi gida dan ta had'o musu abun karyawa.


Bata samu kowa a gidan ba daga Ramatu har Ilyan aikin ta fara cikin gaggawa tayi musu ta d'auraye jikinta ta sake kaya saida ta dau abincin zata tafi taga Ilyah ya shigo kamar dai baya hayyacinsa kila yasha 'kwaya ne da kallo ta bishi tana cewa.

"Iliyasu Baffan ku fa bashi da lafiya tun jiya yana asibiti acan muka kwana ko baka sani bane".

"Bai saurareta ba saida yaje ya samu guri ya zauna kafin ya d'ago idonsa jajur yana cewa.

"Na sani mana to mezanje nayo"?.

"Me zakaje kayo kuma Ilyah mahaifin kane fa"🙄.

"Oh dan mahaifi nane dole sai naje gurin sa me zanyi masa zan bashi lafiya ne zuwa na bazai 'kareshi da komai ba sannan rashin zuwana bazai sa ya warke ba".

Cikin mamaki Salamatu ta kuma bud'e ido a kansa tana cewa "haba Iliyasu me kake cewa n................


Katse ta yai da cewa "kinga da Allah ware bana son jin wata magana" shiru Salamatu tai tana kallon sa wannan wacce irin ta'bewa ce Allah ya shirya wanda ya kauce hanya juyawa tai ta fita daga gidan.

Tabbas albarka tana tare ga wanda yabi iyayen sa sau da 'kafa yanzu da take kallon Sabi'u da Habu ta tabbata rahma tana tare dasu shiyasa take fatan Ilyah ya dawo kan hanya da wuri.

"Babah tunanin me kike"? Taji muryar Habu d'an kallonsa tai tana murmushin dole tare da girgiza kai tace.

"Ba komai Habu kuci abinci gashinan".

Mi'kewa Habu yai yana cewa "a'a yaya Sabi'u tashi muje sai mun fara baiwa Baffah".

Dakatar dashi Salamatu tayi "tsaya Habubakar kaga zauna ku karya ka bari likita yai magana kada hakan ya zama laifi" d'an sauke numfashi yai yana zama suka fara karyawa har suka gama sai sha biyu likita ya bukaci su ganshi sannan sa iya shiga masa da shayi.

Wajen asibitin Sabi'u ya fita gurin wani me sayar da shayi da yake can tsallake ya sayo yana dawowa suka shiga kwance suka samu Baffah idonsa a rufe da sauri Habu da ba kaya a hannunsa ya karasa yana d'aga shi ya zaunar dashi yana zama a bayansa ya jingina shi a jikinsa yana cewa.

"Sannu Baffah ya jikin naka"?.

Kai Baffah ya d'aga a hankali yana kallon su aje kayan Sabi'u yai yana dauko shayin ya zauna shima yana cewa.

"Sannu da jiki Baffah fatan kaji sauki"?.

Nan ma kai ya d'aga baice komai ba soma bashi shayin Sabi'u yai a hankali yake sha har yasha da d'an yawa saidai baici biredi ko kad'an ba bayan ya gama shanyewa aje kofin yai yana goge masa baki.

"Sannu Baffah" suka ji likita yai magana d'an murmushi yai yana cewa "allhdllh jiki ya fara sau'ki Allah ya karo afuwa Sabi'u kuje waje zan sake duba shi" to suka ce suna ficewa.

Iya yanayin fuskokinsu da Salamatu ta gani suna walwala yasa taji dad'i kuma hakan ya nuna mata cewa jikin Baffah yayi sauki itama fuskarta da annuri tace.

"Ya jikin Baffan naku"?.

"Da sauki babah yasha shayi ma yanzu Lukman ne yake duba shi".

"To alhamdulillahi yanzu bari naje gida naga rana ta fara zuwa jimawa saina dawo Allah yasa Ramatun ma tana gida saimu taho tare" mikewa tai tana daukar kwanukan ta tafi.

Tsaki Habu yayi yana cewa "nifa wallh Ilyah yana bani mamaki wai tsakani da Allah kamar ba Baffah ne yahaifeshi ba yake irin wannan nuna halin ko in kula akansa amma dai yaya Ilyah ko agola ne babah Ramatu tazo dashi gidan zaiyi biyayya a Baffah a nawa haukan al'amarin nan na yaya Ilyah ya fara isata wallahi dan Allah yaya Sabi'u muyi wani abu mu tsaya mu jajirce harsai ya dawo kan hanya, amma me kace"?.

Kai Sabi'u ya girgiza tare da sauke ajiyar zuciya yana cewa "eh haka ne Habubakar amma yanzu damuwa ta ciwon Baffah fatana ya warke koma maye sai muyi dan ni kaina abun ya gama kaini bango, kaga ga likita can ya fito tashi muje mu sake ganin jikin Baffan".

Mi'kewa Habu yai suna shiga a zaune suka samu Baffah sunyi mamakin ganin yadda ya sake warwarewa fiye da d'azu har mamakin nasu ya kasa 'boyuwa d'agowa yai yana kallon su tare da sakar musu farin kyakkyawan murmushi ri'ko hannun Habu yai yana sakawa a cikin na Sabi'u kuma har lokacin da murmushin sa a fuskarsa yace.

"Sabi'u Habubakar Allah yai muku albarka ya albarkaci rayuwar ku da zuriyar ku Allah ya baku bud'i Allah ya d'aukaka ku ya tsare ku a duk inda kuka tsinci kanku wannan kauna soyayya biyayya kulawa dakuke nuna min ku ma Allah yabaku 'ya'ya na gari masu jin 'kan iyayensu irinku kunyi min komai a rayuwa kuma nayi farin ciki da samunku kun fara tara min jikanu 'ya'yanku Aminullahi mai suna na Hajiya mai sunan Salamatu naka ne Sabi'u kai kuma Habubakar Asma'u Allah ya raya muku su akan tafarkin shiriya madaidaiciya ya tsare min ku da kiyayewarsa duk abinda zai zama alkairi gareku Allah ya had'a ku dashi ina ji a jikina akwai nasara anan gaba da zata riskeku nasan bazanga wannan lokacin ba amma ina addu'ar samun farin ciki da walwalarku".

Shiru Baffah yai yana kallon su gabadaya hankalin yayi mugun tashi suna jin tamkar wasiyya Baffah ke musu abun yana basu tsoro lamari da firgici share hawaye Sabi'u yai yana cewa "insha Allahu Baffah zaka ga wannan lokaci zaka warke".

Kai Baffah ya girgiza "a'a Sabi'u bazan gani ba ka barshi a haka" sannan ya mayar da kallonsa kan Habu kafin yaci gaba "na sani kun nuna min fitacciyar 'kauna da kowanne d'a zai nunawa ubansa kuma nayi matukar jin dad'in hakan da godiya ta a gareku duk rintsi kada ku bari a raba kanku ko a shiga tsakanin ku kuzama 'yan uwa na gari ku rufa asirin junanku dan Allah kumin alkawarin haka, shin zaku min wannan alfarmar"?.

Ya fad'a yana ri'ko hannuwansu yasa cikin nasa tab Allah sarki kuka suka saka masa cikin damuwa sosai da tausayawa halin da zasu shiga idan aka wayi gari rana ta fito ace babu Baffah a duniya yabar cikin ta yabar zama tare dasu har abada innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

Baffah bai hana su kuka ba domin yasan zai rage musu wani rad'ad'i dake damun ransu da rayuwarsu yace.

"Abubakar Sabi'u dan Allah kuyi shiru haka kuyi hakuri kada kusa naji wani iri nima" kai Habu ya d'aga cikin daurewa da jaruma ya goge hawayen fuskarsa yana daukar kofin da Salamatu ta kawo na kunun safe ya zauna a gefen Baffan ya soma bashi Sabi'u kuma na tsaye.

Dr Usman tare da Dr Lukman suka karaso gurin cike da murmushi Dr Usman yace "alhmdllh gaskiya Baffah kayi dacen 'ya'ya nagari masu so da kaunarka suna kula dakai amma abun haushi yanzun nan daga d'akin masu ciwon ciki muke bakiji yadda wani tsohu yake ambatar suna yaransa ba d'aya bayan d'aya yana tsine musu albarka kuma ba rad'ad'in ciwo bace sai tsabar rashin biyayyar su nayi farin ciki ga kaunarku ga mahaifin ku".

Murmushi Baffah "ai likita wadannan 'ya'yan nawa babu kamar su kuma baza a samu ba tunda sukai wayo suka d'ago suka mallaki hankalin kansu basu sake bari na shiga wata matsala ko 'kuncin rayuwa ba saidai in basu sani ba shiyasa bani da fata sai Allah ya basu 'ya'ya jarumtattu irinsu suma su kula dasu fiye da yadda sukai min".

Kai Dr Lukman ya jinjina "gaskiya ne Baffah irin wannan za'a dad'e ana nema kafin a samu dan wallahi nidai ban ta'ba had'uwa da masu kaunar mahaifi da tattali irin su ba".

Baffah yayi matukar jin dad'in yadda doctors din nan suke bada shedar arziki akan su Sabi'u ya sani albarka zataci ga a da bibiyar su da zuriyar su har abada.

"Baffah bari na sake daura maka sauran ruwanka tunda naka alhmdllh gaskiya jikin naka yayi sauki sosai".

Mi'kewa Sabi'u da Habu sukai yayin da Baffah ya koma ya kwanta Dr Lukman ya matso yana saka masa ruwan kafin ya basu takardar maganin da zasu sayo masa da allurai kar'ba Sabi'u yai yana fita dan ya sayo yayin da yabar Habu shi kadai tsaye a gaban Baffah yana ri'ke da d'ayan hannun da ba'a jiki aka d'aura masa ruwan ba.

Idanuwan Baffah na rufe Habu na kallonsa yana karanta masa addu'a lura dayai kamar ruwan ya daina tafiya ya tsaya yasa da sauri ya sake kallon fuskar Baffan tare da cewa.

"Baffahh".

Jin shiru baiyi masa magana yasa ya d'an ta'ba shi yana sake cewa "Baffah Baffah innalillahi wa inna ilaihi raji'un likita likita kawo mana taimako wayo Allah na Baffah".

'Daga hannunsa yai ganin ya saki yasa ya fasa 'kara da gudu yai waje dan kiran Dr Lukman.

Babu irin magungunan anan cikin asibitin saida Sabi'u ya fita wajen can tsallaken titi ya samo daidai zai shigo gate din hospital d'in yaci karo da wani saurayi wanda shima mahaifin sa room dinsu daya da Baffan tararsa yai murya a sanyaye yace.

"Ka sayo maganin"?.

Jin yadda ya masa magana ga fuskar ba walwala yasa jikin Sabi'u na rawa yace.

"Eh na sayo meya faru? Ko ya rasu ne"?.

'Dan shiru saurayin yai sai kuma ya girgiza kai yana cewa "kawai idan ka sayo mi'ko na mayar".

Sabi'u najin haka baisan lokacin daya jefar da ledar maganin ba aguje yai cikin asibitin yana shiga d'akin yaga Dr Lukman da Usman tsaye a bakin gadon idonsu kowa da ruwa ga Habu ya kifa kai yana kuka karasawa yai da sauri yana bud'e Baffah dake rufe yace.

"Likita meya faru ka rufe shi likita karkace min mahaifi na ya rasu kar kace shikenan Baffah ya tafi ya barmu, likita ka fad'a min cewa lafiyarsa kalau bacci ya samu".

Shiru Dr Lukman yai tare da sunkuyar da kansa kasa ya kasa fuskantar Sabi'un balle ya ce masa 'kala.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un durkusawa a gurin Sabi'u yai yana fashewa da kuka na ban tausayi shikenan Baffah ya musu nisa shikenan Baffah ya rabu dasu har abada shikenan Baffah ya tafi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login