Showing 105001 words to 108000 words out of 130249 words
karaso mu gaisa ke"
"Aiko kun kyauta Maryam nagode muku kunfi Ahmad zumunci gashi a kwanakin nan kusan zuwanku hudu amma yaron nan shiru kamar baya gari rabo dana ganshi harna manta sai yanzu da bikinsa ya tashi zanje mu had'u ai sai naci 'kaniyarsa".
'Yar dariya Maryam tana mi'kewa tace "ina Ikram ko bata nan banji motsinta ba"?.
"Oh Ikram tana kitchen wai saurayinta nefa zai zo daga nan-nan Yadi shine take masa iyayi tun d'azu a kitchen ko uwar me take girka masa oho shima da bajajjan hancinsa a gurin".
Murmushi Maryam tai tana cewa "bari na gano abinda take yi ku jira ni" Maryam na rufe Nabilah tace "ai gara kizo mu tafi dan Allah wallhi yanzu idan kika shiga gurin Aunty Ikram sai mun 'bata lokaci muzo munata jiranki baki fito bakuma kin manta zamuje saloon"?.
Wucewa Maryam tai tana cewa "a'a ban manta ba ku jirani minti daya shigewa hanyar da zata kitchen tai tun kafin ta karasa taji Ikram na sakin ashar loya-loya a waya da sauri ta karasa tana cewa.
"Iki miya faru kike zagi"?.
Da sauri Ikram ta rungume Maryam cikin murna tace "ke sis yaushe kika zo kullum ina kiran wayar ki amma ta'ki shiga"?.
Had'e rai Maryam tai "humm ban yarda ba Ikram ganin idona yasa kika ce haka"?.
"Ke wallahi da gaske bata shiga but idan kin koma ki tambayi ya Ahmad zai fad'a miki ai shi muna waya dashi".
"Na'ki na tambaye shi idan da gaske ne ki bari saina koma zan tambaye shi domin daga nan Miyetti muka nufa bari na tafi dama Nabilah tana can a falon Aunty umma tana min 'korafi".
"Oh harda Nabilah kika taho"? Ikram tai maganar tana d'auko abinda data dafa masa da wanda ta soya dukka ta d'ebo musu shi zuwa falor amma Maryam tace bazasu zauna ba kar lokaci ya kure a yau zasuje saloon da lalle gashi yaune farin biki yace sai anyi 'kauyawa party suna shirin tafiya Ikram tace.
"Ku jirani kawai bari na dauko kayana mu tafi nima tunda nasan umma zuwa jimawa zaki le'ka kema ko"?.
Kaita d'aga mata "eh zanje mana zamuje mu gano 'kauyawa party dole" wucewa Ikram tai tana d'auko kayanta a jaka zasu tafi sukaiwa Aunty umma sallama .
Saida suka gama safgoginsu sannan suka kar'bi ashobin suna komawa gida ko zama basuyi ba iya kayan suka aje cikin sauri ganin lokacin yana neman fita musu suka tafi saloon basu suka dawo ba sai la'asar sosai a harabar gida suka ga Ahmad da wasu abokansa suna magana ganinsu yasa yace.
"Amatu dama ke nake nema dan Allah ki fad'a min ya shigar 'kauyawa take mun rasa yadda zamuyi"?.
'Dan harararsa Amatu tai tana had'e rai tace "ai nima ban sani ba saidai kayi sacin a gogul zaka gani" dariya Ahmad yai "haba ke kuwa sorry gani nayi ke kin sani shiyasa Allah kuwa serious nake tambayarki ki fad'a min yadda zanyi"? "Shikenan zan fad'a maka sai zuwa jimawa dan wallhi yanzu a gajiye nake" .
"ok ba damuwa ki huta zamuyi magana an jima kafin lokacin shiri yayi" to kawai Amatu tace masa tana wucewa ciki domin ita yau bata jin dad'i sosai zazza'bi ne yake neman rufeta tana shiga bedroom kwanciya tai taja bargo dan har taji sanyi ya mata kad'ata kallonta Maryam tai "Amatu yada kwanciya"? Kaita d'aga "eh bana jin dad'i ne".
"Ok Allah ya sauwake amma da kin tashi kinga la'asar fa tayi idan an Kira sallah saiki kwanta" "eh zam tashi wanda nake son maybe hakan zaisa naji d'an dama dama zazza'bi keson kamani".
"Subahanallahi Amatu zazza'bi kuma Bari naiwa ya Ahmad magana yazo ya duba ki".
"A'a karki kira shi ban tabbatar ba tukuna sanyin da nakeji ne ga jikina yai zafi" tun kafin Maryam tayi maja Ikram taja tsaki tana jan hannun Maryam tace.
"Ke dan Allah zo mu tafi yar rainin hankali wai tazo birni ta waye sai wani wahalar dake take wai ita ga maamaa kema kina biye mata muje share ta" murmushi Maryam tai tana dafa goshin Amatu da gaske jikinta d'au yake da zafi kamar wuta kai ta jinjina tana cewa.
"Amatu zazza'bi man kike bari na kirashi" fita sukai Ikram sai harararta take tabe baki Amatu tai tana gyara kwanciyar ta tace "wannan budurwar akwai yar jin kai amma babu komai ina daidai da zamaninki wallhi ba kyaleki zanyi naga take-takenki nima zan fito miki cikin kalata idan ba haka nayi miki baza mu zauna lafiya ba baki isa raina niba dan daga 'kauye nazo".
Bayan sallar magriba suka fara taruwa a harabar gidan inda zasuyi 'kauyawa kowa yayi shiga kayayyaki komai daban-dabam harda amarya Lailah tasha had'in gambiza da tawagarta daga gida dubu ba shigar wanda tafi hargitsa ba'a ci dariya an more har ciki yai ciwo ba saida ango yazo da abokansa riga daban wando daban takalmin 'kafarsa d'aya fari d'aya ba'ki silifas da combus😂😂 ga d'aurin kara a wuya🤣🤣innalillahi wai maimakon a d'aure a d'auko aka shine suka d'add'auro shi a wuya sun datsa shi 'kanana yadda zai dadi daurewa ansha dariya fuskar amarya Lailah tasha kwalliya da bakin kwalli idan ka ganka birad'al kamar ka gudu ga takalma an zurasu a jikin gyale kowa ta d'aure a kugu ga kuma sandunan rake ana sha 'kawayen amarya kuma sunyi d'an malele yasha manja da yajin maggi😋😃 sun yanka albarka da cocumber abun dai sai wanda ya gani 'kauyawa party yayi kyau ansha dije sosai an girgije dama Ahmad yace kunyarsa galan d'aya ce kuma ranar aurensa zai tintsirar dashi haka ne kuwa ya faru ya gyagiye ba laifi kalangu ya daku a gurin makad'i sai kusan karfe goma ta dare suka koma gida sannan Amatu ta dad'e dayin barci domin bataje ba zazza'bi ya hanata zuwa.
Washe gari tun wuri gida ya sake cika Binta ma tazo tare dasu Aisha harda Saude da A'i Amatu tayi farin ciki ta 'kara ganin ahlinta anan Binta take fad'a mata malam Habu ya tashi sun tafi neman kud'i tare da Sadi tuni murna ta sake lullu'be ta harda hawayenta ta d'aga hannu tana rokar nasa samun abinda yaje nema duk sai taji zazza'bin nata ya warke da Binta ta mata wannan albishir mai dad'i.
'Karfe hudu aka d'aura auren Ahmad da Lailah a babban masallacin sallar idi da yake wajen gida dubu bakin Ahmad kamar zai yage😂 tsabar murna bayan an gama daurin abokan sa sai taya farin ciki suke suna bashi hannu haka da suka shiga gaisuwar iyaye Ahmad ba kunya harda 'kara jawo Lailah jikinsa a gaban mutane sukai photuna kafin zuwa yace ta sanar da 'kawayen ta dinner nan da 'karfe biyar a moderling event center🌆.
Biki yayi biki haske ya gama haskawa a wajen kid'ane mai mugun 'karfi yatshi kamar kunnen mutum zai fice tsabar 'karar tai yawa Amatu da su Maryam suna gurin harda su Aisha Asma'u da Jamila sun zo balle iyaye 'kirjin biki su Safiyah da Aunty umma su maman Asraf sune akan gaba suna rawa 'ya'yansu sunai🤠Binta dai dasu A'i suna gefe suna kallon abinda yafi karfinsu suna mamaki su abun saiya zama sabo a gurin su anyi bajinta an raba kyautuka na fad'a a gurin humm Safiyah tayi kokari.
Har dare yai sosai ba'a basu ankara motoci da yawa sun tafi wasu ma babu mutane ga guri ya d'au duhu hankali tashe Amatu tace.
"Maryam wai me muka tsaya yine kalli fa babu kowa daga mu sai masu dije kuma suma tafiya zasuyi dan Allah ki Kira ys Ahmad idan bazai samu damar zuwa ya d'auke muba ya turo mana mota".
Shiru Maryam tai cikin tunani da rashin madafa tana kallon su tace "kuzo muje" ta juya zata fara tafiya Amatu ta dakatar da it's "muje ina Maryam date nefa"? Amsa Maryam ta bata suna kokarin fita tace "eh aina sani zan Kira ya Ahmad amma gara mubar wajajen nan haka baki gani ba masu dijen kamar marasa gaskiya sai kallonmu su d'ayan harda murmushi suna fitowa ta dialing numbar wayar Ahmad tana kiransa yana d'agawa tace.
"Ya Ahmad an baro mu acan fa babu mota ka turo a d'auke mu".
Daga can 'bangaren cikin fad'a Ahmad yace "azo a d'auke ku duk da uban me kuka tsaya yi har aka watse"?.
Kallon Amatu Maryam tai kamar zatai kuka "tace dan Allah yanxu ba lokacin tambaya bane la rufa mana asiri kazo ka d'auke mu daga baya saikayi mana fad'an" tana rufe baki d'ittt taji ya kashe kiran kallon su tai jiki a sanyaye tace.
"Bazai zoba gara mu tafi da wannan tsaiwar tamu anan bamu sani ba ko wani ya fake yana kallon su da asara gara gidadanci da zaman banza gara aikin kishiya ko zata zagi uwarka🤪😠ku muje mubar wannan" aiko tana rufe baki suka d'eba a guje suka bar gurin tun suna tafiya da sauri har suka gaji suka dawo tafiya a hankali da azaba tai azaba duk cire takalman kafarsu masu tsini👠sukai suna rikeshi a hannu sunaci gaba da tafiya gashin sun fahimci kamar binsu ake motar bayansu kamar daga gurin event din domin mai motar yaiwa Amatu magana bata kulashi yaiwa Ikram ita kuwa harda ashar ta sakar masa dama saida ya jinjina kai kafin yabar gurin da suke a modeling din daga haka basu sake ganin wulginsa ba Nabilah tsabar wuya tayi wuya har kuka take dayake dama ita raguwa ce ga shagwa'ba bata juri wuya ba.
"Haba ke kuwa Nabilah wannan kukan ba magani zai miki ba abinda yafi sau'ki kiyi shiru insha Allahu babu abinda zai samemu har muje gida" Amatu tai maganar tana ri'ko hannunta tare da kar'bar takalman data ri'ke da jaka duk dan ta rage mata kaya ko tayi shiru hatta gyalenta da d'an kwalin kanta suna hannu duk tabi ta burkice ganin motar tayi kusa dasu yasa ta kara fashewa da kuka tana cewa.
"Wayyo Abbana ka taimake mu zai kashe mu".
A fusace Maryam ta juyo tana cewa "wai ke Nabilah kinyi hauka ne ubanwa kike fad'awa anan d'in kin wangame baki sai kuka kike 'yar tselan uwa kawai wallahi idan baki rufa min baki ba saina fasa shi".
Cikin jin haushi da gajiya Ikram tace "Maryam 'kyale 'yar bura uba ta zauna anan d'in Abban yazo ya ceceta kinga nan da kwana uku sai muci waina aikin banza kawai mstttt haba dan masifa kin dame mu da kuka keba jaririya ba waye bai gaji ba ya danne saike ce fallalliya harda kiran Abba ai mu kuma daga sama muka fad'o bamu da uba shiyasa bamu kirashi yazo ya cecemu ba saike ko na sake jin bakin nan".
"Haba dan Allah kuwa wannan tai mata wannan tai mata dame zataji da gajiya koda jarabarku"?.
Harara Ikram ta sakarwa Amatu tana cewa "to uwar iyayi ban sako dake ba bana son shishshigi ga da wacce nake idan kuma bazata iya yin shiru ba saidai mu raba tafiya tunda duk wani harkar 'kauyanci ta iya".
"Baza'a raba tafiya ba amma dai ku 'kyale ta gaskiya takurar taku tai yawa irin haka da a gida d'aya kuke wannan ai saiku sa ta rame keda Maryam hum'um".
"Ke rufe min baki ina ruwanki ne a tunani da Nabilah nake magana ta bada ke ba dan haka karki sake shiga ciki" Ikram na rufe baki Amatu tace "idan kinyi da ita kamar kinyi dani ne domin yar uwata ce kuma jini na ke bari fa kiji baki isa kice zaki fad'a min magana na 'kyale kiba never in history kin gane"? Cikin 'bacin rai Ikram ta kalli Amatu tana shirin magana sukaga hasken motar ya haske musu idanu tuni suka manta da abinda suke kowa ta rud'e ciki ya d'uri ruwa ri'ke hannun Nabilah Amatu tai cikin jarumta tace "kada kiji babu abinda zai same mu insha Allahu zamu koma gida lafiya" janta tai suka cigaba da tafiya yayin da Maryam da kuma Ikram suka tsaya guri d'aya sun kasa gaba ganin har Amatu tai nisa yasa Maryam d'aga murya tace.
"A'a Amatu kada kibi tanan bakisan waye ba kizo mu canza hanya".
Amatu bata tsaya da tafiyar da take ba kuma bata juyo ba tace "wallahi Maryam bazan canza hanya ba tanan zanbi babu wani mutum da yake da ikon da zai cutar da d'an uwansa sai Allah yaso idan kuna iyawa ku taho mu tafi idan bakwa iyawa ku tsaya anan d'in ko ku canza hanyar mukam mun wuce".
A rikice Maryam tace "a'a Amatu kada kije kizo mubi tanan".
Ko juyowa Amatu batai ba suka yi gaba sunje daidai motar suka tsaya su Maryam na tsaye daga nesa jiki na'bari suna kallonsu suga abinda zai faru a mamakin su gani sukai sun shiga motar tabar gurin ihu Maryam tayi tana cewa "na shiga uku na lalace idan na koma gida ba tare dasu ba me zance waye wannan ya d'auke su kar suje a kashesu" ta'be baki Ikram tai tana cewa "a kashe sun mana uban waye ya kaisu ba kinyi musu magana ba sukai kunnen uwar shegu dake Allah yasa kidnapping d'insu akai naga ta tsiya" harara Maryam ta zafga mata "ba amain ba mai bakin tsiya insha Allahu babu abinda zai samesu" tsaki Ikram taja daidai wani mai keke napep yazo wucewa suka tsayar dashi suna ce masa Mopal-Base sannan suka shiga babu kud'i a hannunsu saida suka sauka Maryam ta kar'bo ta kawo masa a gajiye suka shiga bedroom turus suka tsaya suna 'kare musu kallon mamaki dama gida suka zo d'agowa Nabilah tai tana kallon su ganin yadda sukai yasa ta kwashe da dariya tana cewa.
"Sai yanzu kuka 'karaso? sannunku da hanya".
A fusace Ikram tace "ke dawa kike uban wa kikewa sannu"?.
Shiru Nabilah tai bata, bata amsa ba sai mi'kewa datai tabar d'akin tsaki Ikram taja tana cewa "zanci ubanki ne Nabilah kafin nabar gidan nan maza cigaba da shiga safgata jikin kine zaiyi tsami" kallon ta Amatu tai baki bud'e dariya na kamata tasan duk cikin jin haushin su taho sun barsu ne ga gajiya maida hankalin ta tai kan Maryam data cire kayan tana sauke numfashi tace.
"Sannunku da zuwa abinda bakwa so d'in dai zan fada sai yanzun kuka karaso"?.
A masife Ikram tace "oho miki kema ba'a sani ba".
"Kada Allah yasa ki sani idan ke nake tambaya" mutsssssss Amatu taja tsaki tana kallon Maryam tace "amma a abin hawa kuka zo dan naga da 'yar tafiya kuma kunyi saurin zuwa"? Kai Maryam ta d'aga "eh d'an napep muka tara badon haka ba ai da yanzu muna can a hanya to amma ke Amatu waye mai motar daya kawo ku"? Dariya Amatu tai cikin tsokana tace "wannan saurayin ne dayai min magana ban kula Shiba ya koma kan Nabilah itama ta share shi to shine ya d'auko mu" zaro ido Maryam tai "haba dai dan Allah da gaske bakuji tsoron ya sace kuba"?.
Kai Amatu ta d'aga "eh man ba wani sace mu dazaiyi bayan tare suke da ya Ahmad".
Da mamaki Maryam tace "kai dan Allah harda ya Ahmad amma baki mana magana kawai kuka shiga kuka tahowarku"?.
"Eh shine yace na 'kyaleku ku taho da sayyadarku ('kafa)".
"Humm ai shikenan ya Ahmad ya kyauta kuma wallahi tunda haka ne gobe bazanje G9 (jinayin) gidansa ba na kara shan wahala balle yana zumud'in amarya ko ta kanmu bazai bi ba".
Dariya Amatu tai "kai Maryam kema dai wallahi aiko zuwa gidan sa ya zama dole gobe 'karfe hud'u da rabi na asuba zaki tashi ki musu breakfast kuma kikai idan da dama sai kinyi seving d'insu kin jira sunci sannan ki wanke kayan ki mata shara sai ki dawo😂" ta karasa maganar tana kanne mata ido😜.
Ta'be baki Maryam tai tana cewa "tab wallahi ba inda zanje saidai driver yakai".
"Umm kuma idan momy ce tace kije fa ya zakiyi"?.
"Insha Allahu ma bazatace ba ki daina min fata".
"To ai shikenan bari nikam naje gurin umma na nasan yanxu batai barci ba" tana fad'in haka ta fice mi'kewa Maryam tai bayan fitar Amatu ta shiga wanka Ikram dake zaune akan stool tana chat ta ta'be baki tare da kunna voice tana dannar ashar iri iri ta tura fitowar Maryam ta kalleta da mamaki tace.
"Haba Ikki dawa kike wannan zagin haka kamar ba musulma ba dan Allah ki rage zafin zuciyar nan karki manta kefa mace ce wata rana gidan wani zakije".
Tsuka Ikram taja tana cewa "rabu dani Maryam wannan akwai tsinanne baki san halinsa bane shiyasa kike ganin laifi na amma mugun tantiri ne dan raini hankali jiya kina gani lokacin da kukaje gidan nayi masa hidima na kashe kud'i amma yace bazai samu damar xuwa ba baya gari tafiyar ujila ce ta kamashi yau kuma wani wai ya kira ni d'azu muna modeling dan ban d'aga ba shine yake min masifa da 'korafi aikin banza".
"To ke Ikram dole ne soyayya da wannan yaren nifa gaskiya dama garinsu yayi nisa har Abia state gaskiya ki barshi zaki samu wanda ya fishi".
Kai Ikram ta girgiza tana cewa "bazan iya ba Maryam ina son sa shine mafarki na had'dd'an gayene na kwatance ga kud'i d'an gidan Minister gud'a ne fa taya zan 'kyale shi".
Kad'a kai Maryam tai tana sake kallon Ikram tace "um um Ikki kada fa, ki tsaya kiyi nazari karki bi son zuciya".
"Maryam aiba son zuciya bane waye zai samu dama ya sake gayen akwai sakin hannu yana zubar min da naira🤨 shiyasa na narke ashi yanzu zamuyi fad'a naci 'kaniyarsa yanzu zamu shirya kin gani ko gashi harya turo min stikers da typing na bada ha'kuri ai nasan bazai ta'ba zuciya dani ba shiyasa nake masa abinda naga dama na zageshi naci mai mutunci duk ya had'iye".
"Hummmm" kawai shine abinda Maryam tace tana daukar kayan barci tasa tayi kwanciyar ta bata sake bi takan Ikram ba wacce take video call sai dariya take har barci ya fara d'aukarta taji Ikram tana she'ka dariya a firgice ta farka tana kallonta tace "dan Allah ikki badan niba kiyi shiru ko ki kasa da murya wallahi kin d'au alhaki na domin barci ya faramin dad'i kika katseni" tsaki Ikram tai tana juya mata baya tace "dama kuma ni na hanaki yin barci ne harda wani nayi kasa da murya bazan ba gara kiyi barcinki a haka ko ki ha'kura saina gama" Maryam bata sake kulata ba ta gyara kwanciyarta tana jan bargo.
🌴CAMEROON🌴
Su malam Habu sun sauka lafiya cikin garin