Showing 42001 words to 45000 words out of 130249 words
cikin zaure ya samu me anguwa da tsirarun mutane sunzo gaida shi zama yayi bayan sun gaisa yace "dama naji wata magana ne a bakin mutane shine nake so na tabbatar wai jiya an kawo wata mata gidanka ta kwana"? Kai me anguwa ya d'aga "eh shakka babu zahiri jiya nikam ina barci ma aka tashe ni nayi mamaki dana ganta harda rauni a goshi wai ana ihun barawo aka rad'e ta ba'a sani anyi tunanin barawon ne shine aka kawo ta nan ta kwana kafin yau ayi bincike a kanta dan ni tsoro ma ta bani da fari, baka ji zagi iri iri ba a bakinta da diban albarka sai loya ashar take kamar ba musulma ba".
Shiru Musbahu yayi na d'an lokaci kafin yace "zan iya ganinta"? "Eh ba matsala zaka iya Bismillah muje tana kewayen bangaren gidana domin ban bari ta kwana cikin gidan ba domin yanzu rayuwa ba tabbas mutane ba abinda yarda bane kar naje da dare ta tashe tayi mana wani abu ta gudu shiyasa nasa aka kulle ta amma muje ka ganta" mi'kewa sukai suna zagayawa Musbahu na binsa yana mamaki a ransa saida yaje ya tabbatar kamar a mafarki ya ganta zaune akan tabarma tana karyawa ga bandeji a goshinta kai ya jinjina yana cewa "Ramatu dama nasan haka zata faru zargina ya tabbata" d'agowa Ramatu tai tana kallon sa tace "dama kasan haka zata faru meh? annamimi shiyasa ka dauko min 'yata gashi nan a garin biyoka na dauke ta wani d'an Allah tsinen ya buga min sanda jiya wallahi ka sani bazan ta'ba yafe maka ba Allah ya isa ce zata rabamu" da mamaki mai anguwa dake gefe a tsaye yace "amma dai tana da ta'bin kwakwalwa ko idan ba zararre ba babu wanda zai ri'ka magana kamar haka" tun Musbahu baiyi magana ba Ramatu tace "tsohuwar kace me ta'bin kai ba niba dama wa ya sako dakai harka dauka in banda yawon gulma wanda ya cuce ni nake wa magana ba kai d'an gayyar sod'i ba bai shafe ka ba dan haka kaja bakin ka kayi shiru idan kuma ka matsa zakaga tashin hankali in kuma akan wannan d'an iskan tuwon da kokon da kuka kawo min ne saika fad'a na biyaka donni ba matsiyaciya bace irinka😲" tofa wai ikon Allah sai kallo fad'an daya fi karfin ka akace ka mayar dashi wasa me anguwa mamaki ne ya rufe shi harya kasa magana sai ido da yake binta dashi lallai matar nan ba 'yar arziki bace da yasan abinda zata saka masa dashi kenan wallahi da bazai karbeta jiya ba saidai ta kwana a layi ko tasan inda dare yai mata.
Katse masa tunani Musbahu yayi da cewa "dan Allah me anguwa kayi hakuri ta sanadi nane da duk haka bata faru ba kai da baka santa ba kaine zakaji mamakin abinda datai maka wannan halin nata yana daya daga cikin butulci irin nata.................
Yana rufe baki Ramatu tace "tsohon ka ubanka Saboh shine butulu ba niba" kai me anguwa ya jinjina yana cewa "tabdijan Allah ya sauwake kada Allah ya kara hada ni da irin ki Musbahu ta tashi ku tafi" me anguwa ya fad'a cikin takaici mi'kewa Ramatu tai tana sake kai lomar tuwon tace "basai ka koreni ba wata tsiyar ce a gidan naka badan kana me anguwa anacin na haram ba 'beran masallaci ma bazai fad'a maka babu ba" daukar kofin kokon tayi ta karasa shanyewa kafin ta d'ure wainar a leda tana cewa "ga gidan ka nan na bar ma saika dafa ka cinye dama in banda kaddara me zai kawo ni garin balle nazo gidan ka wannan me ba'kin idon ne ya jawo komai" tari me anguwa bai sake yiba har suka fita suna tafe tana cin waina a layi ga kafarta ba takalmi kuma ko a jikinta gajiya Musbahu yayi ganin sai kallon sa mutane keyi yace "dan Allah kibar cin wainar nan a layi nan fa ba karkara bace ki bari sai munje gida" harararsa tayi "to ubana dama an fad'a maka idan naje gidan naka zama zanyi ba arziki ne ya kawo ni ba" bai bi takan maganar da take fad'a ba yaci gaba "haba Ramatu gaskiya baki kyauta ba tsakani da Allah yanzu Saida kika biyo yarinyar nan da kinyi hakuri ma da anyi musu hutu zan mayar miki ita.....................
Katse shi Ramatu tay "au haba jimin munafiki a gidan uban wa harda zaka mayar min ita to bana so na hutar dakai kuma kasa Allah a ranka ban yafe maka wannan ciwon da aka ji min ta sanadinka ba" ta karasa maganar tana sake kaiwa lomar waina Musbahu ikon Allah kawai yake kallo dan gaskiya fitinar Ramatu tafi karfin gaban kwatance.
"Kana jina kayi shiru ko? Amma bari na gama idan na d'ebo maka yan sanda zakai bayani".
'Dan kallon gefen da take Musbahu yayi yana cewa "ki kwantar da hankalin ki dama Lami ba daukota nayi dan na raba ta dake ba karatu zatai kuma tunda bakya so shikenan muje ki tafi da kayarki gida" washe baki Ramatu tai jin abinda yace tace "uhum d'an gari ba d'an garari ba muje yanzu ta had'a kayanta mu tafi kaima baka fi jin dad'i ba amma abu kamar naka kabi ka kanainaye saboda kwadayi da son zuciya" suna tafe tana masa bala'i mutane sai kallon ta suke suna mamakin a inda Musbahu ya samota.
Suna shiga gidan ta gansu zaune suna karyawa salati ta saki tana cewa "Lami ahh dole ki 'ki zama kauye kiyo birni inda zaki ci abinda kike so tabdijan to maza taso daga yau maganar cin abu mai dad'i ya 'kare zaki koma garin da kika fito kauye inda kika fi wayo".
Duk d'agowa dukai Lami data zaro ido waje cike da tsananin mamaki take kallon Ramatu yayin da mama tace "baiwar Allah wace ke daga ina me kike anan"? Hararar ta Ramatu tai tana cewa "a lallai kam samun gu harda zage zage ai ba dole saikin sanni ba wacce nazo gurinta ita ta sani".
Kallon Lami mama tayi taga ta sunkuyar dakai tana share hawaye wato inta fahimta babarta ce wacce Musbahu yake bata labari mafad'aciyar nan mai jawo fitina kara kallon Ramatu mama tayi tace "kiyi hakuri karaso ki zauna".
"Zama? Zama fa kika ce? Dama shi nazo yi banzo da niyyar ko kallon arziki nayi muku ba dan haka ki zuba min ido kawai shine naki kija bakin ki kiyi shiru" maida hankalin ta kan Lami tayi tana cewa "ke kuma dan ubanki da kika tsaya sauraron mu zaki tashi ki dauko kayan ki mu tafi ko saina fasa miki jiki da duka shashashar yarinya kawai".
Mi'kewa Lami tai cikin damuwa tana shiga d'aki hawaye na zata hado kayanta Naja'atu dake ta bin Ramatu da kallo tace "dan Allah ki 'kyale mana ita anan meyasa zaki raba mu".
Wani kallo Ramatu tayi mata "ke kuma asuwa kare da gudun layya ki bari nayi da tsofin ki dan ko kallo su d'in ma basu ishe niba kin gane".
Kuka Naja'atu ta fashe dashi cikin takaici tana kallon Ramatu daidai Lami ta fito da kayanta itama tana kuka tazo gaban Musbahu tare da durkusawa cikin kuka ta soma magana.
"Abba zan tafi dan Allah kuyi hakuri zamana daku idan na ta'ba muku rai ku gafarce ni ba lallai mu sake had'uwa ba a rayuwa amma ina fata kada ku manta dani zan tafi mama ku yafe ni" ta karasa maganar da tsananin kuka sosai kasa cewa komai Musbahu yayi sai kallo da yake bin Lami dashi cikin tausayawa tasowa mama tayi tana zuwa ta d'agota tare da share mata hawaye tace.
"kada ki damu Lami ki daina kuka kinji ai bamu rabu ba tunda zaki auri Alpha wata rana zaki dawo kusa damu mu zauna tare iya rai da mutuwa tashi ku tafi ki kasance me wa uwarki biyayya kada ki sa'bawa umarninta in Allah ya yarda zaki zamo cikin nasara".
Mi'kewa Lami tayi tana goge hawayen fuskarta da d'an murmushi kadan tace "nagode mama Allah ya saka da alkairi irin ri'kon da kika min".
Kai mama ta girgiza "karki damu kinji Allah ya tsare".
Karaso Ramatu tay tana fisgar kayan hannun Lami ta figeta tana cewa "ke dan 'kwal ubanki bariki nace ku nuna min kun bar ni a tsaye so'ko'ko ya 'kawar bora suna ta karanta miki kalaman tsiya wallahi baki isa ki aure a garin nan ba ko ke mayya ce uban Alpha zaki aura ba Alpha ba zaki zo mu tafi ko sai nayi miki duka" ta karasa maganar tana jan hannunta fuuuuu sukai waje, fashewa Najat tayi da kuka da gudu ta biyo bayan su ta rike hannun lami tana cewa.
"Dan girman Allah na roke ki kada ku tafi ki barta anan Lami ki tsaya".
Janta Najat keyi ta tirje ta'ki bari Ramatu ta tafi da ita cikin masifa Ramatu ta juyo tana cewa "ke sakar min hannun 'ya dan buhun ubanki ko tare aka haife ku"? Yau nake ganin mayyar yarinya zaki saketa ko saina ham'bare ki".
'Kin sakinta Najat tayi ta 'kankame Lami tana kuka sosai mama na kallon su itama sai hawayen take ta kasa magana.
"Dake nake kika tsaya kina kallo na ko nayi miki kama da gyatumarki ne kizo ki janye min wannan mayyar 'yar taki data hana mu tafiya" Ramatu ta fad'a tana kallon mama.
Musbahu yana daga zaune yace ""Naja'atu sake ta su tafi ki daina jawo wa mamanki zagi Lami zata dawo" Najat na kuka tana kallon sa tace "Abba bazan iya barinta ta tafi ba bana so tayi nisa dani mun saba" kai Musbahu ya girgiza cikin lallahi yace "kinga Najat nasani zata dawo ki bari su tafi" sakinta Najat tayi kamar gaske Ramatu na janta da gudu Najat ta kuma rungume ta".
Zaro ido Ramatu tai tana cewa "ke anya wannan yarinyar ba 'yar shan jini bace yau nake ganin jaraba zaki saketa mu tafi ko sai naci malafar kan uban ki" takaici ne ya kama Musbahu lokaci guda ya mi'ke yana zuwa gaban Ramatu yace "Naja'atu ki saketa kinji ki daina sa tana ja miki alkaba'i" "Abba dan Allah ka 'kyale na bisu garin su".
Ture hannunta Ramatu keyi tana cewa "uban wa zaki bi? Amma dai ba niba tabdijan lallai yarinyar nan baki da hankali garin mu zaki bimu? Aiko wallahi da sai kin yabawa aya za'kin ta" ta karasa maganar tana kallon Musbahu tace "kai marar zuciya kace ta sake min 'ya".
Kallon yadda Najat ke kuka harda shid'ewa take yayi kafin yace "Naja'atu ki saketa idan na isa dake idan kin dauke ni a mahaifi" d'agowa Najat tayi zatai magana Musbahu ya dakarta da ita "karki magana basai kince komai ba ki sake ta" ganin ta 'ki sakinta yasa Musbahu ya daka mata tsawa tare da rike hannun ta yana 'bam'bare ta da 'karfi daga jikin Lami kafin ya kalli Ramatu yana cewa.
"Ta sakar miki 'ya sannan ita ba mayya bace zaki iya tafiya".
Wata uwar harara Ramatu ta sakar masa tana cewa "dallacan rufe min baki duk bakai ne sila ba na fad'a mayya kuma gidan ka kai kaso nazo tunda ka ta'bo ni idan ka cika d'an halak daga yau baku ba Lami ko tunanin ta kukai ban yafe muku ba" tana fadin haka ta ja Lami fuuu suka fita yayin da tabar su Musbahu tsaye cikin tsananin mamakin ta lallai Ramatu batasan san halacci ba batasan me kyautata mata ba.
Da gudu Najat ta shige d'aki tana daukar waya ta kira Alpha bai d'aga ba a gigice ta sake kiransa nan ma dai no answer zata danna kira na uku taga ya biyo baya da sauri ta d'aga cikin kuka tace.
"Hello Alpha dan Allah ka taimaki Lami ga babarta nan yanzu ta zo har garin nan ta tafi da ita kayi wani abu dan Allah Alpha kada ka bari ta tafi da ita".
A firgice Alpha ya mi'ke tsaye daga zaunen da yake cikin mamaki yace "what ta tafi ko suna gidan naku"?.
"A'a basa gidan mu ta tafi da ita yanzu dan Allah kayi sauri karsu shiga mota".
"Ok shikenan karki damu bari naje" yana katse kiran da gudu yabar palor ya shiga bedroom yana dauko key din mota gabadaya ya fita hayyacin sa zai fita daidai yayan sa Auwal ya shigo saura kadan su gwaru da sauri Auwal ya matsa gefe yana kallon sa cikin mamaki ganin ya nufi mota yasa yabi bayansa yana cewa.
"Kai Alpha 'kalau kake ina zakaje"?.
Bai kalli Auwal ba yace "tasha zanje yanzu zan dawo".
Da sabon mamaki Auwal yace "tasha amma me zakayo kake irin wannan saurin haka"?.
Alpha na tada mota yace "wani abu zanyo Lami ce zata tafi garinsu zanje na dawo da ita".
Zaro ido Auwal yai "ka dawo da ita kuma akan me sai kace wanda ka aureta".
Alpha bai tsaya sauraron sa ba fuuu ya d'ebi mota da mugun gudu ya fita a gidan kai Auwal ya jinjina yana shiga cikin gidan ganin mom dinsu tsaye yasa ya karasa zaiyi magana ta katse shi.
"zancen me kuke da Alpha ina zaije naji kana hana shi"? Zama Auwal yai yana sauke ajiyar zuciya yace "wai budurwarsa Lami ce zata koma garin ku shine zai bita bansan me zaiyo ba gaskiya Alpha ya zauce da yawa".
Kai mom ta girgiza tana cewa "to nikam me zance Alpha yayi nisa a son yarinyar nan fatana da addu'a ta kullum shine Allah yasa rabonsa ce idan ya rasa ta a rayuwa bansan wanne irin hali zai shiga ba".
Mi'kewa Auwal yai yana shirin fita a parlon yace "bari nabi bayansa ko a mashin ne" mom batai magana ba har ya fita samun guri tai tana zaman jiran dawowar su.
A tasha ya samu Alpha yana ta duba motoci duk ya had'a gumi karasawa yai yana cewa "ka gansu ne ko sun tafi"? Kai Alpha ya girgiza "a'a ban gansu inaga saidai naje mu tafi da Najat ta raka ni garin idan ban ganta ba hankali bazai ta'ba kwanciya ba" ya karasa maganar yana yin wajen inda yai parking da motar da sauri Auwal ya bishi yana rike shi yace.
"A'a Alpha kada kayi haka dan Allah mom bazata ji dad'i ba ka bari mu koma gida saika fada mata nima zanyi maka rakiyar ka nutsu" shiru Alpha yai ya kasa magana Auwal dake kallon shi yace "shiga muje" kaiya girgiza "bazan iya tu'ki ba" "ok bani key din shiga mu tafi" bashi yai yana shiga Auwal ya tada mota suka wuce zuwa gida.
Har lokacin mom tana zaune a gurin ganin sun shigo da yanayin da Alpha yake ciki yasa ta fahimci basu sameta ba zama sukai mom dake bin Alpha da kallo tace "baku samesu ba"? Kai Auwal ya d'aga "eh mom sun tafi da binsu zaiyi amma na hana nace ya bari mu dawo gida yaje daga baya" kai mom ta d'aga tana kallon alpha tace "kaga auta na kayi hakuri in Allah ya yarda wannan yarinyar zaka aureta bari Abbanku ya dawo zan sanar masa sai musan me za'ai" shidai Alpha yana shiru baice 'kala ba Auwal daya mi'ke yace "ai mom wannan soyayyar tasu irinta ake so kaso mutum tsakani da Allah Alpha yana burgeni nima inaso ya aureta domin ta kasance farin cikin sace Allah ya tabbatar da alkairi" Amin mom tace tana sake kallon fuskar Alpha wanda ya shiga mood altering kawai baya cikin hayyacin sa dan girgiza kai tayi tana masa addu'ar samun nutsuwa a zuciyarsa
Ramatu kam suna tafe tana zazzaga mata bala'i har suka hau mota bata daina kumfan baki ba kowa a motar sai mamaki yake
Lami tari da bai kamata ba batai ba har suka sauka kowa a garin kallon yake ana ta tsegumin Ramatu taje ta taho da 'yarta haka suka shigo gida Baffah na zaune kan tabarma a kofar d'akinsa gefen sa Habu ne da Sabi'u suna hira sai ganinta sukai kamar an jefota ga Lami a bayanta ko kallon inda suke batai ba ta wuce d'aki karasowa gaban su tai tana kallon Baffah zatai magana sai kuma tana fashe da kuka tare da durkusawa.
'Dagowa Baffah yayi yana kallon ta tausayi da damuwa fal a ransa yace "Lami kiyi hakuri da irin uwar da kika samu ki dau kaddara ki jure wata rana sai labari kuma duk abunda zatai miki ki bita mahaifiyar kice kada ki sa'bawa umarninta kinji insha Allahu zaki samu nasara" kai Lami ta d'aga tana mi'kewa tace "nagode Baffah na gode da samun ubah na gari irinka me share hawayen 'yarsa".
"Karki damu Allah ya miki albarka" Amin Baffah Lami ta fad'a tana wucewa da kallo suka bita duk su ukun tsaki Habu yayi yana cewa "Wai dan Allah Baffah yanzu haka zamu zuba ido mu bar yarinyar nan tana cin ba'kar wahala kamar ba a gurin uwarta take ba gaskiya nifa babah Ramatu ta kaini bango zan dau mataki akanta".
Gyara zama Sabi'u yai "eh kayi gaskiya Habu dole mu gyara zaman gidan kamar ba mafad'i Baffah koda ace baka raye iyakaci kenan balle kana nan gamu amma ace gida ya lalace dole mu canza al'amarin gidan nan zamu zauna gabadaya yau da dare mu ji matsalar kowa mu gyara zaman mu kaji Baffah".
Kai Baffah ya d'aga "to naji zancen ku kuma na amince domin nima ina son hakan ina kaunar ganin ahlina cikin farin ciki ina son naga suna walwala musamman yarinyar nan Lami ina jin tausayin ta a raina har bansan yadda zan kwatanta muku ba na amince kuyi komai kun cancanta ku 'ya'ya ne na gari".
Kai Habu ya d'aga "shikenan Baffah idan anyi sallar isha zamu samu zama dukkan mu don magance damuwar gidan nan kowa ya fad'i abinda ke ransa".
"Kwarai Habu kayi gaskiya haka za'ai Allah ya kaimu daren" Sabi'u yayi maganar yana mi'kewa yace "lokacin dawo da dabbobi gida yayi Habu taso muje" tashi habu yai suna fita yayin da Baffah ya bisu da kyakkyawar addu'a cikin jin dad'in samun su dayai matsayin 'ya'yansa nagartattu.
Bayan sallar isha kamar yadda suka tsaya haka suka shigo suna shimfida manyan tabarma guda biyu Baffah ya zaune suma suka zauna ga Salamatu da Ramatu Lami na gefe kad'an da Baffah saida suka nutsu kowa yai shiru Baffah yace Sabi'u ya bud'e musu taro da addu'a.
Duk hannu suka d'aga Sabi'u yana jero addu'o'i suna