Showing 129001 words to 130249 words out of 130249 words
maganar".
Mi'kewa Ahmad yai yana cewa "sai ku taso ai kun tsayar dani tun d'azu da yanxu na manta da naje gida haba safga da yara ko safga da wahala".
"Wai kai 'kalau kuwa wannan fad'an fa me zakai a gidan idan ka koma ne inace yau ba hospital zakaje ba to maye abin saurin"?.
"Amma umma koba inda zanje nafa baro 'yar mutane ita kad'ai babu kowa gida kuma 'katon gida".
"Umhum dama nasan abinda zakace kenan Allah ya yaye maka rashin kunya" su Maryam ta kalla tana cewa "amma sai gobe zaku dawo tunda ba school" tun basuyi magana ba Ahmad ya zaro ido yana cewa "a ina zasu kwana mom? Had'e rai Aunty Safiyah tai tana cewa "a gidanka" kai ya girgiza yana cewa "a'a yau zan dawo dasu wadannan yaran banda headache babu abinda zasu d'orawa mutum" ri'ke ha'ba aunty Safiyyah tai zatai magana Alhaji Bashir ya rigata "ok kuje zuwa sallar magriba ka dawo dasu" yana rufe baki Ahmad yace "yauwa daddy haka nake son ji kai kumuje" fita sukai aunty Safiyyah na dariya tace.
"A'a ikon Allah sai kallo Ahmad umm" murmushi Alhaji Bashir yai yana kallon ta yace "kinga laifinsa ne yanzu lokacin sane ni nafada miki nan gaba zakigani da kansa zai kira waya yace suje gigin angwanci ne yake d'iban sa🙊 zai dawo daidai😂 yaro man kaza🐔 muma muyi mun sau'ke sai labari" ita dai Aunty Safiyyah dariya take harda tafa hannu saboda tuna baya 'kuruciyar Ahmad sak ta Alhaji Bashir.
Suna kan hanya harsun kusa gidan Ahmad yace "kunyi mata tsaraba"?😲 duk zaro ido sukai suna kallonsa ta mudubin motar ya kallesu ganin shi suke kallo yace "bakuji abinda nace bane"?.
"Amma yaya wacce irin tsaraba"? Maryam ta tambaya tana 'kureshi da kallo.
"Oh tambaya ma kike saboda kin manta? Ita lokacin da tazo gaida mom bata kawo muku chocolates ba to kuma yau zaku ramawa kura aniyarta ku mi'ko min kud'i"?.
"Ni dai wallahi ya Ahmad ban fito da kud'i ba" Maryam na rufe baki Amatu tace "balle kuma ni bansan sanda tazo ba tunda sannan ina garinmu".
"Ai kuma yarinyar haka zaki bayar ko 2k two kece wallahi baku isa mu shiga gidan nan da babu tsaraba ba dan haka zan arawa kowacce ku dubu bibiyu bari muje Sahat".
Zaro ido Nabilah tai "amma dai yaya banda ni"?.
"Ubanwa kika fi zane? harda ke man kuma kina komawa gida ki kar'ba min kud'ina agun Daddy" ya karasa maganar yana parking a bakin Sahat ya fito suma dole suka fito suna turo baki suka shiga ciki tare bangaren kayan za'ki haka ya ri'ka jibga mata chocolates🍬🍭🍡🍫 suna shan kallon sa dan wallahi sukam ba ruwansu ai matarsa ce🤨.
Saida ya gama sannan suka fito suna shigo mota suka wuce cikin tsokana Maryam tace "ya Ahmad nawa ka ara mana"?.
Hankalin sa nakan tu'ki yace "ina ruwanki" rufe baki tai tana dariya Amatu kam tunani take akan abinda ta gani dazu a laptop har suka 'karasa gidan bayan yayi parking sun fito jiransa sukai yai musu jagora suka shiga gidan tana zaune a parlor ta d'au kwalliya cikin less da glass cup🥛fal da had'add'iyar marada mai d'umi tana sha kai Maryam ta jinjina a ranta tace "uhm aure manya ji dan Allah😂" ke uban me naji kince😁"? Ahmad ya tambaye ta yana juyowa rufe baki tai tare da fatan Allah yasa baiji ba tace "ni ba komai nace ba" "ok yayi karasawa cikin falon sukai da murmushi akan fuskar Lailah tamike tana rungume Ahmad🙈 ta bashi kiss zaro ido sukai suna kallon juna Amatu da sauri ta juya musu baya murmushi ne ya su'bucewa Maryam kawai ta girgiza kai Nabilah kuwa ta tsayar da idonta tarrr akansu tana kallon yadda ake soyayya😝.
Sakinsa Lailah tai tana kallon su tace "sannunku da zuwa sisters sai yau kukazo ku zauna karasowa sukai suna zama Ahmad kam ciki ya wuce Lailah kuma tai hanyar kitchen taje ta had'o musu kayan ciye-ciye da shaye-shaye ta kawo musu tana cewa "bismilllah kuci bari nazo" bin bayan mijinta tayi ta basu guri su d'an sake.
Tana barin parlon Maryam tace "tofa bari nai gulma ji dan Allah matar nan ko kunyamu ta wani rungumeshi shima harda kara matseta a jikinsa yana zullo mana ido😂🙊".
Dariya Amatu tai tana cewa "ke kuma sa idon naki haryai yawa laifin waye dakin juya musu baya kamar yadda nayi shikenan da kin hutar da kanki bakiga komai ba balle abun ya dameki".
Ta'be baki Maryam tai tana cewa "Hum'um wallahi bazan juya musu baya ba ni nace su rungumi juna🙈 ko yanzu suka fito suka sake runguma zan kalla".
Murmushi Amatu tai tana girgiza kai ta d'au apple guda daya tana ci bata sake magana Maryam kam ledar tsarabar da sukayowa Lailah ta d'auka tana d'ebo chocolate da sauri Nabilah tace.
"Aunty Maryam kar yaya Ahmad ya fito ya sameki da chocolate fa kinsa halinsa"?.
Bud'ewa Maryam tai tana cewa "wallahi saina sha garama kiyi shiru🤫".
"A'a Maryam karfa yazo yana gwangwazarki bazamu iya cetonki ba" Amatu ta fad'a tana kallon kofar shiga part d'in Ahmad.
"Allah Amatu kome zaiyi saina sha inace dama aro yabamu kud'in? To a nawa 'bangaren na d'auka" tana rufe baki taga sun fito ya sanya kayan shan iska jesi mai adon fari da blue d'an kau dakai Amatu tai tana cewa "ya Ahmad amma yanzu zaka mayar damu"?.
Dakatawa yai yana kallon ta yace "na mayar daku ina"?.
Kai lallai jishi da wata magana kamar baisan me nake nufi ba "nace na mayar daku ina amma badai gida ba"?.
"Eh gida".
"Sai anyi sallar magriba bakuji me Daddy yace ba yanzu lokacin Wasa ne".
Cikin alamun tambaya Amatu tace "wasan me"?.
"Dame kika ganni? 'kwallon qafa zamuyi idan kuna sha'awar kallo ku biyomu"😝 yana fad'in haka suka fita a falon shida Lailah dake ri'ke da ball a hannunta kai Amatu ta jinjina tana cewa.
"Uhm yaufa nake ganin duniya Maryam kina jinsa fa abinda yake cewa wai mu bisu muje muyi kallo muga me"?.
"Oho masa Allah ya Ahmad d'in nan wani lokacin idan yai wani abu yadda kikasan na kamashi da duka haka nakeji amma fa yin auren nan ya sake susutar dashi gara mu lalla'ba a jima ya mayar damu gida salin alin karatun fatiha aiko bazan sake xuwa ba sai nan da kamar shekara".
Dariya Amatu tai "shekara dai Maryam tab fad'a kike amma dai sannan saidai kizo suna ko"?.
Zaro ido Maryam "su me? suna fa kikace ya Ahmad da d'a? Uhmmm wai ranar za'aga girgiza😛".
"Meyasa kika ce haka"?.
"To Amatu kina ganin yadda yakeyi a gabanmu inaga su kad'ai ne a gidan"?.
"Maryam sa idon ya isa haka ki kyalesu lokacin sune".
"Hum lokacin sune kam tunda gashi nan harda fita 'kwallon ball nikam bari nayi kitchen dan gaskiya wannan abincin data kawo mana ya huce wani zan d'ebo" Maryam ta karasa maganar tana d'aukar plate din tai hanyar kitchen Nabilah kuma ta mi'ke tana fita kallon qwaqwaf suka bar iya Amatu a falon.
🏕️'KAUYE🏕️
Kamar yadda aka sanyawa bikin Dauda da Indo lokaci haka ne ya faru tafiya sannu sannu kwana nesa yau alkawari ya cika an d'aura Indo ta zamo amarya a gidan Daudansy😝 Asabe kamar tai hauka ranar gashi Bahijjah bata gida wai tabi Iluh zata gano garinsu humm Asabe tayi kuka tayi ba'kin ciki har saida hawan jini ya hauta haka tana ji ana gani an kankatsa biki akai hidima kwana biyu da d'aurin auren Dauda yad'au amaryarsa suka tafi Osun tare abinsu cas haka 'bangaren Dalah tayi farin ciki da wannan rana ta godewa Allah ta qara yanzu bata da damuwa ta daina kwana cikin fargaba da halin da Indo d'in take yanxu tasan zata koma rayuwar 'yanci.