Showing 6001 words to 9000 words out of 130249 words

Chapter 3 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17581

Kar dakai Asabe tai tana dariyar cin nasara zata hada bom yau a gidan tace "au wai dama bata fad'a maka ba ta fita? Ganin bai magana ba ta d'ora "gaskiya malam bakai dacen mace ba ashe dama ba tambayar ka take ba Amma kullum saita fita" "kullum ina take zuwa"? Balarabe ya fad'a bud'e baki Asabe tai zatai magana Dala ta shigo da sallama da kwano a hannun ta Wanda da sauri Asabe tace "ka gani ko maula taje anguwa ta na nunawa mutane kasawar ka cewa baka iya rike mu baka iya ciyar damu gaskiya malam kai maganin ta kullum fa haka take wannan yawon kamar taci kafar kare".

Bai saurari Asabe ba sai Dala daya zubawa na mujiya kafin a tsawace yace "Dala uban waye ya fasa a gari na nemi Indo har yanzu aka goranta min a majalisar zaman mu ki fad'a min"? Da mamaki sosai Dala tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un malam wallahi ba sani ba" a hasale yace " baki sani ba? Karki maida ni wani gailo man an fad'a miki cewa duk wani siddabu da kike a gidan nan da asirce asirce ban sani ba zuba miki ido nai dake da matsiyaciyar 'yar taki naki domin gadon ki tayo gadon tsiya da bakin hali ina Indo din itama dan kambun ubanta? Ke Indo kina ina"?.

Da gudu Indo ta fito daga d'aki tana sharar hawaye ta tsuguna a gabansa jiki na rawa wanda asabe a nata 'bangaren ji take kamar ta taka rawa dan murna burinta ya cika lallai Marka aikinta mai kyau zata sake dagewa harsai ta fitar da Dalah daga cikin wannan gidan ya zama daga ita sai yayanta ta wanda biyar ta tsoma goma....................


Tunanin tane ya katse jin tsawar da Balarabe ya daka yana kaiwa Indo duka yace "dan bantan uban ki dan darar ubanki dan 'kashin singallin uwarki yau saikin barmin gida na kore ki bani bake har abada Indo ki kama gabanki'.
Kukan takaici da damuwa Indo ta fashe dashi tana sake durkusawa sosai ta soma bashi hakuri da batasan laifin datai masa ba ace uba na garine amma ya tsani yarsa ya rikajin duk duniya ba wanda baya son gani sai ita, "baki ji me nace bane zaki tashi a gabana ko saina fasa miki baki" yai maganar yana kai mata harbi da kafa jan kujera Asabe tai tana zama tare da zubo musu ido bakinta har kunne tace "malam kayi hakuri ka kyale ta tana mace idan ka koreta yanzu ina zataje duniya zata shiga karshe ta dirko cikin shege kuma ta dawo ta haife maka shi a gida" a zafafe Balarabe yace "Allah ya sauwake saidai ta nufi gidan marina amma ba gida ba dan ni na sallama ta" "to yanzun dai kayi hakuri na fanshe ta da sharadin zata rika yi mini duk wani aikin gida kama daga shara wanki wanke kwanuka aikin abinci kai inaso Bahijjah ma ta huta Indo ta dawo fita min da abincin sayarwa ta" ta karasa maganar tana sakarwa Indo muguwar harara.

"Wannan shi kike bukata"? Balarabe ya tambaya jiki na mazari d'aga kai Asabe tai "eh hakan ma yayi daga yau ka zama sarki ni gimbiya Indo da Dala bayin mu ko me kace"? Da sauri ya amsa mata "eh na amince na amince ba damuwa dama ai bayin ne aikin jakuna ne ya dace dasu" murmushi Asabe tai yauwa bari a fara yanzu ke Indo dauki bokatin san kije yanzu ki kawo min ruwa ke kuma Dala saiki dora mana tuwo".

Cikin takaici Dala tace "baki isa ba Asabe kinyi kadan a gidan nan kikazo kika sameni dan haka baza ki min mulkin mallaka ba" zaro ido Asabe tai tare da fashewa da dariya tace "au ashe har yanzu da d'an saurin karfin ki Dalah lallai kam na jinjina miki" sai kuma ta hade rai cikin tsawa tana kallon Indo tace "ke kuma ubanki kike jira da bazaki tashi ki fara abinda nace miki ba idan kin debo ga wankin Bahijjah can ya na jiran ki" mikewa Indo tai tana sake goge hawayen fuskarta tadau bokiti tana yin waje.

"Malam gaskiya nifa ban gane anyi gabas da kare ya zanyi magana Dala ta musa min kuma kana jinta baka dau mataki ba ko tsoron ta kake domin labari yazo min idan bana nan nayi tafiya wai wannan abar mai kamar ta'barya har ka zauna tana maka masifa to wallahi bazai yiwu ba gaskiya da sake idan baka gyara ba zan karbe kudade na dana baka kake juyawa" jin barazanar da Asabe ke masa yasa cikin rarrashi yace " kiyi hakuri hakan bata ta'ba faruwa ba karya ake min har nine zan tsaya sauraron wannan abar kibar wata magana kawai ke kadai nake so da Bahijjan ki" dariya Asabe tai "da gaske kake"? Cikin nuna an gama dashi an shanye shi yace "kwarai Asabe da gaske nake " hade rai Asabe tai tana cewa "to ni ban yarda ba baka nuna min a zahiri ba saika saitawa wannan agwagwar matar taka hanya idan kuma ba haka ba daga yau baka sake mora ta sisi kaji na fad'a maka" jiki na rawa cikin tsawa Balarabe yace "ke wai Dalah wacce iriyar bulkuma ce gidahuma bance ki wuce ki fara aiki ba so kike ki silar auren ki yanzun nan kinsan halina sarai ni ba ba'kon ki bane" a damuwance Dalah ta wuce ta barsu a gurin da harara Balarabe ya bita yana cewa "ke kam Dalah kinyi asara mace sai bakin hali yadda fuskar take haka Zuciyar take wuluk da baki da mugun hali nayi da nasanin auren ki Dalah dole ce tasa nake zaune dake amma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe" yana fadin haka ya fita yana sake babbaka fad'a kamar bazai ta'ba shiru.


Yayin da Asabe tasa Dalah a gaba tana sheka dariya kamar zata kifa harda hawaye tace "to ya kikaji irin salon nawa Dalah kenan na fad'a miki baza ki iya ja dani ba bakisan wace ni Asabe ba suna a kawai kikeji amma daga yanzu ina fata sunan ya zauna a Zuciyar ki har abada domin nayi alkawarin saina 'kuntata miki daga yanzun kin fara shan dandanon azaba dake da 'yarki a hannu na mu zuba mu gani waye zai nasara saina kaiki kasa" dagowa Dalah tai tana kallon Asabe da jin maganganun da take fad'a saidai batai mamaki domin tun lokacin da Balarabe zai aureta mutane ke tausaya masa suna koka mata cewa zai auro mata masifa Asabe tsiya ce mai lasisi gashi kuwa abinda ake fad'i ya tabbata.................... "Meye kike kallo na maiya"? Muryar Asabe ce ta katse mata tunani danne damuwa da bacin ran dake cin ta Dalah tai tana kankaro murmushi tace "Allah ya shirye ki domin ke abar tausayi ce daga ranar da duniya ta juya miki baya zaki bayani" dariya dariya Asabe tai "ahayye nanaye yau ake yinta lallai kam Dalah kina lokacin yanzu har kece zakice kina tausayin wani? Ta fad'a tanai mata wani kallo na tsantsan rashin mutunci Sai kuma ta sake bushewa da dariya tana cewa amma kinci abinci a kanki shin kina duba mudubi kuwa kodan ina za'a samu darajar mudubi bayan komai bai wadata ba har kice zaki wa wani gori tirrrrr anji kunya 'yar ba'ki ai labari ya same ni tun bayan na auri Balarabe cewa ke maiya ce yar mayu jikar mayu iyayen ki korar maiya akayo musu daga wani tsinannan kauye suka dawo nan suka addabe mu wato da dare baban ki har kura yake zama ko🙊? Daidai Indo ta shigo da bokatin ruwa ta dire asabe dake binta da kallon banza tace bance kayan Bahijjah zaki wanke ba yar gwana jikar maiya Asabe take Aiko mata da mugayen kalaman da take fad'awa uwar ga tsinuwar Balarabe a kanta kuka kawai take kamar ranta zai fita bangare na Zuciyar na adduar Allah ya kawo mata sauyi cikin rayuwarta.


Amatu na zaune a kofar d'akinsu tana duba wani littafin addua Jamila na gefenta tana gyarawa A'i kayan miyar abincin saidawar su ta kalli yadda Aisha ta shigo jikinta duk a jike shakaf da gumi alamar daga aikatau take tana haki da sassarfa ta iso inda suke tana zama sai haki tace cikin tausayawa Jamila yace "sannu Aisha Allah dai ya rufa mana asiri ya kawo mana canji a rayuwar mu" murmushin karfi hali Aisha tai tana cewa "amin Amatullahi me kike dubawa ne"? Murmushi Amatu tai batare data d'ago ba domin ita ba ma'abociyar 'kure mutum da kallo bace tace "sannu Aisha kiji yadda kike haki fa dan Allah idan aiki yafi karfin ki kina ragewa wannan gajiya fa da kuke dibawa jikin ku zata tambaye ku sai lokacin tsufa" fuskar Aisha cike da damuwa tace "to ya zanyi Amatu rashi ne yasa nasan da baban mu nada shi duk haka bazata faru ba" sauke ajiyar zuciya Amatu tai tare da jinjina kai tace "haka ne amma dan Allah a rika ragewa aikin na yawa" dariya Aisha tai tana cewa "shikenan babbar aunty za a kiyaye kaka mai kamar uwa hajiya Hauwa's mai zamani" dariya sukai Amatu na mata hararar wasa tace "meye na Kiran suna na haka babu ko dan kara"? Har lokacin fuskar Aisha da fara'a tace " kakar mu na tuno duk da bamu Santa ba Allah sarki hajiya Hauwa naji mutuwar 'yar tsohuwar nan" maida hankalin ta kan littafi Amatu tai tana cewa "to ta zamuyi wanda ya fimu sonta ne ya karbeta duk wata kulawa da kauna da zamu gwada mata bayan nasa ne shike iko da kowa" sauke ajiyar zuciya Aisha tai tana kallon Saude data fito a d'aki tana mata kallon mamaki na ke kuma yaushe kika shigo mikewa tai tare da nufar ta yayin da Jamila ma ta mike tana daukar kayan miyar ta tafi gidan ni'ka.

Shiru Amatu tai tana kallon kowa da komai gida babban gida amma yanayin tsarinsa da gyara gashi babanta nada dangi amma duk laifinsa suke gani wai ya zauna kara zube ba sana'a yasa rashin zuciya gashi ya tara iyalai shiru tai ta nutsa cikin tunani lokacin da baban ta yaje gurin yayansa ya bashi kud'i zai biya mata ta zana jarrabawa ya hana dan rufe ido tai maganganun da kawu Ilyah ya fad'awa babanta na mata yawo a kunne daga lokacin data tambayi kudin jarrabawar.

Cikin mamaki shigowar malam habu ganin Amatu zaune tana kuka yasa ya karaso da sauri yana d'ago ta tare da goge mata hawaye cikin lallahi yace "Mamana kukan me kike ba na raka ki har makaranta ba meyasa kika dawo" Amatu na shashshekar kuka tace "baba wai malamin yace ban bada kud'i ba wannan shekarar ma bazan zana jarrabawa ba saidai na jira yan ajin baya" dafe kai malam Habu yai yana kallonta yace "kiyi hakuri Mamana kinji taho taso muje gurin yaya kila yau tunda yaga dake yaji tausayin na ko aro ya bani kudin nan na biya miki" rike hannunta yai suna fita daga gidan suka shiga dayan daya kasance gidan yayansa da sallama ya samu matansa zaune suna gyaran kaji gefe ga yara can suna ta fama da kan saniyar da sukai dafgensa abu yaji ya tsirga masa mai d'aci amma ya daure bayan sun gaisa yace "ko yaya na nan"? Da'kyar suka bashi amsa a wulakance ganin ko shi yayan nasa Ilyah yadda yake masa kenan yana tutture shi babbar matar ce ta budi baki tace "eh kamar dai yana ciki karasa ka duba".

"Karasa ka duba"? Malam Habu ya tambaya cikin mamaki yana juyowa ya kalleta a gadarance tace "eh haka nace ko kana tunanin muna aiki akwai wanda zai tashi maka wahala bayan kai kazo nema" ran malam Habu a 'bace yace "Bara'atu kinsan abinda kike fada kuwa" wani kallo tai masa tana cewa "ni nasan abinda nake cewa domin ni a hayyaci na nake ina ci ina sha banda matsalar komai saidai azo inuwa ta a ra'bu a fake kai kuwa fa tun karayar arziki ta same ka kullum kana yawon maula a gidan kamar duk kauyen nan mune muka fi kowa arzik..................


"BARA'ATU!!!😡 Malam Habu ya fad'a cikin tsawa wanda hatta yaran dake zaune gefe suna cin nama saida suka tsorata nuna ta yake da yatsa idonsa yai ja na bacin rai yace "Bara'atu ki iya bakin ki a kaina wadatar da mijin ki yake dashi baki isa kice zaki wulakanta niba domin uban mu daya dashi baki San wahalar saba kawai kin ganshi a saurayin sa kika aure shi kuma shine kike neman zagi na"? Tabe baki tai tana cewa "eh ai isa nai" malam Habu zai magana suka jiyo muryar Ilyah na cewa "ke Bara'atu ke dawaye ne anan nake jin hayaniya haka"? Mikewa tai tana shiga d'akin sa ta dade kafin ta fito tana sake wuce su ta shiga wani wuri da alama dakin ajiyar abinci ne sai gata ta fito da daurin leda tana cewa "dama maula ce abinda ya kawo ku shi kanshi ya fahimta gashi nan garin kwaki ne yace a baka koda gishi kwa tsama kuci" ta karasa maganar tana aje masa a gaban sa kafin ta koma ta zauna.

Cikin fushi malam Habu yai bol da wannan ledar garin ya tarwatse yana huci yace "ai dama d'an talaka bai iya samun waje ba wato ke harkin manta irin ke wahalar da kika sha a gidan ku yanzu kin samu guri har kike gorantawa wani meye a gidan naku wacce tsiyar ce fad'a min" mikewa Bara'atu tai ta fara masifa ta zazzaga bala'i irir iri wanda yasa sauran yan matan gidan fitowa da sauri Nafisa ta karaso tana cewa "wanne d'an hauren ne ya ta'bo ki umma? Gaskiya mu mun gaji da wannan maula da ake zuwa mana hakan ma bai isa sai anyi cin mutunci to wallahi bazamu dauka ba"..............


Tana rufe baki taji saukar zazzafan mari a fuskar ta Wanda yasa ta fasa Kara tana durkusawa a gurin ta fashe da kuka da sauri Ilyah ya fito wanda duk abinda ake da yana ji bai fito sai yanzu da aka mari yar lelensa cikin fad'a ya soma magana.

"Wai Habubakar wanne irin wulakanci ne wannan ka zagi mata ta ka goranta mata ka shigo gidana kai tsaye ba neman izni na duk hakan bai ishe kaba saika marar mun 'ya to yanzu kam ya isa haka na gode zaka iya tafiya ba an baka abinda kazo nema ba" a fusace malam Habu yace "yaya Ilyah yau ni kake fad'awa haka a gaban matan ka da 'ya'yan ka nagode kuma ka nuna min iya matsayi na" jan hannun Amatu yai suka fita yana fita Bara'atu taja tsaki tana cewa "wallahi ko kadan bakai sa'ar dan uwa ba haba inaga da baka fito ba saidai a debi gawata yadda ya zuciya ya hauro dinnan tsaki Ilyah yaja yana huci yace "ni na rasa me yake damun sa saikace nine dora masa talaucin duk yabi ya addabe ni tunda karayar arziki ta same shi ya hana naji dad'i amma zanyi maganinsa kodan yanzu ma alhamdulillah nasan shi da zuciya watakila bazai sake zuwa gidan nan ba ni kuwa haka nake so kuyi sauri ku gyara kajin nan a dafa su in anjima zanyi manya baki wanda nake sarar kaya a hannun yan kauyukan nan nake sarar musu daga binni zasu zo dan Allah ku tsara abincin nan sosai" ya karasa maganar yana komawa d'aki ta tafar sauke Habiba amaryar Ilyah batace saidai tana mamakin bakin hali irin na Ilyah ace kana da wadata d'an uwanka baida shi Amma saidai ka wadata bare ka barshi yana yarfe gumi yana aunar abinci a shago da kasuwanni Allah ya sauwake ta fad'a a ranta tanajin takaici da nadamar aurensa haka Nafisa ta share fuskar yatsunsa kuwa d'as a fuskarta sun fito hakan yasa ta dau alkawarin daukar fansan.

Malam Habu na fita daga gidan Ilyah yai nufin zuwa gidan dayan yayan nasa Sabi'u yai sa'a kuwa ya same shi a kofar gidan sa zaune mutane sun kewaye shi irin masu neman na kayan miyar nan ganinsa cikin jama'a yasa bayan yayi sallama sun gaisa ya nemi su d'an ke'be can nisa da mutane suka tafi karkashin wata bishiyan kuka malam Habu yasan da kamar wuya amma zai gwada kokarinsa yana fatan yakai nasara "ina jinka Habubakar ya akai ne na ganka duk a hargitse"?.

Ran malam Habu a bace yace "yanzu tsakani da Allah yaya abinda matar yaya Ilyah tai min tayi daidai yanzu shi daya goya mata baya bayan yanajin irin cin fuskar datai min ya kyauta min kenan ya kyautawa Bappan mu"?.

"Meya faru ne Habu meya hada ku me kaje yi gidan"?.

A hankali cikin nutsuwa malam Habu yai masa bayanin komai kai Sabi'u ya jinjina yana cewa "ai indai Bara'atu zatai yafi haka ba kirki gareta ba ta maganar kane dan talaka bai iya samun waje ba amma babu komai karka damu za'a biya mana ina maman namu take nawa ne kudin ai na fad'a maka duk wata matsalar ka idan ta tashi ka rika zuwa kana fad'a min ka kyale Ilyah indai ba harkar zumunci bane yanzu ka wannan maza da sauri kaje ka biya mata" karba malam Habu yai cikin jin dad'i da kaunar yayan nasa Wanda yake share masa kuka a duk sanda ya kawo korafin sa bai ta'ba nuna gajiwa ba ya mike yana sake masa godiya da fatan alkairi kafin yaje ya rike hannun Amatu suka wuce da kwarin gwiwa ya mayar da it's makarantar ya biya mata komai sannan ya shiga cikin gari dayake makarantar ba a garinsu take ba kusa da kauyen sune saida aka tashi ya biya ya dauketa suka tafi gida.

Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tare share hawayen fuskarta bayan ta dawo daga tunanin da take ta sani mahaifin ta mutum ne na 'kwarai mai kyawawan halaye sannan ya na son farantawa ahlin sa amma babu ta gama mamaye shi sauke kanta kasa tai ganin Binta ta zo wuce wa dan kada taga cewa kuka take, Amma me tuni ta hango ta tun daga nesa Saida tazo saitin ta tace "Amatullahi me akai miki kike kuka"? Jin tambayar datai mata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login