Showing 27001 words to 30000 words out of 130249 words

Chapter 10 - ME KAMAR SARKI

  

04 Oct 2024

17616

yazo ya fesa anan cewa kwarton ma tsoho ne yaje gurin yarinyar da bata fi jikarsa ba ashe ya yaudare ta a kasuwa duk sati yakan sayi lemo da ayaba ya bata ita kuma yarinyar tallar dankali take shiga kasuwar duk sati ya dad'e yana bata kayan kasuwa sai ranar yace mata yana son zasuyi magana tace masa to suka fita daga kasuwa sai yace suyi nesa da mutane yake ta janta har suka wani sabon gida da ake gininsa ba'a karasa ba suka shiga nan ya bata kud'i mai yawa yake ta janta da hira idan tace zata tafi saiya hanata har akai kiran sallar magriba karshe dayaga ta damu ta tafi gida saiya nuna mata abinda yake so nan fa yarinya tai tsalle ta dire tace batasan da wannan maganar ba da yaga tana shirin gudu ya kamata da komawa yarinya d'anya shakaf taga za'ai mata zarrar data zarce ma tunanin ta ta fara zunduma masa ihu tana kururuwa nan mutane suka taro aka tara masa gayya 'kiii aka fito dashi sai kare fuskarsa yake matasa suka d'ebo makamai suna cewa a barsu su kashe shi da'kyar aka tattare su aka hana su aka jashi gaban mai gari nan akaita shari'a akaci tararsa kud'i haka ya tafi garin su jikinsa a sali'be yana d'ari d'arin shiga cikin mutane amma da yake yafi kowa idon akuya ganin anyi burus dashi ba'a nuna masa ansan komai ba saiya ware yaci gaba da fella tsiyar sa kunga wannan shi za'a Kira da yayi new ba malam Habu ba" yana kaiwa nan yai gaba.

Da ido suka bishi cikin mamakin dawa malam Habu yake wannan maganar kafin Tanko yace "kai Mudi kasan da wa Malam Habu yake wannan maganar"? A fusace Mudi yace "ban sani ba meyasa baka tambaye shi ba ka bari ya tafi sannan zaka zo ka dame ni' yana kaiwa nan ya kad'e rigarsa fuuuu yabar gurin da harara Tanko ya bishi yana cewa "jimin tsinanne wato harda ni zakai fushi? Aiko saina nuna maka na fika hauka" kowa na jinsu yai shiru domin sun fi kusa haka Tanko yai ta balbalin bala'i har ya gaji ya 'kyale.

Dutse mopal Base
Satin su Binta biyu take shirin komawa domin ta huta har tayi 'kiba ta murje suna zaune da 'kaninta Bashir ranar da zasu koma gida take ce masa.

"Bashir dan Allah ina da bukata a gurin ka" kai Bashir ya d'aga yana cewa "meya faru fad'a min Allah yasa ina da damar dazan magance miki matsalarki".

Bayani Binta ta fara yi masa "dama matsalar akan malam ne Bashir dan Allah ka taimaka masa da jari wallahi malam yana cikin damuwa da fuskantar 'kalubale a kauyen nan bai isa nuna wani abu da sunan nasa ba komai ya ta'ba a narke ya rasa inda zaisa kansa hatta yarinyar nan Amatullahi tana cikin damuwar mahaifin ta kullum tana cikin kuka da fad'a min cewa taya zata taimaki babanta wannan dalilin yasa nazo dan Allah Bashir ka taimakawa malam".

"Shikenan aunty kada ki damu insha Allahu za'a bashi jari malam Habu mutum ne na 'kwarai lokacin da kukazo banji dad'in yadda na ganku a rame ba saidai wannan bayanin da kikai min na gamsu dashi zan baki dubu d'ari ki tafi masa dashi a cikin kudin da zanyi zakka ba fitar ki bashi dubu hamsin ki dauki dubu talatin ki bawa kishiyoyin ki dubu goma goma zansa a mayar dake gida a mota zan fad'awa Safiyyah zata zuba kayan abinci a motar ki tafi muku dashi nasan zai ishe shi kice zansa a kawo masa kayan da zai ri'ka saidawa daga baya hakan yayi" sosai Binta tai masa godiya cikin tsananin farin ciki harda hawaye Bashir ya nuna mata babu komai.

Harta mike zata tafi sai kuma ta sake zama tana cewa "karka gaji dani dai Bashir ka taimaka kasa Amatu makaranta tayi karatu yarinyar nan nason tayi karatu babanta ma naso amma rashin kud'i ya hana tun daga secondary batai gaba ba ko zata samu"?.

"Ba matsala aunty kada ki damu ina takardun ta"?.

"Suna nan na taho dasu a jakata" "ki kawo min yanzu na duba idan zan fita zanje dasu a yanko mata fom ta fara zuwa wanne bangare take son karanta"? "Ban sani ba saidai na tambaye ta" "ok shikenan babu damuwa ki kawo min takardun yanzu zan fita" to tace tana mikewa ta fita cikin jin dad'i taiwa Amatu albishir din abinda Bashir yai musu da jarin dazai baiwa malam Habu tsaba farin ciki Amatu fashewa tai da kuka tare da kifa kanta akan cinyar Binta.

Shafa bayanta Binta keyi cikin lallashi tace "kiyi shiru kinji ai a tunani na farin ciki zaki ba kuka ba"? 'Dagowa Amatu tai tana cewa "umma kukan farin cikin nake nasan cewa yanzu shima baba zai samu abin kansa ya rike mu abar yi masa gori da nunensa" kai Binta ta d'aga "eh haka ne Amatu kuma nayi magana da Bashir akan ci gaba da karatun ki yace na kai masa takardun ki zai fita dasu ya miki rijista ki fara zuwa da haka anan zan barki" da mamaki Amatu tace "yanzu zanyi karatu kenan nima zan samu ilimi gaskiya naji dad'i saidai bazan juri sai anyi hutu na ri'ka zuwa ganin ku ba" "a'a Amatu zaki jura dan Allah ki tsaya ki nutsu kiyi karatun ki" "to shikenan nan umma zanyi" "yauwa Amatu Allah yai miki albarka tashi muje ki masa godiya nima inaso zanje miyatti zuwa la'asar na tafi" mi'kewa tai suna fita a d'akin domin suje tayi masa godiyar.


Yana shirin fitowa daga part din nasa suna shiga dan haka yace su karaso main parlon sunyi maganar zama sukai Amatu na kasan carpet da fara'a Bashir yace "Amatullahi kina son karatu ko"? Kai ta d'aga "eh ina so Abba" "ok kada ki damu insha Allahu yau zan fita da takardar ki basai gobe ba zan yanka miki fom ki fara karatu kinji" "to Abba nagode Allah ya saka da alkairi" Amin yace yana shirin mi'kewa ya kuma jefa mata tambaya "wanne 'bangare kike son karanta likita 'yar jarida lauya teacher ko business zaki karanta sauke ajiyar zuciya Amatu tai tana kara yin kasa da kanta ganin batai magana ba yasa Binta cewa "Amatu dake fa ake me zaki karanta ki za'ba yana sauri zai tafi wajen aiki" d'agowa tayi tana kallon mahaifiyar ta sannan muryarta cikin sanyi dan batasan a yadda zasu dau maganar ba tace "SOJAπŸ™Š" "a'a kamar ya soja kuma shine amsar"? Binta ta tambaya tana kallon Amatu kai Amatu ta girgiza tana cewa "karatun bangaren aikin soja zanyi shine buri na" ba Bashir da Binta ba hatta Safiyyah dake gefe kan dinning ita da yaranta sun sha mamaki basuyi tunanin haka ba a d'ari kowa ya zaro ido waje yana kallon ta Nabilah har 'kwaruwa tayi wajen cewa "soja kuma Amatu"? Maryam tace "tabdijan a banza zakije a kashe ki nikwa ko hauka nake ai bazanyi aikin soja ba koni namiji ce balle ina mace" dariya Safiyyah tayi tana kallonsu tace "ra'ayi kenan cin d'an wake da diga kunga laifinta ne abinda ke ranta ta fada" raf raf sukaji ana tafi duk kallon gurin sukai Ahmad ne tsaye da murmushi a fuskarsa yace.

"Haka nake son ji jaruma ta gaskiyar aikin soja babban aiki ne kuma babu wanda zai hana ki cika burinki ni nan da kike gani zan tsaya tsayin daka naga fatan ki ya samu nayi matukar jin dad'in haka Amatullahi kuma na jinjina miki da hannu dubuπŸ˜…" "uhm haka dai ka iya matsoraci ka refaye baki sai zuba zance kake kamar gaske bayan kai aka fara yiwa tayin aikin sojan ka 'ki wai tsoron mutuwa to yanzu fad'a min bakaji kunya ba ga mace a gaban ka tana cewa ita kuma aikin take so"?.

Cikin fuskewa Ahmad ya maze tare da cewa "mom ai ba tsoro ya hana nayi ba kawai aikin ne bana so kullum mutum yana ciki tashin hankali da aiki kamar wani agogo sannan bana son nayi nisa daku" "humm ba wani ka iya yawan gulma ai ya kunun ni'ka yanzu ba hospital zakaje meyasa ka dau wannan"? Ta fad'a tana nuna jakar matan dake hannunsa d'an hade fuska yayi yana cewa "ai kuma mom baza a duba wannan ba nayi mata alkawari ne kuma idan na karya babu kyau ko a addinance bayan haka zataga kamar ba sonta nake ba kawai ina mata yawo da hankali ne" "ok yayi na gaji da surutun zaka iya fecewa kullum kana sanye da farar riga kamar wani fatalwa" dariya yayi yana kallon farar rigar uniform din doctor din dake jikin shi yace "martaba ta kenan ni shine buri na shiyasa itama nake so ta cika nata burin domin nasan da d'aci ka nemi abu baka samu ba" yana kai nan yai waje yana sake cewa "Amatu karki damu in Allah ya yarda zaki cika burinki zaki zama soja wata rana" ita dai Amatu shiru tayi tana jiran hukuncin da Bashir zai yanke mata saidai tana fatan ya amince idan kuma yace a'a dole zatai hakuri tabi son ransa.

"AMATULLAHI" taji Bashir ya fad'a wanda ya katse mata tunani muryarta na d'an rawa tace "na'am Abba" cigaba Bashir yayi "naji abinda kike so ki zama soja indai shine burinki zanyi kokarin cika miki sannan na biki da fatan alkairi da sa albarka a duk inda kika tsinci kanki ki zama mai juriya da tawakkali ki yarda da kaddara mai kyau ko akasin ta kinji" kai ta d'aga "eh Abba nagode Allah ya saka maka da alkairi ya kara arziki" "Amin yace yana mikewa shima ya fita Binta da bakinta ya'ki rufuwa tace "tofa maman masu gida ke kuma abinda kike sha'awar yi kenan soja ikon Allah babu abinda nake tsoro a rayuwa ta kamar naga sojaπŸ˜‚ ashe wata rana zan bud'e ido naga 'yata jini na da kayan sojoji" murmushi Safiyyah tayi tana cewa "ai aunty haka al'amarin yake sai godiya kin gani dai ga Amatullahin ki tace soja take so masha Allah" huuuuuuh sauke ajiyar zuciya Binta tai tana mi'kewa tace "kinga kar zuwa miyattin nan ya shiririce min bari na tashi" katse ta Safiyyah tayi "ai aunty na ta kaina dakin barshi idan naje zance kinzo kina ma gaishe dasu" kaita girgiza "a'a barni Safiyyah dole naje mu gaisa da mahaifanki sun iya bada tarbiyyah tsakanin mu dasu sai son barka irin ahlinku ake nema a had'a jini dasu" murmushin jin dad'i Safiyyah tayi na yabon da Binta kewa mahaifanta tace "shikenan aunty mu gode sai kin dawo ni kuma Amatu tashi ki raka ni yadi gidan 'kawata" to tace tana mi'kewa Nabilah data dauko jaka tace "nima dai momy binku zanyi" hararar ta Maryam tai "baki isa ki rusa min tafiya ba tun shekaran jiya nake bin yarinyar nan ta raka ni na kar'bo dinkuna na tace sai yau kuma dan rainin hankali kice wani bazaki jeba aiko baki isa ba" had'e rai Nabilah "ina ce 'kafa tace bata mutum ba kuma nace na fasa rakiyar ko dole ne"? Kai Maryam ta jinjina tana cewa "mom kina jinta tanai min raahin kunya ko"? Cikin son raba fad'an tace "kinga Nabilah ba'a haka kin manta kome kikacewa Maryam kina so tanai miki idan har baki raka ta ba nan gaba kikaga wani abu a gurinta kina so ko kice ta baki kaza ko tayi miki kaza ni da kaina zan hana ta domin ba kece kika gina ta ba" kwa'be fuskarta Nabilah tayi "ni mom ke nake son bi" "na sani Nabilah kiyi hakuri ki raka ta meye zan taho miki dashi nasan yanzu tayo sarin kaya" Nabilah na kumbura fuska tace "takalmi da jaka sai mayafi shi nake so" "ok karki damu zan sayo miki tashi kuje ki rakata" badan ranta yaso ba tana jujjuya kai suka fita Maryam na balbale ta da masifa "wallahi Nabilah kina bani mamaki wai tsabar wulakanci in kina son abu a gurina kiyi ta min ladabin kura ga mai akuya amma babu komai bari Abbanmu ya dawo zan hada ki dashi" ita dai Nabilah shiru tai tana bin bayanta har suka fita harabar gida ta jirata taje ta dauko motar tana shawo kwana da ita sannan ta tsaya bud'e kofa Nabilah tayi ta shiga suka wuce.

A zaune Malam Habu yake a cikin d'akinsa ya zuba wani uban tagumi mai ban tausayi yayi zurfi cikin tunanin rayuwarsu ta baya tun daga tasawarsu har zuwa yanxu da yake shan wannan ba'kar wahala da quncin rayuwa baisan hawaye yana ta zuba a idonsa ba ko motsi baiyi tsabar nisan dayai da duniyar mutane ya fad'a duniyar tunani da tuna baya yadda rayuwarsu ta kasance kifa kai yai yana rufe ido kawai ya soma kuka sosai kamar qaramin yaro saboda tuno mahaifansu kawai ya zurfafa da tunanin da.

TUNA BAYAπŸ€”.
AYYA ALLAH SARKI MALAM HABUπŸ˜£πŸ˜žπŸ˜”πŸ˜’.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘😘😘

Sai mun sake haduwa idan Allah ya kaimu gobe darai da lafiya zakuji asalin tushen tarihin labarin suπŸ€”.
Reader's baku tambaye niba shin ya akai malam Habu ya talauce πŸ˜”?
Meye asalinsuπŸ™ƒ?
Wanne kalar 'kalubale ya fuskanta a baya😭?
Me ya jawo silar tauyar arzikin sa?

Domin samun amsoshin wadannan tambayoyin ku kasance tare daniπŸ‘‡.

+2348160983083
YUSRAH MUSA ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTYπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ.

We will meet again.
πŸŽΉπŸŽΊπŸŽ·πŸ’ƒπŸ’ƒπŸŽΆπŸŽ΅πŸŽ» Ranar kuce masoya maza kada kuyi sanya muyi rausaya 'yan uwa mu taho da baya baya mune muke shagali 😘 ranar mu tayi haske πŸŒƒ.

TYPING πŸ“² TUE, MAR 5 /24 8:10AM🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈.

πŸ’ŽME KAMAR SARKI πŸ’Ž


ANNURI WRITER'S ASSOCIATION πŸ’« HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY.


Story and written by
πŸ“šβœοΈMrs al'ameen Ahmad ce 😘.

Tnk u masoya godiya sosai sosai godiyaπŸ’–πŸ’•.

Always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your life 🌌 always 🌹.

Be good be helpful everybody will like u to be a happy child like my daughter Fatima Ilham πŸ‘Œ then people will like u.

Ayi hakuri idan an samu typing error matsalar keyboard ne.

πŸ€”Think before you do 🚨


15~AL-KAHHARU
The subduer
16~AL-WAHHAB
The bestover.

8~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Hamidina.

πŸ“šβœοΈYUSRAHMSπŸ’žπŸŒΉπŸ’ƒπŸ‘Œ.

πŸŒ„ REMEMBER ND STRUGGLE πŸŒ„
Episode 15&16
Asalin su duka 'yan wani 'karamin 'kauye ne wanda ya shahara da mutane ba'ki 'yan garin d'ai d'ai ne mahaifin malam Habu ya kasance a wannan garin matan sa uku Salamatu itace uwar gida danta daya Sabi'u sai 'yar tsakiya Ramatu ita ce mai yara biyu Ilyah da 'kanwarsa Lami sai kuma amarya Kulu wato Hauwa amma ta rasu d'anta daya Habubakar suna wata kalar rayuwa a hagunce wacce babu girmamawa ga wanda ka fi hakan kuma ya samo asali ne a wurin 'yar tsakiya Ramatu sam bata da kirki kuma bata da kara batasan meye mutunci ba Baffa mijin su kullum yana nusar da ita yayi yayi ta gane amma ta'ki ta kauda kai.

Zaune suke a tsakar gida kowa na harkar gaban shi wata yarinya ta shigo dauke da farantin talla a kanta tana kuka wiwi kamar ranta zai fita da gudu Ramatu ta fito daga d'aki tana cewa "ke Lami me akai miki kike kuka keda waye wanne d'an iskan ne la'ananne fad'a min yanzu nan naje gidan uwarsa na tsige mata gashin albarka tassss".

Har lokacin kuka Lami keyi ta kasa magana "ki fad'a min uban me akai miki ko shashancin naki ne ya mitsa dama yau naga ba'a son ranki kika fita tallar nan ba".

Kai Lami ta girgiza tana cewa "a'a Innah ba haka bane yaran gidan su Abu ne suke ce wai banyi karatu ba ni jahila ce jaka dakikiya bansan komai ba sai daukar kaya kamar 'yar dako".

Cikin masifa Ramatu tace "kuturun uban can lallai yaran nan akwai matsiyata ba kece jahila ubanninsu ne kwashashshu masu kai duk 'kwar'kwata".

Share hawaye Lami tayi tana cewa "dan Allah Innah na gaji da wannan gorin da ake min ki taimaka ki barni na ri'ka zuwa makaranta ko sau biyu ne a sati".

Zaro ido waje Ramatu tai kamar an fad'a mata abu mai muni har tana make Lamin cikin fad'a tace "uban karatu zaki kinsan Allah Lami indai ina raye bakiyi makarantar boko ba zaki 'kari maitarki ki barni domin tallar da kike yafi min da ubanki zan saya miki kayan d'akin? Dama hakan ne yasa ki dawowa gida da kuka tashi ki koma ko kija abinda zanyi miki tsinannan dukan da sai kin kasa tashi".

Mi'kewa Lami tai cikin ladabi ta sake daukar farantin ta fita Allah ya d'igawa yarinyar hakuri na kwatance kome za'ai mata bata fushi bata nuna gajiyawa.

Daidai zata fita Baffa ya shawo kwanar gida gida suka had'u a zaure ganinsa yasa da sauri ta goge sauran hawayen fuskarta tana cewa "sannu Baffa kawo tabarmar na kai maka" murmushi ya mata yana matukar kaunar yarinyar domin tana da cikakken hankali tun kafin ta mallaki hankalin kanta sake kallon ta yai karo na biyu kafin yace.

"A'a jeki tallar ki kinji zan 'karasa Allah ya miki albarka" "Amin Baffa ta fad'a tana juyawa ta fita shi kuma ya shiga cikin gidan ko bari ya karasa sallama Ramatu batai ba ta soma babbaka fad'a "malam yanzu haka rayuwa take wai 'yan iskan yaran nan gidan can harda tare Lami a waje suna ce mata jahila uban wa aka haifa da sani dama jiran ka nake ka shigo na dauki mayafina naje gidan saina yiwa Jummai tass zagi na tsamar nama domin banga dalilin da 'ya'yan ta zasu hana tawa zaman lafiya".

Ganin ta yayimo gyale daga jikin igiya tana shirin fita Baffa ya katseta Ramatu ina zaki je babu neman izini na" bata saurara ba tace "yo malam ai kaji inda nace zanje indai ba son maimaita magana ba dole na 'kwatawa 'yata yanci cikin 'kawayen ta domin ni ban haifi jahila ba".

"Ban baki izinin fita ba Ramatu ki dawo ai basuyi karya abinda suka fad'a ina jin lokacin da suke fad'an har mutane na cewa kaji gorin da akewa 'yarka tsabar kunya na kasa magana ji nayi kamar nayi nutso cikin 'kasa".

Tabe baki Ramatu tai "yo malam ai ka nutse a cikin 'kasar hakan ma da kyau nikam zuwa zanyi naja musu kunne akan 'yata bazan dauka ba" zata fita ya kuma dakatar da ita da cewa "Ramatu kada kije gidan mutanen nan kiyi musu wani abu Allah ya la'anci mai tashin fitana kibi a sannu idan kinsan farkon sa baki san karshen

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login